Ticker

6/recent/ticker-posts

Yabo Fitilar Mawaka: Tsokaci Daga Wakokin Siyasa na Alhaji Kamilu Dan Almajirin Mawaka Nguru

Citation: Bashir, A.S., Halilu, S. and Sadiq, A. (2024). Yabo Fitilar Mawaƙa: Tsokaci Daga Waƙoƙin Siyasa na Alhaji Kamilu Dan Almajirin Mawaƙa Nguru. Ginshiƙin Nazarin Salon Waƙoƙin Hausa, 299-307. www.doi.org/10.36349/djhs.2024.v03i01.037.

YABO FITILAR MAWAƘA: TSOKACI DAGA WAƘOƘIN SIYASA NA ALHAJI KAMILU DAN ALMAJIRIN MAWAƘA NGURU

Akilu Suleiman Bashir
Department of Nigerian Languages
Federal University of Lafia, Nasarawa State

Shehu Halilu
Department of Hausa Language Education
Adamawa State Polytechnic, Yola

Abubakar Sadiq
Department of Hausa
College of Education, Zing, Taraba State

Tsakure:

Muhimmancin marubuta waƙoƙin Hausa a cikin al’umma ya fi gaban a bayyana, mutane ne da Allah ya yi wa baiwa da basira da ilimin sanin yadda zasu isar da saƙo ga jama’a ta hanyar waƙoƙinsu. Don haka wannan aikin an raɗa masa suna da “Yabo Fitilar Mawaƙa: Tsokaci Daga Waƙoƙin Siyasa Na Alhaji Kamilu Ɗan Almajirin Mawaƙa Nguru.” An yi ƙoƙarin nazarin yadda mawaƙin ya yi amfani da jigogin Yabo, a waƙoƙinsa na siyasa da aka nazarta. Binciken ya fito da jigogin yabo da yadda mawaƙin ya yi amfani da su domin isar da saƙoninsa, ga masu sauraro da kuma masu nazari. Dabarun da aka bi don gudanar da wannan aikin su ne, leƙa wasu Littattafai da Kundaye da kuma Maƙalu da suke da alaƙa da wannan aikin, haka kuma an tuntuɓi sha’irin dangane da waƙoƙinsa da aka yi amfani da su a wannan aikin. Manufar wannan aikin ne ya fito da hanyoyin da sha’irin yake bi, wajen yabon iyayen gidansa da ma jam’iyyar da ya ke yi wa waƙa. Aikin ya gano sha’irin ya yi amfani da kyawon hali, da jaruntaka, da riƙon amana, da asali, da kyauta, da iya mulki, da son jama’a,da kuma tausayi na gwanayen nasa wajen ya yaba musu.

Fitilun Kalmomi: Yabo, Fitila, Mawaƙa, Waƙoƙi, Siyasa

Gabatarwa

Ɗaya daga cikin hanyoyin da ɗan Adam yake more wa harshensa, shi ne furta kalamai ta sigar waƙa. Sauran hanyoyin kuma sun haɗa da wasa da kuma bayani a zube. A ƙasar Hausa amfani da waƙa domin isar da saƙo na addini ko na siyasa ko na wani abin da ya shafi rayuwa ba baƙon abu ba ne, musamman bayan zuwan Musulunci a cikin ƙarni na sha tara da na ashirin har ya zuwa yau (Idris 2010:1).

Waƙa a ƙasar Hausa, aba ce da ta jima sosai tana rayuwa tana bunƙasa har zuwa yau. A cikin ta ne mawaƙa ke bayyana alamurran da suka shafi rayuwar Hausawa wanda ya haɗada lele (yabo), ko faɗakarwa (ilmantar da al’umma). Waƙoƙin Alhaji Kamilu Dan Almajirin Mawaƙa, suna ɗauke da irin waɗannan jigogina yabo.Jigon yabo shi ne madubin dubawa a wannan makalar. Don haka ne, ake hasashen muƙalar ta share fage, ko kuma ta zamo ƙari, wanda aka ce ya fi ƙara a fagen karatu.

1.1 Taƙaitaccen Tarihin Alhaji Kamilu Ɗan Almajirin Mawaƙa Nguru

An haifi Kamilu Hussaini a shekarar 1980[1]a ƙauyen Beta, da ke Ƙaramar Hukumar Sumaila a jihar Kano a Tarayyar Nijeriya. Cikakken sunan shi ne Kamilu, amma sunansa na alkunya shi ne “Almajirin Mawaƙa”. Sunan mahaifinsa Malam Hussaini, wanda shi ne Na’ibin Limamin Masallacin Juma’a na ƙauyen Beta a wancan lokaci, kafin daga baya ya yi ƙaura zuwa Ƙaramar Hukumar Nguru da ke jihar Yobe.

