Citation: Bakura, A.R. & Sani, A-U. (2024). Gurbin Makaɗa Sa’idu Faru a Sikelin Manazartan Ƙarni Na 21. Four Decades of Hausa Royal Songs: Proceedings from the International Conference on the Life and Songs of Makaɗa Sa'idu Faru, 3(3), 37-49. www.doi.org/10.36349/tjllc.2024.v03i03.005.
GURBIN MAKAƊA SA’IDU FARU A SIKELIN MANAZARTAN ƘARNI NA 21
Daga
Dr.
Adamu Rabi’u Bakura
Department
of Languages and Cultures
Federal
University Gusau, Zamfara State, Nigeria
Email:
arbakura62@gmail.com
Phone:
08064893336
Da
Abu-Ubaida
SANI
Department
of Languages and Cultures,
Federal
University,
Gusau, Zamfara
State, Nigeria
Email: abu-ubaidallah@fugusau.edu.ng |
abuubaidasani5@gmail.com
Site:
www.abu-ubaida.com |
www.amsoshi.com
WhatsApp:
+2348133529736
Tsakure
Masana suna la’akari da waɗansu alƙaluma yayin ayyana makaɗan Hausa a ƙarƙashin wani rukuni na musamman daga cikin
tarin rukunonin makaɗa da ake da su a
farfajiyar adabi da al’adun Hausawa. Waƙoƙin fada na daga cikin
shahararrun rukunonin waƙoƙin baka. Wani abin lura shi
ne, akan samu makaɗan da ke ƙarƙashin wannan rukuni da suke sauya sheƙa ko su kasance jemagu sakamakon tasirin
zamani ko waɗansu dalilai masu alaƙa da tattalin arziki ko waninsa. Binciken
nan yana da manufar bitar rayuwa da waƙoƙin Alhaji Sa’idu
Faru domin ganin ko ya sauya sheƙa ko kuma ya kasance
makaɗin sarauta kaifi ɗaya na tsawon zamanin kiɗansa? An yi amfani
da dabarun ƙalailaice waƙoƙin makaɗin da kuma yin
hira da masana a wannan fanni a matsayin hanyoyin tattara bayanai. Sakamakon binciken
ya tabbatar da cewa, Sa’idu Faru ya tabbata makaɗin sarauta na yankan
shakku, domin kuwa dukkannin waƙoƙinsa ba su fita daga da’irar sarauta
da masarauta ba. Daga ƙarshe binciken ya ba
da shawarwari da suka haɗa da nuna dacewar tattarawa
da kundace waƙoƙin wannan shahararren makaɗi domin gudun salwantar su.
Fitilun Kalmomi: Kiɗa, Waƙa, Waƙoƙin Fada, Waƙoƙin Sarauta, Makaɗan Fada, Makaɗan Sarauta
Allah ya arzurta mawaƙan Hausa da ɗimbin hikima da basira tare da fasahar sarrafa harshen
Hausa wajen ƙaga waƙoƙi. Wannan ne ya sa sukan rera waƙoƙin da suka danganci fannonin rayuwar ɗan’adam daban-daban.
A sakamakon haka ne masana da manazarta adabin Hausa suka karkasa makaɗan zuwa azuzuwa ta
la’akari da rukunonin al’ummar da makaɗan ke yi wa kiɗa da waƙa. Masana kamar Bello (1982) da Yahaya (1983/85) da Mashi
(1986) da Gusau (1996) sun raba mawaƙan zuwa rukuni-rukuni
gwargwadon fahimtarsu, ta la’akari da abubuwa kamar haka:
(i)
Muhallin waƙoƙinsu
(ii) Kayan
kiɗansu
(iii) Jigogin
waƙoƙinsu
Hasali ma kowane rukunin da makaɗan ke yi wa kiɗa da waƙa akwai kayan kiɗan da suka keɓanta da su wajen sarrafawa a yayin da suke aiwatar da
sana’arsu ta waƙa. Bello (1982) da Ibrahim (1985) da Gusau (1996) sun
raba mawaƙan Hausa ta la’akari da muhallin waƙoƙinsu, kamar haka:
(i)
Mawaƙan sarauta/Fada
(ii) Mawaƙan jama’a
(iii) Mawaƙan Sana’a
(iv) Mawaƙan ban dariya
(v) Mawaƙan sha’awa
Wannan aiki ya karkata kan binciko gurbin Makaɗa Sa’idu Faru a cikin makaɗan fada. Makaɗan fada sun shahara wajen
luguden kalmomin Hausa ta fuskar salo, raha, ƙaƙale, yabo, zambo, habaici, shaguɓe, zuga da adana tarihi, da sauransu. Sukan sauya
falsafar da suka gada kaka da kakanni sakamakon sauyawar zamani da ire-iren
sauye-sauyen da ke wanzuwa a tsarin sarauta da raguwar ƙarfin ikon sarakunan ƙasar Hausa. Wannan ya sa wasu makaɗan suka zama
bigi-sa-bigi-taiki domin neman tara abin duniya. Fahimtar haka ne ya sa wannan
muƙalar ta yi azamar ɗora waƙoƙin Ɗan’umma Uban Kiɗi bisa sikelin bin diddigin gano ko makaɗin ya sauya sheƙa sakamakon sauyawar zamani, ko kuwa yana kamilin makaɗan sarauta har ya karɓa kiran Ubangijinsa?
2.0 Bitar Muhimman Batutuwa
2.1 Kiɗa
Kiɗa Bahaushiyar kalma ce wadda Hausawa suke kiran ta kiɗaa. Kalmar tana cikin jerin kalmomi na suna jisin maza. Jam’in
kalmar kuwa shi ne kaɗe-kaɗe. A wani karin harshen
kuwa sukan ce kiɗe-kiɗe. Kalmar tana ƙunshe da ma’ana kamar haka:
(i)
Buga ganga ko kalangu da abin bugawa.
(ii) Bugun
ƙwarya ko goge ko garaya da hannu ko da makiɗi ko da wani abu,
kamar yadda Kano, (2006 p. 243) ya bayyana.
Garba, (1990 p. 89) cewa ya yi kiɗa na nufin: “Yin amfani da abubuwa
don ta da amo iri daban-daban.” A wata ma’anar kuwa cewa ya yi kiɗa na nufin,
“Fasahar tsara amo na muryar mutum ko daga abubuwa ko duka a haɗe.” Yayin da aka dubi
waɗannan ma’anonin za a iya cewa, kiɗa yana nufin buga
wani abu a kan wani domin samar da wani amon sauti da ka iya jan hakalin mai
saurare.
2.2 Waƙa
Kalmar waƙa tana cikin jerin kalmomin suna jinsi mace. Jam’inta kuwa waƙoƙi ko waƙe-waƙe. Kalmar tana ƙunshe da ma’anar: “Magana wadda akan
rera da baki, aka tsara bisa wani zubi na musamman” kamar yadda Garba (1990 p.
152) ya nuna. Shi kuwa Kano, (2006 p. 466) ya bayyana ta da ma’anar, “Tsararriyar
magana da ake rerawa a kan kari ko rauji.”
Waƙa a bisa ma’anarta, tana nufin furta abin da ke cikin ƙwaƙwalwa. Sau da yawa akan ji Bahaushe na cewa:
a. Na
waƙa yi masa dukan fitar arziki.
b. Na
sha waƙa zuwa aikin Hajji.
c. Na
waƙa masa farashin kayan.
d. To,
Allah ya sa ba waƙa ba ce.
A wata ma’anar kuwa, waƙa takan kasance wata murya ko zaƙin murya mai shiga zuciya da faranta rayuwa. Misali , Bahaushe
kan ce:
a. Ai
na zaci waƙa ce.
b. Ya
matse sauti kamar mai waƙa.
c. Zaƙin murya sai ka ce zabiya.
Ta wata fuskar kuwa, waƙa takan kasance wata magana wadda akan rera da baki, wadda
kuma aka tsara bisa wani zubi na musamman.
Dangane da ma’anar waƙa ta ɓangaren adabi kuwa, za a ga masana adabin baka da dama
sun ba da ma’anarta a wurare mabambanta gwarwadon fahimtarsu. Daga cikin
masanan, Gusau (1984 p. 3) cewa ya yi:
Waƙar baka ita ce wani saƙo cikin zance na azanci da ake rerawa ba faɗa kurum ba, ta cikin
hikima da fasaha da zaɓaɓɓun kalmomi, waɗanda suka dace da saƙon. Kuma tana zuwa gunduwa-gunduwa, dangane da sautin
murya da kiɗa da amshi da gaɗa da taɓi ko zabiyanu mai saka zuciya jin daɗi.”
