Citation: Musa, A. (2024). Nazarin Salon Kamance a Cikin Waƙoƙin Bawa Namiji Jega. Ginshiƙin Nazarin Salon Waƙoƙin Hausa, 308-314. www.doi.org/10.36349/djhs.2024.v03i01.038.
NAZARIN SALON KAMANCE A CIKIN WAƘOƘIN BAWA NAMIJI JEGA
Abbas Musa
Department of Nigerian Languages, Usmanu Danfodiyo
University, Sokoto
Tsakure:
Wannan
bincike mai taken 'Salon Kamance A Cikin Waƙoƙin Bawa Namiji Jega'.
Manufarsa ita ce nazarin waƙoƙin Bawa Namiji Jega don a fito da irin baiwa da
hikimomin da Allah ya ba shi waɗanda
yake amfani da su wajen shirya waƙoƙinsa. An bi hanyoyi guda biyu wajen tattara
binciken, wato yin hira da mawaƙin da kuma nazarin waƙoƙin. Bayan nazarin waƙoƙin
sakamakon ya nuna lallai akwai salailai na kamance a cikin waƙoƙin,
wanda ya rabu gida uku, wato salon kamancen fifiko, salon kamancen daidaito da
kuma salon kamancen kasawa, an yi sharhin salon da rabe-rabensa a cikin waƙoƙin.
Fitilun Kalmomi:
Bawa Namiji Jega, Baiwa, Hikima, Shirya Waƙa, Salailan Kamance
Gabatarwa
Allah mai hikima wadda ba ta misaltuwa
ya ƙagi halittu daban-daban, ya kuma hore
musu dabarun da za su yi amfani da hikimomi domin isar da saƙo. Daga cikin halittun Allah waɗanda
ke amfani da harshe da hikimomi daban-daban, akwai mawaƙa. Makaɗa da mawaƙa a ƙasar Hausa sun jima suna amfani da salailai daban-daban
wajen isar da saƙon waƙoƙin da suke
yi. Harshen waƙar baka ta
Hausa harshe ne da ake amfani da dabaru iri-iri wajen shirya waƙoƙin ta
la'akari da lokacin da ake shirya waƙoƙin. Harshen waƙa
cikakke ne, duk da wani lokaci yakan bauɗewa ƙa'ida sananniya ta nahawu. Akan shirya waƙoƙin baka na
Hausa bisa zubin kalmomi da jumloli dogaye ko gajeru. Masana suna ganin an fara
waƙoƙin
baka ne tun lokacin da aka samu hanyar yin farauta, sai kuma waƙar ta ƙara haɓaka
a lokacin da aka fara yaƙe-yaƙe. Daga cikin abubuwan da suka ƙara bunƙasa waƙar baka akwai sarauta da noma wanda akan yi wa sarakuna
da manoma. (Gusau: 2008). An jima ana yi wa sarakuna waƙa, daga nan kuma aka ɓullo
da yanayi na yi wa sauran jama'a masu sana'o'i daban-daban irin manoma, da masaƙa, da maƙera, da
masunta, da wanzamai. Har wayau an ci gaba da waƙoƙi waɗanda
ba na sana'a ba, kamar waƙoƙi na wasanni irin na tashe da waƙoƙin gaɗa
da waƙoƙin
yara maza da mata da sauran wasannin al'adun gargajiya. Saboda haka waƙoƙin da ake
samu daga bakin wasu makaɗan maza a yau, galibinsu suna da nason waƙoƙin da aka
yi ne lokacin yaƙe-yaƙen da aka yi a ƙasar
Hausa tun kafin zuwan Musulunci. Haka aka ci gaba da samun waƙoƙin har zuwa
yau da aka samu waƙoƙin bandiri da na fiyano da waƙoƙin talla da
ake yi wa kanfanoni ko masana'antu da sauransu.