Alhaji Kamilu yana ɗan shekara huɗu mahaifinsa ya tura shi Ƙaramar Hukumar Nguru, da ke jihar Yobe inda ya fara karatun Alƙur’ani mai girma a wurin Malam Sani Dogon Ƙwami. Bayan ya fara tasowa ne, sai ya shiga neman ilimin littattafai. Ya yi karatu a wurin Malam Hamidu da ke ƙauyen Mamuda a ƙasar Wudil da ke jihar Kano.Daga baya ya koma Ƙaramar Hukumar Nguru. Bayan ya ɗauki kamar shekara goma sha biyar, sai mahaifansa suka yi ƙaura suka koma Nguru.

A ɓangaren sana’a kuwa, bayan ya gama karatun Alƙur’ani mai tsarki da wasu littattafan Addinin Musulunci, sai ya fara sana’ar ɗinki, inda ya ƙware matuƙa, har ma yana da yara a ƙarƙashinsa. Ta fuskar waƙa kuwa, Kamilu taka-haye ya yi, domin bai gaje ta daga iyaye ba, sha’awa ce ta sanya shi fara waƙa, inda kuma ya fara a shekarar 2008, amma bai iya tuna waƙar da ya fara ba. Kamilu ya dai tabbatar da cewa, akwai waƙar da ta fito da shi duniya aka san shi, wato waƙar da ya yi mai taken “Kai Ka Zagi Bala”.

Bugu da ƙari, Kamilu ya bayyana cewa, waƙa ta yi masa riga da wando a rayuwa, domin a dalilinta sunansa ya ɗaukaka, ya je aikin hajji. Ya mallaki kayan more rayuwa na duniya. Yanzu haka shi ne mai kamfanin Beta Studio da ke kan kwanar Total, Titin Zoo Road, sannan yana zaune a Birnin Kano tare da iyalansa. Ya yi waƙoƙi da dama a ɓangarori daban-daban, amma sunansa ya fi shahara a ɓangaren waƙoƙin siyasa (Adamu, 2014).

1.2 Yabo

Ɗangulbi (2003) a cikin Suleiman (2017:81) cewa ya yi, “Yabo shi ne faɗar wasu abubuwa ko kalamai nagari game da wani mutum ko wata ƙungiya ta mutane waɗanda idan aka ji su za a so mutumin ko mutanen ko a ƙara ganin girmansa da ƙwarjininsa”.

Shi kuma Tsoho (2011:87) ya fassara yabo kamar haka “Yabo na nufin ba da shela mai kyau game da mutum bayan ya yi wani abin a yaba, na burgewa ko kuma ana so ya aikata abin burgewa ko na a yaba”.

CNHN (2006:476) Yabo faɗar wata kalma mai daɗi ga wani mutum da ya aikata wani kyakkyawan abu.

Yabo a cikin waƙar siyasa abu ne da ke da tasirin gaske, musamman wajen fito da kwarjinin ɗan takara, ko jam’iyya ga magoya bayansu. Wannan yabo da marubuta waƙoƙin siyasa ke amfani da shi cikin waƙoƙinsu, ya shafi ƙwarewa ga iya siyasa na wasu gaggan ‘yan siyasa da kuma irin ƙarfin da jam’iyya take da shi a cikin faɗin ƙasa. Haka kuma ana yaba wasu shugabannin jam’iyyu ko masu riƙe da muƙamai daban-daban a cikin majalisun ƙasa tun daga ƙananan hukumomi har zuwa kujerar shugaban ƙasa.

Mawaƙin ya yi amfani da jigon yabo a waƙoƙinsa da aka yi nazarinsu kamar haka:-

1.2.1 Yabon Jaruntaka

Jaruntaka itace aikata wani abu wanda ke buƙatar sadaukar da lafiya ko ma rayuwa. Dunfawa, (2011:136)

Sha’irin ya yi amfani da wannan dabara wajen yabon jigonsa a waƙarsa mai suna “Tilas Na Je Wajen Gwamnan Kebbi”. Ga abinda m ya ke cewa a wannan baitin

bt. 3: To yanzu zana fara bayani Gwamna da gaskiya ɗan Bagudu,

Tafiya da jarumi nasara da azaba da tsanani ba ya gudu,

Noman shinkafa a kwari yake dawa tafarnuwa kuma a tudu,

Na yi binkice na tarihin Kebbi kuka da tsamiya ba sa ƙaya.

(Kamilu Ɗan Almajirin Mawaƙa Nguru:Tilas Na Je Wajen Gwamnan Kebbi)

A wannan baiti bayyana jaruntakar Gwamnan jihar Kebbi Atiku Bagudu yake yi, cewa ya yi mutum ne da ba ya gudun talakawansa, duktsanani da azaba yana tare da su.

Ya sake amfani da yabon jarumtaka a waƙarsa mai taken “Taraba Mutanenka Ne”. inda yake yabawa wani ɗan takaran kujerar gwamna a jihar Taraba. Ga abinda mawaƙin yake cewa a wannan baiti

bt. 7: Komai ya faɗa munafuki wancan gaibu ne,

‘Yan uwa kad da mu bi shi masu ƙarya a Taraba ne,

Miƙe gaba jarumi ka bar wancan tsugune,

Ina Contact zo ka ja mu don kai mai son mu ne,

Lema mun bar ta tun da dai layin tsubbu ne,

Akwai magana ta da na faɗa kalma a bayyane,

Waɗancan mu guje su tun da ‘yan gizo da ƙoƙi ne,

Idan shari’a ta fito a adalcin kotu ne,

 Sani Ɗanladi jarumi kai dodonsu ne.