Shi kuwa Umar (1987 p. 7) ya bayyana ma’anar da cewa:
Waƙa ita ce nau’in sarrafaffen harshe da ake gabatarwa da
sigar gunduwoyin zantuttukan da ake kira baitoci ko ɗiyoyi, waɗanda ake ginawa a kan
kari ƙayyadadde, kuma ake rerawa da wani irin sautin murya na
musamman.
Yayin da aka nazarci waɗannan ma’anoni da
masana suka bayyana, za a ga cewa, suna ƙoƙarin nuna cewa, waƙa na nufin tsararriyar magana da ke ƙunshe da fasaha da hikimar sarrafa harshe da ake rerawa
gunduwa-gunduwa, cikin wani amo na musamman.
2.3 Waƙoƙi Fada
Su ne wasu manazarta kan kira da waƙoƙin sarauta.
Waƙoƙi ne da ake yi wa duk wani da ya jiɓinci jinin sarauta ko
aka ba shi wani matsayi na musamman a majalisar sarki, inda ake taro domin
gudanar da mulkin al’umma cikin tsari irin na gargajiya. Masu aiwatar da waɗannan waƙoƙin su ake yi wa laƙabi da makaɗan sarauta ko mawaƙan sarauta.
Ta fuskar ma’ana kuwa, Gusau (1988 p. 165) cewa ya yi:
Waƙoƙin baka na fada su ne waɗanda makaɗa na musamman ke
gudanarwa ga sarakunan gargajiya da iyayen ƙasa da hakimai da dagatai da masu unguwanni da ‘ya’yan sarakuna
da fadawa da masu riƙe
da da muƙaman sarauta da sauran ƙungiyoyin da suka jiɓinci sarauta.
Waƙar fada na zuwa ne a rere cikin sautin murya da daidaita
shi, wanda ya sa take zuwa gutsure-gutsure (gunduwa-gunduwa) tare da maimaita
gindinta a tsakaninsu. Kowane gutsure kammalalle ne ga kansa, amma wani zubin
ma’anarsa takan cika ta tumbatsa har ta tsallaka ga gutsuren da ke bi masa.
Gutsuren nan ne ake kira ɗan waƙa, jam’insa kuwa, ɗiyan waƙa.
Ana iya cewa, waƙar fada shiryayyen
zance ne mai zuwa gaɓa-gaɓa bisa ƙa’idojin tsari da daidaitawa da ake yi wa wanda ya shafi
sarauta domin a yabe shi, ko zuga shi ko kambama shi tare da fito da shi fili
kowa ya san shi. Takan ƙunshi nakasa (aibanta) abokan hamayyar wanda ake yi wa waƙar ta hanyar yi musu zambo da habaici da shaguɓe da nuna hushi da
tsoratarwa da firgitarwa da sauransu.
2.3.1 Wanzuwar Waƙar Fada
Ana kyautata zaton an soma waƙa ne a farfajiyar doron duniya a daidai lokacin aka ƙirƙiro farauta da samuwar addinin gargajiya. Gusau (1988 p. 167)
ya nuna cewa, waƙa ta ƙara bunƙasa da haɓaka sanadiyyar yaƙe-yaƙe da bayyanar sana’o’i da wasannin motsa jiki da wasu
lamurran da suka jiɓimci al’adun gargajiya. Masanin ya nuna cewa, a
farfajiyar ƙasar Hausa farauta ta kasance daɗaɗɗiyar sana’a da aka
fara aiwatarwa. Hasalima an sami waƙoƙin da suka dangance ta.
Ana cikin irin wannan yanayi ne, sai sarautun gargajiya
suka bayyana sakamakon taruwar al’ummar Hausa tsangaya-tsangaya. Wannan ya faru
ne tun daga lokacin da suka kafa mazaunai don samar da wurin zama na dindindin,
domin samun damar gudanar da sana’ar noma da kiwo da wasu abubuwan inganta
rayuwa tare da kare kai daga farmakin namun daji. Ana kyautata zaton daga
lokacin ne aka soma yi wa sarki waƙoƙi gajeru. Bayan bunƙasar waɗannan tsangayoyin
mazaunin farko zuwa ƙauyuka da garuruwa da birane, sai yaƙe-yaƙe suka haddasu a tsakaninsu, domin ƙoƙarin tabbatar da mulkin danniya. Ana cikin irin wannan
yanayi ne yaƙe-yaƙen ƙabilanci suka wakana a tsakanin ƙabilu da Hausawa domin son mulki da iko da kuma
shugabanci na sarakuna da ke mulkin su, ko kuma don neman faɗaɗa ƙasa ta mulki domin ta zama babbar daula.
Sakamakon irin waɗannan yaƙe-yaƙe da suka auku ne ya wanzar da samuwar wasu masu rauni da
ke da kishin al’ummarsu; waɗanda ba su da ƙarfin karawa da dakarun yaƙi. Su ne suka dinga
amfani da hikimarsu da basirarsu da zalaƙarsu wajen gudanar da
kirari na yabon sarakunansu tare da zuga jarumansu domin ƙara musu ƙwarin guiwar fatattakar abokan adawa.
A wani ƙaulin kuma, Gusau (1988 p. 167) ya nuna cewa, makaɗan da suka rinƙa yi wa sarakunansu guntayen waƙoƙi tun kafin a fara yaƙe-yaƙe ne suka cigaba da koɗa sarakunansu a fagen
daga tun kafin a fita yaƙi ko bayan an dawo.
A wani ƙaulin kuwa an bayyana cewa, a lokacin da ake kaɗa wasu kayan kiɗan yaƙi kamar: Tambari da kurya, sai Ɗanma’abba ya rinƙa aiwatar da kirari tare da zuga sarkinsu. Daga irin haka
ne ‘Yanma’abban suka samu
sukunin ɗinka ganguna da ƙudurin in an tafi yaƙi ko bayan an dawo su dinga cicciɓa sarki da jama’arsa.
Hasali ma tare da su ake zuwa yaƙin. Ko an samu ɓacin rana, ba za a kashe su ba, sai dai su bi sarkin da
ya samu nasara su dinga yi masa waƙoƙi suna zuga shi kan bajintarsa (Gusau, 1988 p. 168). A
sakamakon haka ne wasu ƙasashe suka samu damar mallakar tamburran abokan
hamayyarsu. Misali, kamar yadda ake hasashen cewa irin haka ne ya haifar da
Gumawa suka mallaki tamburran Zamfarawan Anka.
A tsakanin shekarar 1910 zuwa 1915 a daidai lokacin
mulkin Sarkin Musulmi Muhammadu Maiturare aka daina kiɗan yaƙi, kamar yadda Gusau (1988 p. 170) ya nuna. Daga nan sai
makaɗan suka koma ga aiwatar da waƙoƙin ga sarakuna suna yabon su ta hanyar bayyana musu irin
bajintar da kakanninsu suka nuna a fagen fama.
Wannan salon kiɗan shi ne ake yi wa laƙabi da kiɗan fada ko kuma a ce kiɗan sarauta ko na iko ko mulki. Hasali ma shi ne ya
maye gurbin kiɗan yaƙi. Daga lokacin ne sarki kan gayyato mawaƙi ya yi masa waƙa a inda zai yabe
shi, ya kuma zuga shi, kana kuma ya kushe abokin gabarsa. Yayin da mawaƙi ya gama rera waƙoƙinsa, sai sarkin ya yi masa gagarumar kyauta ta ƙasaita. A sakamakon wannan, mawakin yakan ji yana ƙaunar sarkin. Soyayyarsa takan sa ba wanda yake yi wa waƙa sai sarkin. Sakamakon haka ne sarakuna suka samu damar
mallakar makaɗa da mawaƙa a fadojinsu, har suka zama makaɗan fada, kamar yadda
Gusau (1988 p. 170) ya bayyana.
