Ticker

6/recent/ticker-posts

Gwagwarmayar Kare Kimar Hausa: Tunawa Da Hambali Jinju Da Sauran Bijimai

GWAGWARMAYAR KARE ƘIMAR HAUSA: TUNAWA DA HAMBALI JINJU DA SAURAN BIJIMAI

Daga:

Najib Abubakar Yusuf

Ɗalibin Kimiyyar harshe, manazarcin al’adu, ɗan gwagwarmayar kare asalin Hausawa

Lokacin da ruwan tagging ya fara zubowa daga yan uwa da abokan hulɗa, zuciyata ta cika da farin ciki da kuma alhini. Farin ciki, saboda an fara fahimtar irin gwagwarmayar da aka shafe shekaru ana yi wajen kare harshen Hausa da al’adunta. Alhini kuwa, domin mafi yawan waɗanda suka fara wannan tafiya, Allah ya riga su da mu – musamman Marigayi Sheikh Hambali Jinju.

Hambali Jinju

Sheikh Hambali Jinju – Gwarzon da Bai Yi Haske  a Rana ba

Ban san fuskar Marigayin ba, amma ban rasa alamar hasken da ya bari a kan hanya ba. Na fara jin sunansa daga Shehin malamaina, Prof. Dan Ladi Yalwa na Jami’ar Bayero – wani babban masani a fannin ilimin harshe. Daga wannan ambato ne na fara kwaranya bincike, ina bibiya a dakin karatu na gidan Ɗan Hausa dake Nassarawa a Kano. A nan ne na fara karanta wasu daga cikin muhimman ayyukansa da suka shafi Hausawa da Hausar da kuma ilimin magungunan gargajiya. Wata hanya ce da take haɗa kimiyya da al’ada cikin salo mai tsabta.    Gwagwarmayar Kare ƙimar Hausa: Tunawa da Hambali Jinju da Sauran Bijimai

Lokacin da ruwan tagging ya fara zubowa daga yan uwa da abokan hulɗa, zuciyata ta cika da farin ciki da kuma alhini. Farin ciki, saboda an fara fahimtar irin gwagwarmayar da aka shafe shekaru ana yi wajen kare harshen Hausa da al’adunta. Alhini kuwa, domin mafi yawan waɗanda suka fara wannan tafiya, Allah ya riga su da mu – musamman Marigayi Sheikh Hambali Jinju.

Sheikh Hambali Jinju – Gwarzon da Bai Yi Haske  a Rana ba

Ban san fuskar Marigayin ba, amma ban rasa alamar hasken da ya bari a kan hanya ba. Na fara jin sunansa daga Shehin malamaina, Prof. Dan Ladi Yalwa na Jami’ar Bayero – wani babban masani a fannin ilimin harshe. Daga wannan ambato ne na fara kwaranya bincike, ina bibiya a dakin karatu na gidan Ɗan Hausa dake Nassarawa a Kano. A nan ne na fara karanta wasu daga cikin muhimman ayyukansa da suka shafi Hausawa da Hausar da kuma ilimin magungunan gargajiya. Wata hanya ce da take haɗa kimiyya da al’ada cikin salo mai tsabta.

Na samo wani littafi daga ayyukansa wanda ya yi cikakken bayani kan itatuwan da ake amfani da su wajen magani. Yana bayyana matakan sarrafa su da kuma yadda ake amfani da su cikin hikima da tsari. Sai dai mafi wahala da ban zan manta da ita ba, ita ce lokacin da nake nemo"Garkuwar Hausa". Na zaga Kano, Zariya, Niamey da Dosso – amma sai da Ɗan Marigayin, Abdullahi Hambali Jinju , ya taimaka da hotunan littafin kafin na samu.

 Duk da har yanzu hotunan ba cikakku bane, ina fatan zai sake turo su domin a mayar da su pdf, a saka su cikin archive domin kowa ya ci moriyar su.