Nazarin waƙa abu ne daɗaɗɗe wanda aka fara a lokacin da aka fara karatun darasin
Hausa a matsayin kwas a manyan makarantun gaba da sakandare har zuwa yau. An yi
nazarin waƙoƙi
daban-daban tun daga na baka zuwa rubutattun waƙoƙi, wanda
wasu sukan dubi tarihin mawaƙi da irin
waƙoƙinsa,
da nazarin zubi da tsarin waƙoƙi. Wasu
kuma sukan dubi waƙoƙin a yi nazarin salo daban-daban
da ake samu a cikin waƙoƙin. Wannan binciken kamar yadda
sunan ya bayyana an yi nazarin salon kamance a cikin waƙoƙin Bawa Namiji Jega, inda aka dubi dabarun daban-daban da mawaƙin ya yi amfani da su a cikin
mafi yawancin waƙoƙinsa. Makaɗa
kan ƙulla waƙoƙinsu a gida
kafin su je inda za su aiwatar da su. Amma galibi nan take suke shirya waƙoƙin, kuma
hikimomi da azancin waƙar da
salailain sukan zo musu ne a lokacin da suke rera waƙoƙin.Bawa
Namiji Jega mawaƙin waƙoƙin baka ne.
An kalli mafi yawan daga cikin waƙoƙinsa, aka yi ƙoƙari aka zaƙulo salon
kamance a ciki.
An kasa wannan aikin maƙala zuwa matakai huɗu kamar
haka; A mataki na wanda shi ne gabatarwa ga aikin gaba ɗaya,
sai mataki na biyu inda aka yi waiwaye a kan asalin Bawa Namiji Jega, sannan
kuma aka ci gaba a matakin da bayyana yadda waƙa take a wajen Bawa Namiji Jega, an rufe matakin da da
bayanin ire-iren waƙoƙin Bawa Namiji Jega inda aka bayyana turakun waƙoƙin. A
mataki na uku binciken ya dubi salon kamance da kashe-kashen salon kamance ta
yadda aka kawo misalai a cikin waƙoƙin Bawa Namiji Jega, an fara da salon kamancen daidaito,
salon kamancen fifiko ya biyo shi a baya, sannan aka rufe da salon kamancen
kasawa, sai mataki na huɗu wanda shi ne kammalawa a cikin maƙalar.
2.0 Asalin Bawa Namiji Jega Da Haihuwarsa
Mahaifan Bawa Namiji Jega, mutanen ƙasar Dumbegu ne, wani gari yamma daga garin Jega, daga
baya suka yi ƙaura suka
dawo Jega da zama, sunan mahaifinsa shi ne Umaru, magini ne sosai, har akan yi
masa kirari da "Ragi ma ci ƙasa ɗan
Bawa" mahaifiyarsa kuma sunanta Faɗimatu, amma
akan kira ta da Ma'inna, duk da cewa ko da Bawa ya tashi bai santa ba, wato ta
rasu a lokacin yana da ƙuruciya, ya
tashi ne a riƙon kishiyar
uwa. Saboda haka asalin sunan Bawa shi ne Musa ɗan
Umaru magini. Mahaifiyarsa kuwa sunanta Faɗimatu
Ma'inna.
An saka masa suna Bawa ne saboda yawan
wabi da mahaifiyarsa ta jima tana yi, wato ta jima tana haihuwar ‘ya’ya suna
mutuwa, to daga Bawa ne ‘ya’yanta suka fara tsayawa kuma shi ne na ƙarshe, daga kan shi, ba ta kuma haihuwa ba, Allah ya yi
mata rasuwa a lokacin yana da ƙananan
shekaru, domin ko sanin fuskar mahaifiyarsa bai yi ba. Asalin laƙabin Namiji da aka saka masa kuwa ya biyo bayan tallar
man kaɗe da ake ɗorawa yayunsa mata, a lokacin yana ƙuruciya sosai, sai ya matsa a kan sai ya bi su wajen
talla, kuma ya nace a kan sai an yi masa shiga irin tasu, wato a ɗaura
masa zani. Idan suka fara talla gidajen mutane, za a dube shi, sai a gan shi
kamar namiji amma kuma da shigar mata, wasu mutane sukan kasa haƙuri har sai sun tambaya, ko kuma su kwance zanin da ake ɗora
masa, to daga nan sai su gane ashe namiji ne, to daga nan sunan Namiji ya fara.
