Ticker

6/recent/ticker-posts

Tarken Fadakarwa a Wakar ‘Annobar Korona’ Ta Khalid Imam

Citation: Karofi, I.A., Rabeh, H. and Darma, A.Y. (2024). Tarken Faɗakarwa a Waƙar ‘Annobar Korona’ ta Khalid Imam..Ginshiƙin Nazarin Salon Waƙoƙin Hausa, 487-495. www.doi.org/10.36349/djhs.2024.ɓ03i01.060.

TARKEN FAƊAKARWA A WAƘAR ‘ANNOBAR KORONA’ TA KHALID IMAM

Isah Abubakar Karofi

Hassan Rabeh

Abdullahi Yakubu Darma

Sashen Hausa, Kwalejin Ilimi ta Isa Kaita, Dutsinma, Katsina

Tsakure

Manufar takardar ita ce yin nazari a kan waƙar Annobar Korona da hanyar yi wa waƙar filla-filla ta amfani da hanyoyin nazarin rubutattun waƙoƙin Hausa domin a bayyana muhimman ɓangarori da nazari ya dogara da su, kuma masana suka amince a yi nazarin kowace rubutacciyar waƙa da waɗannan hanyoyin. Da yake nazari ne a kan rubutacciyar waƙa, an karanta waƙar (Annobar Korona) sosai ta yadda aka iya fayyace waɗannan muhimman ɓangarorin nazari, sannan aka kafa hujjoji daga baitocin waƙar. A sakamakon binciken takardar an gano cewa waƙar tana ɗauke da turke ko jigon faɗakarwa a kan cutar Korona, kuma ta cancanci a yi nazarin ta domin ta hau matakin nazari da masana da manazarta na adabin Hausa suka amince kowace rubutacciyar waƙa ta hau kamar salsalar waƙar da tarihin marubuci da shekarar wallafa da jigon waƙar da warwarar jigo da salo da sarrafa harshe da dabarun jawo hankali da dai sauran hanyoyi yin tarke ko nazari. Don haka, an bayyana dukkannin hanyoyin tarke ko nazari a cikin waƙar, sannan aka kafa hujjoji daga baitocin waƙar.

Fitilun Kalmomi: Tarke, Faɗakarwa,Waƙar ‘Annobar Korona, Khalid Imam

Gabatarwa

Annobar Korona, wato Kobid19 kamar yadda ake kiran ta,ta faro daga gabashin duniya a ƙasar Sin, sannu ta yaɗu tamkar wutar daji zuwa sassan duniya gabas da yamma, kudu da arewa. Cutar ba ta bar manyan garuruwa ba bare ƙananan da suke koma-baya wajen harkar kula da lafiya. Wannan annoba ta nuna yatsunta ga manyan ƙasashe da hukumomin lafiya masu ji da kansu ganin yadda suka kasa kataɓus wajen daƙile ta tun farkon ɓullowarta. Wannan dalilin ya sa marubuta da ma’abota ayyukan adabi bibiyar wannan muguwar annoba da nufin bayar da gagarumar gudummuwa akan irin tasirinta da illolinta ga al’umma. Kai! Har ma da nuni ko tattaunawa akan sanin haƙiƙanin wannan annoba a idon mutanen da suke sun yi nisa a ilimin zamani da ma waɗanda ba su yi zurfi ba.

2.0 Manufar Bincike

An gudanar da wannan bincike bisa manufar bayyana hanyoyin nazari da masana suka samar domin yin tarken faɗakarwa a rubutattun waƙoƙi a Hausa.

Haka kuma, ana son a bayyana salsalar waƙa da tarihin marubuci da shekarar wallafa da babban jigon da jigo a gajarce da warwararsa a waƙar da Khalid Imam ya yi ta Annobar Korona.

Bayan nan, ana son a kuma bayyana yadda Malam Khalid ya yi amfani da zubi da tsarin baitoci da kari da amsa-amo da salo da sarrafa harshe da dubarun jan hankali da kuma Hausar nahiya a wajen gina waƙarsa ta faɗakarwa a kan annobar Korona.