(Kamilu Ɗan Almajirin Mawaƙa Nguru: Taraba Mutanenka Ne)

A wannan baitin yabon wani ɗan takaran kujerar gwamnan jihar Taraba yake yi, dangane da jaruntakarsa. Da farko kira ya yi wa talakawan jihar Taraba, da kada su amince abokin adawarsu,sai ya nuna cewa gwaninsa jarumi ne don haka shi ne a gaba, abokan adawa na baya. Bai tsaya a nan ba sai ya danganta abokan hamayyarsu da gizo da ƙoƙi wato marasa gaskiya ga zalunci da ha’inci da yaudara da sata da wayo da sauransu kamar yadda aka san halayen gizo a tatsuniyoyi.

1.2.2 Yabon Riƙon Amana

CNHN (2006:15), an bayyanaamana da cewa, ba mutum ajiyar kaya ko wani abu yadda zai adana shi kamar nasa ba tare da wani abu ya salwanta, ko wani abu ya same shi ba.

Riƙon amana wani ginshiƙi ne na ginuwar al’umma, kuma shi ya sa Bahaushe yake ƙarin tabbatar da muhimmancinsa a cikin zukatan mutane. Mawallafa waƙoƙin siyasa kan yi amfani da wannan dabarar wajen yabon gwaninsu su nuna wa talakawa cewa yana da riƙon amana don haka a zaɓe shi.

Don haka, Mawaƙin ya yi amfani da wannan dabararwajen yabon wasu gwanayensa kamar yadda aka tsinto a cikin wasu baitocin waƙoƙinsa kamar haka:

An sami yabon riƙon amana a waƙarsa da ya raɗa wa suna “Mai Mala Buni”. Ga abinda sha’irin yake cewa a wannan baiti:

bt. 21: A cikin waƙar ni ko ban kai caffa ba,

Ban waƙo Oga mai rigar aiki ba,

Buhari wurin aiki bai san ganda ba,

Tun sanda yana Gwamna bai yo sata ba,

Har ya zo PTF bai ha’inci ba,

Bai kwashe kuɗin people ya kai Landon ba,

Buhari ina kishinka fasihi babba,

Ban bar bodin mota in hau taya ba,

Ban bar bin Tarakta in bi fatanya ba,

Domin burina ne nai noma babba,

Duk wanda yake kishi bai bar Janaral ba,

Ga APC Maja ba mu je lema.

(Kamilu Ɗan Almajirin Mawaƙa Nguru: Mai Mala Buni)

A wannan baiti, marubucin yabon Janaral Buhari game da riƙon amanar jiha, a matsayinsa na gwamna bai ci amana ba, bai saci kuɗin jihar ba, bai taɓa dukiyar da aka ba shi don amfanin jiharsa ba. Sai sha’irin ya ƙara bayyanawa talakawa a Hukumar Tattara Rarar Man Fetur (Petroleum Trust Fund) da ya shugabanta bai yi ha’inci ba. Har ila yau, bai saci kuɗaɗen jama’a ya kai ƙasar Landan don ya ɓoye ba kamar yadda wasu mahukunta suke yi. Daga ƙarshe sai ya yi kira ga talakawa da su shigo jam’iyyar APC.

1.2.3 Yabon Asali

Asali na nufin “Mafari ko tushe ko salsala”. CNHN, (2006:20). Sanin asali ya sa kare cin alli in ji Hausawa. Mawaƙan siyasa kan yi amfani da asalin gwanayensu ko jigoginsu su yaba musu. Wani lokaci har hannunka-mai-sanda suke yi wa abokan adawa, su kushe su ko su ɓata su a idon talakawa.

Sha’irin ya yi amfani da mafarin gwaninsa ya yaba masa, an sami hakan a wataw aƙarsa mai taken “Mai Mala Buni”. Ga abin da ya ce a wannan baiti:

bt. 18 Mu je Kano Kwankwaso jijiyar Arewanmu ne,

Rabi’u Musa mai tallafin mutanenmu ne,

Yana da aiki mai agajin mutanensa ne,

Hasken Kano fes fes fes dukka don kulawarsa ne,

Ɗan Agalawa Nasiru ma masoyinsa ne,

Mala’iku sun shaida Nasiru masoyinsa ne,

Chairman na CRC ɗan garin Kanon Dabo ne,

Da shi da Gwamna asalinsu ‘yan Kanon Dabo ne,

Rabi’u Musa Dodo a ɓangaren Duna ne,

A binkito asali Duna ɗan mutan Chadi ne,

Komai ya ce kar da ku ji shi zantukan gaibu ne,

Rannan mutanen Jamaina sun faɗi nasu ne,

Shi dai ya samu kuɗi ko gaban su Fir’auna ne,

Tun ma ina yaro can a baya mai babu ne,

Akwai matsawa bai gode wahidun rabbu ba.