Kamar yadda Bawa Namiji Jega ya faɗa da bakinsa bisa ƙiyasi
an haife shi ne a shekara ta 1947. Bawa Namiji Jega ya zo ne bayan mahaifiyarsa
ta jima tana haihuwar ‘ya’ya suna mutuwa, daga kan Bawa ne ‘ya’yanta suka fara
tsayawa kuma a kan shi ne ta ƙare
haihuwa, domin ba ta jima da haihuwar shi ba, Allah ya yi mata rasuwa, kamar
yadda ya ce ko da ya tashi bai san mahaifiyarsa ba, ya tashi ne a riƙon kishiyar uwa. Bawa Namiji Jega, Allah cikin ikonsa ya
tayar da shi ne a cikin unguwar Birnin Yari, unguwa ce wadda ta tara mutane waɗanda
aka shede su da sana'o'i daban-daban masu ƙoƙarin neman
na kansu, mazansu da matansu. Rasuwar mahaifiya a irin yanayin da Bawa Namiji
Jega yake a ciki, ba abu ne mai sauƙi
ba, saboda haka Bawa Namiji Jega ya tashi cikin mutanen unguwa masu sana'o'i
daban-daban, kan haka ne ya tashi da sha'awar ɗibar
ƙasa da jakuna yana kai gidajen mutane
masu son gini suna biyan shi kuɗi. Saboda haka Bawa Namiji Jega ya tashi da karsashi da
neman na kai.
2.1 Waƙa A Wajen Bawa Namiji Jega
Bawa Namiji Jega ya fara wa tun lokacin
Sarkin Kabi Haruna Na Biyu, a lokacin ana yin gadar Jega, a shekarar 1963.
Daga cikin Injiniyoyin da suka yi aikin gadar Jega, waɗanda
yake iya tunawa akwai wasu Turawa, su ne:
"Kwana Da Hama"
"Ɗan'indiya".
Bawa Namiji Jega ya yi hayen waƙa ne, ba wai ya koya ne a wajen wani ba, ko ya gada,
kawai dai ya ji abubuwan suna zo masa ne.Ya ce idan ya tashi waƙa a lokacin basira ke zo masa. Bawa Namiji Jega tun yana
matashi yake waƙa, a
lokacin babu kayan sauti na ɗauka a cewarsa, sai dai ba zai tuna takamaimiyyar waƙar da ya fara yi ba. Sai dai yakan tuna wani ɗiyan
waƙa a cikin tsofaffin waƙoƙinsa inda a
ciki yake cewa:
Jagoro: "In mutum bai son ka ɗaga
mai,
Amshi: Zaman ƙiyayya ba shi da daɗi".
(Bawa Namiji Jega).
Da kuma wata waƙa
ta Sarkin Magina da ya yi wadda yake cewa a ciki:
Jagora: "In na fara waƙar sarkin magina,
Sarkin
maginanmu ya kai magini,
Ku zan lallaɓatai
ku bat takaratai,
Amshi: Don in mutum ya taɓa shi,
Shi ce ma ƙasa riƙe min waɗanga,
Ke ko katanga ki taushe waɗancan,
Kahin shigihwa ta aiko matacci".
(Bawa Namiji Jega: Waƙar
Sarkin Magina).
Bawa Namiji Jega bai gaji waƙa ba, hasalima su gidansu, gidan sarauta ne, wato sarautar
Ubandawakin Dumbegu, ke nan su gadonsu shi ne a kiɗa musu ba wai su yi wa wani ba, a cewarsa shaƙiyanci ya kai shi kiɗa.
Jagora: "Shalla barayak kaɗa,
Fadama da sanyi take,
Bawa ban gadi roƙo ba,
Ga shi yau
shi ni kai,
Harakag ga sai sa ido".
(Bawa Namiji Jega: Waƙar
Shalla).
Bawa yana amfani da abin kiɗa
da ake kira da suna 'Sheshe ko kuma Sarewa', da kuma'Gambara', sai dai wani
lokaci yakan taɓa amfani da kalangu idan zai yi
amfani da ‘yan amshi, duk da bai cika amfani da su ba, saboda da wuya a samu waƙoƙinsa da aka naɗa (Recording) waɗanda ya yi da kalangu. Bawa Namiji makaɗin jama'a ne.
3.0 Salon Kamance
Cikin wannan dabara akan kwatanta abubuwa biyu ko fiye masu
halayya iri daban-daban. (Ɗangambo,
2007:40).
Salon kamance shi ne, a yi ƙoƙarin fito
da ma’ana da manufar abin da ake misaltawa ko ake yabo ko kushewa a yi ƙoƙarin kwatanta shi ko kamanta shi da wani abin da ba shi ba.
(Bunza, 2014:69).