2.3.2 Musabbabin Yin Waƙoƙin Fada
Akwai abubuwa da dama da suka sabbaba ƙaga kiɗan fada. Ire-iren waɗannan abubuwan sun ƙunshi, nuna buwaya
(gagara) da rinjaye (fifiko) da dawwama cikin samun nasara da galaba a kan maƙiya da soyayya da kyauta da sauransu. Sakamakon irin waɗannan abubuwa da
mazaje suka keɓanta da su ne, ke sa a shirya musu waƙoƙi domin ƙara zuga su tare da fito da martabarsu da kwarjininsu a
idon jama’a. Misali, ga abin da Malamin Kiɗa Sa’idu Faru ke bayyana wa Sarkin Kiyawa na Ƙaura Alhaji Abubakar, a inda yake cewa:
Ni kiɗin yaƙi nay yi ma Abu na Isau,
Ba ni son kana zaunawa banza,
Ka ɗauki takobi da bindigogi da bakukuwa.
Ba mu sansani sai bakin Tsabre,
Kano da Katsina hak Kwantagora,
Duk riƙon Namoda na, shi na
ac can,
Garba ka amshe riƙon duk da Umaru,
Umaru yab bam ma.
(Sa’idu Faru: Gwabron giwa na Shamaki, Baba Ubangandu)
2.3.3 Makaɗan Fada/Sarauta
Su ne makaɗan da ke yi wa sarakuna waƙa kawai. Ba kasafai suke yi wa sauran jama’a waƙa ba. Sun fi mayar da hankalinsu a kan uwayen gidansu.
Sarakuna su ne iyayen gijinsu. A sakamakon haka, ba sa yi wa kowa waƙa sai da izinin sarkinsu. Wannan na faruwa musamman
kasancewar sarakunan ne suke ɗaukar ɗawainiyarsu, kuma sun fi kowa ganin ɗaukaka da darajar
sarakunansu. Makaɗa da dama da ke cikin rukunin farko na makaɗan sarauta suna da
wannan falsafar a cikin zukatansu. Misali, Mu’azu Na’alalo cewa ya yi:
Darajar kaza gashinta,
Darajar makaɗi sarkinai,
(Gital, 1984) a cikin Abba da Zulyadaini (2002)
Haka shi ma Jankiɗi ya ce:
Jumirin kwaram a kwana ana tafiya sai goga,
Jaki bai kai nan ba,
‘Yan yara masu kurin waƙa ku bar wargi,
Ma’ana ba ta zama ɗai ba.
Ni ba ni kiɗin iska sai ga sarkina.
Idan aka dubi waɗannan ɗiyan waƙa, mawaƙan fada suna nuni da cewa, yi wa sarakuna waƙa ya fi kome martaba, don haka suna kallon yi wa talaka
waƙa kamar aikin banza ne. A ɓangaren sarakunan da ake yi wa waƙar kuwa, sukan ɗauki ɗawainiyarsu da ta iyalansu tun daga muhallinsu, har abin
da za su ci da kuma suturarsu. Sa’idu Faru ma ya nuna yadda ubangidansa ke ɗauke da lalurarsa a
cikin ɗiyan waƙoƙinsa. Misali, ga abin da
yake cewa:
Sarki zamaninka na ruhwa,
Na ta da kaina,
Kowag gane ni da Daudu,
Ya san sarki garan gawurtacce.
(Sa’idu Faru: Waƙar Abubakar Sarkin
Kiyawan Ƙaura)
A nan za a fahimci cewa, makaɗin na ishara ne da
cewa shi makaɗin sarauta ne, don haka ne sarkinsa ke ɗauke da buƙatunsa.
Haka kuma ya fito fili ya na bayyana wa al’umma cewa, shi
ne kawai makaɗin sarauta da ya rage a wannan zamanin. Sauran makaɗa sun koma makaɗan jama’a sakamakon
juyin zamani. Ga abin da yake cewa kamar haka:
Sa’idu Faru ka waƙar iko,
Komai kaj jiya ƙarya a kai,
Sa’idu Faru ka waƙam mulki,
Komai kaj jiya ƙarya a kai.
(Sa’idu Faru: Turakin Kano Amadu)
2.3.4 Rabe-Raben Makaɗan Sarauta
A wannan rukuni na makaɗan sarauta (makaɗan fada) za a tarar
cewa Gusau (1996) ya kasa su zuwa ɓangarori biyu. Kashi na ɗaya (1) da na biyu
(2). Jerin makaɗan da suka faɗo ƙarƙashin kaso na
farko su ne:
a. Abdu
Kurna
b. Abubakar
Akwara
c. Alhaji
Muhammadu Sarkin Taushin Katsina
d. Aliyu
Ɗandawo
e. Buda
Ɗantanoma
f.
Ibrahim Gurso
g. Ibrahim
Narambaɗa
h. Idi
Ɗangiwa Zuru
i.
Jibo Maituru
j.
Muhammadu Dodo Maitabshi
k. Muhammadu
Inyaga
l.
Salihu Jankiɗi
Kashi na biyu kuwa ya ƙunshi makaɗan da suka haɗa da:
a. Alhaji
Ɗankurma Maru.
b. Alhaji
Musa Ɗankwairo Maradun.
c. Alhaji
Sa’idu Faru
d. Alhaji
Sa’idu Maidaji Sabon-Birni
e. Alhaji
Sani Aliyu Ɗandawo
f.
Muhammadu Ango Maitabshi
g. Muhammadu
Maidamma Sarkin Taushi
h. Sarkin
Taushi Muhammadu Ɗanbunguɗu
i.
Umaru Maisa’a Tubali
2.3.5 Alaƙar
Makaɗan Fada Da Sarauta
Makaɗan fada na ɗaya daga cikin rukunin al’umma da sarakuna ke ɗauke da lalurorinsu
na yau da kullun. Sarki yakan zama ubangidan makaɗi, shi yakan ɗauki lalurar cinsa da
shansa, ya yi masa gida ya ba shi gona, ya kuma rinƙa yi msa sutura tare da iyalansa. Haka kuma yakan ba shi
kuɗaɗen ɓatarwa.
Sarki yakan amince wa makaɗinsa fiye da sauran
fadawansa. Yakan zauna tare da shi su yi hira cikin sakin fuska sosai da zaman
amana da taimakon juna. Shi kuma makaɗin zai dinga girmama sarkin da mutunta shi tare da yi
masa ladabi da biyayya tamkar yadda al’ummar fada ke yi masa.
A al’ada, makaɗin fada bai fita waje ya yi wa wani sarki ko jinin
sarauta waƙa, sai da izinin ubangidansa. Yayin da ya je waƙa gun wani, zai nuna wa sarkinsa duk nau’in abin alherin
da aka yi masa. Wani lokaci, yana iya bayyana masa a cikin sigar waƙa.
3.1 Siffofin Makaɗan Sarauta Da
Matsayin Sa’idu Faru
Makaɗan sarauta suna da
waɗansu siffofi da
suka fi alaƙantuwa da su. Sun
haɗa da:
a. Makaɗin sarauta shi ne
wanda kan samu wani basarake ya zauna a wajensa ya kasance ubangidansa da zai
rinƙa yi masa yammaci (kiɗa daren Juma’a) ko
daren salla. Sukan bi sarki a duk lokacin da zai fita rangadi (kewayar gundumar
da ke ƙarƙashin mulkinsa).
b. Sukan
nemi izinin ubangidansu kafin su tafi yawon kiɗa gidan wani sarki ko
alƙali ko bafade ko wani mai arziki da ke ɗasawa da ubangidansu.
c. Akasarinsu
sun gadi kiɗa da waƙa irin na sarauta idan aka cire Aliyu Ɗandawo Shuni, wanda ya kasance ɗan wani shahararren
malami da aka yi a can Shuni ɗin da ake kira da suna Modibbo Aliyu, Kamar yadda Gusau
(1984) ya nuna.
d. Sun
fi kowane Bahaushe sanya tufafin gargajiya, wato sanya manyan riguna da
wandunan buje da taguwoyi masu manyan hannaye. Sukan kuma naɗa rawani. Suna riƙe wannan al’ada ce saboda irin wannan suturar sarakuna
kan ba su. Abin la’akari shi ne, sarakuna ba sa rabuwa da sanya manyan suturu
komi gumi ko zafi. Hasali ma sarki ba zai fito gidansa ba rawani a kansa ba.
shi ya sa makaɗan sarauta suka riƙe wannan ɗabi’a domin kare
martaba da alfarmar sarauta. Shi ya bambanta su da sauran makaɗa da mawaƙan ƙasar Hausa.
