Ticker

6/recent/ticker-posts

Da Munguwar Rawa Gara Kin Tashi – Kashi Na Biyar (5)

YAYE SHUBUHAR KAFA HUJJA DA MAGANGANUN MALAMAI DON KARE SAYYID QUTUB A KAN AKIDARSA TA KHAWARIJANCI:

Jahilci da rashin fahimtar Nassoshi da maganganun Malamai yana daga cikin manyan siffofin da Khawarijawa suka siffantu da su. Saboda wannan jahilcin ne ya sa suke daukar Ayoyin da suka sauka a kan Kafirai suna dorawa a kan Musulmai, suna halasta jinanensu, kamar yadda Abdullahi bn Umar (ra) ya ce:

«إنهم انطلقوا إلى آيات نزلت في الكفار، فجعلوها على المؤمنين».

صحيح البخاري (9/ 16)

"Sun nufi zuwa ga ayoyin da suka sauka a kan kafirai sai suka dora su a kan muminai".

Haka ya tabbata cewa; Sayyidina Aliyu (ra) ya aika dan'uwansa Abdullahi bn Abbas (ra) zuwa ga Khawarijawa don ya tattauna da su, a cikin tattaunawar da ta gudana tsakaninsu ya bayyana cewa; Jahilci ne ya kai Khawarijawa ga mummunar fahimtarsu ga Addini da guluwwi a cikinsa, da fassara Alkur'ani da yin tawilinsa ba bisa tawilinsa da fassararsa a wajen Malamai masana ma'anoninsa ba. Wanda hakan ya kai su ga kirkirar Bidi'ar "Tahkimi" (Hakimiyya), suka kafirta Musulmai da ita, suka halasta jinanensu.

A lokacin da Ibnu Abbas (ra) ya isa gare su, ya tambayi Khawarijawan dalilansu na kafirta Aliyu (ra) da yakarsa. Sai suka ambaci wasu shubuhohi guda uku. Shubuharsu ta farko a kan "Tahkimi" (Hakimiyya) ce. Ga kadan daga abin da ya gudana tsakaninsu:

Farko ya fara nuna musu matsayinsu ne, cewa; sun rudu sun yi watsi da fahimtar Malamai Sahabban Annabi (saw), inda ya ce:

((قلت: أتيتكم من عند صحابة النبي صلى الله عليه وسلم من المهاجرين والأنصار، لأبلغكم ما يقولون المخبرون بما يقولون فعليهم نزل القرآن، وهم أعلم بالوحي منكم، وفيهم أنزل، وليس فيكم منهم أحد)).

((Na ce musu: Na zo muku ne daga wajen Sahabban Annabi (saw) cikin Muhajirun da Ansar, don na isar muku da abin suke fada, kuma sun san abin da suke fadan, da ilimi suka fada, saboda a cikinsu Alkur'ani ya sauka, sun fi ku sanin Wahayin da aka yi wa Annabi (saw), a cikinsu Wahayin ya sauka, kuma babu dayansu (Sahabai) a cikinku)).

Wannan bayani ya kunshi bayanin jahilcin Khawarijawa da yadda suke saba fassarar Malamai ga Nassoshin Shari'a.

Sai kuma ya tambaye su a kan shubuhohin nasu, inda ya ce:

((قلت: أخبروني ماذا نقمتم على ابن عم رسول الله صلى الله عليه وسلم، وصهره والمهاجرين والأنصار؟ قالوا: ثلاثا. قلت: ما هن؟ قالوا: أما إحداهن فإنه حكم الرجال في أمر الله، وقال الله تعالى: {إن الحكم إلا لله} [الأنعام: 57] وما للرجال وما للحكم؟ فقلت: هذه واحدة...)).

((Ku fada min dalilin fushinku a kan dan baffan Manzon Allah (saw), kuma surukinsa, tare da sauran Muhajirai da Ansar. Sai suka ce: abubuwa ne guda uku: Sai ya ce: menene su? Sai suka ce: Amma na farkonsu shi ne; ya nada mazaje su yi hukunci a lamarin Allah, alhali Allah ya ce: {Babu Hukunci sai na Allah}, don haka me ya hada mazaje da hukunci? Sai ya ce: na ji daya…)).

