Citation: Mohammed, R. (2024). Mace da Kisan Gilla a Taskar Adabi: Tsokaci a Cikin Wasu Waƙoƙin Hausa na Zamani. Ginshiƙin Nazarin Salon Waƙoƙin Hausa, 496-505. www.doi.org/10.36349/djhs.2024.v03i01.061.
MACE DA KISAN
GILLA A TASKAR ADABI: TSOKACI A CIKIN WASU WAƘOƘIN
HAUSA NA ZAMANI
Rabi Mohammed
Sashen Nazarin
Harsunan Nijeriya da Kimiyyar Harshe, Jami’ar Jihar Kaduna
Tsakure
Ɗabi’ar
kashe mazaje da matan wannan zamani kan yi wata sabuwar al’ada ce da ta samu kuma abin
takaici. Dangane da haka ne aka sami wasu mawaƙan zamani waɗanda suka samar da waƙoƙi game da matsalar. Wato
Mawaƙi
Abubakar Sani ɗan
asalin Jihar Kano da kuma Isa Sani Ranɗawa,
ɗan asalin Jihar
Katsina. Ganin cewa ba a ga wani nazari
a kan wannan ɗabi’a
daga waƙoƙin da
waɗannan mawaƙa biyu
suka yi ba, ya sa aka zaɓi
a yi tsokaci a kansu. Manufar wannan maƙala ita ce, ta fito da gudummawar waɗannan mawaƙa a
fagen ilimi domin al’umma
su amfana. Ko ba komai an yarda da cewa adabi hoto ne na rayuwar al’umma. Maƙalar
ta saurari waƙar da kowannensu ya yi, tare da tattaunawa da mawaƙan, ta
tace muhimman bayanai daga gare su. Ta haka ne wannnan maƙala ta
fito da ɗabi’ar kisan
gilla a waƙar
da Abubakar Sani ya yi ta hanyar nuna takaicinsa da lallashin mace da tsoratar
da ita domin ta guje wa ɗabi’ar.
A waƙar
da Isa Sani Ranɗawa ya
yi kuma aka fito da wasu dalilan da ya ce su suke saka mata su kashe mazajensu
na aure domin ya jawo hankalin maza a kan nasu kurakuren tare da tsoratarwa ga
mata a kan sakamakon aikata ɗabi’ar
ko da kuwa an saɓa
masu ne. Daga ƙarshe an gano cewa waɗannan
mawaƙa
sun fito da gaskiyar abin da yake faruwa ne a cikin al’ummar da suke rayuwa, wato ba shaci-faɗi kawai irin na adabi ba.
Sannan an gano cewa, waƙoƙin ba su kasance masu tunzura mata ba, face faɗakarwa kurum domin mace
Bahaushiya ta ci gaba da kasancewa mai mutunci a idon duniya kamar yadda aka
san ta. Haka kuma, domin su maza su sauya taku wajen zama da mace, su fahimci
cewa jiya ba yau ba ce.
Fitilun Kalmomi: Mace, Kisan Gilla, Taskar Adabi, Waƙoƙin
Hausa, Zamani
Gabatarwa
Kisan gilla ko kisan kai shi ne aka kira da ‘Murder’ a
Ingilishi kamar yadda (Ƙamusun Newman 1997:177) ya fassara. Ma’anar murder kuma
an kawo ta’arifinta a ƙamusun Oxford (Hornby: 2010: 972) da cewa: The crime of
killing somebody deliberately, wato kisan wani da gangar. A Ƙamusun Hausa
(2006:246-247) kuwa, kalmar kisa tana ɗaukar ma’ana ta fuskoki da dama. Akwai
kisan rai da kisan aure da kisan garari da kisan kai da kisan raɓa da kisan
goro da kisan daɓe da kisan gilla da kisan mummuƙe da sauransu. To kamar yadda
aka gani, a nan ana magana ne a kan kisan kai kuma na gilla wanda ƙamusun na
Hausa ya bayyana ma’anarsu da cewa, kisan kai shi ne, Haddasa mutuwar wani.
Yayin da kisan gilla yake nufin kisan zalunci ba bisa doka ba. Dangane da
wannan ɗabi’a, idan an bibiyi tarihin rayuwar Hausawa tun daga zamanin
Maguzanci ya zuwa ƙarni na sha tara, ba a ji ɗuriyar cewa mata suna kisan gilla
ga mazajen aurensu ko `ya’yan kishiya saboda tsabar kishi ba. A wannan zamani
kuwa ana samun wasu mata daga cikin Hausawa suna aikatawa saboda wani dalili
musamman kishi. Wannan shi ya sa ake ganin cewa an samu sauyin ɗabi’a tunda haƙuri
da kau da kai da tsabar biyayya da tsoro da sauransu, a yau sun yi ƙaranci a
zukatan wasu mata a cikin al’ummar Hausawa.
Da yake adabi hoto ne na rayuwar al’umma, an samu wasu maza
mawaƙa waɗanda suka hasko faruwar wannan ɗabi’a a cikin waƙoƙinsu. Mawaƙan kuwa
su ne: Abubakar Sani (Ɗanhausa) daga Kano da Isa Sani Ranɗawa daga Jihar
Katsina. Waɗannan mawaƙa sun fito ƙarara sun bayyana cewa an sami wasu mata a
cikin al’ummar Hausawa da suka kashe mazansu na aure wanda shi ne dalilin ma da
ya sa suka yi waƙoƙin domin kawo gyara. Dukkansu za a iya cewa sun yi tarayya
ga manufar nuna wa mata musamman waɗanda ba su aikata ba aibu ko illar aikata
wannan ɗanyen aiki da nufin su yi hattara kada su aikata. Waɗanda kuma suka
aikata sun riga sun makara sun ɓata wa kansu rayuwa.
Domin ci ma manufar wannan maƙala, an yi bitar wasu ayyuka
game fitattun ɗabi’un mata a Bahaushiyar al’ada da kuma wasu ayyuka da suka
fito da wasu munanan ɗabi’un mata a adabin Hausa. Daga ƙarshe aka yi nazarin ɗabi’ar
kisan gilla da mace take yi a cikin waƙoƙin da aka ambata.
