Ticker

6/recent/ticker-posts

Auren Dole da Ilolinsa: Sharhi a Kan Wakar Sama’ila Abdullahi Fircin Koko

Citation: Bunza, D.B. (2024). Auren Dole da Ilolinsa: Sharhi a Kan Waƙar Samaila Abdullahi Fircin Koko. Ginshiƙin Nazarin Salon Waƙoƙin Hausa, 175-187. www.doi.org/10.36349/djhs.2024.v03i01.021.

Auren Dole da Ilolinsa: Sharhi a Kan Waƙar Sama’ila Abdullahi Fircin Koko

Dano Balarabe Bunza
Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya
Tsangayar Fasaha
Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato.
Lambar Waya: 07035141980
Email: danobunza@gmail.com

Tsakure: Sunan maƙalar Auren Dole da Illolinsa: Sharhi a Kan Waƙar Samaila Abdullahi FircinKoko. An samar da maƙalar ta hanyar yin hira da marubucin waƙar da samun kwafin waƙar daga gare shi. Haka kuma an sami rerarrar waƙar ga MP3 da ke ɗauke da muryar mawallafin waƙar, aka saurara domin nazari da shirin fitowa da abubuwan da ake buƙatar kawowa a cikin maƙalar.Bayan an nazarci waƙar an fito da batutuwa masu yawa da suka shafi auren dole da suka haɗa da dalilan da suka sa iyaye na yi wa ‘ya’yansu auren dole da kuma illolinsa. Idan aka shiga maƙalar za a sami dukkan bayanai. An yi tunanin samar da maƙalar domin ta yi susa daidai wurin da ke ƙaiƙayi a matsayin gargaɗi ga wanda yayi wa ‘ya’yansa auren dole da ya daina, wanda bai riga yayi baya nisance shi, shi kuma wanda ke da niyyar yi ya fasa. An yi amfani da hanyar nazarin waƙa ta Farfesa Abdullahi Bayero Yahya da ke cikin littafinsa mai suna Jigon Nazarin Waƙa. An kawo sakamakon binciken da aka gano sanadiyyar rubuta wannan maƙala tare da shawarwari da za su taimaka don samun mafita daga matsalolin da auren dole ke jawo wa al’umma.

Fitilun Kalmomi: Aure, Auren Dole, Ilolinsa, Sama’ila Abdullahi Fircin Koko

Gabatarwa

Idan aka yi la’akari da auren dole da iyaye ke yi wa ‘ya’yansu, za a iya cewa wayewar addinin Musulunci a yau ya rage aukuwar wannan matsala, musamman idan aka lurada yadda yawancin iyaye ke barin ‘ya’yansu maza da mata na zaɓa wa kansu mata da mazan aure. Wannan ne ya sa auren dole ya ƙaranta a birane da ƙauyuka a yau. A da, auren dole tamkar ruwan dare ne game duniya, wanda aka fi alaƙanta yawaitar karuwanci a cikin birane da ƙauyuka. Duk da yake akwai masu shiga karuwanci ta hanyar laɓawa ga sabara ana harbin barewa, ba donan yi musu auren dole ba. Auren dole aure ne da iyaye ko ‘yan uwa ke tilasta ‘ya’yansu domin su auri wasu daga cikin ‘yan uwansu na ɓangaren mahaifa biyu (uwa ko uba) ko ma wani can na daban wand aba su da zumunta. Akan yi auren dolen saboda wasu dalilai ba tare da yin la’akari da ɗinbin illolin da yake tattare da suba. Bisa wannan dalili ne aka yi tunanin samar da wannan takarda domin ta yi susa gurbin da ke yin ƙaiƙayi ta hanyar yin la’akari da abin da Sama’ila Abdullahi Fircin koko ya ambata a cikin waƙarsa mai suna ‘Auren Dole’.Tare da haka kuma, a lura da cewa, Koko ya shirya waƙarsa ta yin la’akari da lokuta biyu, wato kafin yin auren dole da kuma bayan an yi shi. Za a kawo hujjoji ta hanyar amfani da baiti ko baitoci ga kowane dalili ko illar da aka kawo kamar yadda marubucin ya faɗa a cikin waƙarsa.