Duban ire-iren waɗannan siffofi da aka ambata a sama da la’akari da irin
sigar yanayin shigar Alhaji Sa’idu Faru za ka tabbatar shi cikakken makaɗin sarauta ne. A lokacin
rayuwarsa ba ka raba shi da shiga irin ta iyayen gidansa.
3.2 Kayan Kiɗan Makaɗan Fada Da Gurbin Sa’idu Faru
Ta sigar kayan kiɗa kuwa, makaɗan sarauta sun sha bamban da sauran makaɗa da mawaƙan baka na ƙasar Hausa. Haka kuma sun kasu kashi-kashi dangane da
kayan kiɗan da suke amfani da su, da nau’o’in waƙoƙin da kuma uwa-uba irin garuruwan da suke zaune da kuma
inda suka ƙaurato. Ta fannin kayan kiɗa, za a iya kasa su
zuwa kashi uku kamar haka:
a. Masu
kaɗe-kaɗe
b. Masu
bushe-bushe
c. Bambaɗawa (masu kirari)
(Ibrahim, 1983 p. 2).
Ta wannan haujin kuwa, Alhaji Saidu Faru yana cikin sahun
makaɗan fada da ke amfani da kayan kiɗa dangin na sarauta.
Su ma kayan kiɗan sarauta sun karkasu kamar haka:
(i) Tafshi
(ii) Kotso[1]
(iii) Jauje
(iv) Tambari
(v) Banga
Waɗannan kayan kiɗa akan yi amfani da su wajen tsima sarki ta hanyar kambama
shi da magabatansa.
Kashi na biyu kuwa sun ƙunshi abubuwan busawa ne da suka danganci:
(i) Algaita
(ii) Kakaki
(iii) Ƙaho
(iv) Farai
Waɗannan kayan busa
suna ba wa talakawa labari ne cewa, sarauta tana nan daram ta kafu. Suna kuma
jawo hankulan masoya sarki da cewa su zo su ji abin da za a faɗa game da masoyinsu.
3.3 Sauya Sheƙar
Makaɗan Sarauta Zuwa Na Jama’a
Sauye-sauyen ubangida ga makaɗan fada yakan faru ne
a zamanin da sarakuna ke da ƙarfin ikon gudanar da al’amuran tafiyar da ragamar mulkin
al’ummominsu, kafin mulkin Jamhuriya ta farko. A waɗansu lokuta makaɗa na sauya ubangidansu, musamman saboda dalilai kamar haka:
a. Yayin
da ubangida (sarki) ya karɓa kiran Mahaliccinsa.
b. Yayin
da aka fitar da shi daga sarautarsa.
c. Yayin
da ya daina yi wa makaɗinsa alheri.
4.1 Nau’o’in Waƙoƙin Makaɗa Sa’idu Faru
Sa’idu Faru ya yi wa sarakuna da jinin sarauta waƙoƙi da dama waɗanda shi ma kansa bai san adadinsu ba saboda yawansu.
Hasali ma, dukkan waƙoƙin shi ne ya ƙaga su da kansa. Shi
ba kamar sauran makaɗan sarauta ba ne da ke maimaita waƙoƙin da mahaifansu suka aiwatar ba. A ƙasa an kawo waɗansu sarakuna da hakimai da uwayen ƙasa da ya yi wa waƙa:
1. Sarkin
Yamman Faru Ibrahim
2. Sarkin
Yaƙin Banga Sule
3. Sarkin
Kiyawan Ƙaura Abubakar Garba
4. Sarkin
Gabas Na Mafara Muhammadu
5. Sarkin
Musulmi Abubakar III
6. Sarkin
Yawuri Alhaji Muhammadu Tukur
7. Sarkin
Sudan Na Wurno Alhaji Shehu Malami
8. Sarkin
Kano Ado Bayero
9. Sarkin
Kudu Muhammadu Macciɗo
10. Sarkin
Gabas Shehu Uban Ƙasar Talata Mafara
11. Turakin
Kano Amadu
12. Muhammadu
Muhammadu Maidabo Tudun Falale
13. Alhaji
Muhammadu Mode, Ɗan Alin Birnin Magaji
14. Sarkin
Zamfaran Zurmi, Suleiman Muhammadu Sambo
15. Sarkin
Zazzau Alhaji Dr. Shehu Idris, da sauransu
Ta fuskar waƙoƙin da ya yi wa ubangidansa kuwa, ya yi wa Sarkin Kudu
Muhammadu Macciɗo waƙoƙi da dama. Abin da hannaye suka samu nasarar dafawa su
ne:
1. Farin
cikin Musulmi duk kai muka taƙama yau,
Muhammadun Muhammadu ɗan Abdu mai darajja.
2. Sai
na zo in yi mai kiɗi in ƙaro ilmi,
Mamman Bajinin Magaji
mai takakkay yaƙi.
3. Farin
cikin Musulmin Duniya, mai martaba na Abubakar,
Ci fansa Alhaji Macciɗo.
4. Kana
shire Baban Yan Ruwa,
Na Bello Jikan Ɗanfodiyo.
5. Bajinin
gidan Bello Mamman Na Yari,
Sarkin Kudu Macciɗo ci maraya.
6. Shugaban
sahun gabas riƙa ƙwarai,
Muhammadun Amadu Uban
Zagi.
7. Hattara
Bajinin gidan Bello Jikan Hassan maganin wargi.
8. Ya
yi Sarki daidai wada mai yanzu yar riƙa,
Alhaji Macciɗo jikan Mamman mai
dubun bara.
9. Mai
babban rabo ginshiƙin Sarkin Shariffai.
10. Hattara
mai martaba Bello ɗan Bubakar,
Sarkin Kudun Hausa.[2]
Yayin da aka kwatanta Alhaji Musa Ɗankwairo a matsayinsa na mawaƙin sarauta kuma Sarkin kiɗan ‘Yandoton Tsahe
Alhaji Aliyu, da Alhaji Sa’idu Faru, za a iya cewa, Ɗanƙwairo ya canza sheƙa sakamakon juyin
zamani. Hasali ma ana hasashen cewa, tun waƙar Shirya Kayan Faɗa ba wata waƙa da ya sake yi wa ubangidansa. A madadin haka, sai ya
karkata ga yin waƙoƙin jama’a da suka ƙunshi ‘yan kasuwa da
‘yan siyasa da malamai da tajirai. Wannan ne ya sa mafi yawan waƙoƙinsa suka zama na gama-gari. Misalan waƙoƙin sun haɗa da ta:
a. Alhaji
Shehu Kangiwa
b. Kanal
Umaru Muhammad
c. Alhaji
Ahmadu Aruwa
d. Alhaji
Kabiru Mado
e. Alhaji
Ali na Malan Bawa
f.
Alhaji Garba A.D. Kano
g. Alhaji
Garba Nadama
h. Alhaji
Ahmad Muhammad
i.
Alhaji Bala Maiyafe
j.
Malan Lawal Ƙalarawi
k. Alhaji
Bala Salisu
l.
Alhaji Sikofiyo
m. Alhaji
Bature Dogon Tela
n. Alhaji
Ibrahim Maganinta
o. Waƙoƙin Faɗakarwa
p. Waƙoƙin Jam’iyyun Siyasa
Ta la’akari da jerin waɗannan waƙoƙin, za su iya kawar da Ɗanƙwairo daga cikin sahun mawaƙan sarauta. Ta fuskar Sa’idu Faru kuwa, babu waƙar da ya aiwatar da za
ta iya fitar da shi daga cikin sahun makaɗan sarauta.
4.2 Turakun Waƙoƙin Makaɗa Sa’idu Faru
Kasancewar Sa’idu makaɗin sarauta ne na
asali, bai sake juyin zamani da kwaɗayin tara abin duniya ya ruɗe shi ba. Shi ya sa
ya tsaya wajen gina waƙoƙinsa a kan turakun da iyaye da kakanni suka assasa
tushensu tun farkon fara kaɗe-kaɗen fada (sarauta). Binciken masana kamar Gusau (1996 p. 121)
ya tabbatar da cewa, Makaɗa Sa’idu faru ba ya yi wa kowa waƙa sai sarki da wanda ya kasance jinin sarauta. Waƙar farko da ya fara aiwatarwa ita ce ta Sarkin Yamman
Faru Ibrahim. Gindin waƙar shi ne:
Bi da maza ɗan Joɗi na Iro,
Iro magajin Shehu da Bello.