3.0 Hanyoyin Gudanar da Bincike

An yi amfani da hanyoyi biyu wajen gudanar da wannan bincike. Hanyar farko ita ce karantawa daga wasu rubutattun bayanai, waɗanda suka haɗa da bugaggun littattafai da kundayen bincike da mujallu da sauransu.

Hanya ta biyu kuwa, ita ce ta yin hira da masana adabi, musamman na rubutacciyar waƙar Hausa. A nan, an yi hira da ɗaya daga cikin editocin littafin wato Khalid Imam, wanda aka samu wasu bayanai da aka sanya a cikin wannan bincike. Haka kuma, an yi hira da wasu masana rubutaccen adabin Hausa. A wajensu aka samu wasu bayanai nahanyoyin nazarin waƙoƙin baka na Hausa kamar yadda Ɗangambo, 1975, 1981 da 2007 ya shimfiɗa a Mazhabar tarken rubutacciyar waƙar Hausa.

4.0 Hanyar Ɗora Aiki

An ɗora wannan takarda bisa ‘Mazhabar Rubutacciyar Waƙar Baka’. Wannan ra’i ne wanda ya fi mayar da hankali ne ga tattaro ra’ayoyin manazarta kan hanyar nazarin rubutacciyar waƙar Hausa. Masanin da ya assasa wanna ra’i shi ne Farfesa Abdulƙadir Ɗangambo a shekara ta 1975 har ya rubuta littafi mai suna Gadon Feɗe Waƙa. A kuma 1981 ya fito da Ɗaurayar Gadon Feɗe Waƙa da kuma Ɗaurayar Gadon Feɗe Waƙa (sabon salo) a shekara ta 2007. Masanin ya assasa wannan ra’in domin samar da wata hanyar nazarin rubutacciyar waƙa na bai-ɗaya karɓaɓɓe ga kowane mai nazarin rubutacciyar waƙa ta Hausa. Daga cikin magoya wannan ra’i akwai; Abdullahi Bayero Yahya da Isa Mukhtar da Aminu Lawal Auta da Halima Abdulƙadir Ɗangambo da Ɗahiru Abdulƙadir da Mustapha Shu’aibu da sauransu (Gusau, 2015:21-22).

Da yake takardar tana magana ne a kan tarken faɗakarwa a waƙar ‘Annobar Korona’ an yi amfani da hanyoyin da Mazhabar Rubutacciyar Waƙar Baka ta shimfiɗa wajen yin tarken kowace rubutacciyar waƙa ta Hausa. Kamar yadda hanyoyin suka zo a cikin littafin Ɗaurayar Gadon Feɗe Waƙa (sabon tsari).

5.0 Tarken Faɗakarwa a Waƙar Annobar Korona

Tarke ya ƙunshi wasu keɓaɓɓun hanyoyin nazari da masana suka amince a ɗora kowane aiki a kansa kafin ya cancanci ya zama karɓaɓɓen nazari ga masana. Don haka, a nan an yi tarken waƙar ‘Annobar Korona’ ta Khalid Imam kamar yadda Mazhabar Rubutacciyar Waƙar Baka ta Hausa ta shimfiɗa domin tarken faɗakarwa a rubutattun waƙoƙin baka na Hausa.

5.1 Salsalar Waƙar

An sami wannan waƙar ne a cikin littafin Corona Blues (A Bilingual Anthology of Poetry) shafi na 108-114. Kamfanin ɗab’i na Whetstone Publishers, Kano ne ya buga wannan littafin a shekarar 2020. Waƙar ta Annobar Korona ita ce ta 2 a jerin waƙoƙin da aka yi da harshen Hausa da suke cikin littafin.