2.1 Fitattun Ɗabi’un Mace a Bahaushiyar Al’ada
Daga cikin muhimman abubuwan da aka faɗa game da wasu ɗabi’un
mace Bahaushiya tun a Maguzanci akwai cewa tana tsare gaskiya, domin a bisa
al’ada, kafin a kai ta ɗakin miji akan kai ta wurin tsafin da gidansu suka
yarda da shi ta rantse a kan ba ta taɓa sanin ɗa namiji ba. Idan ta rantse bisa
ƙarya kuwa, takan tozarta kai tsaye ko ma ta rasu. Hakan kan kasance ne
gwargwadon irin tanadin da tsafin ya yi (Ibrahim 2008:63). Don jin yadda ake
gane budurwa ta san ɗa namiji a sake duba Sallau (2018:4-8).
Haka kuma, Bahaushiyar mace tana ƙoƙarin guje wa zina domin
akwai takunkumi wanda al’ada ta tanadar kamar yadda aka faɗa a sama, kuma wurin
wasu Maguzawan ma, har bayan an haihu sai sun tabbatar da cewa ɗansu ne ba na
wani a waje ba. (Ibrahim, 2008:66). Wannan ya nuna mace tana da ƙoƙarin kare ɗiyaucinta
domin tsare mutuncinta da na zuri’ar gidansu. Sannan an sanya mata Hausawa a
cikin masu ladabi da biyayya a rayuwar Maguzanci wanda sukan gudanar a cikin
gida. (Ibrahim 2008:67). Saboda tsananin biyayyar Bahaushiyar mace ne ma ya sa
a lokacin jihadin, Shehu Usman Ɗanfodiyo ya nuna wa al’ummar Hausawa kuskurensu
wajen rashin ba mace muhimmanci a kan wasu al’amura waɗanda Musulunci bai yi
mata takunkumi ba. Kamar neman ilimi da maza ba su koya wa matansu, kuma ba su
yarda su fita su nemo, sai dai su yi ta aikace-aikacen gida da sauran ayyukan
gona da sauransu. (Talata Mafara 1999: 162-166).
Dangane da sutura a da, mata Hausawa a rayuwar Maguzanci ɗan
zane kawai suke ɗaurawa a kwankwaso (ƙugu). Ba abin kunya ba ne ga Bamagujiya
ta saki ƙirjinta a gaban kowa ba. Ƙananan yara suna saka durwa (bante da mata
suke yi don tsare kansu daga fyaɗe kamar yadda Ƙamusun Hausa 2006:115 ya
bayyana) har sai lokacin da za a yi masu aure suke fara ɗaura zani. An ce ma
kalmar durwa ita ce ta samar da kalmar ‘budurwa’ wato yarinyar da ta girma ta
isa aure. Daga baya suturar Maguzawa tana sauyawa amma ba wani ado na
a-zo-a-gani suke yi ba. Matan aure ba kowa ke sa riga ba, sai dai su ɗaura zane
a ƙirji. Sukan dai sa riga da zani idan za a yi biki ko in za a je kasuwa.
(Ibrahim 2008: 74-75). Bayan da Musulunci ya zo, an sami wasu sauye-sauye.
Misali game da sanya sutura ta mata, Hausawa waɗanda suka zamo musulmi, suna
rufe jikinsu daidai da koyarwar addinin. Wannan ya sanya ake kallon waɗanda ba
su rufe jikinsu ba a sahun masu ɗabi’a mara kyau a cikin al’umma.
2.2 Munanan Ɗabi’un Mace a Adabin Hausa
Akwai ayyuka da dama waɗanda suka fito da wasu halayen mata
marasa kyau a adabin Hausa. Ire-irensu sun haɗa da Mohammed (1994) da Zulai,
(1994) da Rabi (1998) da Abdullahi (1999) da Sakina (2005) da Hauwa, (2009) da Rabi,
(2011) da Hadiza, (2014) da Rabi, (2015) da Rabi, (2017). Waɗannan
nazarce-nazarce sun fito da wasu munanan ɗabi’u waɗanda mata suke aikatawa
daidai da yadda suka bayyana a adabin Hausa. Wasu sun yi nazarin a waƙa; wasu a
wasannin kwaikwayo; wasu a ƙagaggun labarai; wasu kuma a adabin gargajiya.
Ire-iren ɗabi’un da suka bayyana a ayyukan sun haɗa da kishi da ƙarya da cin
amana da karuwanci da bin bokaye da gulma da halin ƙeta/mugunta da da
ragganci/lalaci rashin kunya da rashin son addini da son shagali da
kissa/makirci da butulci sauransu.
Duba da ayyukan da aka yi bita, babu aikin da ya hasko ɗabi’ar
kisan gilla da mace ta yi. Abin da aka lura shi ne, waɗannan nazarce-nazarce
yawanci an yi su ne a cikin adabin da suka wanzu gabanin wannan ƙarni na
ashirin da ɗaya. Wataƙila a lokacin wannan ɗabi’a ba ta kunno kai cikin
al’ummar Hausawa ba. Waɗanda kuma suka a wannan ƙarnin, ba a wani nau’in adabin
zamani suka mayar da hankali ba. Kamar Sakina, (2005) wadda ta zaƙulo wasu
munanan halayen mata a cikin rubutattun waƙoƙin Hausa irin na su Halliru Wurno
da Aƙilu Aliyu da Alhaji Sani Daneji da Aliyu Maikuɗi Giɗaɗawa da Muhammadu
Sambo Waliyi da Muhammadu Kwanna da sauransu.
Bayan waɗanda suka shiga adabi, akwai wasu nazarce-nazarce
waɗanda kai-tsaye suka duba tasirin sauye-sauyen zamani ga wasu kyawawan ɗabi’un
mata Hausawa. Daga cikin ayyukan akwai Rabi, (2016: 390-397) wadda ta bayyana
yadda kyawawan fitattun ɗabi’un matan Hausawa suke salwanta a rayuwar zamani.
Misali kamar ladabi da biyayya da kara da kawaici da kunya duk sun yi ƙaranci a
tattare da Bahaushiyar mace. Ta nuna cewa rashin ladabi da biyayyar yana daga
cikin dalilan da ya sa mace a yau idonta ya bushe har take ɗaukar makami ta yi
kisa.