Salon kamance ɓangare ne na salon siffantawa,
salo ne da yake bayyana wani abu ta fuskar kwatanta shi da wani abu, ta hanyar
amfani da wasu kalmomi da aka aza kan mizani. (Yahya, 2016:90).
Kalmomin da ake amfani da su wajen kamance akwai: Tamkar,
kamar, awa, ka ce, ya zam, da dai sauransu. (Muhammad, 2019:48).
Salon kamance salo ne da marubuta ko mawaƙa ke amfani da shi wajen
kwatanta wasu abubuwa guda biyu. (Bunguɗu, 2022:120)
Salon kamance yana da ɓangare har guda uku kamar haka:
3.1 Salon Kamancen
Daidaito
Kamancen Daidaito: kamar yadda sunan ya nuna, salo ne da
mawaƙi ke amfani da shi wajen
kwatanta abubuwa biyu ta yadda mai sauraren waƙa zai ɗauke su a matsayi ɗaya. Salon kamancen daidaito yana da mizanan da ake gane shi
kamar haka:
Kamar, wa, i, ƙoƙa, ‘ya, ce, kake, da kuma daidai
da.
Yanzu za mu zo da misalai daban-daban da suka zo da kamance
na daidaito a cikin waƙoƙin Bawa Namiji Jega. Manufar
salon ita ce ya kawo maka hoton wani abu da ka sani ko hali ko siffarsa ko wani
abu da ya shafe shi, idan ya ƙare
kawo maka wannan abin, sai ya ce maka yadda ka san wancan abin, to haka abin da
wannan waƙa ke
bayani a kai yake. Wato salon kamance yakan siffanta maka abin da waƙa da wani abu daban da ya ɗauka ka sani, to sai ya ce maka to wancan abin da ka riga da
ka sani da wanda waƙa ke
magana a kai duk ɗaya suke ta wannan fuska. Misali:
Maza sun yo
kunnen doki,
Sun ce
Rambo na yag gilma,
Ɗan
sanda mai kayan aiki.
(Bawa Namiji Jega: Waƙar
Rambo).
A cikin wannan ɗan waƙa mawaƙin ya siffanta gudun da wasu
mutane suka yi a lokacin da suka ci karo da Rambo sai ga su aguje gudun da suke
yi a tare wato ba wanda ya tsere wani. Ke nan kamancen daidaito ya fito a wurin
da Bawa ya ambaci kunnen doki. Mizanin da aka samu a nan shi ne mizanin ‘daidai
da’ (kunnen doki)
Ga wani misali:
Ni na ga mazaizai sun sheƙo,
Kamam mota tah hau gero.
(Bawa Namiji Jega: Waƙar
Rambo).
A cikin wannan ɗan waƙa Bawa Namiji Jega ya siffanta
mana yadda aka yi wani gudun fitar rai, har aka tattake shukar da aka yi ta
gero da ƙafafu,
amma da aka duba geron ga shi nan kamar mota ce ta tattake shi. Kamancen
daidaito ya fito a inda Bawa ya ce ya ga mazaizai (maza) sun rugo da gudu sun
hau gero kamar hawan mota, ko kamar mota ta haushi ba mutane ba. Mizanin da aka
samu shi ne ‘kamar’.
Ga wani misali kuma:
Shekarar bana sai addu'a,
Kullum tsaba ƙari takai,
Kakab bana an yi kamar ba a yi
ba,
An kashe kuɗɗi an hau ƙaya,
An kashe gumbi an hau ƙaya,
Kullum tsaba ƙari takai,
Su ko zaurori na yawa,
Kakab bana an yi kamar ba a yi ba.
(Bawa Namiji Jega: Waƙar
Shekarar Bana Sai Addu'a).
A wannan ɗan waƙa cikin layi na uku, Bawa Namiji
Jega, ya kamanta kakar bana da cewa saboda rashin samun amfanin gona da yawa,
har ta zama kamar ma ba a yi damana ba. Wato damanar da rashin yin ta duk
daidai suke. Ya ƙara da
cewa yadda tsaba kullum ke ƙara
kuɗi tana hauhawa, har ma a yi
zaton bana kamar ba a yi damana ba, balle a yi shuka. A nan mawaƙin yana son ya isar da saƙon yadda ake cikin yanayi na
tsadar rayuwa da irin yadda wannan tsadar rayuwar ta mamaye, hatta tsabar da ke
yin sauƙi lokacin
kaka, amma saboda tsadar da tsabar ke yi, yana ji a jikinsa cewa kamar ma dai
ba a yi damana ba a bana. Kowace ma'ana aka ɗauka
a nan tana iya dacewa da abin da shi mawaƙin
ke nufi. Mizanin da aka samu shi ne ‘kamar’.