5.2 Tarihin Marubucin a Taƙaice

An haifi Khalid Imam a cikin birnin Kano a shekarar 1973. Khalid Imam marubuci ne cikin harsunan Hausa da Turanci kuma malamin makaranta ne a garin Kano. Khalid Imam ya yi karatun digiri na ɗaya da na biyu a Jami’ar Bayero, Kano. Shi manazarci ne wanda yake da matuƙar sha’awa ta gudanar da bincike na ilimi a fannonin adabi da al’ada da tarihi da kumarubutu a kan kare haƙƙi, musamman na yara da mata.Zuwa yanzu, Khalid Imam ya wallafa littattafai sama da goma sha biyu (12) cikin harsunan Hausa da Turanci. An wallafa rubuce-rubucensa na adabi da muƙalun ilimi da dama a cikin gida Nijeriya da ƙasashen waje kamar su Amurka da Indiya da Jamus da Poland da Lebanon da sauransu. Khalid Imam shi ne Shugaban kamfanin fassara da talifi mai suna Whetstone Arts and Translation Serɓices. Haka kuma, Babban Darakta ne a makarantar Khalid Imam Academy da take a Kano. Ya taɓa zama Mataimakin Shugaban Ƙungiyar Marubuta ta Nijeriya reshen jihar Kano. Khalid Imam ne ya kafa wani muhimmin dandali na marubuta a kafar sadarwa ta zamani ta WhatsApp mai suna All Poets Network. Haka nan kuma, Khalid Imam shi ne yake rubutu a shafin faɗakar da matasa akan muhimmancin rayuwa da sana’a a mujallar Muryar Arewa mai suna Sirrin Arziki da Nasara. Khalid Imam yana da mata biyu da yara da yawa. Allah ya yi wa rayuwarsa albarka amin[1].

5.3 Shekarar Wallafa

An wallafa waƙar ‘Annobar Korona’ a cikin littafin Corona Blues (A Bilingual Anthology of Poetry) a shekarar 2020, kamfanin ɗab’i na Whetstone Kano ya wallafa littafin.

5.4 Jigon Waƙar

Muhammad (2003:143) ya bayyana jigo da “Shi ne gangariyar muhimmin saƙo ko manufar mawaƙi”.

Jigon wannan waƙar dai shi ne faɗakarwa a kan annobar Korona. A baiti na 18,

marubucin ya bayyanar da manufar waƙarsa a kan Korona, wato a wannan baitin ne ya bayyana ƙwayar jigonsa na cutar Korona kamar yadda sunan waƙar ya nuna:

Ita annobar Korona,

Cuta ce babu shakka.

(baiti na 18)

Wannan saƙo ko jigon ne ya yi ta ƙoƙarin nanatawa da jawo hankali a kan cutar Korona a baitoci daban-daban na waƙarsa. Misali, a baiti na 30 zuwa baiti na 34 kamar yadda za a gani a ƙasa:

Ni Khalid bani shakka,

Tabbas cutar Korona.

Jan kunne ce gare mu.

Mu bar saɓo da sharri.

(baiti na 30)

Mu so junanmu gaske,

Hakan zai taimake mu.

(baiti na 31)

Ni Imam Khalid na Indo,

Jikan Hauwa’u tabbas.

(baiti na 32)

Nasan cutar Korona,

Ƙanwa ce gun talauci.

(baiti na 33)

Wajen ƙeta da sharri,

Har ma yawo a dangi.

(baiti na 34)

Haka dai mawallafin ya yi ta kawo baitoci masu nuna illa ko munin Korona da masifun da take haifarwa cikin al’umma domin a faɗakar da jama’a.

5.5 Jigo a Gajarce

Jigo a gajarce shi ne masana suke dangantawa da gundarin jigo wato, saƙo a taƙaice da marubuci yake son isarwa ga jama’a (Muhammad, 2003:143).

Idan aka yi nazarin waƙar za a iya fitar da jigonta a gajarce kamar haka:

Tabbas cutar Korona,

Annoba ce ta gaske.

(baiti na 10)

Ita annobar Korona,

Cuta ce babu shakka.

(baiti na 18)

5.6 Warwarar Jigo

Warwarar jigo shi ne cikakken bayanin hanyoyin da mawaƙi ya bi ya cim ma jigonsa. Ma’ana ya fito da saƙon ƙuru-ƙuru, a fili ta hanyar yin sharhi (Muhammad, 2003:144).

Wannan waƙar tana ɗaya daga cikin waƙoƙin da suke faɗakarwa a kan annobar Korona domin jama’a su hankalta tareda ɗaukar matakai da za su kare kansu daga gare ta. Ga misali, daga waƙar:

Ita annobar Korona,

Cuta ce babu shakka.