Shi ma Sallau (2018: 12-14) ya fito da yadda wasu al’adun
Hausawa suka taɓarɓare a rayuwar Hausawa musamman Jami’a. Daga cikin abubuwan
da ya kawo ya tattauna akwai batun biyayya ga shuwagabanni wanda ya ce ya yi
rauni sosai a Jami’o’i domin wasu ɗalibai ba ruwansu da dukkan malamin da ba ya
ɗaukar su darasi. Wasu ɗaliban kuma ba su da gaskiya da zumunci da ƙwazon aiki
tuƙuru. Sannan wasu ɗalibai mata suna zubar da mutuncinsu ga wasu malamai domin
a ba su sakamakon da ba su cancanta ba. Daga ƙarshe ya bayyana cewa saboda
matsalolin da ake samu ya sa mafi yawancin Jami’o’in da suke a arewacin
Nijeriya, sun aba ɗalibai shedar kamala karatu wadda ba su cancanta ba a ƙarni
na ashirin da ɗaya.
3.1 Abubakar Sani a Taƙaice
Wannan mawaƙi fitaccen mawaƙin zamani ne ɗan asalin Jihar
Kano wanda aka haife shi a garin Kano a shekarar 1980, a Ƙaramar Hukumar Gwale,
a wata Unguwa Aisami Kabuga (Kabuga Aisami).”
A yanzu yana zaune a Na’ibawa. Ana yi masa laƙabi da Ɗanhausa saboda
yanayin yadda ya fi yawaita amfani da kalmomin Hausa a cikin waƙoƙinsa. Karin
waƙoƙinsa ma bai yarda ya kwafi na Indiyanci ko wani abu da ba shi da alaƙa da
al’adarsa ba.
Game da neman ilimi da gwagwarmayar rayuwa kuwa ya bayyana
cewa, ya fara da karatun addini, don ya samu kamar izu goma a Alƙur’ani. Daga
bisani aka saka shi a makarantar boko inda ya haɗa biyu yana yi. Idan ya taso
daga makaranta yakan tafi kasuwa inda ya riƙa yin harkar sayar da duwatsu ɗin
nan da ake ratayawa Fulani da `yankwalaye da irin su riga da siket na Fulani.
Yakan tafi kasuwannin ƙauye; shi ne Ɗanbatta; shi ne Megatari; shi ne Talatar
Kanya; shi ne Rimin Gado; shi ne kasuwanni Bici da Butumi da makamantansu.
A lokacin da harkar fim ta shigo, ya je ya shiga wata ƙungiya
a Fage a cikin soshiyal welfaya. Sunan ƙungiyar Tauraruwa inda in ana buƙatar ɗan
fim, nan ake zuwa irin ƙungiyoyin nan a duba, sai a ɗauki mutum. Daga nan ne kuma sai ya koma kamfanin
Iyantama Moltimidiya, sai aka buɗe sabuwar Sitidiyo, aka ba shi Manaja a gurin.
Zamansa a Sitidiyo ne ya sa ya zama mawaƙi, har ya zama furodusa, har kawo
yanzu dai ana nan ana ta bugawa da shi. Daga bisani ne kuma, da ya fuskanci
yadda harkar fim take, wadda ya kamata a shige ta da ilimin zamani, sai ya je
ya nemi gurbin karatu a kan kwas ɗin Wasan Fim da na talabijin. Ya sami shaidar
Difloma a nan, ya kuma zarce zuwa BUK ya karanta Maskom.
A taƙace farkon fara waƙasa da shaharasa, aƙalla ya kai
shekara ashirin da uku zuwa da huɗu.
Shaharasa kuma aƙalla ya kai shekara goma sha bakwai. Yawan waƙoƙinsa
kuma gaskiya ya ce ba zai iya faɗin adadinsu ba sakamakon suna yi ne a lokacin
babu wani tunanin adanawa. Ya koka da cewa abin kunya ne wani lokacin su riƙa
faɗin yawan waƙoƙinsu sakamakon `yan’uwansu mawaƙa na Kudancin Nijeriya, za a
ga mutum ya zo ya yi waƙa biyu, uku, huɗu biyar, ya zama biloniya. Amma su `yan
arewacin Nijeriya sai a tambayi mutum ka ji ya ce ya yi waƙa ɗari, ɗari biyu,
dubu ɗaya, amma a kan naira dubu ɗari sai ka gan shi a bayan kanta an ɗaure
shi. Abin da ya janyo masu wannan matsalar shi ne, har yanzu `yan’uwa Hausawa
sun ƙi karɓar su yadda ya kamata. Kullum suna masu kallon mutanen banza masu ɓata
tarbiyyar yara alhali suna bayar da gudummawa ga harshen Hausa da adabinsa.
Dangane da alaƙarsa da mata ya nuna cewa, ya fi karkata ga ɓangaren
waƙoƙin soyayya inda ya fi ba wa mata dama. A cewarsa, ya tsinci kansa a mai
tausayin mata, wanda ya sa a ƙananun shekarunsa ya kasance da mata huɗu, na
aure. Ya ƙara da cewa da ana auren mace goma, a tausayin da yake wa mace, zai
iya auren su. Domin haka ya sa yakan yi waƙa, ya ba su shawara a kan su gyara
kaza, su bar kaza, shawarwari dai waɗanda za su riƙa tsira da mutuncinsu.
3.2 Isa Sani Ranɗawa
a Taƙaice
Shi ma wannan fitaccen mawaƙi ne na zamani wanda asalin
iyayensa da kakanninsa sun fito daga garin Ranɗawa (wani ƙauye a Ƙaramar
Hukumar Mani). Sunan mahaifisa Sani Ibrahim Ranɗawa, mahaifiyasa kuma sunanta
Hajiya Hajara Adam Ranɗawa. An haife shi ranar ɗaya ga watan ɗaya, shekarar
1991 a cikin garin Katsina a Unguwar da ake kira ‘Gidan Waya’ wato (Post
Office), na cikin garin Katsina. Sannan kuma shi ne na bakwai a wajen iyayensa
saboda akwai yayyensa mutum shida.
