Ticker

6/recent/ticker-posts

Damfara a Duniyar Intanet

Gabatarwa

Damfara hanya ce ta amfani da dabarun yaudara don kwaɗaitar da wani samun wani abin alfanu dangin kuɗi ko wani abu mai daraja, domin karɓar wani abu daga gare shi na dindindin. A ɓangare guda kuwa, intanet fasaha ce ta zamani wadda ta ƙunshi haɗakar tsauraran al’amura da suka haɗa da yaruka da na’urori da sabis waɗanda haɗuwarsu take samar da al’amari ko bagire da yake tattare da hadahada da fannoni tamkar waɗanda suke duniyar yau-da-kullum, ciki har da abubuwan da suka shafi sadarwa da makarantu da bankuna da kasuwanni da shaguna tare da sauran halittu kamar mutane da dabbobi da waninsu.

Samuwa da bunƙasar intanet a duniya ya buɗe sabon babin damfara, wato damfara a duniyar intanet. Damfarar kan intanet ta fi shafar waɗanda suke hawa intanet ta hanyar kafafen intanet ko na sada zumunta ko kuma manhajoji. A yau, akan dama da Hausawa da dama a duniyar intanet dangane da kasuwanci da sada zumunta da sauran abubuwan da suka shafi tura bayanai ko amfani da su a kan intanet. Hakan ya sa Hausawan suka shiga cikin jerin waɗanda suke fuskantar ƙalubalen damfara a kan intanet. Wannan ya sa ya zama dole a gudanar da binciken da zai faɗakar da Hausawa game da matakan kare kai daga faɗawa tarkon ‘yan damfarar kan intanet.

Littafin yana ɗauke da babuka guda shida (6). Babi na farko ya fara da bayani dangane da ma’anar damfara. Daga nan ya kawo tsokaci game da ma’ana tare da taƙaitaccen tarihin samuwa da bunƙasar intanet. Babi na biyu kuwa ya mayar da hankali ne a kan tattauna batutuwan da suka shafi neman kuɗi a kan intanet.” An fi mayar da hankali a kan nau’o’in kasuwanci da ƙwadagon kan intanet waɗanda suka shafi Hausawa. Babin ya bayyana cewa, masu gudanar da harkokin neman kuɗi a kan intanet sun fi fuskantar ƙalubalen damfara.

Babi na uku kuwa ya tattauna nau’o’in damfara ta kan intanet daban-daban. Fahimtar ciki da wajen waɗannan nau’o’in damfarar kan intanet wani muhimmin mataki ne na kare kai daga faɗawa tarkon ‘yan damfara. A babi na huɗu, an tattauna wasu misalan manyan damfarar kan intanet da aka yi wa Hausawa, waɗanda aka gudanar da su a cikin sigar kasuwanci. Hausawa masu yawa sun faɗa wannan tarkon damfara inda aka yaudare su da sunan kasuwanci. Nazartar wannan babi zai taimaka wa masu karatu, musamman Hausawa, wajen naƙaltar matakan tantance kasuwancin kan intanet na gaskiya da na bogi

Babi na biyar ya tattauna wasu fitattun misalan damfarar kan intanet da suka ritsa da Hausawa ta sigar kasuwancin kuɗin intanet (kirifto). An yaudari Hausawa masu yawa da wasu nau’o’in kirifto na damfara. Sun haɗa da Insknation da Telegram P2P da AI Mining da sauran makamantansu. Bayanan da suke cikin wannan babin za su taimaka wa makaranta musamman Hausawa wajen bambance aya da tsakuwa, tsakanin harkokin kirifto na gaskiya da na damfara.

Babi na shida ya kawo wasu muhamman dabarun kare kai daga faɗawa cikin tarkon ‘yan damfara a kan intanet. Dabarun sun haɗa da bayanai game da yadda ake gane saƙonnin damfara da kafafen intanet na bogi. Haka kuma, sun shafi bayani game da muhimman matakai da ya kamata mutum ya ɗauka domin kare akawun ɗinsa daga barazanar ‘yan damfara. Akawun ɗin yana iya kasancewa na kafafen intanet (websites da blogs) da manhajoji (applications) da kuma kafafen sada zumunta (social media).

Muna da yaƙinin cewa, wannan littafin zai yi matuƙar taimakawa wajen fahimtar damfarar kan intanet da nau’o’inta da ma matakan kare kai daga wannan annoba ta damfara a kan intanet.

Damfara a Duniyar Intanet


“A iya sanina, babu wani littafi da aka rubuta da Hausa da ya tsattsefe bayanai game da intanet da kuma ire-iren kwazazzaban da suke cikin duniyarsa kamar wannan.”

Dr. Abba Sagir Abubakar
Department of Nigerian Languages
Nasarawa State University, Keffi, Nigeria

*** 

“Damfara a Duniyar Intanet is a highly recommended work that fills a critical gap in Hausa-language literature on digital security.”

Dr. Adamu Ago Saleh
Department of African Languages and Cultures
Ahmadu Bello University Zaria, Nigeria

*** 

“… the book will open a new chapter in the aspect of Hausa cultural studies and as well serve the needs of both the academia and the business-oriented minds who surf the internet to make a living...”

Assoc. Prof. Musa Fadama Gummi
HOD, Department of Languages and Cultures
Federal University Gusau, Zamfara State, Nigeria

***

 

Abu-Ubaida Sani ya rubuta littattafai da maƙalu sama da 70 da aka wallafa a cikin gida Nijeriya da ƙasashen waje. Ya gabatar da kimanin maƙalu 20 a tarukan ƙara wa juna sani. Edita ne na mujallu daban-daban a ƙasashen da suka haɗa da Nijeriya da Amurka da Indiya da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa. Shi ne ya assasa babbar kafar intenet ta Hausar nan wato Amsoshi (www.amsoshi.com). A yanzu yana koyarwa a Sashen Harsuna da Al’adu da ke Jami’ar Tarayya Gusau. A dubawww.abu-ubaida.com.

***

Dr. Jibril Yusuf ya koyar na ɗan wani lokaci a Jami'ar Gwamnatin Tarayya ta Gusau. A yanzu haka malami ne a Sashen Harsunan Nijeriya da Kimiyyar Harshe na Jami'ar Jihar Kaduna. Ya wallafa maƙalu da dama a mujallun ilimi daban-daban wanda duniyar ilimi take amfana da su. Ya fi mayar da hankali a ɓangaren adabi da kuma ayyukan fassara.

***

Dr. Muhammad S. Abdullahi malamin harshen Hausa ne daga Sashen Koyar da Harsunan Najeriya, a Jami'ar Bayero da ke Kano. Yana zurfafa bincike a kan fannin harshe da fasahar zamani, musamman ta fannin Fassara da Tsarin Sauti. Yana gabatar da rubuce-rubuce da sauran nazarce-nazarce a harshen Hausa ta fuskar zamani da al'adun al'umma. A yanzu shi ne mataimakin darakta na Cibiyar Bincike a Harsunan Najeriya da Fassara da Fasahohin al'umma da ke Jami'ar Bayero a Kano. Yana da rubuce-rubuce da dama game da harshen Hausa a Soshiyal Midiya da sauran kafafe.

Contact:

WhatsApp: +2348133529736
Email: abuubaidasani5@gmail.com

Damfara a Duniyar Intanet

Damfara a Duniyar Intanet

Post a Comment

0 Comments