(baiti na 18)

Wannan baitin ya fito da tabbacin Korona cuta ce babu shakka a kanta. Don haka, mutane su ɗauki matakin kare kansu daga sharrinta.

Ba ta kunya ba ta tsoro,

Ba ta sabo ba sanayya.

(baiti na 19)

Baitin na gaba yana daɗa fito da munin Korona ga jama’a domin tana iya kama kowa watao ba ta nuna sani ko ragowa ga kowa da kowa.

Yau mutum ya gane cewa,

Bai da ƙarfi sai na Allah.

(baiti na 20)

Bai da sauran duk dabara,

Kariyarsa tana ga Rabbu.

(baiti na 21)

Waɗannan baitoci biyu suna ƙoƙarin jan hankali ga mutane su gane cewa babu wanda ya gagari wannan cuta ta Korona komai dubararsa domin ta kama mutane daga ƙasashen da suka yi zarra a duniya ta fuskar kimiyyar magunguna. Don haka kariya daga gare ta sai dai Allah.

5.8 Zubi da Tsarin Waƙar

Zubi da tsari ya danganci yadda mawaƙi ya shimfiɗa waƙarsa dangane da salon buɗewa da rufewa da gina baitoci ko tsarin layuka da amsa amo da karin waƙar da sauransu (Muhammad, 2003:144).

Wannan waƙar ta Annobar Korona matsakaiciya ce domin tana da baitoci 36 ne kawai. Mafi yawancinta ƙwar biyu mai gajerun jimloli. A taƙaice dai waƙar ‘yar tagwai ce, amma an samu ƙwar huɗu a baiti na 15 da kuma 30 a cikin waƙar.

Mawallafin ya jeranta tunaninsa, bai yi wa waƙar zubin kwan-gaba-kwan-baya ba yadda za ta yi wahalar ganewa. Wannan dalili ya sa ana iya fahimtar jigonta da wuri wato faɗakarwa a kan annonbar Korona.

Mawallafin ya jaddada manufarsa inda ya riƙa maimaita wasu baitoci a fakaice ba kai tsaye ba. Misali,

Tabbas cutar Korona,

Annoba ce ta gaske.

(baiti na 10)

 Ita annobar Korona,

Cuta ce babu shakka.

(baiti na 18)

A taƙaice dai jerin carbin tunanin mawallafin bai tsinke ba.Misali:

Baiti na 1-5 ya nuna yadda ‘yan bariki da wurare irin su kasuwanni da mashaya da makarantu da sinima da ‘yan ƙwallo da kuma ‘yan dambe duk sun ɓace saboda gudun kamuwa da Korona.

Baiti na 6-9 mawallafin ya nuna munin sharrin Korona domin ta shafi gwamna da minista da manyan ƙasashen duniya ba wanda ta bari.

Baiti na 10-18 ya bayyana munin Korona a faɗin duniya domin a dalilin Korona duk wasanni da sharholiya sun gagara buɗewa a manyan ƙasashen Turai.

Baiti na 19-29mawallafin ya fito da mafita ɗaya domin kawo ƙarshen Korona shi ne komawa ga Allah ana masu tuba akan zunuban da ake aikatawa.

Baiti-30-36 mawallafin ya gaskata cutar Korona da kuma jan kunne a kan cutar da jan hankalin jama’a a kan komawa ga Allah da tuba domin kowa ya rabauta daga sharrin Korona.

5.9 Zubi da Tsarin Baitoci

Wannan waƙar dai tana da baitoci 36 ne kuma‘yar tagwai ce, sannan tana da gajerun jimloli. Mafi yawan jimlolinta suna da cikakkiyar ma’ana.

5.10 Amsa-amo (Kafiya)

Waƙar ba ta da amsa amo saboda ba daidaito na haruffan waƙar a farko ko a ciki ko wajen baiti. Kowane baiti yana ƙarewa daban.

5.11 Salon Waƙar

Waƙar tana ɗauke da kalmomin aro daga Turanci (kamar minister da billa da sinima da coci da champions League) da kuma Larabci (kamar Allah da Rabbu da Ilahu da sharri). Haka nan mawallafin ya yi amfani da miƙaƙƙen salo da ya isar da saƙonsa kai tsaye. Da an karanta waƙar za a fahimci cewa mawaƙin yana ƙoƙarin faɗakarwa ne da jawo hankalin mutane a kan cutar Korona da abubuwan da ta haifar a cikin duniya.