Lokacin ƙuruciyarsa da tasowa da, ya bayyana cewa, sun zauna
wuri-wuri saboda yanayin aiki na mahaifinsu. Saboda haka kusan ya yi ƙuruciyarsa
a tsakanin Unguwanni daban-daban a cikin garin Katsina. A sabuwar Unguwa ne ya
yi karatun firamare har dai wannan lokacin zuwa lokacin da ya fara tasowa haka,
ya shiga makarantar gaba da firamare, wadda aka fi sani da K.T.C. Sannu a
hankali ya ci gaba da karatu zuwa lokacin da Allah ya sa suka bar garin Katsina
kuma suka tafi garin Funtuwa (Ƙaramar Hukuma ce a cikin Jihar Katsina) inda har
ya je Government Technical College (G.T.C), wato makarantar Kimiyya da Fasaha
ya ci gaba da karatunsa ya ƙarƙare har ya dawo gida ya ci gaba da harkokinsa.
Sai kuma maganar iyali da sana’arsa wanda ya ce zuwa yanzu
dai ba shi da iyali gaskiya, amma akwai niyya. Sana’a kuma, ya ce shi da ma tun
tasawarsa marubuci ne. Yakan yi rubutu na labari irin na littafi na Hausa ya
buga shi. Haka ma yakan ɗauki littattafai ya je kasuwa ya baza domin sayarwa.
Ya ce a haka har rumfa ma yana da ita a wata kasuwa da ake kira `Yarkutungu. A lokacin nan idan ya tashi sai ya je wannan
kasuwa ya baza a ranakun da kasuwa ke ci. Haka kuma idan ana son labarin fim,
shi ma yna rubutawa. Sannan akwai aikin jarida, wanda ya ɗarsanu da zuciyarsa
wanda shi ne abin da ya sanya ya yi ta ƙoƙarin ganin cewa ya zauna a kafafun yaɗa
labarai inda nan ya samu ya iya aiki kuma ya ci gaba da tafiya da aikin yadda
ya kamata.
Dangane da yin waƙoƙi kuwa, ya kasance fitacce wajen yi wa
mata waƙa. Mafi yawanci a kan faɗakarwa da su riƙa kasancewa masu halaye na ƙwarai
da guje wa munanan ɗabi’u. Yakan yi kira ga maza masu cutar da mata da wasu ɗabi’u
kamar yadda ya yi waƙar Namiji mai dukan mata da waƙar Fyaɗe.
3.3 Mace da Kisan Miji Daga Bakin Abubakar Sani
Shi dai Abubakar Sani wanda ya yi waƙar Kar ki Yanka Mijinki
Uwargida/Amarya, ya bayyana dalilin da
ya sa ya yi waƙar da cewa:
Akwai batutuwa da yawa da suka sa na yi wannan waƙar. To,
dalilin da ya sa na yi waƙar Kar ki Yanka Mijinki, gaskiya a kwanakin baya
akwai wani lokaci da tun daga lokacin da aka yi kes ɗin Maryam Sanda, to kuma
sai ya zamana mata sun zama kamar an hankaɗo su, saboda ina ga a lokacin an ga
kamar za ta yi firi ne haka. To sai ka ga da man akwai tsanani na yawan auren
dole, ko kuma ka ga namiji ya auri mace ya bar ta cikin wahala da makamantan
irin waɗannan. Sannan kuma tai magana ka ga zai iya zagi ko ya kai duka. Wani
lokacin dai mazajen sukan fusata matan, kuma sai ka ga matan sun aikata abun da
ba shi ke nan ba. Wata za ka ga an ce ta kwara wa mijinta ruwan zafi; wata ta
buga wa miji wuƙa; wata ta zuba mai foizin ma. Don a nan Kano ma a wani Lokal
gamman Ungoggo, akwai yarinyar da saboda tana son ta kashe mijin, haka ta yi ɗanwake,
ta zuba shinkafar ɓera, ina ga da shi da abokanansa, mutane da dama sun mutu,
wasu sun jikkata a kan shi kaɗai kawai. Akwai kuma wadda ma, shi kuma soyayya
ya shigo yana yin waya da mace a barandar bene. Garin ƙoƙarin ƙwatar wayar, ta ƙwace
wayar, i zame ya faɗa, shi ma ya mutu. Akwai su dai da yawa ga su nan dai. To
kuma yawanci gaskiya duk kes ɗin Maryam sanda ne i janyo wannan matsalolin
saboda suna ganin kamar ta yi firi, don haka in ma mace ta kashe namiji ba wata
tsiya ba ne, ba wani abu za ai ba. To ni kuma a matsayina na mawaƙi, sai na ga
ai ina da gudummawar da zan bayar tunda dai mata sukan ji wannan waƙoƙin. Kusan
su ne ma mafi yawan odiyans ɗinmu wanda suke jin waƙoƙinmu, na ce to, bari na
yi kira tunda an ce duk abun da kake ganin za ka iya ba da gudummawa ka yi.
Wanda ba za ka iya yi da kuɗi ba ka yi da ƙarfinka. Wanda ba za ka iya yi da ƙarfinka
ba, ka yi da bakinka. Wanda ba za ka iya yi da bakinka ba, ka yi a zuciyarka.
Sai na ga to ni ma ina da gudummawar da zan bayar a kan waƙoƙi, bari na yi
nasiha ta cikin waƙa, wataƙila in Allah ya taimaka sai ka ga ta samu karɓuwa.
To gaskiya dai ire-iren waɗannan dalilan shi ne suka sa na yi wannan waƙa ta
Kar ki Yanka Mijinki.