Hakama a waƙar
Tonton akwai wannan salo na kamancen daidaito wajen da yake cewa:
Ka ji kiɗin Tonton,
Shekarar bana ban iya ƙyalewa,
Tonton ga
dauri zumunci na,
Ga yanzu abin ga sana'a ta mun gane,
(Bawa Namiji Jega: Waƙar Tonton).
A wannan ɗan
waƙa Bawa Namiji Jega ya yi amfani da salo
wajen kamanta tonton da sana'a inda ya bayyana cewa duka daidai suke ba su da
wani bambanci. Tonton kamar yadda wasu sukan kira shi da "Watanda"
al'ada ce da mutane ke yi a lokacin Azumin Ramadan ana gab da a kammala azumi
kamar irin salla kafin kwana ɗaya ko biyu, sai a haɗa
kuɗi a sayi bajimin sa ko saniya a yanka a karkasa kowa ya
kwashi nashi kaso ta la'akari da kuɗin da ya
bayar. Ga alama Bawa Namiji Jega a wannan shekarar da ya yi waƙar bai ji daɗin yadda aka gudanar da rabon naman ba, a kan haka ne ya
kwatanta tonton na wannan lokaci da cewa ba su da wani bambanci da sana'ar fawa
wadda mahauta ke yi, wato tonton da sana’ar fawa daidai suke.Mizanin da ya fito
a wannan ɗan waƙar shi ne
‘daidai da’.
4.3.2.2
Salon Kamancen Fifiko
Kamar yadda sunan ya nuna, shi wannan
kamancen yakan ɗauki abubuwa guda biyu wato wanda yake ƙoƙarin ya
siffanta da kuma wanda shi ne ke ƙoƙarin ya siffanta na farko, wato sai ya ce wannan na farko
da aka kawo wanda aka riga da aka sani, to gwarzon da yake wa waƙa, to shi ne a gaba da wancan abin da ka sani. (Yahya,
2016: 94). Idan an lura banbancinsu da na daidaito shi ne, yayin da na daidaito
ke ƙoƙarin
daidaita darajar nashi gwarzon da abin da ka sani, to shi na fifiko yana ƙoƙarin ya
nuna maka cewa nashi gwarzon ya wuce wannan abin da ka sani.Yana da mizani
kamar haka: wuce, zarce, fi, take, gota, furce, tsere, da kuma ɗara.
Misali:
Kiɗin
ga na manya,
Tsalha ba na zama na ba,
Na kashe yawon dare don ba shi
da anhwani,
Yaro yaro na,
Yaro ka ji kiɗin algo,
Cikin magudana duka Kyasto ab babba.
(Bawa Namiji Jega: Waƙar
Algon).
A wannan waƙa
ta Algon a layi na shida kuma na ƙarshe,
Bawa Namiji Jega ya kamanta Kyasto da cewa cikin magudana duk ya wuce kowa, ba
wanda zai tsere mai, hasali ma shi ke gaban kowa, a wajen tsere. A nan Bawa
Namiji Jega yana son mai sauraren waƙar
ya ji a cikin ransa cewa Kyasto ya fi kowa gudu. Wannan gudu kuwa ba na komi ba
ne sai gudun ceton rai a lokacin da aka yi ido biyu da motar ‘yan sanda, wadda
Hausawa kan kira da 'Shiga-ba-biya'. Ita ce ake kira Algon musamman a lokacin
mulkin Adamu Aliero aka raba wa ‘yan sanda wannan motar saboda su riƙa yin sintiri suna kamun masu
kai dare a waje da kuma sauran masu laifi a cikin dare. Shi ne Bawa Namiji Jega
ya suranta cewa ga ‘yan sanda nan sun koro masu laifi, kuma Kyasto yana ciki,
kai shi ne ma a gaba. A nan salon fifiko ya fito, wanda ya fi, shi ne Kyasto,
waɗanda ya fiya, su ne sauran mutane masu gudu.