Bayan sun gama ambato sauran shubuhohin nasu na kafirta Sayyidina Aliyu (ra) da yakarsa, sai ya fara da mafi girmansu wato shubuhar "Tahkimi" (Hakimiyya), sai ya ce:

((فقلت لهم: أرأيتم إن قرأت عليكم من كتاب الله ومن سنة نبيه صلى الله عليه وسلم ما يرد به قولكم أترضون؟ قالوا: نعم. فقلت: أما قولكم: حكم الرجال في أمر الله فأنا أقرأ عليكم ما قد رد حكمه إلى الرجال في ثمن ربع درهم في أرنب، ونحوها من الصيد، فقال: {يا أيها الذين آمنوا لا تقتلوا الصيد وأنتم حرم} [المائدة: 95] إلى قوله {يحكم به ذوا عدل منكم} [المائدة: 95] فنشدتكم الله أحكم الرجال في أرنب ونحوها من الصيد أفضل، أم حكمهم في دمائهم وصلاح ذات بينهم؟، وأن تعلموا أن الله لو شاء لحكم ولم يصير ذلك إلى الرجال، وفي المرأة وزوجها قال الله عز وجل: {وإن خفتم شقاق بينهما فابعثوا حكما من أهله وحكما من أهلها إن يريدا إصلاحا يوفق الله بينهما} [النساء: 35] فجعل الله حكم الرجال سنة مأمونة، أخرجت عن هذه؟ قالوا: نعم...)).

المستدرك على الصحيحين للحاكم (2/ 164)

Sai Ibnu Abbas (ra) ya kafa musu hujja da Ayoyin Alkur'ani inda Allah Madaukaki ya nada mazaje a matsayin masu hukunci, ta yadda ya yi umurni ga adilai biyu su yi hukunci a kan dabbar farauta. Haka kuma Allah ya yi umurni da mazaje biyu su yi hukunci a tsakanin ma'aurata biyu idan an samu sabani.

Wannan sai ya nuna jahilcin Khawarijawa a fili, suna raya bin Alkur'ani, amma kuma sun fi kowa jahiltar hakikanin ma'anoninsa, saboda ba su dauki iliminsa daga Malamai ba. Kuma haka suke a kowane zamani.

Abin nufi a nan, jahilci da rashin fahimtar maganar Allah ne ya kai Khawarijawan farko ga kafirta Musulmai, sun zo sun dauko Ayoyi suna kafa hujja da su, alhali ba su san ma'anoninsu ba. Kuma wannar sifa ba ta gushe a tare da Khawarijawa a kowane zamani ba. Har Khawarijawan wannan zamani; kungiyoyin Ta'addancin da suka tasirantu da Fikrorin Sayyid Qutub. Ba sa fahimtar maganar Allah da maganar Manzonsa (saw) da maganganun Malamai, amma sai su dauko su suna dora su kan mutane suna kafirta su, suna halasta jinanensu.

A wannan zamani Khawarijawa 'Yan Ta'adda suna dauko maganganun Malamai Ahlus Sunna suna kafa hujja da su a kan ta'addancinsu, alhali a bisa hakika maganganun ba sa nuni ga ta'addancin nasu ta kusa ko ta nesa. Amma fa ga wanda yake iya fahimtar maganganun Malaman, kuma ya san ma'anoninsu.

Asali fikrar ta'addancinsu a wannan zamani ya samo asali ne daga Sayyid Qutub, amma don kokarin kawata bidi'arsu da boye barnarsu sai suna dauko maganganun Malamai suna kafa hujja da su, don a dauka cewa; Manhajin nasu ya ginu ne a bisa Alkur'ani da Sunna da Fahimtar Malaman Sunna. Alhali ba haka lamarin yake ba.

Daga cikin irin maganganun Malaman zamani da suke kafa hujja da su akwai:

(1) Maganar Shaikh Muhammad bn Ibrahim Alu-Shaikh:

((إن من الكفر الأكبر المستبين تنزيل القانون اللعين منزلة ما نزل به الروح الأمين على قلب محمد صلى الله عليه وسلم، ليكون من المنذرين بلسان عربي مبين))

فتاوى ورسائل سماحة الشيخ محمد بن إبراهيم بن عبد اللطيف آل الشيخ (12/ 284)

Da fadinsa:

((البلد التي يحكم فيها بالقانون ليست بلد إسلام، تجب الهجرة منها. وكذلك إذا ظهرت الوثنية من غير نكير ولا غُيرت فتجب الهجرة، فالكفر بفشو الكفر وظهوره. هذه بلد كفر)).