(Tattaunawa da
Abubakar Sani ranar Talata, 10/08/2021 da misalin ƙarfe 10: 52 na dare ta kafar
sadar da zumunta ta wats’af)
Wannan taƙaitaccen bayani da mawaƙin ya yi a sama, ya haska
wa wannan nazari tabbatar da hasashensa dangane da ƙunshiyar waƙar da Abubakar
Sani ya yi. Abubakar Sani farawa ya yi da cewa:
Kar ki soke mijinki,
Kar ki yanka mijinki,
Uwargida
Kar ki ƙona mijinki,
Kar ki kasshe mijinki `yar’uwa,
Kar ki ƙona mijinki `yar’uwa,
Kar ki ƙona mijinki uwargida,
Kar ki kasshe mijinki,
Uwargida
Kar ki yanka mijinki kin ji ko,
Kar ki yanka mijinki uwargida,
Kar ki soke mijinki,
Uwargida
Kar ki yanka mijinki,
Uwargida
Kar ki ƙona mijinki,
Ƙarshe ki saka mana kuka,
Daga nan ne sai ya fara tuna wa mace mai wannan mummunan
hali, cikin lallashi dangane da dangantakarta da mijinta, cewa ta tuna fa zaman
ƙauna ne Allah ya haɗa su wanda kuma ya kamata a zauna da juna cikin haƙuri har
zuwa lokacin da Allah zai raba su da kansa (wato mutuwa). Bai kamata a ce an
samu haka daga gare ta ba, inda ya nuna kada ma’aurata su riƙa biyewa masu
tayar da zaune tsaye a kan ɗan ƙanƙanin abu har aure ya rabu. Ga yadda yake
cewa:
Wanda ya yi ki shi ne yay yo shi har i zo ya haɗa ku,
Ƙauna ta saka kuka zam mata da miji kuma ga ku,
Abu ɗan ƙanƙani ƙalilan kar ya zamo ya raba ku,
Haƙuri in kukai da juna za ku ga har zai raba ku
Kar ku ɓata shirinku,
Uwargida,
Na zaman ɗakinku,
Uwargida,
Kar a zo a haɗa ku,
Uwargida,
Ma’ana a raba ku,
Uwargida,
Kar a sa ku yiwo da-na-sani,
Ƙarshe a raba ku da juna,
Mawaƙi Abubakar Sani ya tabbatar da cewa wannan ɗabi’a ta
kisan gilla da ake samun mata na aikatawa sabon lamari ne wanda al’ummar
Hausawa ba su san da ita ba. Ya rafka salati na ban mamaki game da wannnan hali
inda ya nuna lallai zamani ne ya kawo haka.
In ba haka ba ya za a yi mace ta dubi mijinta har ta yanka shi kamar
wani rago, jini yana kwarara; Ko ta fafe cikinsa ƙiri-ƙiri ana ganin kayan
cikinsa gwanin ban ƙyama; ko kuma ta ɗebo ruwan zafi ta antaya masa. Sai yake
tambaya wannan ɗabi’a tsantsan jahilci ne ƙin jinin mutum ne ko kishi ko hauka?
Ga dai ta bakin mawaƙin:
La’ilaha’ilallah duniya tana ruɗarwa na gani,
Sha’anin yau na da wuyar gani,
Wai ki duba mijinki ki yanka shi kamar wani rago sai jini,
Wanga jahilci ne ko ƙini,
Ko ki duba cikinshi ki fafe shi a hango tumbi ƙyanƙyani,
Zuciya ta zo da baƙin hali,
Ko ki ɗebo ruwan zafi ki antaya masa ba wani lamuni,
Hakan kishi ko hauka?
Mawaƙin ya ci gaba da nusar da macen da duk ta aikata wannan
ɗanyen aiki game da halin da za ta shiga na da-na-sani wanda Hausawa ke cewa ƙeya
ce. Sakamakonta ta faɗa hannaun alƙali wanda a ƙarshe zai yanke mata hukunci
shiga gidan yari inda ba ta da mabiya (magoya baya), domin kuwa ta aikata
mummunan aikin zuciya, ta ja wa kanta baƙin jini har a wajen `ya`yanta na
cikinta tunda ta kashe masu uba ta mayar da su marayun ƙarfi da yaji. Ta yaya
kuwa yaro zai so mamarsa? Mawaƙin sai ya nuna haka inda ya ce:
Kin kashe shi kina da-na-sani,
Kin sa wa kanki baƙin jini,
Alƙali bai miki lamuni,
Ya ɗaure ki a gun da inda ba kya samun mabiya,
Kullum ki ta nadama har ƙarshe sai zagin maƙiya,
Yanzu `ya`yayanku da shi kin maida su marayu,
Kin kashe masu Abbansu ciyar ko duk ta soyu,
Kun ga canji na rayuwa da ke da su kun juyu,
Za ki dawwama yari can ne gidan da za ki ki rayu,
A yayin da mai wannan laifi ta je gidan yari, sai mawaƙin ya
ƙara nusar da matan da ba su riga sun faɗa wannan tarko ba irin sakamakon da
macen da ta aikata kisan gilla take shiga, don dai su yi hattara kada su
kuskura su aikata. Ga ƙarin abin da ya ce:
`Yan’uwa danginki,
Uwargida,
Tun suna duba ki,
Uwargida,
Kowa ya yo ƙyale ki,
Uwargida,
Har saboda mijinki,
Uwargida,
Tunda kin kar shi,
Duk ɗanki bai ganin kimarki gaba ɗaya,
Wai idan kika kar shi me za ya zama riba gunki uwargida?
Sha’anin yau na da wuyar gani,
Ci da sha duk shi ne in babu shi ki zamko kanki a gargada,
Wanga jahilci ne ko ƙini?
Alhakin rai nashi ya rataye wuyanki ina wata fa’ida?
Zuciya ta zo da baƙin hali,
To rashin haƙurinki ya kai ki ya baro ki cikin hassada,
Haka kishi ko hauka?
Haka kuma, ya fito ƙarara ya nuna cewa babban abin da yake
jefa mace aikata kisan gilla shi ne batun kishi inda takan biye wa wasu matan
waɗanda mawaƙin ya kira da maƙiya masu zuga mace su ce kishiya in an yo wa mace
matsala ce, fitina ce ko illa ce. Hakan kuma shi ne yakan jefa mace shiga cikin
ƙunci wanda mawaƙin ya ce sun koma sun zama ɗaya da masu zuga ta. Ga yadda ya
ce:
Maƙiyanki sukan ce,
Uwargida,
Kishiya matsala ce,
Uwargida,
Kishiya fitina ce,
Uwargida,
Kishiya illa ce,
Uwargida,
Sun saka ki cikin gigita da ke da su kun zamto bai ɗaya.