Haka kuma ya yi amfani da wannan salon na fifiko kamar haka:
Mai ginar
rijiya bai yi laihi ba,
Masu yason
ta sun hi jin daɗi,
Maƙiyinka in ka kiyaye shi,
Ya rabe giwa kana kallo,
Ka san da bai ‘yamma,
Shi masoyinka in ka laƙance shi,
In ya kama kusu shi na ‘yamma.
(Bawa Namiji Jega: Waƙar
‘Yan Kai Zakka).
A nan Bawa Namiji Jega, yana kamanta mai ginar rijiya da
cewa masu yason rijiyar sun fi shi jin daɗi, wato dai kamar yana son ya ce
ma, wanda ya wahala da wani abu, ba shi ne ke cin amfanin abin ba, cewa mai
yason rijiya ya fi mai ginar rijiya jin daɗi, salon kamancen fifiko ne,
wanda wannan salon ya fito ne a layi na biyu, inda Bawa ya ce sun hi jin daɗi. Wato mizianin ‘fi’ shi ne ya fito a nan.
Bawa ya ci gaba da kawo wannan salo a cikin wannan waƙar kamar haka:
Wani yaron
zamani na ga wautatai,
Matan mutum
ta hi Innatai,
Abokin
mutum ya hi Babanai,
Ga abokin
mutum na ta jin daɗi,
Ga ubanai
da yunwa yana kallo,
Yaron zamani ka yi hwaɗaɗɗa.
(Bawa Namiji Jega: Waƙar ‘Yan Kai Zakka).
Bawa Namiji Jega ya ci gaba da amfani
da kamancen fifiko inda ya kamanta matar wani yaron zamani da innar yaron
zamani da cewa ya fi darajanta mata a kan uwa, da kuma fifita aboki kan uba,
inda ya nuna cewa daga cikin haukar yaron zamani ita ce yakan fifita aboki a
kan mahaifinsa. An
samu abin da ake nema na kamancen fifiko har a layuka guda biyu, wato a layi na
biyu da kuma layi na uku. Mizanin da ya fito shi ne ‘hi’ wato ‘fi’
4.3.2.3 Salon Kamancen Kasawa
Wannan shi ne kashi na uku na salon
kamance. Da irin wannan salo mawaƙi yakan
kwatanta abubuwa biyu sai ya ce ɗaya bai kai ɗaya ba. (Yahya,2016:98). Wato abin da yake nunawa shi ne,
bayyana kasawar wani abu da aka san yana da daraja a gaban gwarzonsa wanda ya
fi shi. Salon yana da mizanan da ake gane shi kamar haka:
Gaza, kasa, wane, da kuma kalmomi masu
soke samuwar abu kamar bai. Akwai kuma kalmomi masu tambayar nuna kushewa kamar
ina ya yi…? Da ina zai kai?
Misali:
Allah
waddan ka daure,
Ka ba raggo
ɗiyakka,
Ka ɗauki buhu ka ba shi,
Gobe ka
koma bai,
Yau da gobe
wuya gare ta,
Kana amsat ɗiyakka,
Raggo bai da abki.
(Bawa Namiji Jega: Awwal Wa'u).
A wannan ɗan waƙa Bawa Namiji Jega ya yi amfani
da salon kamancen kasawa ta inda ya nuna halin raggo na rashin jajircewa ya ɗebe wa kansa takaici. Wato bai da wani amfani, sai dai
kullum shi so yake ya samu a banza, salon ya fito a layi na ƙarshe a cikin wannan ɗan waƙa
kamar yadda aka gani. Tabbas raggo ya kasa a nan, saboda ya zama cima kwance,
mai jiran a yi masa lalura, ba kamar sauran mutane da ke neman na kansu
ba.Mizanin da aka samu shi ne na sokewar samuwar auki ga raggo, wato mizanin
‘bai da’
Haka kuma akwai wannan salo a cikin wani ɗan waƙa
kamar haka:
Matsala
guda-guda,
Kowa tashi
ta i...,
Ga wani bai
da hankali,
Shi ma
tashi ta isai,
Wani ko
rashin kuɗi,
Shi ma tashi ta isai.
(Bawa Namiji Jega: Awwal Wa'u).