Bayanin Fitillun Kalmomi: Ma’anar Aure, Dole da Auren Dole

An sami masana da manazartan da suka harari ma’anar aurea cikin rubuce-rubucen da suka yi gwargwadon fahimtarsu. A wannan muƙala za a kawo ma’anonin aure kaɗan ba da yawa ba, daga wasu masana da manazartan kamar haka:

Wani ya fassara aure zuwa harshen Turanci da cewa shi ne, marriage (Bargery, 1934:44).

Haka ma wasu sun kawo tasu ma’ana kamar haka: Aure: (auree, sn, nj, jam: aure-aure) (i) dangantaka tsakanin namiji da mace ta hanyar Shari’a. (ii) mace da namijin tantabara (iii) haɗa wani tsiro da wani don samun ingantaccen iri (Ƙamusun Hausa, 2006: 22).

A ɓangare ɗaya kuma, an bayar da ma’anar kalmar dole da cewa: Kalma ce mai bayyana tilasta yin abu ko barin sa. Misali, dole ne duk mai rai ya mutu (Ƙamusun Hausa, 2006: 107).

Dangane da ma’anar auren dole kuwa, idan aka haɗa ma’anar aure da ma’anar dole za a ga ma’anar ta fito kamar haka: Auren dole dangantaka ce tsakanin namiji da mace ta hanyar Shari’a da aka tilasta yin sa tsakanin namiji da mace. Marubucin ya kawo ma’anar auren dole a cikin wasu ɗaiɗaikun ɗamgaye a cikin waɗansu baitocin waƙarsa a wurare da dama inda ya ce:

Auren ga shi ne an na tashin hankali,

Ko can daɗai mai son sa sai mara hankali,

Duw wanda ke dasani da tarin hankali,

Wallahi bai sha’awa ga auren dole.

(Fircin Koko, Waƙar Auren Dole, baiti na 31)

Idan aka natsu aka dubi baitocin da aka kawo a sama, sun fito da ma’anar auren dole gwargwado kamar yadda marubuci waƙar ya faɗa. Fircin Koko ya kawo ma’anar auren dole a baiti na 31 a inda ya ce, auren dole aure ne na tashin hankali. Ai saboda kasancewar na tashin hankali ya sanya marubucin tun a cikin baiti na shida na wannan waƙa ya ce, “Zan yo kira a gudani auren dole”. A hankalin tuwo kurum idan aka ce mutum ya gudani abu, ana kyautata zaton ba mai alheri ba ne a gare shi. Haka kuma, idan aka nazarci waƙar baki ɗaya, marubucin bai kawo alfanun auren dole ba daga farkon waƙar har ƙarshenta, face illolinsa ga al’umma. Don haka, cewar da ya yi auren dole aure ne na tashin hankali, gaskiya ne. Ga abin da y ace a wani baiti:

……………………………………,

…………………………………….,

Auren ga ko da ta ƙi ɗaurawa sukai,

Daɗa sai su tilasta ta auren dole.

(Fircin Koko, Waƙar Auren Dole, baiti na 38)

Haka ma a cikin baiti na 38, marubucin ya ƙara fitowa da ma’anar auren dole a layi na uku, wurin da ya ce “Auren ga ko da ta ƙi ɗaurawa sukai”. Ma’ana a nan ita ce, aure ne da ake ɗaurawa ko da yarinya ba ta son wanda aka haɗa ta da shi. Idan aka yi haka kuwa, wannan layi ya fito da ma’anar auren dole a fili. Bayan haka, ga abin da ya ƙara faɗa dangane da ma’anar aren dole:

Mi a’ abin so banda kwancin hankali?

Kun wa ɗiya aure na tashin hankali,

In kun yi wannan to ku san kun yi izgili,

Domin ko ba nasara ga auren dole.

(Fircin Koko, Waƙar Auren Dole, baiti na 45)

A baiti na 45 ma a layi na biyu Sama’ila ya ƙara bayyana abin da ake nufi da auren dole a wurin da ya ce “Kun wa ɗiya aure na tashin hankali”. Babu shakka idan aka tambayi ma’anar auren dole, aka sami mai ba da amsa ya ce, auren dole na nufin auren tashin hankali ake nufi, ya yi daidai domin daga farkon auren dole har zuwa ƙarshensa babu kwanciyar hankali a cikinsa, kamar yadda marubucin ya tabbatar a cikin ƙasidarsa. Har yanzu ga abin da y ace a wani baitin waƙarsa kamar haka:

Auren da duk aka yi shi ba soyayya,

Ƙarshe kana iske shi ya zama kunya,

To sai a ɗunguma kotu gun jayayya,

Ka san akwai kunya ga auren dole.