(Kamilu Ɗan Almajirin Mawaƙa Nguru: Mai Mala Buni)

A wannan baiti bayan yabon Gwamna Kano Rabi’u Musa Kwankwaso da ya yi, dangane da irin tallafawa talakawa da yake yi. Bayan haka, ya bayyana yadda gwamnan ya gyara garin Kano fes-fes. Sai ya koma yabon Nasiru Gawuna da Gwamna Rabi’u Musa Kwankwaso kasancewarsu ‘yan asalin jihar Kano ne. Mawaƙin bai tsaya a nan ba, sai ya yi wa zambo ga abokin hamayyarsu, ya kira shi da Duna[2] sai ya ƙara da cewa in an bincika asalin abokin adawan nasu ba ɗan Nijeriya ba ne, ɗan ƙasar Chadi ne ba ɗan Najeriya ba ne, uwa uba ba ɗan asalin jihar Kano ba ne. Daga nan sai ya ƙara da cewa ya ma ji mutanen Jamaina ma sun ce ɗan garinsu ne.

1.2.4 Yabon Kyauta

CNHN (2006:27) an bayyana kyauta ta fuskoki guda biyu:

a.  Kyauta bai wa mutum wani abu don ra’ayi ba tare da ya yi wani aiki ba

b.  Kyauta yin abin kirki

Hausawa sun ce “yaba kyauta tukuici”. Yin godiya domin kyautar da aka yi wamawaƙi ba ƙaramin abu ba ne, ganin duk wanda yaba da kyauta yana duban godiya ta biyo baya. Rashin yin godiya ga kyautar da mutum ya yi kan haddasa yankewar wannan kyauta daga lokacin da aka ba da ita. Yin godiya ga kyauta naƙara jawo kyautar da ta fi ta farko. Marubuta waƙoƙin siyasa kanyaba wani jigo ko ɗan takara ta hanyar amfani da irin kyautar da yake yi wa jama’a. Baya ga haka, sai su nuna wa talakawa irin halin kirki da jigon ko ɗan takaran yake da shi don su amince da shi kuma su zaɓe shi.

A waƙarsa mai taken “Tilas Na Je Wajen Gwamnan Kebbi”. Ga abin da yake cewa a wannan baiti dangane da halin kyautar ubangidansa

bt. 21: Tun can a baya ba ka da rowa duk wanda ya taho samu shi ke,

Fannin tsaro fa kun inganta people cika sahun sallah ake,

Duk san da ka taho jarman Kebbi Gwamna a gaskiya murna shi ke,

Na Janar Buhari nagode maka gwanda da kankana nai inkiya.

(Kamilu Ɗan Almajirin Mawaƙa Nguru: Tilas Na Je Wajen Gwamnan Kebbi)

A wannan baiti mawaƙinna yabawagwamnan Jihar Kebbi Atiku Bagudu dangane da irin kyautar da yake yi, inda ya nuna cewa haka gwanin nasa yake tun a can baya bai da rowa kowa ya zo wurinsa da buƙata yana biya masa, don haka sai ya yaba da wannan hali na kyauta.

An sake samun wasu kyawawan misalai na yabon kyauta a waƙarsa mai taken “Sanata Ahmed Lawan Ka Burge Ni”.Ga abin da yake cewa a waɗannan baitocin:

bt. 11: Ka raba Firiji da yawa Sanata ɗan yankina,

Sannan keken ɗinki jama’a mun amfana,

A ba ka mota da kuɗin taya sai Sanatana,

Ana ta min surutai wai ba ka ban mota ba.

bt. 12: Kyautar Injin bayi ka raba don su manoma,

Jama’a sun yi ta tafi Sanata sun gode ma,

Almakashi mai kaifi ba ya shakkun suma,

 Wannan wani ɗan saƙo na yi ba wai zagi ba.

bt. 13: Motoci na ambulance Sanata kai ta raba su,

Transformer birni ƙauye ka miƙa su,

Injin murza taliya ka raba kuma mun gamsu,

 Senate President Ahmad kai ba ka san rowa ba.

bt. 14: Haka kyautar jari ma Sanata ya ba da shi,

Yunwa ta kauce kowa na kwanan ƙoshi,

Ba mai kushe Sanata sai mai halin ƙyashi,

 Alkhairi danƙo ne ni ba zan ƙi hwaɗi ba.

(Kamilu Ɗan Almajirin Mawaƙa Nguru: Sanata Ahmed Lawan Ka Burge Ni)

Daga baiti na 11-14 duk yabonirin kyaututtukan da gwaninsa ya yi ne, ya ba da kyautar Firiji, da kekunan ɗinki, da motoci har da kuɗin sayan tayoyi na motocin, da injuan bayi ga manoma. Har ila yau, a baiti na 13 sha’irin ya ƙara da cewa Ɗan Majalisar yaba da kyautar motoci na ɗaukar marasa lafiya da transfomomi a ƙauyuka da birane don inganta hasken wutan lantarki da injin murza taliya daga ƙarshe har da kyautar Jari ga talakawa don su bunƙasa kasuwancinsu.