A wannan waƙa Bawa Namiji Jega ya yi amfani da salon kamancen kasawa
ta yadda ya nuna cewa ga wani daga cikin matsalar da ke damun shi, ita ce bai
da hankali, kore hankali ga abin kamance a nan, shi ne kasawa. Bawa ya nuna
fifikon da ke akwai tsakanin mai hankali da maras hankali (mahaukaci). A
nan ma mizanin da fito shi ne ‘bai da’.
Haka dai a cikin wannan waƙar aka koma samun salon kamancen kasawar kamar haka:
Ga ƙato cikin gari,
Amma babu ko ɗari,
Da inda yac ci shinkahwa,
Sai ya yarda roba,
Shi ko shi walwale,
Domin bai da ko ɗari.
(Bawa Namiji Jega: Waƙar Kowa Tashi Ta Isai)
A wannan ɗan
waƙa an koma amfani da salon kamancen
kasawa, inda aka yi amfani da mizanin kasawa na 'bai da' a cikin layi na biyu
da kuma na ƙarshe da aka ambata. Ta yadda aka
siffanta halin ƙato ta
yadda da ya ci abincin mutane sai ya jefar da robar abincin ya ruga da gudu
saboda bai da kuɗin biya. Babu shakka duk inda aka samu ƙato mai ƙarfi a jika
ya ci abincin sayarwa har ya jefar da abin da aka sa masa abinci sannan ya ruga
da gudu saboda rashin abin biya, kasawa ce kuma abin kunya ga kowane ƙato ba shi kaɗai ba. Ai
shi ne dalilin da Hausawa suka ba shi suna 'ƙaton banza' mai nufin kasasshe ko wanda ya kasa.Bawa ya
ci gaba da amfani da salon kasawar a cikin waƙar kamar haka:
Ruwan tulu
bai ɗai da na randa,
Ruwan tulu
bai ɗai da na randa,
Randa sa ƙwaryakka ka kwalhwa,
Tulu sai ka karkata baki.
(Bawa Namiji Jega: Waƙar
Gangab Bawa Tana Nan).
A nan ma idan aka lura Bawa Namiji Jega ya yi amfani da
salon kasawa, inda ya kwatanta tulu da randa, a ƙarshe sai ya bayyana kasawar tulu idan aka kwatanta shi da
randa. Ya yi amfani da mizanin 'bai' a layi na farko da kuma na biyu. Duk inda
aka gwama abu biyu aka ce ba ɗai suke ba, akwai tabbacin wani
ya kasa wani. Bawa na nufin ruwan da ke cikin tulu ba su kai na cikin randa sauƙin ɗiba ba. A nan buri ya cika tunda an gano cewa ruwan da ke
cikin randa sun fi na cikin tulu sauƙin
ɗiba, saboda randa ta fi tulu
babban baki. Ana iya ɗiban ruwan da ke cikin randa kai
tsaye ba tare da wahala ba. Su kuwa na tulu sai an karkata.Haka ma Bawa Namiji
Jega, ya ci gaba da amfani da salon kasawa kamar haka:
Allah shi
agaza,
Ɗankanoma sa ciyyon daji,
Su aka wa
talla,
Ciyyon tsuhwa bai da magani.
(Bawa Namiji Jega: Waƙar Zamani Mai Baƙaw
Wuya).
Kamar yadda aka gani Bawa Namiji Jega
ya koma amfani da salon kamancen kasawa ta inda ya kwatanta ciyon tsufa da
ciyon ɗankanoma da ciyon daji, sai ya bayyana cewa na tsufa bai
da magani, ya yi amfani da mizanin 'bai' wanda ke bayyana kasawar abin
kwatance. Babu tantama an saba da ganin mutanen da shekarunsu suka ja, wato
suka tsufa ake ci gaba da neman musu magani, har a kai lokacin da za su zama
yau ciwo gobe lafiya, kuma haka za a ci gaba da tafiya har a cim ma lokacin
mutuwa. A kan haka ne Bawa ya siffanta ciwon tsufa da cewa duk cikin cutukan da
mutane ke yi, ana iya ba su magani, amma shi ciwon tsufa bai da magani, shi ne
ma dalilin da ya sa ko tallar maganin ciwon ba a yi, sai dai a tallata ɗankanoma
da ciyon daji.Ya ci gaba da amfani da salon kasawa a cikin wata waƙa kamar haka:
Sussuka da
bara sana'a ta,
Mata ku riƙe taɓaryakku,
Sussuka da
bara sana'a ta,
Sata ab ba sana'a ba,
In kai sata a kama ka,
Ka sha kashi a ɗarme ka.