فتاوى ورسائل سماحة الشيخ محمد بن إبراهيم بن عبد اللطيف آل الشيخ (6/ 188)

(2) Maganar Shaikh Abdul'azeez Ibn Baaz:

((وكل دولة لا تحكم بشرع الله، ولا تنصاع لحكم الله ولا ترضاه فهي دولة جاهلية كافرة ظالمة فاسقة بنص هذه الآيات المحكمات، يجب على أهل الإسلام بغضها ومعاداتها في الله، وتحرم عليهم مودتها وموالاتها حتى تؤمن بالله وحده وتحكم شريعته وترضى بذلك لها وعليها)).

نقد القومية العربية على ضوء الإسلام والواقع (ص: 40)

(3) Maganar Shaikh Muhammad Ibn Uthaimeen:

((وهؤلاء المحكمون للقوانين لا يحكمونها في قضية معينة خالفوا فيها الكتاب والسنة، لهوى أو لظلم، ولكنهم استبدلوا الدين بهذا القانون، وجعلوا هذا القانون يحل محل شريعة الله، وهذا كفر؛ حتى لو صلوا وصاموا وتصدقوا وحجوا، فهم كفار ما داموا عدلوا عن حكم الله ـ وهم يعلمون بحكم الله ـ وإلى هذه القوانين المخالفة لحكم الله)).

شرح رياض الصالحين (2/ 261)

(4) Maganar Shaikh Muhammad al-Ameen al-Shankitiy:

((إن الذين يتبعون القوانين الوضعية التي شرعها الشيطان على ألسنة أوليائه مخالفة لما شرعه الله جل وعلا على ألسنة رسله صلى الله عليهم وسلم، أنه لا يشك في كفرهم وشركهم إلا من طمس الله بصيرته، وأعماه عن نور الوحي مثلهم)).

أضواء البيان في إيضاح القرآن بالقرآن (3/ 259)

Idan ka duba ma'anonin kafirtawan da ke cikin maganganun wadannan Malamai za ka ga cewa; kafirtawa ne a sake, wanda ba a dora shi a kan kowa ba. Wato kafirtawa ne da aiki ko sifa, ba tare da dora hukuncin kafircin a kan mutum sananne wanda ya aikata aikin ba. Kuma duk wanda ya san littatafan Fiqhu, idan ya duba Babin Ridda, zai ga irin wannan salo shi ne salon maganar Malamai wajen bayanin kafirtawa, amma ba a taba cewa: sun kafirta wani mutum sananne ba. Saboda da ma kafirtawa nau'i uku ne. Nau'i biyu su ne na Ahlus Sunna, nau'i daya kuma na Khawarijawa. Ga su kamar haka:

1. Kafirtawa a sake (التكفير المطلق), ta hanyar rataya hukuncin kafircin a kan sifa ko aiki ba tare da an dora hukuncin kafircin a kan wani mutum sananne ko wata jama'a sananniya ba.

2. Kafirtawa da aka dora hukuncin kafircin a kan sanannen mutum ko sananniyar jama'a ko al'umma (تكفير المعين).

Misali a ce: Tanko kafiri ne.

Shi wannan nau'i na biyu na kafirtawan ba a hanun kowa yake ba, a hanun Malamai masu Alkalanci da yanke hukunci yake, wadanda suka san hanyoyin dora hukunci a kan wanda ya aikata aikin na kafirci, ya cancanci a kafirta shi, bayan sun tsayar da hujja a kan wanda ya aikata abin da ya tabbata kafirci ne a Shari'a.

Da ma abin da muka sani shi ne; Malamai Ahlus Sunna suna kasa kafirtawa zuwa kashi biyu: (التكفير المطلق وتكفير المعين), Ibnu Taimiyya ya yi bayani a kansu a wurare daban – daban, daga ciki ya ce:

((ثبوت التكفير في حق الشخص المعين موقوف على قيام الحجة التي يكفر تاركها. وإن أطلق القول بتكفير من يقول ذلك فهو مثل إطلاق القول بنصوص الوعيد، مع أن ثبوت حكم الوعيد في حق الشخص المعين موقوف على ثبوت شروطه وانتفاء موانعه، ولهذا أطلق الأئمة القول بالتكفير مع أنهم لم يحكموا في عين كل قائل بحكم الكفار)).