(Fircin Koko, Waƙar Auren Dole, baiti na 53)

Haka kuma, wata ma’anar auren dole ta ƙara fitowa a baiti na 53, layi na ɗaya wurin da marubucin ya ce “Auren da duk aka yi shi ba soyayya” shi ne auren dole. Wannan ba a ɓoye yake ba, ai dalilin kiran sa auren dole shi ne tun asali ana haɗawa ne ba tare da son ɗaya daga cikin ma’aurata ba (miji ko mata). Haka idan aka lura da baitin baki ɗaya ya yi bayanin abubuwa marasa kyau da ke faruwa a sanadiyyar yin auren dole irin a ƙarshe ya kasance jin kunya ga waɗanda suka haɗa shi da zuwa kotu wurin alƙali domin raba auren da tonon asirin da zai biyo baya tare da la’anar juna tsakanin dangin mata da na miji. Wani lokaci ma har da jayayyar na amince da abu kaza amma ban aminta da kaza ba, idan aka zo wajen lissafin dukiyar da kowane ɓangare ya kashe. A baitin ƙarshe, marubucin ya ƙara fayyace ma’anar auren dole ta hanyar cewa:

Auren ga cuta ne zuwa ga ɗiyanku,

Mi an na cutawa zuwa ga ɗiyanku?

In har kuna haka ba ku son ‘ya’yanku,

Mai son ɗiya bai sa ta auren dole.

(Fircin Koko, Waƙar Auren Dole, baiti na 57)

A ƙarshe, marubucin ya ƙara bayyana ma’anar auren dole a baiti na 57 wurin da ya ce, “Auren ga cuta ne zuwa ga ɗiyanku” a layin farko. Idan aka tambayi ma’anar auren dole, kuma aka dace da wanda ya ce aure ne da ake yi da ke cutar da ‘ya’ya, ya yi daidai. Waɗannan ne ma’anonin auren dole da muƙalar ta tsinto a cikin waƙar wanda ya kattaba ta, kuma kaɗan ba da yawa ba.

Dabarun Bincike

Daga cikin dabarun binciken da aka yi amfani dasu don gudanar da wannan bincike akwai ta farko samun waƙar domin yin nazari da kuma sauraron ta daga kaset ɗin da muryar marubucin take, domin shi ke rubutawa kuma ya rera da kansa.

Wata dabara da aka yi amfani da ita lokacin gudanar da wannan bincike itace ziyartar ɗakunan karatu domin farauto ayyukan adabi irin wannan. Haka kuma, an yi amfani da dabarar hira da marubucin waƙar auren dole kan wasu abubuwa da suka shige duhu a lokacin gudanar da binciken. Ba wannan kaɗai ba, an yi hira da wasu masana adabin waƙa domin samun ƙarin haske ga binciken da aka gudanar.

Kirarin Aure

A al’adance aure ba abin wasa ba ne a wurin Bahaushe, to ina ga an koma a ɓangaren addinin Musulunci? Hausawa sun san muhimmancin aure a gare su, kuma sun san amfaninsa da da matsayinsa a addininsu kamar yadda Alƙur’ani ya bayyana da hadisan Manzon rahama Annabi Muhammadu (SAW). Wannan ya sanya Bahaushe ya sanya wa wanda ke da mata sunan maigida da matar da ke da miji uwargida. Wanda ya yi aure ya rabu da matarsa ana kiran sa gwauro.Matar da ta rabu da mijinta kan ya sake ta ana kiran ta gwauruwa. Wanda kuma ya kai munzalin aure bai yi ba anakiran sa tuzuru. Saboda haka ne Bahaushe ya tanadi kirari ga aure domin wanda ya san darajar goro shi ka ce mai Gwanja. Ga wasu kirarin da al’ummar Hausawa ke yi wa aure kamar haka:

i.     Aure sha kan yaro, ka ba manya kashi yara na ganin damarka/sauƙinka

Wanda ya yi aure kaɗai ya san lalurorin da ke cikinsa, ba kamar yaro da bai mallaki hankalinsa ba da ke ganin babu wahala cikinsa sai daɗi tare da ganin komai a banza yake. Wannan ya nuna bai san irin wahalar da magidanta ke fama da itaba da ta haɗa da ciyarwa da shayarwa da sauran harakokin gida na tufatarwa da sauransu. Wannan ne ya sa Hausawa suka yi wa aure kirarin.