(Bawa Namiji Jega: Waƙar
‘Yan {aiƙai).
Bawa Namiji Jega, ya ci gaba da amfani da salon kamancen
kasawa a wannan waje a layi na huɗu inda ya kwatanta sata da
sana’ar sussuka, sai ya bayyana kasawar sata a kan sana'ar sussuka. A nan ma
Bawa Namiji Jega ya yi amfani da mizanin 'ba' ta yadda ya nuna kasawar sata a
matsayin ba sana'a ba ce idan aka kwatanta da sana'ar sussuka da mata ke yi.
Sana'ar sussuka sana'a ce da mata ke yi musamman idan aka kai ga kakar gero a
kowace shekara, inda ake yin jinga da su, su sussuke ko cashe damen gero, ko
maiwa ko dai wani nau'i na hatsi, ta yadda za su raba asalin tsabar da soshiya
daga dame ɗaya zuwa abin da ya samu, ƙarshe sai a biya su ladar aikin
da suka yi.Bawa Namiji Jega ya ci gaba da amfani da salon kamancen kasawa a
cikin waƙa kamar
haka:
Ka ji kiɗin tonton,
Harakab bana ta wuce ƙyalewa,
Wani tonton
ba tonton na ba,
Wallai twani suka tura ma ko ƙassa.
(Bawa Namiji Jega: Waƙar Tonton).
A wannan ɗan
waƙa Bawa Namiji Jega ya yi amfani da
salon kasawa a layi na uku inda ya kwatanta tonton guda biyu da wanda suka yi
da kuma wani wanda aka yi a wani waje, sai ya yi amfani da mizanin 'ba' na
kasawa, ya bayyana kasawar tonton ɗin da shi ya shiga, wanda ga alama bai yi masa daɗi
ba. Kamar yadda ya bayyana tonton ɗin da ya shiga tani da ƙassa aka ba shi.Bawa Namiji Jega ya ci gaba da amfani da
salon kamancen kasawa kamar haka:
Halinka ka
tara ma jama'a,
Halinka ka koraɗ ɗan'adam.
Duniya haka nan take,
Kowat taka sai ya gaza,
Ko ba mutuwa tsuhwa kakai.
(Bawa Namiji Jega: Waƙar
Ɗanjami'a).
A wannan ɗan waƙa Bawa Namiji Jega a layi na huɗu ya kwatanta halin mutum da zaman duniya da cewa duk yadda
ka yi sai ka gaza, ko dai ba ka mutu ba, to lallai za ka tsufa. Amfani da
mizanin 'gazawa' shi ya tabbatar mana da salon kasawa a nan, kamar yadda mawaƙin ya bayyana.
4.0 Kammalawa
A wannan maƙala an ga yadda wannan mawaƙi ya ci gajiyar harshe ya yi amfani da dabaru da hikimomi
daban-daban ya saƙa salailan
kamancen daidaito, fifiko da kumakasawa cikin waƙoƙin da ya yi
saboda isar da saƙon da ke
ciki. A maƙalar an ga yadda salo ke yin kwalliya
ga waƙa, kwatankwacin yadda gishiri ke gyaran
miya. Wato idan aka rasa salo cikin waƙa,
to kamar an rasa gishiri ne a cikin miya ko ma fiye da haka.
Manazarta
Bunza,
A.M. (2014). In Ba Ka San Gari Ba, Ka Saurari
Daka Muryar Nazari Cikin Tafashen Gambo. Cairo: Darul Ummah.
Bunguɗu, H.U.
(2020). Waƙoƙin Amali Sububu.
Kaduna: ADK Press, Murtala Muhammad Square.
Ɗangambo, A. (2007). Ɗaurayar Gadon Feɗe
Waƙa. Kaduna: Amana Publishers
Limited.
Gusau,
S.M. (2008). Waƙoƙin
Baka A ƙasar Hausa,
Yanaye-yanayensu Da Sigoginsu. Kano: Benchmark Publishers Limited.
Muhammad, S.S. (2019). Matakan Nazarin Rubutacciyar Waƙar Hausa. Zaria: Ahmadu Bello University
Press and publishers.
Yahya,
A.B. (2016). Salo Asirin Waƙa. Sokoto: Gruanty Printers.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.