An sake samun wani kyakkyawan misali na yabon kyauta da sha’irin ya yi amfani da shi a wata waƙarsa mai taken “Ruwa Baba”. Ga abinda ya ce a wannan baitin:

bt. 18 Ina ta yin kiɗi na ajiye garkuwata

Mairiga zan kirawo Chairlady ta mata,

Kyauta kuke biɗa ga ku amana ta mata,

Mairiga ‘yar halali take ta samu gata,

Ta ba ni raguna nai yi haƙiƙa na suna.

(Kamilu Ɗan Almajirin Mawaƙa Nguru: Ruwa Baba)

A wannan baitin mawallafin na yabawa da kyautar da gwanarsa Mairiga Chairlady ta jam’iyyar APC ta jihar Yobe dangane da kyautar raguna da ta ba shi waɗanda ya yi amfani da su a wajen raɗin suna.

1.2.5 Yabon Kyawon Hali

Kyawon hali shi ne kasancewar mutum managarci. Dayawa mawaƙan siyasa kan dangantakyawon hali ga wanda suke wa waƙa ko da kuwa sun san bai wannan halin domin su daɗaɗawa masu jefa ƙuri’a su so shi har ya kai ga su zaɓe shi Dunfawa (2013) a cikin Suleiman (2017:97)

Marubuta waƙoƙin siyasa kan yi amfani da kyawon halin ɗan takara ko wani gwaninsu su yaba masa don ganin ya samu karɓuwa a wurin talakawa. Sha’irin ya yi amfani da wannan dabarar kyawon hali ya tallata wani ɗan takarar kujerar gwamna a jihar Taraba.

An ga hakan a wata waƙarsa mai suna ‘Taraba Mutanenka Ne”. Ga abin da yake cewa a wannan baitin:

bt. 3: Mun yaba halinka san da kai gwamna tuntuni,

A ɗau alƙawari a kammala wannan sai gwani,

Mu je Contact namu ba zama za ka yi gefe ba.

(Kamilu Ɗan Almajirin Mawaƙa: Taraba Mutanenka Ne)

A wannan baitin yabon kyawon halin ɗan takaran yake saboda cika alƙawari da ya ke yi, “Alƙawari kaya ne" in ji masu iya magana.A duk inda aka sami mutum mai cika alƙawari dole ne ya sami tagomashi a wajen jama’a. Cika alƙawari hali ne mai kyau ga ‘yan takara, mai wannan hali dole ne ya sami gurbin zama a zuciyar talakawansa.

Sha’irin ya sake amfani da wannan hanya ta yabon kyawon hali ya yaba wagwamnan jihar Yobe a wata waƙarsa mai suna “Ruwa Baba”. Ga abin da ya ce a wannan baiti:

bt. 9: Gwamna na Yobe ya sami wadata ta zuci,

Oga Burabura ba shi da harkar ƙaranci,

Gaba dai Burabura ka yi gaban masu ƙunci,

Gaba dai Burabura ja mu mu je mai azanci,

Fara gare ta gashi na biɗa ba jini ba.

(Kamilu Ɗan Almajirin Mawaƙa Nguru: Ruwa Baba)

A wannan baiti yabon kyawon halin gwamnan jihar Yobe yake yi saboda wadatar zuci da Allah ya ba shi, ga shi kuma bai da ƙaranci a rayuwarsa. Don haka mawaƙin yana shaida wa talakawan jihar Yobe sun yi dace domin gwaninsa yana da wadatar zuci kuma ba shi da harkar ƙaranci.

1.2.6 Yabon Iya Mulki

CNHN (2006:350) an bayyana mulki da cewa gudanar da harkokin hukuma kan jama’a. Harkokin hukuma kuwa sun ƙunshi biyan ma’aikata albashi, da alawus-alawus nasu, a kan lokaci da samar da tsaftaccen ruwan sha, da samar da tsaro ga mutane da dukiyoyinsu da dabbobi da giggina hanyoyin mota da gina makarantu da asibitoci da sauransu. Marubuta waƙoƙin siyasa kan yaba wani ko wata jigo da suke wa waƙa ta fuskar iya mulki a wasu lokutan ma sukan nuna babu wanda ya fi su iya mulki.

Sha’irin a wannan hanyar ma, ba a bar shi a baya ba, wajen amfani da wannan dabarar wajen yabon gwaninsa ta fuskar iya mulki.

An ga misali yadda ya yi amfani da yabon iya mulki a waƙarsa mai taken “Tilas Na Je Wajen Gwamnan Kebbi”. Ga abin da ya ce a wannan baitin:

bt. 21: Tun can a baya ba ka da rowa duk wanda ya taho samu shi ke,

Fannin tsaro fa kun inganta people cika sahun sallah ake,

Duk san da ka taho jarman Kebbi Gwamna a gaskiya murna shi ke,

Na janar Buhari na gode maka gwanda da kankana nai inkiya.

