Ticker

6/recent/ticker-posts

Hausa Da Hausawa a Duniyar Intanet

Gabatarwa

X.1 Matashiya

Wannan littafin ya ɗauki intanet a matsayin “duniya” mai zaman kanta. A ciki (duniyar) akan tarar da duk waɗansu al’amura na yau da kullum suna gudana tamkar yadda suke kasancewa a duniyar zahiri. A duniyar intanet akan samɗaiɗaikun mutane (akawun-akawun da kafafen intanet na ɗaiɗaikun mutane). Akan kuma sami unguwanni (zauruka da kafafen intanet na tarayya). Ana kuma samun garuruwa da ƙasashe. Alamuran da suke gudana a kowane daga cikin ɓangarorin sun kasance tamkar a duniya ta daban wadda ta kai ta dogara da kanta. A duniyar intanet, akan:

a. samu cinikayya da kasuwanci suna gudana tamkar yadda ake yi a duniyar zahiri ta mutane (kasuwanni da shaguna da dillalai da makamantansu);

b. samu zamantakewa da rayuwa mai kama da mafarki. Misali, ana iya samun tarayya tsakanin al’ummomi daga ɓangarorin duniya waɗanda ba su taɓa kallon juna a zahiri ba;

c. samu makarantu da azuzuwa har da ɗakunan karatu

d. samu gine-gine da wurare da sauran abubuwan amfani masu matsayi kwatankwacin abubuwan amfanin bil’adama ta rayuwar zahiri.

Wato dai, al’amuran suna kasancewa cikin siga da salo makamanciyar yadda suke a duniyar zahiri. Akan kuma samu cuɗanya tsakanin al’amuran da suke wanzuwa a duniyoyin guda biyu. Daga duniyar zahiri ne ake samun damar cuɗanya da duniyar intanet ta hanyar na’urori. Wasu lokutan akan kai ga dawo da gudanarwar cuɗanyar zuwa duniyar zahiri. Misali, soyayyar duniyar intanet ta Isa Suleiman Fanshekara (ɗan Kano a Nijeriya) da Ba’amurkiya Janine Sanchez ta zama gaskiya. Don ƙarin bayani a duba BBC, (2020 para. 1)2 ko Abubakar, (2020 para. 1).

Babban al’amari kuma shi ne, akan rayu kuma a mutu a duniyar intanet. A rahoton da BBC ta fitar bayan bincike kan Fesbuk a shekarar 2016, ta bayyana kafar Fesbuk a matsayin wata babbar maƙabarta. Rahoton yana da taken: “Yadda Facebook ya zama makekiyar maƙabarta. An tabbatar da cewa, shekaru takwas (8) kacal bayan buɗe Fesbuk, an samu masu amfani da kafar da suka mutu kimanin miliyan talatin (30,000,000). A bisa wannan, ana iya hasashen cewa ya zuwa yau adadin ya ninninka sau tarin yawa. Tun a shekarar 2012, adadin masu amfani da Fesbuk da suke mutuwa a kowace rana ya kai dubu takwas (8,000) (BBC, 2016 para. 1). Hakan yana nuni da cewa, adadin zai ci gaba da hauhawa yayin da ake samun ƙaruwar masu amfani da kafar.

Haƙiƙa akwai buƙatar a samu jakadu da wakilan Hausa da Hausawa a duniyar intanet, tamkar yadda ake da su a duniyar zahiri. Wannan littafi sharar fage ne da zai buɗe hanyar samar da wakilcin al’adun Hausa a duniyar ta intanet.

X.2 Madogaran Littafin

Wannan littafi ya taƙaita ne a kan aladun Hausawa da intanet. Kadadarsa ba ta wuce duniyar intanet ba. Ko a duniyar intanet ɗin ba ko’ina aka duba ba. Littafin ya taƙaita a kafafen intanet na Hausa kawai. Dangane da sauran kafafen intanet, an yi ƙoƙarin duba aladun Hausawa ne kawai daga cikinsu tare da nazartar irin tasirin da suka yi a kan aladun Bahaushe. Maana ke nan, an bibiyi kafafen domin ganin abin da suke faɗa ko suke nunawa dangane da al’adun Hausawa. An cim ma nasarar hakan ta hanyar:

i. Nazartar rubuce-rubucen;

ii. Nazartar hotuna;

iii. Nazartar bidiyoyi; da

iv. Nazartar alamomi.[1]

Ba a iyakance adadin kafafen intanet da aka dubo waɗannan ba. Dalili kuwa shi ne, ya zuwa yau (2020), akwai kafafen intanet a duniya da adadinsu ya haura biliyan ɗaya da miliyan ɗari bakwai da hamsin da ɗaya da dubu talatin da ɗaya da ɗari huɗu da arba’in da bakwai (1,751,031,447) (Internet Live Stats, 2020 para. 2). Zaɓen wasu tsiraru daga cikin kafafen intanet ɗin na iya sa a tsallake wasu muhimman abubuwa da suka dace a yi magana a kansu. Hakan zai faru idan fitilar nazari ba ta haska kafafen intanet da suke ɗauke da waɗannan bayanai ba. A ɓangaren tasiri kuwa, za a yi ƙoƙarin gano irin gurbin kafafen na intanet ga rayuwar Bahaushe, musamman aladunsa.

