Ticker

6/recent/ticker-posts

Ma’anar Harshe Da Adabi

Wannan rubutu ƙarin haske ne ga masu yanke wa ilimin Harshe da Adabi hukunci da mahangar addini, alhali harshe ba shi da addini balle a hukunta shi da shi.

Ma’anar Harshe Da Adabi

Daga

Sani Shehu Lere

Ɗalibi a Tsangayar Nazarin Harsuna da Kimiyyar Harshe, Jami’ar Jihar Kaduna Nijeriya
Lambar Waya: 08062798146

Ma’anar Harshe

Da farko ya kamata mu san cewa idan na ce “harshe ina nufin harshen da ɗan’Adam yake yin amfani da shi wajen sadarwa. Wannan shi yake nuni da cewa harshe shi ne tubalin ginin al’umma.

Duk wata al’umma ta duniya tana da harshen da jama’arta suke yin amfani da shi wajen fahimtar juna a tsakaninsu. Babu wata al’umma da za a kira ta da sunan al’umma sannan a ce kuma ba ta da harshen kanta.

Shi ya sa ya kamata ka ƙara sanin cewa akwai dangantaka ta jini da tsoka tsakanin harshe da al’umma. Al’umma ba ta wanzuwa sai da harshe. Ka ga akwai al’ummar Hausawa harshen da al’ummar suke yin amfani da shi ana kiran sa Hausa.

Saboda haka harshen Hausa halittaccen harshe ne ba jama’a ne suka zauna suka ƙirƙire shi ba. Halittattun harsuna na duniya da ake danganta su da wata al’umma su ne kamar haka: Ingilishi da Jamusanci da Faransanci da Yarabanci da Igbanci da Fulatanci da Angasanci da Larabci da Suwahilanci da makamantansu.

To me ake nufi da harshe?

Masana da dama sun yi ƙoƙarin bayyana ma’anar harshe. Ga bayanin da Zarruq da Wasu suka bayar kamar haka:

Zarruq da Wasu (1986: 1) sun bayyana harshe da cewa “Harshe magana ke nan wadda ake ji a fahimta. Harshe shi ne abin da ya bambanta ɗan’adam da sauran dabbobi. Harshe a wurin ɗan’adam linzami ne na tunani.

Sauran dabbobi sai dai su yi kuka, ko gurnani, ko haushi, ko haniniya, don su nuna fushinsu ko murnarsu, ko wuyarsu, ko daɗinsu. Hatta aku, da yake iya kwaikwayon maganar ɗan’adam, yana yi ne ba tare da tunani ba”.

Ka ga a nan za ka fahimci cewa mutum kaɗai ne yake iya riya abu a zuciyarsa, ko ya gani da idanunsa ko ya ji da kunnuwansa, sannan ya furta da bakinsa. Wannan ne dalilin da ya sa Chomsky (1972) yake cewa ana yin nazarin harshe domin cewa shi harshe shi ne madubin tunanin ɗan’Adam.

Daga ma’anar harshe da na kawo za a fahimci cewa harshe dai muryoyi ne da ake jerantawa bisa kyakkyawan tsari mai ɗauke da ma’ana.

Ma’anar Adabi

Wannan kalma ta ‘adabi’, ararriyar kalma ce daga Larabci (Ɗangambo, 1984; Yahaya, Zariya, Gusau da ‘Yar’aduwa, 1992; Junaidu, da ‘Yar’aduwa, 2002). Ɗangambo (1984), ya ce: “Ma’anarta ta Larabci ita ce “halin ɗa’a, fasaha, ƙwarewa.” To, amma a Hausa, har ma a Larabcin, wannan kalma, tana nufin abubuwan da suka shafi al’adu da rayuwa da fasaha na al’umma; wani lokaci da kuma nazarinsu. A taƙaice, muna iya cewa, adabi, shi ne mudubi ko hoton rayuwa na al’umma.

Wannan, ya ƙunshi yadda al’adunsu, ɗabi’unsu, harshensu, halayyar rayuwasu, abincinsu, tufarsu, makwancinsu, hulɗoɗinsu, tunaninsu, da ra’ayoyinsu da sauran abubuwan da suka shafi dabarun zaman duniya don ci gaba da rayuwa; kai har ma da abubuwan da suka shafi mutuwa.