A ƙarshen waƙar mawaƙin yake cewa duk macen da ta aikata
kisan gilla ga mijinta lallai ta san ta yi gamo da masifa kuma ta zama kura a
cikin al’umma. In ma baƙin kishi ya kai ta ga aikata hakan, to sai a kira ta
zautacciya, wato mahaukaciya tunda aiki ne na marasa hankali ta aikata. Ya kuma
ƙara da cewa duk macen da ta aikata hakan kada ta yi zaton ta huce takaicin da
ya dame ta. Ta sani shara'a dole ta ɗaure ta don ita `ya ce inda a lokacin za
ta gane kurenta. In kuwa ma an ƙyale ta babu hukunci to fa ba yadda za a yi ta
yi rayuwa mai daɗi a cikin al’umma don duniya za ta tsane ta gabaɗaya. Ga dai
ta bakin mawaƙin:
Wacce tai haka ta yi gamo da masifa,
Ta zama kura ce,
In baƙin kishi ne ai ya saka ta,
Ku ce mata karya ce,
In ƙiyayya ce ta saka ta hakan ai,
Wannan ta zauce,
Kar ki dubi mijinki ki yanka,
Ki zaton ai kin huce,
Ko ki ɗau matsalarki da shi ki kashe don,
Ke ma ai `ya ce
Shara’a ta riƙe ki,
Za ki gane kurenki,
Farko a riƙe ki,
Ƙarshe a kashe ki,
In dai ma har an ƙyale ki,
Duniya ta tsane ki gabaɗaya,
Domin haka a bisa fahimta, duk da cewa mawaƙi Abubakar Sani
ya yi waƙa a kan mummunar ɗabi’a wadda mata sukan aikata a yau, za a iya cewa
ya yi ta da usulubi na neman kawo gyara ne a cikin al’ummarsa Hausawa. Shi ya
sa ma a ƙarshen kusan kowane ɗan waƙar yake cewa:
Kar ki soke mijinki,
Uwargida,
Kar ki yanka mijinki,
Amarya,
Kar ki ƙona mijinki,
Ƙarshe ki saka mana kuka.
3.4 Mace da Wuƙa Daga Bakin Isa Sani Ranɗawa
Mawaƙi Isa Sani Ranɗawa ya hasko wannan ɗabi’a a cikin waƙar
da ya yi mai suna Mata da Wuƙa a shekarar 2019. Ya bayyana dalilin da ya sa ya
yi wannan waƙa kamar haka:
Abin da ya ja hankalina na yi wannan waƙa shi ne, lokacin da
na riƙa samun labaran matan da suke ta kashe mazajensu, kuma da wuƙa suke
amfani wajen kisan, musamman kisan da wata mata ta yi wa mijinta ta hanyar
yanke mashi mazakutanshi. Lallai wannan
ya ɗauki hankalina sosai nag a cewar ya zama mani dole in yi amfani da hikimar
da Allah ya ba ni, in yi gargaɗi ga matan da ke kashe mazaje saboda kishi ko
wani ƙaramin dalilin da bai wuce a tsaya a sasanta da magabata ba. A taƙaice
dai wannan shi ne abun da ya zaburo zuciyata na yi wannan waƙa ta Mata da Wuƙa
don al’ummata su hankalta a kan dalilin wasu matan na kashe mazajensu da kuma
abun da ya kamata su matan su yi na haƙuri don su zauna lafiya. Domin ko duk
wacce ta kashe mijinta, ita ma gawa ce, kuma ta bar bakin tarihi ga zuriyarta
daga `ya`ya, iyaye da sauran makusantanta gabaɗaya har duniya ta naɗe.
(Tattaunawa da Isa Sani Ranɗawa a ranar Talata, 10/08/2021
da misalin ƙarfe 10: 43 na dare ta kafar sadar da zumunta ta WhatsApp).
Shi ma ɗin ya hango zahirin rayuwar Hausawa ne inda ya ɗauko
hoton wannan ɗabi’a ta kashe miji da wasu mata Hausawa suka aikata musamman
matar da ya ce ta kashe mijinta ta hanyar yanke mashi mazakutarsa, wanda kuma
shi ya jawo hankalinsa ya yi wannan waƙa ta Mata da Wuƙa. A cikin waƙa, ya
kalli wannan ɗabi’a ta kisan gilla wadda wasu mata suke aikatawa da cewa lallai
akwai dalilan aikata wannan ɗanyen aiki wanda ba a san su da shi ba. Shi ya sa
tun farkon buɗe waƙar ya fara da tambaya cewa:
Oooh!
Mi ya sanya mata ɗaukar wuƙa?
Mi ya sanya mata su riƙe wuƙa?
Wai ina dalilin ɗaukar wuƙa?
Kuma ina dalilin soke maza?
Kai!
Mi ya sanya mata suka ɗau wuƙa?
Wanni darasi mai taɓa rayuwa,
In ka san dalilin ɗaukar wuƙa,
Ba ka bari ba matarka ta ɗau wuƙa,
Mi ya sanya mata ɗaukar wuƙa?
Wanni darasi mai taɓa rayuwa,
In ka san dalilin ɗaukar wuƙa,
Ba ka bari ba matarka ta ɗau wuƙa,
In an lura, mawaƙin ya nuna cewa duk namijin da ya san
dalilin da ya sa mata ke ɗaukar wuƙa da nufin kisa, to kuwa da ya kiyaye. Daga
can gaba kuwa sai ya nuna cewa ya yi nazari ne game da kisan da mata ke wa
mazajen aurensu ta hanyar yi wa mata tambaya inda ya ce sun ba shi amsa. Ga dai
ɗan waƙar:
Na yi nazari kan soka wuƙa,
Mata da wuƙa,
Tambaya nawa mataye,
Ku bar soka wuƙa,
Sun sanar da ni amsoshi haka,
Mata da wuƙa,
Wanda ke saka mace ɗaukar wuƙa,
Mi ya sanya mata ɗaukar wuƙa,
Wanni darasi mai taɓa rayuwa,
In ka san dalilin ɗaukar wuƙa,
Ba ka bari ba matarka ta ɗau wuƙa,
Eee! Batun mazan da ke dukan mata,
Mata da wuƙa,
Wanda bai ganin darajar mata,
bar soka wuƙa,
Ko mijin da ke wa mace ƙeta,
Mata da wuƙa,
Ka san tana dab da ta ɗau wuƙa,
Mi ya sanya mata ɗaukar wuƙa,
Wani darasi mai taɓa rayuwa,
In ka san dalilin ɗaukar wuƙa,
Ba ka bari ba matarka ta ɗau wuƙa,
Wato daga cikin dalilan da ya zayyano akwai batun mijin da
yake dukan matarsa da wanda bai ganin darajar mata, ko mijin da yake yi wa mace
ƙeta. Mawaƙin yana ganin duk namijin da yake da ɗayan waɗannan munanan ɗabi’u
ga matarsa, to ya sani mace tana dab da ɗaukar wuƙa da nufin kashe shi. Babu
shakka wannan halin tausayi ne shi ma Isa Sani Ranɗawa yake nunawa game da
halin da mata suka shiga a yau. Domin kalmomin da ya zaɓa a cikin waƙar haka
suke nunawa, duk da cewa mummunar ɗabi’a ake nunawa. A duba abin da ya ci gaba
da cewa kamar haka:
To amma abun da kunya ku ji gaskiya,
Ranar bikinku murna har da dariya,
Ku bar soka wuƙa,
A ba ka ita amarya ka yi godiya,
Yau kuma `yar daba ka maida ta ta ɗau wuƙa,
A tunanin mawaƙin da abubuwan da ya faɗa a sama shi ne, ai
da mamaki a ce an ƙulla auren soyayya ana murna, miji yana ta godiya, sannan a ƙarshe
a ce ga mace da wuƙa ta kashe miji. Shi ne mawaƙin ya yanke hukunci inda ya ce
to mijin dai shi ne ya mayar da ita `yar daba tunda ta ɗau wuƙa.