Kalmomin da aka yi amfani da su masu sauƙin ganewa ne hatta na Turanci da na Larabcin, kuma mawallafin ya sarƙa saƙonsa cikin gajerun jimloli waɗanda akasari suke da cikakkiyar ma’ana bisa kansu. A taƙaice dai waƙar ta gamsar kuma saƙonta ya fito fili.

Wani salo da aka lura da shi, shi ne mawaƙin bai buɗe waƙarsa da yabo ga Ubangiji ko manzonsa ba, amma ya rufe ta da addu’a. Haka kuma, mawallafin ya buɗe waƙar da bayanin irin tasirin annobar ga yanayin rayuwa inda ya nuna ta sauya irin ayyukan sharholiyar da jama’a suke yi duk sun daina.

5.12 Dabarun Jawo Hankali

Dangane da kalmomin fannu waƙar ta zo da kalmomin da suka dace da jigonta na faɗakarwa da tsoratarwa. An yi amfani da kalmomi kamar su Ilahu da Rabbu da tuba da rabauta da wa’azi da zunubi da shakka da Allahuda sharri da saɓo da sauransu. Waɗannan kalmomi duk sun dace da jigon waƙar. An lura da cewa waƙar ta zo da jaddadar ƙarfafawa domin tabbatar da munin cutar Korona ga jama’a.

5.13 Sarrafa Harshe

Sarrafa harshe ya shafi yadda mawaƙi ya yi amfani da harshe mai sauƙin fahimta ko mai tsauri. Da kuma, yadda mawaƙi ya yi amfani da kalmomin aro na Larabci da Turanci da sauransu. Haka nan kuma, mai nazarin rubutacciyar waƙa zai yi la’akari da luggogin harshe da mawaƙi ya yi amfani da su domin ƙawata waƙarsa ((Muhammad, 2003:145).

Mawallafin ya yi zaɓen kalmomin da suka dace da jigon waƙarsa. Akwai baƙin kalmomin da aka yi amfani da su na Turanci irin su; sinima da gwamna da minista da coci da Champions League da sauransu. Haka kuma, ya sanya wasu baƙin kalmomi daga harshen Larabci irin su; Ilahu da Rabbu da tuba da rabauta da wa’azi da zunubi da shakka da Allahu da sharri da sauransu. Sannan kuma, mawallafin ya yi amfani da Hausar Kananci a waƙarsa. Akwai karin harshen Kananci kamar; mui da kilaki da kufai da sauransu.

Haka nan kuma, marubucin ya amfani da alamtarwa a cikin waƙarsa ta yadda za ta ƙara armashi ga baitocin waƙar kamar haka:

Ta bi gwamna har gidansa,

Ta shaƙi wuyan minister.

(Baiti na 6)

Abuja har Billa,

Ta shige ta yi sheƙa.

(Baiti na 8)

Masu sheƙe aya su more,

A Italiya ko Amurka.

(Baiti na 14)

Ni Khalid ba ni shakka,

Tabbas cutar Korona,

Jan kunne ce gare mu.

(Baiti na 30)

Bayan nan kuma, ya yi amfani da mutuntarwa dadabbantarwa domin ya ƙara fito da yadda Korona ta samu wurin zama a ƙasashe. Misali.

Tai ƙwayaye ta ‘ya’ya,

Ta miƙe ƙafa a fada.

(Baiti na 9)

Ba ta kunya ba ta tsoro,

Ba ta sabo ba sanayya.

(Baiti na 19)

Sannan kuma, ya yi amfani da siffantarwa domin nuna munin Korona a Turai kamar haka:

Kufai a kira yi Turai,

Champion League tsaya cik.

(Baiti na 16)

Haka zalika, marubucin ya sarƙa karin magana a cikin waƙarsa domin ta haskaka, ta faɗakar ta kuma ilimantar da jama’a kamar yadda za a gani a baitocin da ke a ƙasa.