ii.   Aure dodon mata

Dodo na nufin abin da ke ba mutum tsoro kuma ya sha jinin jikinsa duk lokacin da aka ce ga shi nan. Dodancin aure iri biyu ne. Na farko idan mace ta yi aure tana jin tsoron aikata abin da take aikatawa kafin ta yi aure. Na biyu kuma shi ne, a da kafin sauyawar lokaci, duk budurwar da aka yi wa aure tana da shakkun ranar da mijinta zai take ta saboda ba ta saba da hakan ba.

iii. Aure yaƙin mata

A taƙaice wannan na nufin duk yadda miji ke jin kansa ko yake ganin yana da abin lalura, wata rana sai mace ta ce ya kawo ya ce babu. Duk lokacin da aka tambayi miji abu ya ce babu, ana cewa yaƙi ya ci shi, ko yau da gobe ta yi halinta, saboda cefane abin kullum ne. Wannan yaƙin ana nufin na yin cefane da sauran lalurorin gida. Idan kuma aka koma ɓangaren kwanciyar aure, za a ce jarumi a fagen fama mace ke yaƙar sa, kuma taci nasara a kan shamfiɗa.

Taƙaitaccen Tarihin Sama’ila Abdullahi Fircin Koko

An haifi Sama’ila a ranar Laraba 1/11/1970 a garin Koko ta ƙaramar hukumar Koko-Bessen jihar Kebbi. Sunan mahaifinsa Abdullahi Fircin Koko, kakansa na wajen uba kuma shi ne Fircin Sabi’u ɗan malam Amadu Gogan harda wanda ya rayu a garin gumbin Kure ta ƙasar Jega. Sunan mahaifiyarsa Hafsatu (Uwar Ama) ɗiyar malam muhammadu Ɗangindi wanda shi ne kakan Sama’ila a ɓangaren mahaifiyarsa, Bagimbanea ɓangaren mahaifinsa sannan Bakabe aɓangaren mahaifiya.

Mahaifin Sama’ila shi ke riƙe da rabin garin Koko na ɓangaren Yamma. Fircin sunan sarautar gidan su Sama’ila ce. Fircin Sa’adu ne Fircin na farko tun lokacin da aka kafa garin Koko. Haka kuma shi ne ke gaba a cikin mutanen da Malam Muhammadu Ɗangindi ya turo domin kafa garin Koko. Sama’ila ɗan sarauta ne da gidan iliminmalanta.

Sama’ila Abdullahi Fircin Koko ya yi karatun addini da na book. Ya fara karatun addini a wurin mahaifinsa (karatun Alƙur’ani) daga baya ya koma wuurin wasu malamai har ya sauke. Yay i karatun sani na littattafai da yawa a wurin malamansa. Yay i karatun book daga firamare har zuwa matakin jami’a inda ya sami digirinsa na biyu a Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya. Sama’ila yay i karatu da karantarwa a wurare da dama, kuma ya riƙI muƙamai da dama a wuraren aikinsa a cikin gida da waje. Misali a halin yanzu shi ne sakataren Ilmin Firamare na ƙaramar hukumar mulki ta Koko-Besse (LGEA).

Haka kuma ya riƙa matsayin shugaban matasa na ƙungiyar cigaban ƙasar Koko (KODDA Youth Leader) daga ranar Talata 03/12/2006 zuwa 2008. Haka kuma Sama’ila ya sami takardar shedar halattan babban taron haɗin guiwa tsakanin jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo da jami’ar Abdulmumini da ke Niyame Nijar a kan babban taro na gabatar da waƙoƙI kan tsaro a Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo Sakkwato, kuma ya gabatar da ƙasidar da ta ɗayatar a wurin taron.

A ɓangaren iyali kuma, Sama’ila na da mata biyu, ya auri matarsa ta farko a ranar 01/06/2002. Sunan matarsa ta farkoshi ne Ummulkhairu Abubakar Yabo Yauri, kuma ya haifi ‘ya’ya takwas da ita. Ana ce wa matarsa ta biyu Namira Bello, ita ma tana da ‘ya’ya shida tare dashi.