Daga gaba kuma sai mawaƙin ya dawo ga rarrashin mace
uwargida ta hanyar ce mata ta manta da ɗaukar wuƙa domin aikata kisa ba wata
riba za ta samu ba in ta yi, duk da cewa ƙila mijinta ne halinsa mai muni ya
tunzura ta. Ya yi ƙoƙarin nusar da uwargida game da sakamakon da za ta tsinci
kanta a ciki idan har ta yi kisa. Ga dai ta bakin nasa:
Kin ji uwargida ki manta da batun wuƙa,
Ke ma rayuwarki don kar ta zamo baƙa,
Ku bar soka wuƙa,
Ɗaurin rai da rai yana sa rai babbaka,
Ko `ya`yanki ba a son aure mai wuƙa,
Shi ma Isa Sani Ranɗawa ya nuna cewa rayuwar wacce ta aikata
kisa tana zamowa baƙa inda za ta ƙare a gidan yari ɗaurin rai da rai wanda yake
babbaka zuciya. Uwa uba `ya`yanta da al’umma za su guji aurensu duk saboda
munin wannan ɗabi’a ta kisan Babansu. A ƙarshe sai ya ce:
In aure ya zo ya ƙara shi maigida,
Ko ta zo kina da ɗaki a cikin gida,
Sai ma inda kinka ba ta a cikin gida,
Lemu kankana ake sanya wa wuƙa,
Isa Sani ne na Ranɗawa,
Mai son tarbiya ta zam kyakkyawa,
Mace mai son kashe miji ta makaro,
Lokacin baya ne akai indararo,
In zancen miji ake ba na aro,
Wahala ke da kanki ce kinka taro,
Tun daga can sama rufi za ki diro,
In kuma kin kare ba ma ɗorawa,
ba mu muka aza sanwar ba
Idan an lura, ya sake lallashin mata da cewa su bar ɗaukar
wuƙa, su tuna lemo ko kankana su ake sanya wa wuƙa. Isa Sani Ranɗawa ya ƙarƙare
da tabbatar da manufarsa inda ya nuna cewa yana son tarbiyya ta zama kyakkyawa
ne ya sa ya yi wannan waƙa. A bisa fahimta, wannan tausayi ne ga mata domin shi
ma ba lalacewarsu yake ƙoƙarin yayatawa ba. Ƙoƙarin inganta rayuwar matan ne ta
fuskar nusarwa cikin kalamai masu taushi. Sannan ta la’akari da kusan kowane ɗan
waƙa za a ga yana maimaita cewa:
Mi ya sanya mata suka ɗau wuƙa?
Wanni darasi mai taɓa rayuwa,
In ka san dalilin ɗaukar wuƙa,
Ba ka bari ba matarka ta ɗau wuƙa,
Wato wannan ɗabi’a baƙuwa ce a cikin al’umma a ga mace tana
kisa da makami. Ai lallai babban darasi ne mai taɓa zuciya kamar yadda yake ta
nanatawa.
3.5 Sakamakon Bincike
Wannan maƙala ta gano cewa waɗannan mawaƙa sun fito da
gaskiyar abin da yake faruwa ne a cikin al’ummar da suke rayuwa, wato ba
shaci-faɗi kawai irin na adabi ba. Sannan an gano cewa, waƙoƙin ba su kasance
masu tunzura mata ba, face faɗakarwa kurum domin mace Bahaushiya ta ci gaba da
kasancewa mai mutunci a idon duniya kamar yadda aka san ta a da. Haka kuma,
wannan maƙala ta gano cewa, matan Hausawa a wannan zamani ba su da zurfin haƙuri
irin na matan dauri domin ba su ɗaukar cin zarafin da namiji yake yi masu.
Wannan ne ya sa mawaƙi Isa Sani Ranɗawa ya binciki wasu mata a kan dalilin da
ya sa wannan ɓarna ta ɓarke a tsakanin al’ummar Hausawa. Ta haka ne ya ɗora
dalilan a waƙarsa domin ya nusar da maza a kan nasu kurakuren.
3.5 Kammalawa
Bisa taƙaitawa daga abin da wannan maƙala ta tattauna, tun a
farko an yi bita kuma an fahimci cewa kisan gilla da mace Bahaushiya kan yi a
wannan zamani baƙuwar al’ada ce cikin al’ummarta. Wannan tunani ne ya ba
Abubakar Sani da Isa Sani Ranɗawa lasisi suka yi waƙa a kan ɗabi’ar. Kamar
yadda aka ani, wannan maƙala ta ɗan tsakuro tarihin waɗannan mawaƙa sannan ta
nazarci waƙoƙin. Maƙalar ta tabbatar da cewa mawaƙan sun wakilci al’ummar
Hausawa domin sun nuna cewa kashe-kashen da suka ga yana faruwa ne a zahiri ya ɗauki
hankalinsu. Domin haka ne suka fito suka nuna takaicinsu na faruwar wannan ɗabi’a
wadda suka tabbatar wa al’umma baƙuwa ce. Sannan a matsayinsu na maza, sun damu
da mata ƙwarai shi ya sa suka yi kira domin mata su guji wannan halin saboda su
ci gaba da rayuwarsu cikin mutunci da walwala. An fahimci cewa waɗannan mawaƙa
sun bambanta wajen isar da saƙonsu inda
aka ga cewa shi Abubakar Sani kai-tsaye ya fito da saƙon nasa ga mata.