بغية المرتاد في الرد على المتفلسفة والقرامطة والباطنية (ص: 353 - 354)

((Tabbatar kafirtawa a kan mutum sananne ya dogara ne a kan tsayar masa da hujjar da wanda ya barta zai kafirta. Idan an saki magana an ce: wanda ya ce kaza ya kafirta, to dadai yake da sakin Nassoshin azabar Allah a Lahira (misali a ce: wanda ya yi zina dan wuta ne), tare da cewa; tabbatuwar hukuncin "wa'eedi" (shiga wuta) a game da mutum sananne ya dogara ne a kan tabbatuwar sharuda da koruwan abubuwa masu hana tabbatuwar hukuncin "wa'eedin" a kansa. Saboda wannan ne Malamai suka saki kalmar kafirtawa (suka ce wanda ya yi kaza kafiri ne) alhali ba su yanke hukuncin kafircin a kan kowane mutum sananne da ya fadi maganar kafircin ba)).

A wani wajen kuma ya ce:

((إن القول قد يكون كفرا كمقالات الجهمية الذين قالوا: إن الله لا يتكلم ولا يرى في الآخرة؛ ولكن قد يخفى على بعض الناس أنه كفر فيطلق القول بتكفير القائل؛ كما قال السلف من قال: القرآن مخلوق فهو كافر، ومن قال: إن الله لا يرى في الآخرة فهو كافر، ولا يكفر الشخص المعين حتى تقوم عليه الحجة كما تقدم كمن جحد وجوب الصلاة والزكاة واستحل الخمر والزنا وتأول. فإن ظهور تلك الأحكام بين المسلمين أعظم من ظهور هذه، فإذا كان المتأول المخطئ في تلك لا يحكم بكفره إلا بعد البيان له واستتابته - كما فعل الصحابة في الطائفة الذين استحلوا الخمر - ففي غير ذلك أولى وأحرى)).

مجموع الفتاوى (7/ 619)

((Lallai ra'ayi zai iya zama kafirci, kamar ra'ayoyin Jahamiyya wadanda suke cewa; Allah ba ya magana, kuma ba za a ganshi a Lahira ba. Amma sai dai kasancewar hakan kafirci ne zai iya buya ma wasu cikin mutane, sai a saki kalmar kafirta wanda ya fada: (a ce: wanda ya ce kaza kafiri ne), kamar yadda Magabata suka ce: Duk wanda ya ce: "Alkur'ani halitta ne shi kafiri ne", "Wanda ya ce: ba za a ga Allah a Lahira ba shi kafiri ne", amma ba za a kafirta mutum sananne ba har sai an tsayar masa da hujja, kamar yadda bayani ya gabata a game da wanda ya yi musun wajabcin Sallah da Zakka, kuma ya halasta shan giya da zina, ya yi tawili. Lallai bayyanar wadannan hukunce – hukunce a tsakanin Musulmai ya fi girma fiye da bayyanar wadannan ra'ayoyin Jahamiyyan. Don haka idan Mai tawili mai kuskure ya kasance ba za a yi masa hukuncin kafirci a wadannan abubuwa ba (inkarin wajabcin Sallah da Zakka, da halasta zina da shan giya) sai bayan an yi masa bayani an nemi ya tuba - kamar yadda Sahabbai suka yi ma wadanda suka halasta giya – to a wasun wadannan ya fi cancanta da dacewa)).

Ya fadi irin wannar magana a takaice a wani wajen ya ce:

((إن القول قد يكون كفرا فيطلق القول بتكفير صاحبه ويقال من قال كذا فهو كافر، لكن الشخص المعين الذي قاله لا يحكم بكفره حتى تقوم عليه الحجة التي يكفر تاركها)).

مجموع الفتاوى (23/ 345)

Saboda haka idan Malamai sun ce: wanda ya aikata kaza kafiri ne, ba ya nufin kafirta wani mutum sananne daga cikin masu aikata wannan aiki na kafirci. Saboda ba a kafirta mutum sananne, wanda ya aikata kafirci har sai an tsayar masa da hujja, an yaye masa shubuha, an nemi ya tuba.