Hasken hitila ba ɗai da wata ba,
Tauraro haskenka subahin,
Dawaya kora ɗimau na wakili,
Uban sarkin zagi Bello na yari.
Ruwa da kada ɗibgau na Magaji,
Sai tsohon wawa ka shigar su.
(Gusau, 1996 p. 119).
Tun daga wannan waƙar sai ya ci gaba da
yi wa sarakuna da ‘ya’yan sarakuna waƙoƙi. Yana cikin irin wannan yanayi ne, Allah cikin ikonsa
da baiwarsa ya sada shi da Sarkin Kudu Muhammadu Macciɗo ɗan Sarkin Musulmi
Abubakar na III, wanda ya sarauci ƙasar Talata Mafara daga 1953 zuwa 1956, kamar yadda
Talata Mafara (2007 p. 17) ya nuna. Ya fara yi wa Sarkin Kudu Macciɗo waƙoƙi a daidai lokacin da yake riƙe da muƙamin Ubanƙasar Talata Mafara. Ga gindin waƙar da ya fara yi masa, a inda yake cewa:
Kana shirye baban ‘Yanruwa,
Na Bello jikan Ɗanfodiyo.
Gardaye zo ka yi man iso,
Faɗa mashi murna niz zaka,
Ɗan Sardauna jikan Hassan.
Babban ɗa ga Baura Sarkin Kudu,
Na Alƙali baban zagi,
Mai ja ma ya bari ɗan Adamu.
Na Sarkin Gobir Amadu,
Ci fansa ga wan Sarkin Ƙaya.
Waƙag ga da nim maka
Muhammadu,
Na ji daɗin ta Mamman Sarkin Kudu,
Tun dak Kabi hak Kano ham Masar,
Hab birnin Legas hab Bici,
Kowa ya ji waƙar Sarkin Kudu.
(Gusau, 1996 p. 120).
Sa’idu Faru fasihin mawaƙin sarauta ne da ya naƙalci harshen Hausa ga baiwar da Allah ya yi masa ta
fasahar ƙulla waƙa yadda za ta yi daɗi ta kuma yi armashi da ma’ana. Sakamakon haka ne ya kira
kansa da Malamin waƙa, a inda yake cewa:
Sa’idu Malamin waƙa,
Mai kwana ɗumi na Mamman na
Balaraba×2
Ban wuce gonata da irina ba,
Inda Sarkin Kudu nat tsaya.
Gindin Waƙa: Farin cikin Musulmin duniya.
(Faru: Waƙar Sarkin Kudu Muhammadu Macciɗo)
Sa’idu Faru bai taɓa yi wa talakka waƙa ba, komai tarin
dukiyarsa. Hasali ma shi da kansa ya yi nuni da haka, a inda yake cewa:
Ban zo gidan Ɗanbita niy yi roƙo ba,
Ko ya raba lafiya ba ruwana.
A wannan ɗiyan waƙar ya fito ƙarara ya tabbatar wa al’umma cewa shi bai taɓa yi wa talaka waƙa ba. Ya jaddada cewa ba zai yi haka ba ko da mutumin yana samar da kowane irin jin
daɗi da ingancin jiki da kawar da ciwo daga jikin ɗan’adam. Shi bai damu
da duk wannan ba, ballantana ya yi masa kiɗa da waƙa. Kalmar ɗanbita a nan tana nufin leburan da ke aikin gyaran hanyar mota.
A daidai wancan lokacin, sarakuna ne ke bayar da waɗanda za su yi aikin
hanya. Sukan zaɓo waɗanda suka dace da aikin hanyar daga cikin talakawansu. A
daidai wancan lokacin akan ji tsofaffi na maganar aikin diga da ke nuni
da aikin hanya. A sakamakon irin wannan aikin talakawa da dama sun tara abin
duniya.
Malamin waƙa ɗin ya bayyana dalilan da suka sa ba ya yi wa talaka waƙa da kiɗa kamar yadda Gusau (1996 p. 121) ya ruwaito su cewar:
a. Ba
wata hanya da zai bi ya ɓata wa talaka rai. A lokacin da talaka ya wulaƙanta makaɗi, to sai dai makaɗin ya yi na mai bara (haƙuri).
b. Yayin
da Sarki ko jinin sarauta ya yi wa makaɗi abin da ya ɓata masa rai, sai ya rama a cikin waƙa ta hanyar yi masa zambo ko habaici. Ba wani sarki ko
jinin sarautar da yake son makaɗi ya yi masa su.
Za a iya samun wasu rukunin al’umma su ce, idan haka ne
wane dalili ne ya sa Makaɗa Sa’idu Faru ya yi wa Alhaji Shehu Kangiwa waƙa? Amsa a nan ita ce, an yi waƙar ne a shekarar 1976 bayan an naɗa shi Turakin
Kangiwa. Sarauta ce da Masarautar Argungu ta ba shi, a ƙarƙashin Shugabancin Maimartaba Sarkin Kabin Argungu, Alhaji
Muhammadu Mera. Ya zama ɗaya daga cikin jigajigan masarautar. Don haka, an yi masa
waƙar ne a matsayinsa na ɗaya daga cikin masu
riƙe da sarautun gargajiya a Msarautar Argungu. Idan aka yi
la’akari da ma’anar makaɗan sarauta da lokacin da aka aiwatar da waƙar, za a iya tabbatar da cewa Makaɗa Sa’idu Faru bai taɓa yi wa talaka waƙa ba. Shi makaɗin sarauta ne tsantsa.
4.3 Ƙananan Turakun Waƙoƙin Makaɗa Sa’idu Faru
4.3.1 Yabo
Makaɗa Sa’idu Faru a cikin waƙoƙinsa yakan yabi ubangidansa ta haujin ambaton asalinsa.
Yakan kuma danganta shi da asalinsa ta hanyar bayyana
cewa ya gaji gidansu. Ta haka ne ya yabi Sarkin Kudu Macciɗo da irin wannan
sigar a inda yake cewa:
Allah ya ba ka
albarkar nan ta Alu Babba,
Ka gama da kyau cikin
sa’a mun yi roƙon Allah,
Allah shi ba ka albarkar
nan ta Shehu, Amin.
Ka gama da kyau cikin
sa’a mun yi roƙo Allah.
Allah shi ba ka
albarkar nan ta Bello, Amin.
Ka gama da kyau cikin
sa’a mun yi roƙon Allah.
Allah ya ba ka
albarkar nan ta Bubakar na farko.
Ka gama da kyau cikin
sa’a mun roƙon Allah.
Allah shi ba ka
albarkar Bubakar na biyu,
Ka gama lafiya da
imani mun yi roƙon Allah.
Allah ya ba ka
albarkar nan ta Aliyu Babba,
Ka gama da kyau da
imani mun yi roƙon Allah.
Allah ya ba ka
albarkar nan ta Alu ƙarami,
Ka gama da kyau cikin
sa’a mun yi roƙon Allah.
Allah shi ba ka
albarkar Abdullahi,
Ka gama da lafiya da
imani mun yi roƙon Allah.
Allah shi ba ka
albarkar nan ta Hassan Dattijo.
Ka kammale, ka ɗibo jama’arka.
Duk ka shirya mu
gaban Ma’aikin Allah,
Mu yi farin ciki,
Mu ji daɗin da yaf fi daɗi daɗi na Annabi.
Mu ji ƙamshin da yaf fi ƙamshi, ƙamshi na Bubakar,
Allah shi sa ka samun
martabar kakanka.
Yayin da aka dubi waɗannan ɗiyan waƙar, za a ga cewa, Sa’idu Faru na yi wa ubangidansa Sarkin
Kudu Macciɗo fatan Allah ya ba shi albarkar waɗannan kakanni nasa ya
kasance tamkarsu tare da samun martaba irin tasu.
Ba nan kawai ya tsaya ba. Har ma ya yabi Sarkin Kudu
Macciɗo ta haujin iya gudanar da mulki, a inda yake cewa:
Shugaban duniya Alhaji Bello Sarkin Kudu,
Jan damishi Shehu Sarkin Gabas,
Baban su Alƙali.
Gadangadan Shehu Sarkin duniya,
Ba mai riƙo na ba.