Kurciya in ta yi kuka,

Saƙo nata ban da wawa.

(Baitoci na 25).

Marubucin waƙar ba tsaya nan ba, ya yi amfani da kirari da wasa kai ga kansadomin nuna mallaka ga abin ƙaunarsa da kuma nuna nasabarsa kamar yadda yake a baiti na 32.

Ni Imam Khalid na Indo,

Jikan Hauwa’u tabbas.

Daga ƙarshe, ya rufe waƙarsa da addu’ar neman ƙarin fahimta da tuba ga Ubangiji a kan laifuka. Kamar haka:

Allahu kasa mu gane,

Mu tuba zuwa gare Ka.

(Baiti na 36).

5.14 Karin Waƙar

An gina wannan waƙa a kan karin Ramal inda aka samu ƙafa ta 7 ta maimaita kanta wato aka samu:

Faa-i-laa-tun + Faa-i-laa-tun (- Ɓ - - + - Ɓ - -).

Misali a baiti na uku:

Tituna leƙa ka duba, (- ɓ - - + - ɓ - -).

Kasuwanni har mashaya. (- ɓ - - + - ɓ - -).

7 + 7

7 + 7

Ramal.

6.0 Shawarwari

A duk lokacin da mai rubutu ya gama rubutunsa bai rasa bayar da shawara domin inganta ɓangaren da ya zaɓa ya gudanar da bincikensa, don haka muna masu bayar da shawara ga manazarta da masana da su duƙufa wajen yin bicike-bincike a kan ayyukan da mawallafa rubutattun waƙoƙin Hausa suka yi a kan cutar Korona biros domin an yi waƙoƙi masu ma’ana masu ɗauke da jigogi mabambanta a kan cutar waɗanda da suke da buƙatar a gudanar da bincike a kansu.

Wannan kuma shawara ce ga mawallafa da ƙara zage damtse wajen ƙirƙiro sababbin waƙoƙin faɗakarwa a kan cutar Korona saboda waƙoƙinsu suna da saurin isar da saƙo ga jama’a ga shi kuma manazarta suna ƙara samun damar gudanar da bincike-bicike a kansu.

7.0 Kammalawa

Wannan takarda ta ƙunshi muhimman bayanai a kan hanyoyinda masana suka samar domin yin tarken kowace rubutacciyar waƙar Hausa, sannan aka yi amfani da waɗannan hanyoyin domin yin tarken faɗakarwa a waƙar Annobar Korona ta Khalid Imam. Takardar ta ƙunshi salsalar waƙar da tarihin mawallafi da shekarar waƙar da jigo da gajarce jigo da warwarar jigo da zubi da tsarin waƙar da zubi tsarin baitoci da karin waƙar da salo da dabarun jawo hankali da sarrafa harshen waƙar. A sakamakon bincike an gano cewa waƙar ta cancanci a yi nazarinta domin tana ɗauke da muhimmin jigo na faɗakarwa wanda aka gina waƙar a kansa. Kuma waƙar ta mallaki muhimman ɓangarori da tarke yake buƙata a yayin nazari.

Manazarta

Auta, A.L. (2017). Faɗakarwa A Rubutattun Waƙoƙin Hausa. Bayero Uniɓersity, Press.

Bala, I. da Imam. K. (2020). Corona blues (A Bilingual Anthology of Poetry). Whetstone Publishers.

C.N.H.N (2006). Ƙamusun Hausa. Ahmadu Bello Uniɓersity, Printing Press.

Ɗangambo, A. (1975). Gadon Feɗe Waƙa. Takardar da ya Gabatar a Taron Ƙara wa Juna Sani. Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero.

Ɗangambo, A. (1981). Ɗaurayar Gadon Feɗe Waƙa. Amana Printers.

Ɗangambo, A. (2007). Ɗaurayar Gadon Feɗe Waƙa(Sabon tsari). Amana Publishers.

Ɗamgambo, Halima, A. (2012). Kwatanta Tubalan Gina Jigo Tsakanin Rubutattun Waƙoƙi da Ƙagaggun Labarai na Hausa. [Kundin digiri na uku da ba a buga ba]. Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero.