A ɓangaren waƙa kuwa, Sama’ila ya rubuta waƙoƙi masu yawan gaske da suka kai ɗari huɗu da hamsin (450) inda ‘Waƙar Auren Dole’ da ake magana a kai na ɗaya daga cikinsu.Daga cikin waƙoƙinsa wasu na a kaset ko CD, ana jin wasu a kafafen sadarwa da na watsa labarai cikin gida da na ƙasashen waje. A taƙaice, waƙoƙin Sama’ila Fircin Koko sun shiga duniya domin ba a Nijeriya kaɗai ake amfani da su ba kamar yadda ya ambata a cikin tarihinsa. Daga cikin ayyukan da Sama’ila ya rubuta akwai waɗanda aka buga, akwai kuma wasu daba a sami bugawa ba. Tare da haka kuma, akwai ayyukan bincike da dama da wasu ɗalibai suka yi da wasu waƙoƙinsa a matakan karatun N.C.E. da digirin farko a makarantu daban-daban (Kwalejin ilimi da jami’a).

Auren Dole Da Illolinsa: Sharhi Daga Waƙar Auren Dole Ta Sama'ila Abdullahi Fircin Koko

Al’ummar da ke yi wa ‘ya’yanta auren dole, samun dalilan yin sakan bambanta daga wuri zuwa wuri. Haka kuma babu kokwanto idan aka yi auren ala tilas a ci karo da matsalolin da zai janyowa al’umma baki ɗaya. Ganin haka an fara magana a kan dalilai kafin a kai ga illolin auren dole ga al’umma.Ga dalilan da ke sanya yin auren dole kamar yadda ya fito daga wasu baitocin waƙar Sama’ila Abdullahi Fircin Koko kamar haka:

Dalilan Da ke Sanya Iyaye Yi Wa ‘Ya’yansu Auren Dole

Akwai dalilai da dama da ke sanya iyaye na yi wa ‘ya’yansu auren dole, sai dai kowa da borin da yake yi wa tsafi. Ma’ana dalilin wani ya bambanta da na wani. Daga cikin dalilan da takardar ta kalato daga waƙar auren dole ta Sama’ila Abdullahi Fircin Koko akwai:

Kwaɗayin Ƙarfafa Zumunta

Iyaye na yi wa ‘ya’yansu aurendole domin buƙatar ƙara ƙarfafa zumunci musammanwanda ke tsakanin dangi.Bayan wannan akan sami farin ciki mai yawa tsakanin dangin miji da na mata a sanadiyyar yin aure. Tunanin haka ke sanya wasu yi wa ‘ya’yansu auren dole domin a ƙara ƙarfafa zumuncin da ke akwai. Idan an ci nasara a yi farin ciki, idan akasin nasara ya faru zumunci ya gurɓata, kamar yadda Hausawa ke cewa, “In ta yi ruwa rijiya, in ba ta yi ba, masai”.Wannan tunani ya sanya Sama’ila kattaba wannan waƙa ta auren dole sannan ya fito dawannan dalili daga cikin dalilan da ke sanya iyayeyi wa ‘ya’yansu auren dole da aka samu a cikin wasu baitocin waƙarsa kamar haka:

Kai kar ka ce ai wane dai danginmu na.

Zan ba shi ‘yata tunda na ga jininmu na,

In ba ta so nai kar ka ɗaura tosku na,

Don ba a dacewa ga auren dole.

(Fircin Koko, Waƙar Auren Dole, baiti na 46)

Marubuci waƙar ya san da akwai zumunta tsakanin al’umma ƙwarai ba kaɗan ba, amma kuma ya yi gargaɗi ga iyaye cewa kar su yarda su yi wa ‘ya’yansu aure musamman ga wanda ba su so ko da ɗan uwa ne bale sabba. Gani da sanin an sha yi ba a samun nasara ya sanya Sama’ila jan kunnen iyaye da su guji aurar da ‘ya’yansu ba tare da suna so ba. Wannan ya sanya shi kawo baiti na 46inda ya ja kunnen iyaye cewa kar ganin wani ɗan ɗan uwa ya isa aure ya sanya shi aurar da ‘yarsa gare shi ba tare da tana son sa ba. Ya ƙara da cewa yi mata aure ba tare da tana so ba tosku ne, wato wulaƙanci (Tosku). Yin hakan na janyo matsaloli masu yawada ba a sani ba, kuma wulaƙanta kai ne da ‘ya’ya baki ɗaya, domin ko an yi shi ba a jin daɗi bale a more.

