𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu Alaikum malam Dan Allah Ya ake gane daren lailatul qadri? meye alamomin lailatul qadari da falalarsa?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa'alaikumus
Salaam Warahmatallahi Wabarkatahu
Allah ﷻ ya fifita wani
dare a cikin watan Ramadan ya ba shi wata daraja da ɗaukaka ta musamman,
kuma ya keɓance shi da wata falala ta musamman wadda bai bawa sauran
darare ba, wannan kuma zaɓi ne da ganin dama ne daga gare shi maɗaukakin sarki,
domin yana yin abin da ya ga dama a cikin halittarsa. Allah ya ce:
لَيْلَةُ الْقَدْرِ خَيْرٌ مِّنْ أَلْفِ شَهْرٍ
“Daren
Lailatul Qadari ya fi wata dubu alheri” (suratul qadri aya ta 3).
Ma’ana aiki
a cikin wannan dare ya fi aikin wata dubu ba a daren Lailatul Qadari ba. Allah
Mai Girma Da Buwaya ya ce:
سَلَامٌ هِيَ حَتَّىٰ مَطْلَعِ الْفَجْرِ
“Aminci ne a
cikinta har zuwa ɓullowa alfijir”. (Suratul Qadr Aya ta : 5)
Ma’ana
dukkan wannan dare alheri ne, babu wani sharri a cikinsa tun daga farkonsa har
zuwa ɓullowa alfijir.
Dare Ne Mai albarka. Allah Ya ce:
إِنَّا أَنزَلْنَاهُ فِي لَيْلَةٍ مُّبَارَكَةٍ ۚ إِنَّا
كُنَّا مُنذِرِينَ
“Haqiqa mun
saukar da shi a cikin dare mai albarka. Haqiqa mu masu gargadi ne”. (Suratul
Dukhan Aya ta 3).
Abdullahi Ɗan Abbas ya ce, “Yana nufin daren lailatul Qadri”. A
Cikinsa Ne Aka Saukar Da Alkur'ani. Allah Ya ce:
إِنَّا أَنزَلْنَاهُ فِي لَيْلَةِ الْقَدْرِ
“Haqiqa Mun
saukar da shi a cikin daren Lailatul Qadri” (suratul qadr aya ta 1).
A Cikinsa
Ake Qaddara Dukkan Abubuwan Shekara, Allah ya ce:
فِيهَا يُفْرَقُ كُلُّ أَمْرٍ حَكِيمٍ
“A cikinsa
ake rarrabe kowanne lamari abin hukuntawa” (suratul Dukhan Aya ta 4).
Manzon Allah
Sallallahu alaihi Wasallam ya kasance yana ƙara ɗamara a goman
karshe, yana raya dukkan dararrakinsa, kuma yana tada iyalansa. Wanda ya tsayu
ma wannan dare yana mai imani mai neman lada an gafarta masa zunubansa da suka
gabata (Bukhary da Muslim).
Allah ya ɓoye wannan dare don
musulmi ya yi qoqari da himma a goman qarshe ta Ramadan, musamman ma a dararen
da suke mara, waɗanda su ne daren 21, 23, 25, 27, 29, saboda faɗin Manzon Allah (
Sallallahu Alaihi Wasallam) “Ku kintaci daren Lailatul Qadri a cikin marar
goman qarshe ta Ramadan” [Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi].
Wasu malamai
sun yi bayanin cewa daren Lailatul Qadri yana yawo a tsakanin waɗannan darare (Wata
shekarar wannan, wata shekarar wancan) saboda a yi aiki da dalilan da suka zo a
kan haka baki ɗaya.
Dare Ne Mai
Haske, Babu Zafi Ko Sanyi A Cikinsa. An karɓo daga Jabir ɗan Abdullahi –
Allah ya yarda da shi – ya ce, “Haqiqa ni an nuna min daren Lailatul Qadri,
sannan an mantar da ni shi, yana goman qarshe na Ramadan, dare ne babu sanyi ko
zafi a cikinsa, kuma mai haske ne, ba zafi ba sanyi (mai cutarwa acikinsa)”
[Ibn Khuzaima ne ya rawaito shi].
Rana Tana
Fitowa Da Safiyar Daren Fara Tas Ba Haske Tare Da Ita. Yayin da aka tambayi
Ubayyu ɗan Ka’abu – Allah
ya yarda da shi – a kan alamomin daren Lailatul Qadri, sai ya ce, “Alamar da
Manzon Allah ( Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ba mu labari ita ce, rana tana ɓullowa a wannan
rana babu haske tare da ita” [Tirmizi ne ya rawaito shi].
An karɓo daga Aisha –
Allah ya yarda da ita – ta ce, na ce, ya Rasulallahi, idan na dace da daren
Lailatul Qadri, me zan yi addu’a da shi? Sai ya ce, ki ce;
اللّٰهُمَّ إِنَّكَ عَفُوٌّ تُحِبُّ الْعَفْوَ فَاعْفُ
عَنِّيْ
Ma’ana “Ya
Allah kai mai afuwa ne, kana son afuwa, ka yi min afuwa” [Tirmizi ne ya rawaito
shi].
Yan uwa!
Wannan addu'ar ita za mu yawaita yi a cikin Waɗannan kwanaki goma
har mu dace da lailatul Qadr in shaa Allah, Addu'a ce da sunnah ta koyar. Wanda
Allah ya sa ya dace da wannan dare, to ya yawaita Ibada da Addu'a, Karatun
Alkur'ani. Allah ya datar damu da dukkanin alkhairin da ke cikin wannan dare
mai albarka Allah ya bamu ikon lizimtar ta.
WALLAHU
A'ALAM
Zauren
Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...
*** ***
Shin Me Ake Gani A Daren Lailatul Qadri?
𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Shin Gaskiyane Acikin Daren Lailatul Qadari ana Ganin Komai Yanayin Sujada, Kamar Bishiyoyi Da Gidaje Harma Mutum Ya Rinka Hango Ka'aba Daga Duk Inda Yake ???
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wannan bai tabbata ba daga manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam ko magabata na kwarai. Ijtihadin wasu mutane ne ba tareda wani dalili na sharia ba. Amma ya tabbata wasu daga cikin sahabbai "An nuna masu a mafarki cewar daren lailatul Qadari yana cikin bakwai na karshe" Wannan hadisin yanuna cewar an nuna masu ranar ne amma ba wani abu suka gani ba. Amma ana ganin alamomin daren lailatul Qadari kamar yadda Annabi Sallallahu alaihi Wasallam ya bada labari cewa:"Ranar daren lailatul Qadari takan fita batayin zafi. Muslim (Sharhin khadi iyad, 1165). Kuma Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam Ya ce: "A cikinku wa zai tuna daren da wata ya fito kamar rabin akushi? Ana faɗin daren lailatul kadari sai Annabi Sallallahu alaihi Wasallam yafadi haka.
Allah shi ne mafi sani.
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.