Ai! Ina ba magana ba ce yanzu gidan Bani,
Ba mai kamar Macciɗon Hausa.
Girmanka ya kai muƙaminka ya kai,
Riƙon duniya wada
Abubakar yak kai,
(Sa’idu Faru: Waƙar Sarkin Kudu Macciɗo).
A nan mawaƙin ya bayyana cewa, Macciɗo zai iya gudanar da
mulkin wannan duniya sakamakon ƙwarewarsa a fagen mulki.
Ta fuskar addini ma, ya yabi ubangidansa a inda yake
cewa:
Gindin Waƙa: Bajinin gidan Bello Mamman na Yari,
Sarkin Kudu Macciɗo ci maraya.
Jagora: Tsari gaskiya Bello kai Shefu yac ce,
‘Yan Amshi: Bari masu son dus su maishe ka yaro,
Duk kyauta da ilmi da neman dalili,
Da gode ma Allah da istingafari,
Da su Bello ɓello ɗan Shehu yat tcarma kowa,
Ka kai kamab Bello,
Ka gadi Moyi,
Saura ka kai inda mai Hausa yak kai.
Yayin da aka dubi ɗiyan da suka gabata, za a ga yadda
wannan turken ya ƙara tabbatar mana da kasancewar mawaƙin a gurbin makaɗin sarauta. Makaɗan fada ne suka yi fice wurin yabon
uwayen gidansu ta fuskar addini. Hakan na faruwa ne kasancewar sarakunan ƙasar Hausa su ne shugabannin addinin
Musulunci tun kafin jahadin Shehu. Jagorancin nasu ya ƙara bunƙasa ne bayan tabbatuwar jahadi. Da irin
wannan yabon ne sarakuna suke alfahari da makaɗansu.
A nan ya bayyana wasu siffofin da suka keɓanta ga sarakunan ƙasar Hausa, wato, kasancewarsu masu alheri ga al’ummarsu, da zamansu malamai masana
dangogin ilmomin zaman rayuwar duniya, domin su ne tushen samun kyakkyawar
makoma gobe kiyama. Ya kuma ƙara kawo abu da ya kasance tamkar ruwa
da gishiri a fagen sarrafa abinci da sauran lamurran rayuwar duniya. A nan ya
yi masa hannunka mai sanda ne da ya lizimci nuna godiya a kan ni’imomin da
Allah ya yi masa da dagewa ga yin tuba game da kuskuren da yake aikatawa, domin
ta haka magabatansa suka tsere tsara. Idan ya nace a kan haka, zai kai ga samun
matsayin da Sarkin Musulmi Abubakar Sadik yake a kansa.
4.3.2 Zuga
A wannan haujin kuwa, Sa’idu
Faru yakan harzuƙa ko tunzura sarkin da yake yi wa waƙa, ta hanyar kambama
darajarsa. Dubi yadda yake cewa a waƙarsa da ya yi wa Sarkin Kudu Macciɗo mai take:
Gindin waƙa: Kana shire baban ‘yan ruwa.
Jagora: Wani taro da an ka zo Ikko na bariyac can,
Da Turawa da kuma ministoci had da kansiloli,
Sarkin Musulmi da Amdu Bello sun zo
wurin dus sun ziyar tai,
Tafawa Ɓalewa ya sauka ga Lamiɗo Barno,
Nan kudu Shehu Talba,
Sarkin Bidda ya sauka ga Sarkin Ilori,
Kulluhinsu sarakunan majalisa sun taru
Ikko,
Muhammadu Bello jikan Hassan kai sun ka
zaɓa,
Don ka hi su kyawon shirin kawo dalillai.
Idan aka dubi kwayar turken wannan ɗan waƙar, za a ga ya fito ne ƙunshe da zuga Sarkin Kudu Macciɗo tare da fifita shi a kan waɗanda suka halarci taron. A ɗaya ɓangaren kuwa, ya taskace tarihin taron
da aka aiwatar a Ikko tare da fito da maigidan nasa fili domin waɗanda ba su san shi ba su san shi. Irin wannan zugar ke ƙara tabbatar wa masu nazari gurbin da
mawaƙin ya kasance.
4.3.3 Habaici
A cikin waƙoƙinsa akwai wuraren da yakan yi wa abokan adawar ubangidansa habaici ba tare
da faɗa masa wata muguwar magana ba. Wannan
kan iya kasancewa a cikin sigar jifa a kasuwa ko kuma ya san da wanda yake.
Hasali ma makaɗan fada sun fi shahara ta fuskar amfani da habaici domin ƙasƙantar da abokin hamayyar sarkinsu ko muzanta shi a bainar
jama’a a fakaice. Misali Sa’idu
Faru yana cewa:
Zaki mai zama ga
hilin Allah ga shi ga hili,
To wak ka san ya far
mashi,
Kafin maza su shirya
Mamman na Ali ya shirya.
Sun dai yi ɓaɓɓakar dutsi,
Sun yi gyangyaɗar dutsi,
‘Yan hannuwansu sun
gaza.
Na Audu ko da ƙarfin Allah kana shiga gidan.
Na ce mai kama da ƙot,
Haka nij ji gun
Badakkare.
Dogon sarki yana da
ban sha’awa,
Ko da anka zo taro ya
fi kyau da riguna,
Duk wanda ag gajere a
aje shi gun rabon dawo,
Shi kai ma wanga dunƙule.
Aw wurin da mata
ciki,
Har tuman gada yakai.
(Sa’idu Faru: Waƙar Sarkin Tudun Falale).
Da duban waɗannan ɗiyan waƙar za a fahimci Sa’idu Faru ya yi wa wasu ‘ya’yan sarki
habaici ne a kaikaice, domin ya fahimci suna son su yi jayayya da ubangidansa.
4.3.4 Zambo
A nan ma akan samu inda yakan yi wa abokan hamayyar
ubangidansa wata mugunyar magana. Misali a cikin waƙar da ya yi wa Sarkin Kudu Macciɗo yana cewa:
Gindin Waƙa: Gogarman gidan Moyi ci fansa niƙatau,
Mai babban rabo ginshiƙin Sarkin Shariffai.
Jagora: Na ishe dale tai ƙawa ga jama’at ta ba ƙawa.
‘Yan Amshi: Ya murɗe su duy ya zuba dogon akwati,
Rana ta kewayo ya naɗe ya kai Ilori,
Dac can yas sawo man kishe,
Ya sai tabarau.
Yayin da aka nazarci wannan ɗiyar za a ga cewa, ya yi wa wani ɗan sarki zambo ne ta hanyar siffanta shi da wata
tsuntsuwa da ake kira dale. Ita dale akan gan ta ne lokacin kaka. Ta
kasance nau’i biyu. Akwai ja mai baƙi-baƙi ga kai, akwai kuma mai launin ɗorawa da baƙi-baƙi ga kai. Ita dalen ba a ganin ta sai
lokacin da amfanin gona ya kai. Saboda halayyarta ne ya kamanta ɗan sarkin da ita, domin bai amfana wa kowa komai. Hasali ma
idan wani abun alheri ya zo da ya kamata ya ba al’ummarsa, sai ya yi sama-da-faɗi da shi.
4.3.5 Roƙo
Akan sami wasu ɗiyan waƙoƙinsa da Sa’idu Faru yakan yi bara ko ya roƙi ubangidansa wani abu kai tsaye cikin hikima. Wannan wata azaliyya ce da
ta keɓanta ga makaɗan sarauta, wato su bayyana abin da suke so daga ubangidansu kai tsaye ba
tare da wani sakaye-sakaye ba. Shi ma Malamin Waƙa ya aiwatar da shigen wannan a inda yake cewa:
Manyan ma’aikatan
gwamnati,
Manyan ma’aikatan N.A.,
Almajirinku na aike,
Don bisa gare ku
Allah ya shiya mana asiri,
Na roƙe ku in da hali,
Ku zam shirya muna
kujera mui Haji.
Na yi mafarki nai
sallah Makka nai ɗawafi,
Kuma na rungumo
hirami
Da makaru a fuskoki,
An ce mani Alhaji
baitul fasali kake,
Wanga mafarki ya
Allah ya nufa a shirya shi,
Ya zam haka.
(Sa’idu Faru: Waƙar Sarkin Kudu Macciɗo).