3. Kafirtawa mai game Duniya ko al'umma gaba daya (التكفير بالعموم):

Wannan shi ne irin kafirtawan da Khawarijawa suke yi, inda suke kudin goro su kafirta dukkan wanda ba ya tare da su, ba tare da sun tsayar da hujja a kan kowanne daya daga cikin mutane ba. Sai su yi amfani da kalmomi masu gamewa, su ce: dukkan mutane kafirai ne, dukkan mutane sun yi ridda, dukkan mutane sun koma jahiliyya. Ko dukkan mutanen kasa kaza kafirai ne,,, da makamancin haka.

Don haka idan an lura za a ga cewa; wannan nau'i na uku na kafirtawa, wato jefa kalmar kafirtawa kan mai uwa da wabi, kafirtawa mai game Duniya ko al'umma gaba daya (التكفير بالعموم), zai iya shiga karkashin kafirta sanannen mutum ayyananne, saboda duk lokacin da ka yi kudin goro ka ce: kowa kafiri ne, to fa ka ayyana kowane mutum sananne ka kafirta shi ne, alhali ba tare da ka tsayar masa da hujja ba.

Misali a kan haka, ka duba wannar magana ta Sayyid Qutub inda ya ce:

((إن البشرية عادت إلى الجاهلية، وارتدت عن لا إله إلا الله. فأعطت لهؤلاء العباد خصائص الألوهية. ولم تعد توحد الله، وتخلص له الولاء..

البشرية بجملتها، بما فيها أولئك الذين يرددون على المآذن في مشارق الأرض ومغاربها كلمات: «لا إله إلا الله» بلا مدلول ولا واقع.. وهؤلاء أثقل إثماً وأشد عذاباً يوم القيامة، لأنهم ارتدوا إلى عبادة العباد- من بعد ما تبين لهم الهدى- ومن بعد أن كانوا في دين الله!)).

في ظلال القرآن (2/ 1057)

((Duka 'yan-Adam sun koma jahiliyya, sun yi ridda sun bar Kalmar Shahada. Saboda sun bayar ma wadannan bayi kebanbattun siffofin Uluhiyya. 'Yan-Adam gaba daya ba su kasance suna kadaita Allah suna tsarkake masa biyayya ba.

'Yan-Adam gaba dayansu, a cikinsu har da wadancan da suke maimaita Kalmar Shahada ba tare da ma'anarta ba kuma babu ita a aikace, a kan dakalin kiran Sallah, a gabashin Duniya da yammacinta. Wadannan su ne ma suka fi nauyin zunubi, suka fi tsananin azaba a Ranar Kiyama. Saboda sun yi ridda zuwa ga bautar bayi, bayan shiriya ta bayyana gare su, kuma bayan a da suna cikin Addinin Allah)).

To sai ka auna wadancan maganganun Malaman da wannar magana ta Sayyid Qutub ka ga banbancin da ke tsakaninsu.

Saboda haka idan ka lura da wadancan maganganun Malaman za ka ga a nau'i na farko suke (التكفير المطلق). Amma shi kuma Sayyid Qutub, idan ka nazarci irin nasa kafirtawan za ka samu kafirtawa ne mai game Duniya da al'umma gaba daya (التكفير بالعموم).

To su Khawarijawan zamani, irin kafirtawansu iri daya ne da na Sayyid Qutub, daga gare shi suka dauko Fikran. A haka suke kafirta al'ummar kasa guda, su dauki makami suna yakar Musulmai, suna dasa bama – bamai a Masallatai da kasuwanni da tashoshin mota, suna kashe mutane, ba babba, ba yaro, ba malami ba jahili.

Saboda haka nau'i na farko (التكفير المطلق) ba kafirtawa ne abin zargi ba, da sharadin idan aikin tabbata a Shari'a kafirci ne.

Nau'i na biyu kuma (تكفير المعين), a hanun Malamai masu hukunci yake, bayan tsayar da hujja a kan wanda ya aikata kafircin. Don haka wannan ba fage ne na kowa a cikin mutane ba, ya takaita ne a hanun Malamai masu yanke hukunci.

