Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Hada Guiwa Wurin Layya

HAƊA GWIWA WURIN LAYYA:

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

As-Salaam Alaikum Wa Rahmatul Laah. Hadisin Abu-Ayyub Al-Ansaariy (Radiyal Laahu Anhu) wanda An-Nasaa’iy da At-Tirmiziy da Ibn Maajah suka riwaito shi kuma Al-Albaaniy ya inganta shi cewa: A zamanin Annabi (Sallal Laahu Alalihi Wa Alihi Wa Sallam) mutum ɗaya yana yin layya da rago guda ɗaya ga kansa da iyalin gidansa. Da kuma wani audio clip na As-Shaikh Albaaniy Zaria (Rahimahul Laah) wanda yanzu yake yawo a cikin social media cewa: ‘Idan mutum ya ƙuduri aniyyar yanka wata dabba don yin layya shi da iyalinsa, to hukuncin layya ya hau kansa shi da iyalinsa. Tun daga farkon watan nan ba za su yi aski ko yanke ƙumba ba. Tambayata a nan ita ce: Hukuncin ya keɓanci rago ɗaya ko akuya ɗaya ce, ban da shanu ko raƙuma? Ko mutane biyu za su iya yin layyar da rago ko akuya ɗaya?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah Wa Barakaatuh.

Hadisin Sahabi Abu-Ayyuub shi ne wanda Al-Imaam At-Tirmiziy (1587) ya riwaito da isnadinsa cewa: Ataa’u Bn Yasaar ya tambayi Abu-Ayyuub Al-Ansaariy (Radiyal Laahu Anhu) ya ce: Yaya ya kasance ake yin layya a zamanin Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam)? Sai ya ce:

كَانَ الرَّجُلُ يُضَحِّى بِالشَّاةِ عَنْهُ وَعَنْ أَهْلِ بَيْتِهِ فَيَأْكُلُونَ وَيُطْعِمُونَ حَتَّى تَبَاهَى النَّاسُ فَصَارَتْ كَمَا تَرَى

Maigida ya kasance yana yin layya da rago ko tunkiya guda ga kansa da iyalin gidansa, sai su ci kuma su ciyar da waɗansu, har ya kai mutane suna yin alfahari. Sai abin ya koma kamar yadda kake gani.

At-Tirmiziy ya ce: ‘Wannan hadisin kyakkyawa ne ingantacce… Waɗansu daga cikin malamai sun yi aiki da wannan hadisin, shi ne maganar Ahmad da Is’haaq… Waɗansu malaman kuma cewa suka yi: Rago guda ba ya isuwa sai dai ga mutum guda kaɗai. Wannan kuma ita ce maganar Abdullaah Bn Al-Mubaarak da waninsa daga cikin malamai masana ilimi.’

Daga wannan hadisi sahihi ana iya fahimtar cewa:

1. Rago guda ɗaya ya ishi maigida da iyalinsa a wurin layya. Haka ma raƙumi ko sa guda, idan akwai wadata.

2. In akwai wadata mutum guda na iya yin layya da raguna biyu ko sama da haka, kamar yadda yake iya yanka wa kowane daga cikin iyalansa ragonsa na musamman.

3. Mutane biyu ko fiye ba su iya yin layya da rago guda ɗaya, tun da ga shi har wasu malamai ma suna ganin rago ɗayan ba ya isuwa sai dai ga mutum guda kaɗai.

Sannan kuma Al-Imaam Muslim (1318) ya riwaito daga Sahabi Jaabir Bn Abdillaah (Radiyal Laahu Anhumaa) ya ce:

« أَمَرَنَا رَسُولُ اللَّهِ - صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَآلِهِ وَسَلَّمَ - أَنْ نَشْتَرِكَ فِى الإِبِلِ وَالْبَقَرِ كُلُّ سَبْعَةٍ مِنَّا فِى بَدَنَةٍ »

Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya umurce mu da mu haɗa mutane bakwai a cikin raƙumi guda ko saniya guda.

Wannan ya nuna:

1. Kodayake wannan hadisi a kan hadaya ne ya zo amma hukuncin ya shafi layya ma, tun da malamai sun yarda cewa babu bambancin hukunci game da dabbobin da ake yankawa a cikinsu.

2. Mutane bakwai - tare da iyalansu - suna iya haɗa gwiwa a wurin layya da bijimin sa ko raƙumi guda ɗaya, ta yadda kowannensu zai tashi da subu’in (1/7) naman.

3. Mutane ƙasa da bakwai - kamar biyar ko uku - suna iya haɗuwa su ma a cikin layya da raƙumi guda ɗaya ko sa guda ɗaya, tun da dai a asali ya halatta mutum guda mai hali ya yi layya da sa ko raƙumi guda ɗaya.

Haka kuma hadisin Ummul-Mu’mineen Ummu-Salamah (Radiyal Laahu Anhaa) da Al-Imaam Muslim (1977) ya riwaito cewa Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce:

« مَنْ كَانَ لَهُ ذِبْحٌ يَذْبَحُهُ فَإِذَا أُهِلَّ هِلاَلُ ذِى الْحِجَّةِ فَلاَ يَأْخُذَنَّ مِنْ شَعْرِهِ وَلاَ مِنْ أَظْفَارِهِ شَيْئًا حَتَّى يُضَحِّىَ »

Duk wanda yake da abin yankawa da zai yanka a lokacin layya, to idan jinjirin watan Zul-Hijjah ya tsaya kar ya yanke wani abu na gashin jikinsa ko ƙumbarsa har sai ya yi layyar.

Daga wannan hadisin da makamantansa ne malamai suka gano cewa:

1. Wajibi ne ga duk wanda ke son yin layya ya rabu da yanke wani abu da gashinsa ko ƙumbarsa tun daga ɗaya ga watan Zul-Hijjah.

2. Idan mai layya bai ɗaura niyyar yin layyar ba sai a bayan watan ya shiga da kwanaki, to hukuncin barin aski da yanke ƙumba gare shi yana farawa ne daga lokacin da ya ɗaura niyyar.

3. Idan ƙumbarsa ta karye ko kuma wani gashi ya tsiro masa a cikin ido wanda yake cutuwa da shi, to ya halatta ya kawar da su, domin wannan a babin gusar da cuta ne.

4. Idan wani mutum ya wuce iyakar shari’a, ya je ya yanke waɗannan abubuwan da aka hana, to ya yi zunubi kuma babu wata fidiya da zai yi, kuma wannan bai shafi sahihancin layyarsa ba, idan dai an cika sharuɗɗanta.

5. Idan maigida zai shigar da iyalinsa a cikin layyarsa, to ko dokar hana yanke gashi da ƙumba ya shafe su su ma? Malamai sun sha bamban: Waɗansu sun ce: E, domin su ma suna da hukuncin masu layyar ce. Waɗansu kuma sun ce: A’a, domin hadisin bai ambace su ba.

Wal Laahu A’lam.

Sheikh Tambayad Abdullaah Assalafiy

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance damu cikin wannan group domin Fadakarwa...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam 

Post a Comment

0 Comments