HUKUNCIN MACEN DA TA MUSLUNTA ALHALI TA NA ƘARƘASHIN IGIYAR AUREN MIJINTA KAFIRI
𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Mace ce kafira suna tare da Mijinta kafiri sai ita matar ta muslunta to ya halatta musulmi ya aureta ko kuma dole sai in wancan mijin na ta kafiri ya saketa tukuna?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Idan ya kasance mace ta muslunta alhali ta na ƙarƙashin igiyar auren mijinta kafiri, to dukkan
Malamai sunyi ittifaki akan cewa daga lokacin da ta shiga addinin muslunci za
ta yanke dukkan wata alaƙa da ta shafi jima'i ko jin daɗi a tsakaninta
da shi, dan haka ba ya halatta a gareta ta sake bashi kanta ya sadu da ita.
Malamai sun kafa hujja ne da faɗin Aʟʟαн(ﷻ) da Ya ke cewa:
يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا إِذَا جَاءَكُمُ الْمُؤْمِنَاتُ
مُهَاجِرَاتٍ فَامْتَحِنُوهُنَّ ۖ اللَّهُ أَعْلَمُ بِإِيمَانِهِنَّ ۖ فَإِنْ عَلِمْتُمُوهُنَّ
مُؤْمِنَاتٍ فَلَا تَرْجِعُوهُنَّ إِلَى الْكُفَّارِ ۖ لَا هُنَّ حِلٌّ لَّهُمْ وَلَا
هُمْ يَحِلُّونَ لَهُنَّ ۖ وَآتُوهُم مَّا أَنفَقُوا ۚ وَلَا جُنَاحَ عَلَيْكُمْ أَن
تَنكِحُوهُنَّ إِذَا آتَيْتُمُوهُنَّ أُجُورَهُنَّ ۚ وَلَا تُمْسِكُوا بِعِصَمِ الْكَوَافِرِ
وَاسْأَلُوا مَا أَنفَقْتُمْ وَلْيَسْأَلُوا مَا أَنفَقُوا ۚ ذَٰلِكُمْ حُكْمُ اللَّهِ
ۖ يَحْكُمُ بَيْنَكُمْ ۚ وَاللَّهُ عَلِيمٌ حَكِيمٌ
Yã kũ waɗanda suka yi
ĩmãni! Idan mãtã mũminai suka zo muku, sunã mãsu hijira, to, ku jarraba su.
Allah Shĩ ne mafi sani ga ĩmãninsu. To, idan kun san sũ mũminai ne, kada ku
mayar da su zuwa ga kãfirai. Sũ mãtan bã su halatta ga aurensu, sũ kuma kãfiran
bã su halatta ga auren mãtan. Ku bã su abin da suka ɓatar na dũkiya. Kuma bãbu laifi a kanku ga ku aure su
idan kun bã su sadãkõkinsu. Kuma kada ku riƙe auren mãtã kãfirai, kuma ku
tambayi abin da kuka ɓatar daga
dũkiya, su kuma kãfirai su tambayi abin da suka ɓatar na dũkiya. Wannan hukuncin Allah ne Yanã hukunci a
tsakãninku. kuma Allah, Masani ne, Mai hikima (Suratul Mumtahana Aya ta 10).
Dan haka idan ya kasance dama mijin ya riga ya taɓa saduwa da ita, to zataci gaba ne da zama a haka har
zuwa lokacin da za ta ƙare iddarta, idan anyi sa'a Aʟʟαн(ﷻ) ya yiwa mijin TAUFIƘI shima ya shiga Musluncin kafin matar ta ƙare iddar ta, to shikenan aurensu yana nan, kawai
za su ci gaba da zamansu ne a matsayin Mata da Miji kamar yadda Mαиzoи Aʟʟαн(ﷺ) Ya taɓa mayar da auren wasu daga cikin Sahabbai mata Muhajirai
waɗanda daga baya mazajensu suka shiga Muslunci kafin su
kare iddarsu, amma idan har matar ta ƙare idda shi kuma mijin yana nan a kafirinsa bai Musluntaba, to shikenan
yanzu kam ta yi masa nisa, idan kuma dama bai taɓa saduwa da ita ba to shikenan nan take aurensu ya ɓaci. Dan haka babu wata idda da za ta yi kawai ya halatta
a gareta ta auri Musulmi duk wanda takeso.
шαʟʟαнυ-тα'αʟα α'αʟαмυ
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku
kasance damu cikin wannan group domin Fadakarwa...
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.