(Kamilu Ɗan Almajirin Mawaƙa Nguru: Tilas Na Je Wajen Gwamnan Kebbi)

Ganin yadda ‘yan bindiga da ɓarayin daji da kuma boko haram, suka hana wasu ɓangarenjihohin arewa rawar gaban hantsi, jihar Kebbi tana ɗaya daga cikin jihohin da abin ya shafa. Akwai wani lokaci da ya kai  ga mutane sun daina zuwa masallatai don yin sallah a cikin jam’i saboda tsoron ‘yan ta’adda. Sai ga shi yau Gwamnan ya samar da tsaro, don haka a wannan baitin sha’irin na yabon salon iya mulkin Gwamnan ne, domin ya samar da tsaro, har ya kai ga mutane na cika sahun sallah a masallatai kamar yadda sha’irin ya bayyana a baitin.

Mawaƙin ya sake kawo wasu kyawawan misalai na yabon iya mulki a waƙarsa mai taken “Tilas Na Je Wajen Gwamnan Kebbi”. Ga abinda yake cewa a waɗannan baitocin kamar haka:

bt. 17: Fannin ruwa a nan a jihar Kebbi Gwamnanmu ya yi halin a yaba,

Tsabar ruwa a daji da gari bishiyar lafa ta dawo goruba,

Ba mu ruwa dai Baba na Bagudu mu ko mu ɗau maƙunshi mu zuba,

Koyaushe dai cikin tsabta muke ba ma sayan ruwa tun bariya.

bt. 18: Fanni na kasuwanci ‘yan Kebbi gwamnanmu gaskiya sai addu’a,

Ba wanda ke zuwa ci-rani a Legas biɗar kuɗi ba ya zuwa,

Tattali na arziƙi a jihar Kebbi Gwamna da ka taho ya hauhawa,

Sayayya mu je mu Birni a Kebbi hajarsu tahi daɗin tahiya.

bt. 19: Inganta lahiya mun shaida harkar tsaro cikin tsari muke,

Asibitoci ma na jihar Kebbi koyaushe duk cikin tsabta suke,

Yara ƙanana an yahe musu ba a biɗar kuɗi aiki ake,

People a gaskiya mun ƙaru da gwamanmu ɗan ƙwarai namijin jiya.

bt. 21: Tun can a baya ba ka da rowa duk wanda ya taho samu shi ke,

Fannin tsaro fa kun inganta people cika sahun sallah ake,

Duk san da ka taho jarman Kebbi Gwamna a gaskiya murna shi ke,

Na Janar Buhari nagode maka gwanda da kankana nai inkiya.

(Kamilu Ɗan Almajirin Mawaƙa Nguru: Tilas Na Je Wajen Gwamnan Kebbi)

A cikin waɗannan baitoci, mawaƙin ya fito da kyawawan ayyuka da gwamnaAtiku Bagudu na jihar Kebbi ya yi. Ya samar da tsaftaccen ruwan sha, ya inganta kasuwanci, ‘yan jihar sun daina zuwa ci-rani a jihar legas sai ya ƙara da cewa tattalin arziƙin ya haɓaka. Ya inganta kiwon lafiya da harkar tsaro, an tsaftace asibitoci, ana bai wa yara ƙanana magunguna kyauta a jihar Kebbi. A ƙarshe ya nuna iya mulkin jigon nasa ne yau jihar Kebbi ta sami kyakkyawar tsaro.

Har ila yau, mawaƙin ya sake yaba wa gwamnan Kebbi dangane da salon iya mulkinsa a waƙarsa mai taken “Gaskiya Dokin Ƙarfe”. Ga abin da yake cewa a waɗannan baitoci;

bt. 12: Mai gaskiya ɗan Bagudu Gwamnan Kebbi ka ji masoyinmu,

Burinsa aiki Gwamna ya ce kar a watsa kuɗaɗenmu,

Da hawansa ya zaga ya ga tsarin karkara da biranenmu,

Burinsa Gwamnan jahar Kebbi ne ya ga ko’ina ta ƙasaita.

bt. 13 Kebbi ƙwarai ta ƙasaita,

Batu na tsaro ya daidaita,

Harkar noma ta inganta,

Ga motocin tarakta,

Batun sufuri ya inganta,

Ga nan sabbin kwanfuta,

Ga hanyar tafiyar mota,

Kiwon lafiya ya inganta,

Batun ilimi ya inganta,

Dukkan makarantu na tsabta,

Bagudu sam ba ya sata,

Ga taimakon jama’a fata,

Dubu biyu sha tara ga nata,

Mun yarje mun lamunta,

Bagudu kai ka fi cancanta.

(Kamilu Ɗan Almajirin Mawaƙa Nguru: Gaskiya Dokin Ƙarfe)

A waɗannan baitocin sha’irin na yaba wa gwamnan Kebbi Atiku Bagudu wajen salon iya mulki. Bayan da ya bayyana burin gwamnan na yin aikin ci gaba a jihar da hawansa kan ƙaragar mulki, abin da ya fara yi shi ne, ya zaga birane da karkara don ya ga yadda zai inganta su. A  baiti na 13 sha’irin ya lissafo ayyukan da gwamnan ya yi. Yanzu jiharta ƙasaita ya inganta tsaro, ya inganta harkar noma, ya samar da motocin tarakta ga manoma, ya inganta harkar sufuri, ya samar da sabbin kwanfutoci, ya inganta harkar noma, ya inganta harkar kiwon lafiya. Har ila yau,ya inganta harkar ilimi, an tsaftace makarantu. Daga ƙarshe sai ya shelantawa talakawa gwanin nasa ba ya sata, ga shi da taimakon jama’a. Sai ya shaida wa gwamnan talakawa sun amince da shi, sun yarda ya zarce da mulki a zaɓen shekara ta dubu biyu da sha tara.