Na uku kuma, wato kafirta dukkan mutane (التكفير بالعموم), da kafirta dukkan al'umma wannan kam Bidi'a ce ta Khawarijawa, su aka sani suke kafirta mutane gaba daya, su halasta jinanensu, su je kasuwanni da masallatai suna tayar da bama-bamai. Wannan ya zama bidi'a ne da ta'addanci, saboda ba zai yiwu duka wadannan mutanen su zama kowa ya cancanci kafirtawa ba, saboda kafirta kowane mutum sananne yana bukatar tsayar masa da hujja, a yaye masa shubuha, a tabbatar ba shi da wani uzuri a Shari'a. Don haka ba zai yiwu a yau ka ce: mutanen kasa kaza gaba daya kafirai ne ba, balle kuma ka ce: dukkan mutanen Duniya (البشرية) kafirai ne sun yi ridda ba - kamar yadda Sayyid Qutub ya yi ta yi –, kuma ka ce: daga Alkur'ani da Sunna da maganganun Malamai ka fahimci hakan.

Saboda haka banbanci tsakanin nau'o'in kafirtawan da ke cikin maganganun Malamai, da kuma wanda ke cikin maganar Sayyid Qutub a fili yake, amma ga masu ilimi!

To rashin sanin banbancin nau'o'in kafirtawan ne ya sa Khawarijawa 'Yan Ta'adda suke daukar maganganun Malamai, musamman Ibnu Taimiyya da Ibnu Abdilwahhab suna kafa hujja da su, sai jahilai suke cewa: ai ta'addanci a cikin littatafan Ibnu Taimiyya da Ibnu Abdilwahhab yake, alhali maganganun nasu jinsin maganar Allah da Manzonsa ne, da kuma irin maganganun Malaman Fiqhu a Babin Ridda.

Haka a yau muka ga masu kare barnar Sayyid Qutub suna dauko wadancan maganganun Malaman, wadanda suke nau'in (التكفير المطلق) suna daidaita su da kafirtawan da Sayyid Qutub ya yi, wanda yake nau'in (التكفير بالعموم), alhali wannan kuskure ne, imma saboda jahilci da rashin fahimtar maganganun Malamai ko kuma saboda son zuciya.

Saboda haka matsalar Khawarijawa da masu kare barnar Sayyid Qutub ita ce; sun yi tarayya wajen rashin fahimtar maganganun Malamai, da rashin banbance nau'o'in kafirtawa.

Kuma ko da ya tabbata maganar Malamin kuskure ne, ba dadai ba ne a daidaita Malamin da Sayyid Qutub, saboda dalilai kamar haka:

1) Su wadancan Malamai ne, kowa ya yarda mutane ne da suka tsaya suka koyi ilimin Addinin Muslunci, suka shagaltu da shi, sabanin Sayyid Qutub, abin da aka sani a kansa shi ba Malami ba ne, shi kawai Masanin Adabin Larabci ne, Marubuci, ya dauki Alkur'ani ya yi masa sharhi na harka (taratsi), abin da ake kira da "التفسير الحركي". Malamai irin su Shaikh Ibnu Uthaimeen da Shaikh Albaniy - a wurare masu yawa - sun tabbatar da cewa: Sayyid Qutub ba Malami ba ne. Don haka uzurin da za a yi wa Malami ba za a yi shi ga wanda ba Malami ba.

2) Su wadancan Malamai kowa ya san Akidarsu ta Ahlus Sunna ce, amma shi kuma Sayyid Qutub ya tabbata cewa; Akidarsa ta Khawarijawa ce. Don haka shi yana gina maganganunsa ne a kan Akidarsa ta Khawarijanci, amma su kuma idan an samu abin da ya saba ma Akidarsu, to sai dai a dauka cewa; tuntuben harshe ne da zamiyar kafa, sabanin shi da aka san maganarsa ce ta dace da Akidarsa.

A takaice; hanyar Malamai Ahlus Sunna daban, hanyar Sayyid Qutub daban. Hanyar jirgi daban da ta mota. Shi Sayyid Qutub asali ba Malami ba ne, kuma ya tabbatar da Akidar Khawarijawa a cikin littatafansa. Don haka shi idan ya kafirta al'umma an san kafirtawa ne irin na Khawarijawa. Amma su kuma Malaman, idan an samu kuskuren da ya saba Akidar Ahlus Sunna a cikin maganganunsu - in fa ya tabbata kuskuren ne - sai a dauke shi a matsayin kuskure da tuntuben harshe da zamewar kafa, saboda su an san Malamai ne, kuma an san bisa Akidar Ahlus Sunna suke, sabanin Sayyid Qutub wanda yake ba Malami ba ne, kuma Akidarsa irin ta Khawarijawa ce.

✍️ Dr. Aliyu Muh’d Sani (H)

Daga zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

Post a Comment

0 Comments