Shi kuwa Isa Sani Ranɗawa ya bugi jaki ya kuma bugi taiki. Wato sai da ya fara
kawo dalilan da suka sa wasu mata suke ɗaukar makami su yi kisa domin ya jawo
hankalin maza su kiyaye. Sannan sai ya
yi kira ga mata da su kasance masu haƙuri, kada su riƙa aikata kisa. Daga ƙarshe,
duba da waƙar Isa Sani Ramɗawa, abin da wannan nazari ya lura shi ne, ashe idan
maza suka kiyaye cin mutunci ko cin zarafin mace, zai yi wuya a sami mace tana
kashe mijinta.
Manazarta
Abdullahi R. (1999), “Mata a Adabin Baka: Nazari da Sharhi a
Kan Waƙar Bazawara ta Sanin Balɗo”. Kundin Digiri Na Farko, Sashen Harsunan
Nijeriya, Sakkwato: Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo
CNHN, (2006): Ƙamusun Hausa. Cibiyar Nazarin Harsunan
Nijeriya, Kano: Jami’ar Bayero.
Hadiza, S.K. (2014): “Mace a Idon Bahaushe” Kundin Digiri na
Tsakiya, Sashen Harsunan Nijeriya, Sakkwato: Jami’ar Usmanu.
Hauwa, M.B. (2009): “Kishi Kumallon Mata: Nazarin Kishi Daga
Waƙar Dare Allah Magani da Ta Halima `Yar Buzaye. Harshe 3 Journal of African
Languages, Sashen Harsunan Nijeriya da na Afirka, Zariya: Jami’ar Ahmadu Bello.
Hornby, A.S. (2010): Oxford Advance Learner’s Dictionary of
Current English. London: Oxford
University Press.
Ibrahim, A.S.S. (2008): “Matakan Rayuwar Hausawa Maguzawa:
Aure, Haihuwa da Mutuwa.” Kundin Digiri Na Ƙoli, Sashen Harsunan Nijeriya,
Sakkwato: Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.
Mohammed, I.H. (1994) “Karuwa a Bakin Marubuta Waƙoƙin Hausa
da na Baka”. Kundin Digiri Na Farko, Sashen Harsuna da Al’adun Afirka, Zariya:
Jami’ar Ahmadu Bello.
Newman, R.M. (1997): An English-Hausa Dictionary. ISBN: 978
139 733 0 Lagos: Longman.
Rabi, G. (1998): “Nazarin Jinsi a Adabi: Tsokaci Kan Matsayin
Mace a Rubutattun Wasan Kwaikwayo na Hausa” Kundin Digiri Na Tsakiya, Sashen
Harsuna Nijeriya da na Afirka Zariya: Jami’ar Ahmadu Bello.
Rabi, M. (2011): “Ɗabi’un Mata a Bakin Mawaƙan Baka na
Hausa” Kundin Digiri na Tsakiya, Sashen Harsuna da Al’adun Afirka, Zariya:
Jami’ar Ahmadu Bello.
Rabi, M. (2015): “Nazarin Waƙar Sakaryar Mace Daga Bakin
Barmani Coge da Mamman Duka.” KADAURA Journal of Multidiciplinary Studies, Vol.
1, No 1, Pg 108-119, ISSN 2536-7609. Department of Nigerian Languages and
Linguistics, Kaduna: Kaduna State University.
Rabi, M. (2016): “Kyawawan Fitattun Ɗabi’un Matan Hausawa:
Kwatance da Rayuwar Zamani.” Proceedings of the 1st Annual International
Conference on the Hausa People, Language and History, Past, Present and Future,
Department of Nigerian Languages and Linguistics Kaduna State University. Pg
390-399, ISBN: 978-978-956-169-8. Kaduna: Garkuwa Publishing.
Rabi, M. (2017): “Waƙar Zaura ta Sanin Balɗo: Tsakanin
Gaskiya da Ƙarya? Kadaura Journal of Multidiciplinary Studies, Vol. 1, No 3, Pg
146 -159, ISSN 2536-7609. Department of Nigerian Languages and Linguistics,
Kaduna: Kaduna State University.
Sakina, A.A. (2005): “Mata a Idon Marubuta Waƙoƙin Hausa.”
Kundin Digiri na Farko, Sashen Harsunan Nijeriya, Sakkwato: Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.
Sallau, B.A. (2018): “Taɓarɓarewar Al’adun Hausawa a
Jami’o’in Arewacin Nijeriya: Ƙalubale Ga Tsarin Koyo da Koyarwa a Ƙarni Na 21.”
Kadaura Journal of Multidiciplinary Studies (Special Edition). Vol. 1, No. 4 P
2-17, ISSN 2536-7609. Department of Nijerian Languages and Linguistics, Kaduna
State University, Kaduna. Kaduna: Test & Print Ventures
Talata-Mafara, M.I. (1999): Daular Usmaniyya: Rayuwar Shehu
Usman Ɗanfodiyo da Gwagwarmayarsa. Kaduna: Nadabo Print Production, No 2 Waziri
Junaidu Road.
Zulai, S.I. (1994): “Kishi Kumallon Mata: Nazarin Sigoginsa
a Rayuwar Hausawa”. Kundin Digiri Na Biyu, Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya,
Kano: Jami’ar Bayero.
Waɗanda Aka yi Hira da su
Mawaƙi Abubakar Sani a Kwanakin Wata na: 25/11/2019 da na
10/08/2021 da na 22/08/2021 da 24/08/2021
Mawaƙi Isa Sani Ranɗawa a Kwanakin Wata na: 01/09/2020 da na
02/09/2020 da 10/08/2021 da na 22/08/2021 da 24/08/2021
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.