1.2.7 Yabon Son Jama’a

CNHN (2006:397) an kawo ma’anar so ta hanyoyi guda biyu kamar haka;

-  Buƙata ko ƙauna ko shauƙi ko niyya

- Buƙaci ko ƙaunaci ko ɗaura niyya

Zulyadaini da wasu (2000) a cikin Suleiman (2017:113) an nuna cewa, a duk lokacin da Ubangiji ya haɗa jinin mutane biyu, to farkon abin dakan fara aukuwa shi ne, mutanen kan kasance marasa ganin ƙyashin komai a junansu. Saboda haka, za a tarar kowa yana iya ba wa ɗan uwansa duk wani abin da ya san zai iya faranta masa zuciya. Mawaƙan siyasa su ma ba a bar su a bayaba wajen amfanida wannan dabarar a waƙoƙinsu

An sami misali na yabon son jama’a a wata waƙarsa mai taken “Na Je Buni”. Ga abinda marubucin ya ce a baitin da ke ƙasa:

bt. 1: Kowa ya yi ƙarya a ƙasarmu walla za ya yi dakuwa,

Da mu da Baba masoyinmu walla ba ma rabuwa,

Ko an hana mu mu zaɓe shi aiko ba ma hanuwa.

(Kamilu Ɗan Almajirin Mawaƙa Nguru: Na Je Buni)

A wannan baitin sha’irin na shelantawa wani ɗan takarar kujerar gwamna a jihar Yobe yadda talakawa ke son sa, ya bayyana masa cewa da su da masoyinsu ba su rabuwa, ko da an hana su zaɓen shi ba za su hannu ba.

1.2.8 Yabon Tausayi

Jin ƙayi ko nuna damuwa kana bin da ya samu wani na rashin jin daɗi shi ake nufi da tausayi kamar yadda ya zo a cikin CNHN (2006:434)

Mawaƙan siyasa kan yi amfani da tausayawa da jigonsu yake da shi ga talakawa su yaba masa a waƙoƙinsu kamar yadda wannan sha’irin ya yi amfani da wannan dabarar a waƙoƙinsa.

An sami wannan misali da Sha’irin  ya yi amfani da yabon tausayi da jigonsa yake da shi a waƙarsa mai taken Sanata Bangon Madara” Ga abin da ya ce a wannan baitin.

bt.1: Tuƙin tuwo na gayya da ma in za a zuba sai dai masaƙi,

Magana a wajen jama’a da yawa wata tai shuɗi wata ta yi baƙi,

In ka ji ana magana ta naɗi ƙarshe za a yi sabon sarki,

Tausayi da kulawa shi na tuno Ahmad Sanata gatan kowa.

(Kamilu Ɗan Almajirin Mawaƙa Nguru: Sanata Bangon Madara)

A wannan baiti yabon ɗan Majalisar Dattawa Sanata Ahmad Lawan yake yi dangane da halinsa na tausayi da kulawa da talakawa kamar yadda ya faɗa a baitin.

1.2.9 Yabon Alƙawari

CNHN (2006:13) an bayyana alƙawari da ambaton nufin yin wani abu ko niyya.

Alƙawari wani babban al’amari ne wanda siyasa ta gada shi ne ɗaukar alƙawura ga jama’a na irin kyawawan ayyuka da za su yi matuƙar an zaɓe su. Yawanci akan dubi abubuwa da suka fi ci ma talakawa tuwo a ƙwarya ne a ce da zarar an kafa gwamnati, za a gaggauta magance musu waɗannan matsaloli. Alƙawuran da ‘yan siyasa suka fi ɗauka su ne kyautata harkokin ilimi da lafiya da al’amurran noma da abin da ya shafi muhalli da ayyukan yi da al’amuran da suka shafi addini irin su aikin Hajji da ƙaddamar da shari’a da ayyukan gayya da sauransu.

Marubuta waƙoƙin siyasa kan yi amfani da alƙawura da gwanayensu ko da jam’iyya ta ɗauka su yaba musu da waɗannan alƙawura nasu don mutanesu so su. Hakan ya sa wannan sha’irinyin amfani da wannan dabarar kamar yadda za mu gani a waɗannan baitocin a waƙarsa mai taken ‘Bana Runhu An Yi Furen Banza”. Ga abin da yake cewa a waɗannan baitocin:

bt.11: APC in ta hau mulki za ta gyaggyara mu mu san dama,

Taki da iri ta raba kyauta don inganta mu batun noma,

Ilimi kyauta da wutar NEPA APC ka yi a bar nema,

Bore hole bore hole ta gina da yawa don inganta mu batu na ruwa.

bt. 12: Kulil haƙƙa walau kana murran gaskiya mai maganin ƙarya,

Burin APC ta yi aiki manufar jaki ya ɗau kaya,

Jama’a a gare ku na yi kira ga kanya kar ku ɗau ɗinya,

Shawara zan ba ku yayuna Hausawa duk da Yarbawa.