A waɗannan ɗiyan waƙar, za a ga mawaƙin ya fito ƙarara ya nuna buƙatarsa tare da ayyana
dalilinsa wanda ya kasance mafarkin da ya yi da yake son a taimaka masa ya zama
gaskiya. Za a iya cewa, ma’aikatan gwamnati da ya roƙa ai suna cikin rukunin talakawa. Lamarin a wancan
lokacin ba haka yake ba. A daidai lokacin ‘ya’yan ahalul falala ake damƙa wa aikin hukumar En-e da na gwamnati.
4.3.6 Koɗa Kai
Sa’idu Faru fasihin makaɗan fada ne, musamman
idan aka yi la’akari da wuraren da yakan wasa kansa ta hanyar nuna ƙwarewarsa wajen tsara waƙa fiye da sauran makaɗan fada. Kuma yakan yi hakan ne a ciki ɗiyan waƙoƙin da ya ƙulla wa maigidansa Sarkin Kudu Macciɗo. Kasancewar sa makaɗin fada, ya shahara wajen amfani da wasu halaye da siffofi na ɗan’adam, ya ƙaga su ga wani abu wanda ba mutun ba, wato abin da ake kira mutuntarwa.
A waƙar da ya yi wa Sarkin Kudu macciɗo cewa ya yi:
Nan na bi Gusau sai
niw wuce,
Kuma nab bi
Kwatarkwashi niw wuce,
Kuma nib bi ta Tcahe
ina gudu,
Can na kusa kai wa
Zariya,
Sannan Daudu ni kau
sai nit tsaya.
Sai Sarkin Zazzau nig
ga nay,
Ya ce man Muhamman
Sarkin Kudu.
Sai nis saki hanya
nig gabas.
Can na taɓa ‘yar tafiya kaɗan,
Sai ni ishe suda na
kiwo,
Tana barka Sarkin
Kudu,
Allah rai ya daɗe Sarkin Kudu,
Allah sabbinane na
Ahmadu,
Allah shi ƙara mai nasara.
Na ce suda waƙa akai,
Ta ce lalle waƙa ni kai,
Waƙar Mamman Sarkin Kudu,
Waƙar nan da Ɗan’umma ya yi mashi.
Baicin uwar tsuntsaye
nike,
In da kamar mulkina
nikai,
Da nai mai wasiƙa ya yi min kiɗi,
San nan ni kau sai
niw wuce,
Can na taɓa ‘yar tahiya kaɗan,
Sai ni iske burtu na
kiwo,
Yana barka Sarkin
Kudu,
Rai ya daɗe Sarkin kudu,
Allah sabbinane na
Amadu,
Allah shi ƙara mai nasara,
Na ce burtu waƙa akai,
Ya ce lalle waƙa nakai,
Waƙar Mamman Sarkin Kudu,
Waƙar nan da Ɗan’umma ya yi mashi.
In na yi ta za ni
wurin kiwo,
In na so abinci sai
na rufe.
A cikin waɗannan ɗiyan waƙar, za a fahimci cewa mawaƙin ya yi amfani da adon harshe ne domin jaddada cewa ba
ya yi wa kowa kiɗa da waƙa sai sarakuna da waɗanda ke da alaƙa da fada. Ga shi har
da tsuntsaye sun san da haka. A ɗaya ɓangaren kuwa yana ɗaukaka waƙar da ya yi wa Sarkin Kudu, wadda sakamakon yadda ta
tsaru ta yi armashi, har tsuntsaye na maganar waƙar.
Waƙar da ya yi wa Sarkin Sudan Na Wurno Alhaji Shehu Malami, ita ma wata hujja ce mai ƙarfi da ke tabbatar da kasancewarsa makaɗin sarauta ne na
gani-da-faɗa wanda sauyin zamani bai juya shi ba. A wasu ɗiyan waƙar, yana cewa:
Gindin Waƙa: Muzakkarin sarki ɗan Audu,
Abin biya Shehu na Ali.
Jagora: Ɗan talakka komai yac cika huska,2×
Sa’idu ni ba ni kiɗa mai, 2×.
Jagora: Ɗan talakka komai ya aje ƙarhe,
Sa’idu ni ba ni kiɗa mai.
Da duban waɗannan ɗiyan waƙar za a ga ya fito fili yana jaddada cewa shi ba makaɗin talakawa ba ne,
kuma komai bajintarsu da ƙwazo da kuma uwa-uba mallakar tamani (jikkunan kuɗaɗe) ba zai yi musu kiɗa da waƙa ba.
4.4 Sarrafa Harshe a Cikin Waƙoƙin Sa’idu Faru
4.4.1 Ƙarangiya ko Gagara-gwari
Makaɗan fada, musamman waɗanda suka fito daga yankin da ke cikin farfajiyar
tsohuwar Daular Zamfara, wato yakin da ke cikin Masarautar Bakura da Zurmi da abin da ya gangara Sabon
Birnin Gobir har zuwa Dacaɗi da sauransu, sun fi takwarorinsu da ba ‘yan asalin
yankin ba ne wajen mallakar harshen Hausa da iya sarrafa shi. Sa’idu Faru ya yi
wa takwarorinsa da suka yi zamani ɗaya da shi fintinƙau ta fannin sarrafa
sautukan Hausa masu bugun juna ta hanyar maimaita su a cikin ɗiyan waƙa domin nuna ƙwarewarsa a harshen
da yake waƙa da shi (Hausa). Ana kyautata zaton cewa, sukan yi
amfani da wannan hikimar ne domin kawar da wani lamarin da ke ci wa sarki tuwo
a ƙwarya ta yadda zai koma ga hayyacinsa har ya yi ƙoƙarin fahimtar yadda aka yi luguden kalmomin da fahimtar ƙunshiyarsu. A duba misalin inda Sa’idu Faru ke cewa:
Yaro in taƙamar salon magana kaka yi,
Ce tsare tsara,
Ta hi tsantsamin tsantsara,
Ko tsattsame tsari,
Tsaf ga tsamiya.
Tunkuɗa tunku cikin tukar rukuɓu,
Tukuɗin Tumba yai tuɓus,
Tumba taho yau da ke da taɓo,
Da taɓo da’yat tuɓus..
(Sa’idu Faru: Waƙar Sarkin Kiyawa na Ƙaura).
Yayin da aka duba waɗannan ɗiyan waƙar za a tarar cewa Sa’idu Faru ya yi luguden sautukan
Hausa kamar: tsa, tu, ɓa, ɓo, ɓu, ɗa, ɗi, da kuma ɗu, domin ya nuna ya naƙalci harshen Hausa da yake waƙa da shi. Mai nazari zai iya yin tambaya game da hujjar
kawo wannan dalili? Hujja ita ce, tun lokacin da
addinin Musulunci ya shigo ƙasar Hausa, a fada ya soma zama da kafa harsashe. Wannan
ne ya sa Sarakunan ƙasar Hausa suka kasance malamai musamman bayan jahadin
Shehu. Hasali ma sun kakkafa makaratun ilimi (zaure) inda ake koyar da fannonin
addini da luggar Larabci da ake fassarawa cikin harshen Hausa. Wannan ne ya sa
har gobe tsofaffin kalmomi da hikimomin Hausa sun yanke cibiya a makarantun
zaure, ta la’akari da irin hikimomin da ke ƙunshe cikin Muƙamatul Hariyri.
4.4.2 Dangantakar Kalmomi
Ta wannan haujin za a ga cewa makaɗan sarauta sun sha
bamban da na jama’a ta fuskar zaɓen kalmomin da suka dace da ke da dangantaka da juna tare
da tsara su wuri ɗaya cikin waƙarsu. Makaɗa Sa’idu Faru shi ne kan gaba a wannan fagen. Allah ya ba
shi basira da hikimar zaɓen kalmomi masu dangantaka da juna. Yakan kuma tsara su a
wuri ɗaya cikin waƙarsa. Misali, yana cewa:
Ihihiya da kunkuru shawara guda sukai.
Bushiya da beguwa shawara guda sukai.
Kurciya da hasbiya shawara guda sukai.
Bubukuwa da jinjimi shawara guda sukai.
(Sa’idu Faru: Waƙar Muhammadun
Muhammadu).
Ta la’akarida waɗannan ɗiyan waƙar za a ga cewa ya kawo jerin halittu da suke da dangantaka da juna ta siffofin
yanayin halittarsu.