Tarihi Yana Maimaida Kansa – Harshen Hausa a Matsayin Harshen Hukuma

Maganar da ake ta yi yau game da mai da Hausa harshen hukuma, musamman a Nijar karkashin jagorancin Général Abdourahamane Tiani da CSNP, ba sabon abu bane. Wannan tunani yana daga cikin muhimman ra’ayoyin Marigayi Sheikh Hambali Jinju. A lokuta da dama, ya roki hukumomi a Nijar da Najeriya da su duba mahimmancin Hausa a matsayin harshen farko – domin ta mamaye zukata da harsunan maƙwabta.

A cikin "Garkuwar Hausa", Sheikh Jinju ya bayar da ra’ayinsa game da asalin Hausawa. Duk da yake akwai ra’ayoyi da dama daga magabata, na Marigayin yafi kusa da gaskiya. Amma har yanzu bai ɗora hujjojinsa kacokan a kansu ba – domin ya ƙarfafa ci gaba da binkice tare da neman hujjoji daga sabon zamani. Wannan ya nuna cewa bai kulle kofa ba – ya buɗe ta domin sabbin fasahohi da sabbin manazarta su shigo su cika gibi.

Hasashen da Ya Kusa Zama Gaskiya

Idan aka kwatanta ra’ayinsa da na masana na baya-bayan nan kamar Prof.  Malumfashi Ibrahim Aliyu Mohammed , za a ga cewa hasashen Marigayin yana gab da cika. A lokacin sa, ba a da manyan kayan aikin nazari kamar yanzu. Amma a yau, masana kamar Dr. Hamidu Korau, Andre Salifou, da Maitre Souley Garba sun ƙarfafa harsashe da bincikensa ta hanyar amfani da dabarun zamani.

Wannan shi ne hasashen da nake ganin ya kusa tabbata. Mun zo gurin da Marigayin ya yi hasashen za a zo – gurin da za a ɓalle gaskiyar asalin Hausawa.

Batun Siyasa da Tabbatar da Tushen Ƙabila

Harshe da siyasa suna tafiya ne tamkar kaya da ɗan dako. Bincike ya nuna cewa ba kawai iyakar jin harshen Hausa ke gina mutum a matsayin ɗan ƙabila ba – akwai sassa uku masu muhimmanci: gadon asali, assimilating al’ada, da musamman wuri (geographic identity).

A nan ne aka fi samun tashin hankali. Misali, a lokacin Marigayin Sheikh Salihu Bawa Jangwarzo, ya hana kowane Bahaushe yin yaƙi da wata ƙabila – a maimakon haka ya jaddada zaman lafiya da aure tsakanin kabilu. Duk da haka, akwai sarkakiyar tarihin da ke nuna yadda wasu kabilu kamar Zabarmawa da Fulani suka janye daga haɗuwa da Hausawa – saboda fargabar narkewa.

A halin yanzu, tsarin da aka yi a zamanin Sardauna, na haɗa Hausa- Fulani a matsayin tsintsiya madaurinki ɗaya, yana ci gaba da bayyana gaskiyar sauyawar al'adu.

 A sakamakon haka, harshen Hausa ya shafi Arlit, Agadez, Azawad – har da jamhuriyar Mali. Wannan shine abin da Sheikh Jinju ya sha kira da shi: “Hausar zamani tana cinye harsuna”.

Kira Ga Hukumomi da Masana

A matsayina na ɗaya daga cikin masu bincike da masu kishin Hausa, ina roƙon jami’o’in da ke Kasar Hausa – musamman Bayero, Ahmadu Bello, Usman Dan Fodio – su tsunduma cikin faɗaɗa binkice game da Hausawa. A ci gaba da ayyukan Jinju, Malumfashi da sauran bijiman zamani. Hakanan hukumomin hulɗar al'adu su tallafa wa irin wannan bincike – domin shine asalin gina ƙasa mai tushe.

 Gaba dai Hausa, Gaba da Haske

A yau, ya dace mu daina fatan samun ƙasa guda daya da ke amfani da Hausa a matsayin harshen hukuma – mu fara gina ta da kanmu. Yanzu da Nijar ta bude kofa, ya rage namu mu tabbatar da cikar mafarkin Jinju.

Allah ya gafarta wa Marigayin Sheikh Hambali Jinju. Allah ya tsare duk masu kare martabar Hausa. Allah ya ɗaga darajar Hausawa a duniya.

Hambali Jinju

Post a Comment

0 Comments