ADDU'AR NEMAN BUƊI A WAJEN ALLAH
𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaikum malam ni ne abubuwa suka dameni na rayuwa to inasan a taimakamin da addu'o'in da zandinga yi na yau da kullum harkokin sana'ata babu chigaba sama da shekara goma sha sannan dana fara babu chiniki a haka har kayan da chinikin su lalache bansamu na sayo waniba saida kamekame. Allah ya karama malam lfy da ilmi mai albarka amin.
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa alaikumus salam wa rahmatulLahi wa barakatuhu.
Daga cikin manyan zikirai da addu'o'in da mutum
zai yawaita yinsu don neman buɗi aharkar
kasuwanci akwai yawaita istigfari. Domin yazo acikin wani ingantaccen hadisi
wanda Imam Abu Dawud ya riwaito ta hanyar Sayyiduna Abdullahi bn Abbas
(radhiyalLahu anhuma) ya ce Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam Ya ce :
"Wanda ya lazimci istighfari Allah zai sanya masa mafita daga kowanne
Qunci, da kuma yayewar kowanne bakin ciki, kuma zai azurtashi ta inda duk ba ya
tsammani".
Don haka idan zaka iya, ka rika yinsa daruruwa ko
dubunnai a kowacce rana. In shaAllahu zaka ga yayewar damuwarka, kuma arziki
zai yawaita a hannunka. Hakanan albarka zata yawaita acikin iyalanka da
harkokinka. Kamar yadda Annabi Nuhu yake yiwa mutanensa bishara da cewa: NACE
MUSU "KU NEMI GAFARAR UBANGIJINKU HAKIKA SHI MAI GAFARA NE. ZAI SAUKAR
MUKU DA RUWA MAI YAWA DAGA SAMA. KUMA ZAI QAREKU DA YAWAITAR DUKIYA DA 'YA'YA
KUMA ZAI SANYA MUKU (ALBARKA) A GONAKINKU DA QORAMUNKU.. ".
Malamai daga magabata na kwarai irinsu Imam
Hasanul Basariy (rahimahul Lah) suna kafa hujjah da wannan ayar bisa cewa
lallai yawaita istigfari hanya ce ta samun 'ya'ya da dukiya masu albarka.
Sannan idan bashi ne ya dameka, ga wata addu'ar
itama dai daga Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam kamar yadda Imamut
Tirmidhiy ya riwaitota akan lambar hadisi na 3,563 :
اللّهُمَّ اكْفِنِي بِحَلالِكَ
عَنْ حَرَامِكَ، وَأَغْنِنِي بِفَضْلِكِ عَمَّنْ سِوَاكَ.
Ya Allah! Ka wadatar da ni da abin da Ka halatta
barin abin da Ka haramta, kuma Ka wadatar da ni da falalarka ga barin waninka.
Ka yawaita yinta acikin sallolinka na dare, acikin
sujadunka, da sauran wuraren da ake karfafa zaton samun karɓuwar addu'a.
Allah ya yaye maka damuwarka, ya riskar maka da
bukatunka Ameen.
WALLAHU A'ALAM.
DAGA ZAUREN FIQHU 07064213990
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku
kasance damu cikin wannan group domin Fadakarwa...
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.