Adabi shi ne madubin rayuwar al’umma. Misali, idan kana son sanin cikakkiyar al’ummar Hausawa, to ka karanta adabinta. Shi zai bayyana maka komai game da rayuwar Bahaushe kamawa tun daga haihuwa har zuwa mutuwa.

Meye Alaƙar Harshe Da Addini?

Ma’anar Addini: Addini shi ne hanyar rayuwa bisa bautar wani abun bautawa, bisa amfani da tsare-tsaren da wannan abin bautar, ko kuma makusantansa suka tanadar, domin tafiyar da rayuwar yau da kullum ta mabiya wannan Addini, bisa wasu tanaje-tanaje ko tsare-tsare.

Addini ya rabu gida daban-daban, kamar yadda masana addini su ka yi bincike kuma su ka tabbatar. An kasafta Addini gida biyu, wato Addinan Kaɗaitaka da kuma Addinan Tarayya.

Addinan Kaɗaitaka: Waɗannan sune Addinan da suka yarda da wanzuwar abin bauta guda ɗaya tilo, kuma suka tafi akan tabbatuwar wannan abin Bauta a matsayin wanda ya halicci rayuwa da duk abin da rayuwar ta tattara, Mutane, Aljannu, Dabbobi, Tsirrai, Sararin Sammai, Sararin Kassai, Ruwa, Iska da makamantansu.

Addinan da suke a cikin wannan kason sun haɗa da:

Addinin Musulunci Islam. Addinin Kiristanci Christianity. Addinin Yahudanci Yahudanci. Addinin Zarusta.

Littatafan Addinai

Waɗannan addinai sunada littatafai da suka ƙunshi da hukunce-hukuncen na tafiyar da rayuwar jama’a bisa tsari da tsafta da kuma jagoranci. Ubangiji shi ya saukarwa bayinSa littatafan, ta hanyar Mala’ikunSa zuwa ga ManzanninSa domin suyi gargadi da kuma jagoranci bisa hanyarSa.

Addinai da Littatafansu

-Addinin Musulunci (Islam) an saukar masa da Ƙur’ani Mai Girma [Noble Ƙur’an AlKur’ani ta hannun Annabi Muhammad “Sallallaahu Alaihi Wasallam”.

-Addinin Yahudanci Judaism an saukar masa da littafi Zabura [Zaboor Tsohon Alƙawari ta hannun Annabi Musa.

-Addinin Kiristanci Christianity an saukar masa da littafin Injila [Injeel Sabon Alkawari ta hannun Isah ɗan Maryam.

Addinan Tarayya: Wannan nau’in addinai su ne addinan da ba su yadda da bautar Allah ba, mafi yawancinsu su na bautar gumaka ne ko kuma halittu daban-daban kamar Saniya, Macijiya, Birai, Tumaki, shanu, da sauransu. Wasu kuma su na bautar halittu ne kamar su Rana, wata, wuta, Iska, Ruwa, Duwatsu da sauran su.

Ire-iren waɗannan addinai sun yarda da gabatar da hadaya ga ababan bautarsu, kuma basu da wasu tsayayyun dokokin rayuwa ko littatafai da ke dauke da hukunce-hukunce da tsare-tsaren tafiyar da rayuwar yau da kullum, savanin addinan kaɗaitaka.

Addinan da suke cikin wannan kason su ne:

Addinin Buddah. Addinin Hindu. Addinin Aztec Aztec. Addinin Majusanci. Da Sauransu

Addinin Hausawa na Farko

Hausawa kamar sauran mutane suna da addininsu na gargajiya tun kafin zuwan addinin musulunci. A gaskiya ba wanda zai ce ga lokacin da Hausawa suka fara bautar gumaka da tsafe-tsafe. Tarihi ya nuna cewa tun da aka halicci dan’adam, bautar iskoki ta cusu a zuciyarsa. Wannan shi ya sa yake da wuya a bayyana tun sa’ad da abin ya fara.

Dalilai na biyu da ake jin su suka haifar da addinin gargajiya, ba kuma ga Hausawa kadai ba har ma da sauran jinsi iri-iri na duniya. Dalili na farko shi ne, shi dai dan’adam ya dauka cewa kowane abu a duniya yana dabi’a irin tasa, wato wani lokaci zai ji dadi musamman in an faranta masa rai, ya kuma ji zafi in an bakanta masa, har ya kai ga ramuwar gayya.

