Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Asirin Kafin Gida

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum Dan Allah Ina da tambaya mene ne hukuncin/halascin kafe Gida (kamar mutum ya gina sabon Gida se ace wai ya kafe gidan saboda ɓarayi, duk in sun shigo da niyyar yin sata zasu kafe har se anzo an gansu), shin yin Hakan ya halasta ??

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikumus salam wa rahmatulLahi wa barakatuhu.

Abubuwa irin waɗannan hukuncinsu yana danganta ne da abinda akayi awajen. Misali : idan wata addu'a ce akayi awajen, ko aka tofa wasu surori ko ayoyi daga littafin Allah, ko wasu sunaye daga sunayen Allah, to wannan babu komai.

Amma idan wasu abubuwa ne na tsafi ko sihiri ko bokanci akayi awajen ko ta hanyar hidimtar da wasu shaiɗanun aljanu awajen, to wannan haramun ne Musulmi ya aikata, saboda haramcin aikata sihiri da tsafi da chanfi.

Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam Ya ce : "Ba ya tare damu duk wanda ke yin sihiri, ko kuma ya sanya aka aikata masa sihiri".

Kuma hidimtar da aljanu shima haramun ne saboda ayar cikin suratul jinn inda Allah ya ce : "KUMA CEWA WASU MAZAJE DAGA CIKIN 'YAN ADAM SUNA NEMAN MAFAKA AWAJEN WASU MAZAJE" DAGA CIKIN ALJANU, YIN HAKAN SAI SUKE QARA MUSU TSAURIN KAI ('BACEWA DAGA HANYAR ALLAH).

WALLAHU A'ALAM.

DAGA ZAUREN FIQHU 07064213990

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance damu cikin wannan group domin Fadakarwa...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam 

Post a Comment

0 Comments