5.1 Sakamakon Bincike
Daga abin da ya gabata dangane da wannan nazari, ya
fayyace mana tabbatuwar Makaɗa Sa’idu Faru a matsayin sahihantaccen makaɗin sarauta na gwadi
da ya tsayu wajen kiɗan sarauta da sarakuna a manyan gidaje sarauta har ma da ƙananansu da ke farfajiyar ƙasar Hausa. Sauye-sauye zamani da ɓullowar siyasar dimokuraɗiyya da kwaɗayin neman tara abin
duniya bai sa ya bar turbar iyaye da kakanni ba.
Irin wannan dogiya tasa, da ra’ayin mazan jiya sun bambanta shi da
takwarorinsa da suka yi zamani tare har ya zamanto bai taɓa yi wa wani mutun waƙa ba idan ba jinin sarauta ba ne. Hasali ma ko jinin
sarauta sai wanda ke riƙe da wani muƙamin sarautar gargajiya. Ya bambanta da mawaƙa irin su Alhaji Musa Ɗanƙwairo da suka kasance cikin zango guda da shi, wanda ya koma yana karɓar gayyatar jama’a
domin rera musu waƙoƙi.
Haka kuma, an fahimci sarakuna na rungume da makaɗansu ne sakamakon
yadda suke tsara musu waƙoƙi, wanda ke zama sanadin daɗa ɗaukakuwarsu a idon
duniya. Wannan kan auku ne, ta hanyar yadda makaɗan ke ambaton su da
kyawawan halaye da ɗabi’u, waɗanda kan fito da sunayensu fili fiye da kima. Da haka ne
sukan sami ƙwarin guiwar gudanar da harkokinsu na mulki ba tare da
kasala ko tsoro ba, sakamakon zuga da kirarin da mawaƙansu ke yi musu, tare da tunatar da su tarihin iyaye da
kakanninsu, musamman dangane da kyawawan halayensu kamar kyauta, haƙuri, ƙwazo da juriya.
5.2 Kammalawa
Waƙoƙin fada sun kasance wata maƙerar sarrafa harshe da luguden kalmomin fasaha. Haka
kuma, suna mazaunin wata makaranta da ke koyarwa ko cusa waɗansu halayen ƙwarai da kuma ƙarfafa guiwa ga waɗanda ake yi wa waƙoƙin, da ma sauran masu sauraro. A ɓangare guda kuwa, suna
da matsayin rumbun adana al’ada da tarihi. Makaɗa Sa’idu Faru ya
shahara a waɗannan lamura a matsayinsa na makaɗin fada na yankan
shakku. Hasali ma, shi ne babban misali lamba
ta ɗaya idan ana batun kiɗan sarauta.
Manazarta
Abba, M. da
Zulyadaini, B. (2000). Nazari Kan Waƙar
Baka Ta Hausa. Zaria: Gaskiya
Corpora-Tion LTD.
Abubakar, A.T. (2015). Ƙamusun
Harshen Hausa. Zaria: Northern
Nigerian Publishing Company Limited.
Ammani, M.C. (2019). Nazarin
Awon Baka Da Aiwatarwa Da Harshen A waƙoƙin Nafi’u Yakubu
Baba Katsina. Juzu’i
Na Biyu. (Ratayen Matanonin Waƙoƙin Da Aka Yi Nazari A Kansu). Kundin Bincike Da Aka
Gabatar Domin Cikasa wata Ƙa’ida Ta Neman Digiri Na Adabin Hausa, A Sashen Harsunan
Nijeriya Jami’ar Bayero Kano.
Bango, A. & King,
A.B. (1986). “ An Introduction to
Life and Works of Abubakar Akwara (C. –1876-1962)”. Seminer Paper. Zaria:
Ahmadu Bello University.
Bello, G. (1976). “Yabo, Zuga da Zambo a WaƘoƙin Sarauta”. Harsunan Nijeriya, Vol. VI: 21-34.
Bunza, A.M. (2009). Narambaɗa. Lagos: Ibrash Islamic Publication Centre LTD.
Bunza, A.M. (2014). In
Ba ka San Gari Ba Saurari Daka: Muryar Nazari Cikin Tafashen Gambo. Cairo: Elkods Printing House.
Ɗangambo, A. (1984 ). Rabe-Raben Adabin Hausa da Muhimmancinsa ga Rayuwar
Hausawa. Kano: Trimph.
Funtuwa, A.I. da
Gusau, S. M. (edt) (2011). Waƙoƙin Baka Na Hausa.
Kano: Century Research And Publishing Limited.
Gital, G. M. (1984). “Adabin Baka”. Maƙalar da aka gabatar a
Kwalejin Kimiyya da Fasaha, Bauchi.
Gusau, S. M. (1988). “Waƙoƙin Makaɗan Fada: Sigoginsu Da Yanayinsu, Musamman A Ƙasar Sakkwato. Juzi’i Na Ɗaya Da Sharhi. Kundin Binciken Da Aka Gabatar Domin Samun
Shaidar Digiri na Ɗaya.
Gusau, S. M. (1993). Jagoran
Nazarin Waƙar Baka. Kaduna: Fisbas
Media Services.
Gusau, S. M. (1996). Makaɗa Da Mawaƙan Hausa Na 1. Kaduna: Ɗab’in Fisbas Media Services.
Gusau, S. M. (2002). Salihu
JankiɗI Sarkin Taushi.
Kaduna: Baraka Publishes Limited.
Gusau, S. M. (2008). Waƙoƙin Baka A Ƙasar
Hausa: Yanaye-Yanayensu da Sigoginsu. Kano: Benchmark Publishers Limited.
Gusau, S. M. (2009). Diwanin
Waƙoƙin Baka: Zaɓaɓɓun Matanoni na WaƙoƘin Baka na Hausa.Kano: Century
Research and Publishing Limited.
Gusau, S. M (2011). Adabin
Hausa A Sauƙaƙe. Kano: Century
Research and Publishing Limited.
Gusau, S. M. (2014). Diwanin Waƙoƙin Baka, Juzu’i Na Biyu. Kano: Century Research and Publishing Limited.
Gusau, S. M. (2014). Waƙar Baka Bahaushiya (The Hausa Oral Song). Kano:
Published for Bay-Ero University.
Gusau, S. M. (2015). Audu
Karen Gusau. Kano: Century
Research and Publishing Limited.
Gusau, S. M. (2016). Makaɗa Da Mawaƙan Hausa.
Littafi Na Biyu. Kano: Century
Research and Publishing Limited.
Gusau, S. M. (2018). Diwanin Waƙoƙin Baka: Matanonin Wasu Waƙoƙin Alhaji (Dr.) Mamman Shata Katsina. Kano:
Century Research and Publishing Limited.
Gusau, S. M. (2019). Diwanin Waƙoƙin Baka, Juzu’i Na Huɗu: Wasu Waƙoƙin Alhaji Musa
Ɗankwairo Maradun
(1909-1991) Sarkin Kiɗan Sarkin Maradun Jahar Zamfara. Kano: Century Research and Publishing Limited.
Gusau, S. M. (2020). Diwanin Waƙoƙin Baka Juzu’i Na Biyar: Matanonin Wasu Zaɓaɓɓun Waƙoƙin Makaɗan Baka. Kano: K.d.G.
Ibrahim, M.S. (1983). Kowa Ya Sha Kiɗa. Ibadan: Longman Nigeria.
Sa’id, B (edt) (2006). Ƙamusun
Hausa. Kano: Cibiyar
Nazarin Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero.
Yahaya, A. B. (1997). Jigon Nazarin Waƙa. Kaduna: FISBAS MEDIA SERVICE.
Yahaya, A. B. (2001). Salo
Asirin Waƙa. Kaduna: FISBAS MEDIA
SERVICE.
[1]
Kotso abin kiɗa ne na makaɗan sarauta. Ya so ya yi kama da
kalangu, amma shi fuska ɗaya kawai ake rufewa, a kuma kaɗa shi da hannu. Sa’idu Faru yana daga cikin sahun makaɗan da suka fi gwanancewa wajen kiɗan kotso. Ƙwararru kuwa sun haɗa da Ibrahim Narambaɗa da Musa Ɗankwairo.
[2]
[Keɓantacciyar
tattaunawa I. Muhammad, 14 ga watan Yuli, 2024] (A lokacin yana matsayin Ɗanmadamin
Birnin Magaji)
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.