Dangane da waɗannan kafafen intanet na Hausa, an mayar da hankali ne a kan abin da ya shafi al’adu kawai. A cikin kafafen, za a yi ƙoƙarin zaƙulo aladun Hausawa da suka shafi:

i. Nazarin inda aka fito dangane da adanawa da yayata al’adun Hausawa a duniyar intanet;

ii. Nazarin matsayin da al’adun Hausawa suka tsinci kansu a yau cikin waɗannan kafafen intanet na Hausa;

iii. Nazarin matsaloli ko barazanar da al’adun Hausa suke fuskanta a duniyar intanet; da

iv. Nazarin hanyoyi ko matakai da za a iya inganta kafafen.

X.3 Babukan Littafin

Wannan littafin yana ƙunshe da babuka guda biyar. Babi na ɗaya ya kasance shimfiɗa ne. A ciki an waiwaici samuwa da bunƙasar intanet. Bugu da ƙari, babin ya yi bitar kalmar alada domin yin matashiya ga littafin. Bayan haka, babin ya dubi irin tasirin da intanet yake da shi a kan alummomi a duniya.

An gina babi na biyu a kan bunƙasar aladun Hausawa a duniyar intanet. Babin ya duba manyan kafafen intanet a duniya da suka karɓi harshen Hausa. Daga cikinsu har da Fesbuk. Bugu da ƙari, babin ya kalli ire-iren tasirin da intanet yake da shi ga Hausa da kuma Hausawa.

Babi na uku ya mayar da hankali a kan nazarin yaɗuwar al’adun Hausawa a kan intanet. A ciki an duba yadda al’adun Hausawa daban-daban suka yaɗu a kan intanet. Sukan bayyana yayin da aka tura neman da yake da alaƙa da su a cikin injunan nema na kan intanet.

A cikin babi na huɗu, an nazarci amfani da aibun intanet ga Hausa da Hausawa. Ya tabbata cewa, intanet ya zo da alfanu masu tarin yawa waɗanda Hausa da Hausawa za su iya cin gajiyarsu musamman yayin da suka bi hanyoyin da suka kamata. Daga cikin amfaninsa akwai ba da damar sada zumunta da haɓaka Hausa da yayata ta. Yana kuma taimakawa wajen adana al’adun Hausawan. Aibin kafafen intanet ga al’ummar Hausawa sun haɗa da ɓata tarbiyya da ɓata lokaci da samar da kafar damfara da makamantansu. A ɓangare ɗaya kuwa, intanet ya zo da ƙalubale daban-daban waɗanda dole sai an bi kyawawan matakai domin kauce musu.

Babi na biyar ya tattauna nasarorin da kafafen intanet na Hausa suka samu a yau. Wannan ya haɗa da ƙaruwar ƙarfin tasirinsu a duniya da fannonin rayuwa da suka mamaye, ciki har da kasuwanci da ilimi. A ɓangare ɗaya kuwa, babin ya kawo wasu ƙalubale da kafafen suke fuskanta. Sun haɗa da ƙarancin tallafi da goyon baya daga masana da mahukunta da kuma wasu matsaloli da suka shafi yanayi da zamantakewar ƙasar Hausa.

 “Tirƙashi! wannan Littafi mai suna Hausa Da Hausawa a Duniyar Intanet, babu shakka littafi ne kandami a sha a yi wanka, sannan kuma sabulun salo amfaninka dubu, jar kanwa shan ki magani ajiyar ki dabara.”

Assoc. Prof. Mu’azu Sa’adu Muhammad Kudan
Head of Department of Nigerian Languages & Linguistics
Sule Lamiɗo University Kafin Hausa, Jigawa State, Nigeria

*** 

“The book is well-researched, insightful, and highly relevant to contemporary discussions on digital cultural representation.”

Dr. Shuaibu Hassan,
Head of Department of African Languages and Cultures
Ahmadu Bello University, Zaria, Nigeria 

***

“The book excels in several areas. It is backed by extensive research, well-referenced with credible sources, and structured logically into clear chapters. The progression of ideas ensures readability and coherence.”

Prof. Musa Grema
Head of Department of Languages and Linguistics
Yobe State University, Nigeria

 

*** 

Abu-Ubaida Sani ya rubuta littattafai da maƙalu sama da 60 da aka wallafa a cikin gida Nijeriya da ƙasashen waje. Ya gabatar da kimanin maƙalu 20 a tarukan ƙara wa juna sani. Edita ne na mujallu daban-daban a ƙasashen da suka haɗa da Nijeriya da Amurka da Indiya da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa. Shi ne ya assasa babbar kafar intenet ta Hausar nan wato Amsoshi (www.amsoshi.com). A yanzu yana koyarwa a Sashen Harsuna da Al’adu da ke Jami’ar Tarayya Gusau. A dubawww.abu-ubaida.com.

 

 ***

Dr. Adamu Ago Saleh masanin ilimin harsunan Najeriya ne kuma ƙwararre a cikin harsunan Afirka, wanda ya ƙware a fannin harsuna da adabin Hausa. Yana jin harsunan Larabci da Ingilishi da Hausa kuma Bade. Ya yi wallafe-wallafe da dama. Ya yi aiki a matsayin babban mai ba da horo ga ayyukan USAID da DFID a matakin jiha da kuma ƙaramar hukuma, inda ya mai da hankali kan inganta ilimin koyarwa da samarwa da kuma fassara littattafai ga yaran da suke gudun hijira. Dr. Adamu, yana da aure da kuma ‘ya’ya.

Contact:

WhatsApp: +2348133529736
Email: abuubaidasani5@gmail.com

Hausa Da Hausawa a Duniyar Intanet

Post a Comment

0 Comments