Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Ce Wa Mai Azumi Ya Ibada

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Salamun Alaikum, Dr wai wani malami ne yake cewa bai halatta mutum ya cewa ɗan'uwansa musulmi da azumin nan ba ya ibada ba, wai sai dai yace masa ya azumi, Dr. Meye gaskiyar wannan maganar ?.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikum assalam, Azumi ibada ne tun da Allah ya shar'anta shi ne saboda tsoransa, kamar yadda ya fada a suratul Bakara, Ibada ita ce duk abin da Allah yake so kuma ya yarda da shi na daga zance ko aiki, na fili da na ɓoye kamar yadda malaman musulunci suka bayyana.   

Azumi ibada ne tun da Allah ya yarda da shi kuma yana nisanta wanda ya yi shi daga wuta, kuma ya keɓance shi da daraja ta musamman wacce babu irinta, kamar yadda hadisai ingantattu suka tabbatar, ga shi kuma sababin shiga aljanna, ibada kuma ita ce hanyar shiga ni'imomin lahira, wannan yake nuna kuskuran waccar maganar da kuma karancin ilimin wanda ya fade ta.      

Allah ne mafi sani.

✍️ Dr Jamilu Zarewa.

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam 

Post a Comment

0 Comments