𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaikum Malam Ya harkoki To Allah yabada lada. Malam tambaya nake Dan Allah Kamar mutum Zai yi sallah da matar sa Agida To za ta tsaya akusa da shi ne ko kuma abayanshi za ta tsaya? Allah yasakawa malam da alkhairi
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Walaikumus salamam
Warahmatalahi wabarkatahu.
Mace za ta tsaya bayan
namiji idan ya limance ta. Hakanan idan za ta yi sallah da maza za ta tsaya a
bayan sahu ne. Idan mata za su yi sallar jam’i, to a sunnah limamiyarsu za ta tsaya
a tsakiyarsu ne, ba za ta shiga gabansu ba. Idan mata za su yi sallar jam’i
tare da maza, to a sunnah za su yi baya da maza, su yi sahu irin na maza.
An karɓo daga Abu Hurairata – Allah ya yarda da shi – ya ce,
Manzon Allah ( ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ) ya
ce, “Mafi alherin sahun mata na qarshe, mafi sharrinsa na farkonsa” [Ibnu Majah
ne ya rawaitoshi].
WALLAHU A'ALAM
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance damu cikin wannan group domin Fadakarwa...
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.