Alal misali, lokacin da Kanawa ke bautar Tsumburbura a gindin Dala, zamanin Barbushe, duk shekarar da ta zo da wani bala’i sai mutane su dauka cewa lallai an saba wa Tsumburbura. Saboda haka sai a yi yanke-yanken awaki da karnuka don dodon ya sha jini wai ko ya huce. To wasu lokutan kuwa sai a yi sa’a abin ya yi sauki shi ke nan sai a dauka wannan sauki ya faru ne saboda yanke-yanken da aka yi wa gunkin ne.

Dalili na biyu da ake zaton shi ma ya taimaka wajen kago bautar gumaka shi ne ciwo. Sau da yawa akan sami ciwo ya ki ci ya ki cinyewa ga mutum, a yi ta neman magani, amma a banza, sai a dauka ba mai warkar da majinyacin sai dai mutumin da Allah ya yi wa wata daraja ta musamman.

Ana nan har a sami wani boka ya nuna cewa iska kaza ce ta taba mutum amma shi zai warkar da shi. Idan aka yi katari sai kuwa mutumin ya warke. Da zarar haka ta faru fa sai mutane su yi imani da wannan iska da boka ya ambata, shi kuma boka kasuwa ta bude ke nan.

Ana yin bauta ta hanyoyi dabam-daban. Wasu sukan sassaka gunkinsu da kansu, su yi wan mutum-mutum su rika bauta masa. Wasu kuma sukan bauta wa iskokai.

Dangane da bautar gumaka wajen Hausawa, su ba sa sassaka gunki don yi masa bauta, a’a, sai dai bautar iskokai ta hanyar bori. Kanawa suna bautar Tsumburbura a dutsen Dala.

Akwai wasu gumaka makamantan waɗannan a wasu wurarae a ƙasar Hausa. A ƙasar Katsina, akwai mutanen Kainafara, arnan Birci a ƙasar Dutsin ma, masu bautar wani gunki mai suna Dan talle. Sunan mai kula da wannan gunki shi ne Sarkin Noma.

Kamar Barbushe Sarkin Noma shi ne mai ba da labarin sakon da Dan talle ya yi ga mabiyansa. Su ma mabiyan Dan talle kabilar Kainafara na yin bikinsu ne shekara-shekara kuma suna yin yanke-yake kamar dai mutanen Barbushe.

Akwai kuma wasu maguzawa masu bautar wani gunki mai suna Magiro a dutsen Kwatarkwashi a cikin jihar Sakkwato. Mai kula da tsafin shi ne Magajin Ranau. Shi ma ana yi masa yanke-yanke kamar yadda ake yi wa Tsumburbura sai dai su bakin sa ake yanka masa ko bakar akuya.

Bayan wadannan gumaka kuma, Hausawa Maguzawa kan yi tsafe-tsafe na gida. Misali shi ne, kusan kowane Bamaguje ya ajiye wata halitta wadda ya dauka ita ce kan gidansa. Wasu sukan dauki dabbobi kamar damisa, kura ko zomo ya zama kan gidansu. Duk abin da aka dauka ya zama kan gida to ba hali wani dan gidan ya ci namansa, ko ya kashe shi ko kuma ya cuce shi ko ta wace hanya.

Musuluncin Bahaushe

Tasirin Addinin Gargajiya: A halin da ake ciki yanzu, ko da yake mafi yawan Hausawa sun karbi addinin musulunci hannu bibiyu, har ma ta kai fagen da an ambaci sunan Bahaushe sai a kawo addinin musulunci ciki, don ganin cewa Hausa da musulunci sun kusa zama abu daya duk da haka akwai Hausawa wadanda har yanzu tasirin addinin gargajiya bai bar su ba.

Sanin kowa ne cewa har yanzu akwai Maguzawa a ƙasashen Kano da Katsina wadanda ba su daina yin tsafi da bautar gumaka ba. Waɗannan Maguzawa har yanzu sukan yi bukukuwa da tsafe-tsafe iri-iri. Ta hanyarsu ne wasu Hausawan musulmi kan nemi taimako wajen dodo don neman biyan bukata.

Idan muka juyo ta fannin bori (wanda al’ada ce ta Maguzawa masu bin addinin gargajiya), za mu ga cewa har kwanan gobe Hausawa musulmi suna yi kuma duk mai yi ya ba da gaskiya.

www.amsoshi.com

Post a Comment

0 Comments