Gusau, S.M. (2003). Jagoran Nazarin Waƙoƙin Baka. Benchmark Publishers Limited.

Gusau, S.M. (2008). Dabarun Nazarin Adabin Hausa. Fisbas Media Serɓices.

Muhammad, Y.M. (2003). Adabin Hausa. Ahmadu Bello Uniɓersity Press Ltd.

Yahya, A.B. (2014). Gudale Waƙar Soyayya: Misalin Gazl (Ghazal) Cikin Rubutattun Waƙoƙin Hausa. Garkuwan Adabin Hausa a Festschrift in Tribute to Abdulƙadir Ɗangambo. Bayero Uniɓersity Kano. 125-138.

Yahya, A.B. (2015). Rerawa Ruhin Waƙa da Matsayinta a Waƙoƙin Hausa na Baka da Rubutattu. Algaita Journal of Current Research in Hausa Studies. Bayero Uniɓersity. Special Edition, 10-15.

Ratayen Waƙar Annobar Korona

1. Masu gaɗa suna ta shewa,

'Yan caca da masu karta.

2. 'Yan daudu da ma kilaki,

Sun tsere babu kowa.

3.Tituna leƙa ka duba,

Kasuwanni har mashaya.

4. Makarantu har sinima,

'Yan ƙwallo da masu dambe.

5. Sun ɓace duk don Korona,

Ko'ina duka tsit kake ji.

6. Ta bi Gwamna har gidansa,

Ta shaƙi wuyan Minista.

7. Can a Landan ga Yarima,

Ta bi shi cikin turaka.

 

8. A Abuja har a Billa,

Ta shige ciki ta yi sheƙa.

9. Tai ƙwayaye ta yi 'ya'ya,

Ta miƙe ƙafa a fada.

10. Tabbas cutar Korona,

Annoba ce ta gaske.

11. A masallatai da coci,

Duk an koma ga Allah.

12. Sarki mai shirya komai,

Dole ne bauta gare shi.

13. Ba tsumi kuma ba dabara,

Duniya yau an bi Allah.

14. Masu sheƙe aya su more,

A Italiya ko Amurka.

15. Har ƙasar Sin can a Chana,

Ta kai da yawa kushewa.

Ko Farisa har Faransa,

Ba kowa yau a titi.

16. Kufai a kira yi Turai,

Champions League an tsaya cik.

17. Ba a yin zancen Ronaldo,

Har Messi ba batunsa.

18. Ita annobar Korona,

Cuta ce babu shakka.

19. Ba ta kunya ba ta tsoro,

Ba ta sabo ba sanayya.

 

20. Yau mutum ya gane cewa,

Bai da ƙarfi, sai na Allah.

21. Bai da sauran duk dabara,

Kariyarsa tana ga Rabbu.

22. Gatan kowa Ilahu,

Mui ta bauta mai da ɗa'a.

23. Ma rabauata a yau da gobe,

Don ko dai cutar Korona.

24. Wa'azi ce babu shakka,

Me je shi ke asara.

25. Kurciya in ta yi kuka,

Saƙo nata ban da wawa,

26. Bare gaula da soko.

Masu shashanci a hanya.

27. Hankali kura kira shi,

Ta yin zabari na guga.

28. Mai rabo shi ke rabauta,

In an wa'azi ya ɗauka.

29. Zunubansa ya nemi tuba,

Kan ya ji shi cikin kushewa.

30. Ni Khalid bani shakka,

Tabbas cutar Korona.

Jan kunne ce gare mu.

Mu bar saɓo da sharri.

31. Mu so junanmu gaske,

Hakan zai taimake mu.

 

32. Ni Imam Khalid na Indo,

Jikan Hauwa’u tabbas.

33. Nasan cutar Korona,

Ƙanwa ce gun talauci.

34. Wajen ƙeta da sharri,

Har ma yawo a dangi.

35. Ni nan zan sanya aya,

Cikin waƙar Korana.

36. Allahu kasa mu gane,

Mu tuba zuwa gare Ka.

(Bala da Imam, 2020 sh. 108-114).



[1]. Hira da Khalid Imam, a ranar 23/8/2021 a wayar hannu.

Post a Comment

0 Comments