(Kamilu Ɗan Almajirin Mawaƙa Nguru: Bana Runhu An Yi Furen Banza)

A waɗannan baitocin Sha’irin na yabon kyawawan alƙawura da jam’iyyar APC ta ɗauka wa talakawa har idan ta ci zaɓe, ya ce, jam’iyyar tana da burin gyaran ƙasa, za ta samar da taki da irin noma kyauta ga manoma don inganta harkar noma. Har wa yau zata ba da ilimi da samar da hasken wutar NEPA kyauta, kuma zata samar da tsaftataccen ruwan sha.

2.0 Kammalawa

Wannan muƙala wani yunƙuri ne na hasko yadda Alhaji Kamilu Ɗan Almajirin Mawaƙa Nguru yake Yabo, a wasu waƙoƙinsa na siyasa. Takarda ta fito da jigogin yabo kamar yadda mawaƙin ya yi amfani da su domin isar da saƙo ga mai sauraro da nazari waƙoƙinsa. Wannan takarda ta bayyana ma’anar yabo sannan takawo ire-irensa tare da misalai daga baitocin waƙoƙin sha’irin. Aikin ya gano sha’irin yakan yi amfani da kyawon hali, da jaruntaka, da riƙon amana, da asali, da kyauta, da iya mulki, da son jama’a,da kuma tausayi na gwanayen nasa a masayin tubalan da mawaƙin yake amfani da su wajen gina baitocinsa a yayin yaba gwarzayensa. A ƙarshe, takarda ta kammala da cewa, haƙiƙa, jigon yabo wani haske na fitilar mawaƙa, kamar yadda aka gani a waƙoƙin siyasa na Alhaji Kamilu Ɗan Almajirin Mawaƙa Nguru.

Manazarta

Adamu, A.I. (2012). Salo da Sarrafa Harshe a Cikin Wasu Waƙoƙin Jam’iyyun ANPP da PDP a Jihar Kano da Jigawa. Kundin digiri na uku, Sashen Koyar da Harsunan Najeriya da Kimiyyar Harsuna Kano: Jami’ar Bayero.

Ahmad, A.A. (2003). Yankan Kunkurun Bala: Nazarin Zambo-Zagi a Siyasar Arewacin Nijeriya, (1950-I966). Kundin digiri na biyu, Sashen Harsunan Nijeriya, Sakkwato: Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.

Birniwa, H.A. (1987). “Consevatism and Dissent: A Comparative Studies of NPC/NPN and NEPU/PRP Hausa Political Verse from Circa 1946-1983.” Kundin digiri na uku, Sashen Harsunan Nijeriya, Sakkwato: Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.

Birniwa, H.A. (2004). “Siffantawa a Cikin Waƙoƙin Siyasa” Ɗunɗaye Journal of Hausa Studies Vol. 1, No. 1 Sakkwato: Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.

Buhari, M. (1988). “Nazarin Jigon Wasu Littattafan Ƙagaggun Labarai na Hausa”. Kundin digiri na biyu, Kano: Jami’ar Bayero.

C.N.H.N. (2006).Ƙamusun Hausa na Jami’ar Bayero. Zaria: Ahmadu Bello University Press Ltd.

Dunfawa, A.A. (2011). “Waƙoƙin Yara A Matsayin Tafarkin Gina Kyakkyawar Tarbiyya” Maƙala da ta fito a Cikin Algaita Journal of Current Research In Hausa Studies Vol. 2, No. 1 Kano: Jami’ar Bayero

Gusau, S.M. (1983). Kirari da Aiwatar da Shi a Waƙoƙin Noma na Baka. Makalar da aka Gabatar a Taron Kara wa Juna Sani. Center for Hausa Studies Kano: Bayero University, Nigeria.

Idris, Y. (2010). Waƙoƙin Addini Na Siyasa: Nazarin Waƙoƙin Emmanuel Wise Mai Molo. Kundin digiri na biyu, Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya da Afrika. Zaria: Ahmadu Bello University.

Sa’id, B. (2002). Rubutattun Waƙoƙi na Karni na Ashirin a Sakkwato, Kabi da Zamfara. Kundin digiri na uku, Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya. Kano: Bayero University.

Suleiman, A.B. (2017). “Gudummuwar Waƙoƙin Siyasa Wajen Tallata ’Yan Takara A Jihar Taraba A (2007-2014) Nazarin Waƙoƙin Shu’aibu Ibrahim Muhammad Aska” Kundin Digiri nabiyu. Sakkwato: Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.

Yahya, A.B. (1997). Jigon Nazarin Waƙa. Kaduna: Fisbas Media Service.



[1] Babu rana da watan haihuwa

[2]Mutum baƙi ainun

Amsoshi

Post a Comment

0 Comments