Ga kuma wani baiti da Fircin Koko ya ja kunnen wasu daga cikin iyayen ‘ya’ya kamar haka:

Kuma kar ka ce ai wane yarona fa ne,

In ba shi ‘yata ni garan ai dole ne,

In kam tana so nai ka bai alhairu ne,

In ba ta so nai kar ka sa ta a dole.

(Fircin Koko, Waƙar AurenDole, baiti na 47)

Haka ma Fircin Koko ya ja kunnen masu gidajen yara da kar su ƙulla aure tsakanin ‘ya’yansu da yaran da ke biye da su matuƙar babu so. Tare da haka ya faɗi cewa idan har tana so babu laifi a yi domin tsammanin alheri a ciki.

Kwaɗayi

A tawa fahimta, kwaɗayi na nufin rashin samun gamsuwa da abin da Allah ya hore wa mutun tare da sa ran samun abin da ba a mallaka masa ba daga hannun wasu mutane domin son jin daɗi ta hanyar karɓar wani abu daga wani mai hali domin a ba shi ‘ya aure ko bata son sa, amma saboda an ci dukiyar mai halin ta yadda ba a iya biya ko da ta taso, sai a tilasta yarinya auren saa dole. A taƙaice, kwaɗayi na nufin son abin hannun wani wanda mai son bai mallaka ba, ta hanyar ba ni gishiri in ba ka manda, wato ba ni kuɗinka in ba ka ‘yata.

Hausawa kan faɗi cewa “In da kwaɗayi da wulaƙanci, idan kuma babu kwaɗayi babu wulaƙanci”. Haka kuma sukan ƙara da cewa, ‘Kwaɗayi mabuɗin wahala”. Dukkan waɗannan maganganu gaskiya ne, domin ba a wulaƙanta mutumin da ba ya da kwaɗayi face mai kwaɗayi. Babu shakka kwaɗayi na daga cikin dalilan da ke sanya iyaye na yi wa ‘ya’yansu auren dole. Duk mahaifan da suka sanya son jin daɗin rayuwa fiye da yadda Allah ya hore musu, tilas a sami suna da kwaɗayi. Idan suka sami mai hali na son ‘yarsu da aure, za su ci gaba da karɓar kuɗi daga gare shi ko yana son bayarwa ko ba tare da jin daɗin rayuwarsa ba. Haka kuma iyayen kan aza masa lalurorinsu na komai, shi kuma yana jin nauyin nuna musu ba ya iya yi musu lalurorin.

Idan aka sami iyaye sun ci kuɗin mai son ‘yarsu to aurar da ita gare shi ya zama tilas gare su, domin za su matsa ɗiyar sai ta auri mutumin a dole kar abin ya komo musu tonon asiri. Idan yarinya ta ƙi aminta, babu shakka za su je kotu domin su biya abin da suka ci. Daganan tonon asiri da wulaƙanci ya biyo baya, a ƙarshe mutunci ya zube a idon jama’a. Haka kuma girma ya faɗi domin duk lokacin da aka lissafa makwaɗaita a unguwa ko gari, baabin da zai hana a saka mutumin cikin makwaɗaita. Wannan ne ya sanya idan suka shata fi cikinsu dole sai batun aure babu mafita. Wannan ne ya sa Sama’ila faɗar:

55. Wasu sun ci kuɗɗi saisu ce daɗa tilas,

Ai bada wance ga wane ya zama tilas,

Ita ko ɗiya ta ƙi so ga auren tilas,

Su kam nufinsu su ɗaura auren dole.

56. Daga nan ɗiya kuka shi zan hidimarta,

Shi ɗai take kullum idan ta kwanta,

Kullum idonta da ja idan ka gan ta,

Ta damu domin za ta auren dole.

A baiti na 55 an nuna iyaye sun riga sun ci kuɗin wanda ke son ‘yarsu ba tare da shawartar ta tana so ko ba ta so ba. Saboda kwaɗayi a cikin wannan sha’anin neman aure an kaɗa yarinya cikin halin ƙa-ƙa-nika-yi da babu makawa. Kodai a biya abin da aka ci ko kuma yarinya ta zama amaryar dole. Irin wannan aure ya bambanta da dalilin farko wanda ya yi magana a kan kwaɗayin ƙarfafa zumunta. A baiti na gaba marubucin ya ci gaba da matsalolin inda ya nuna idan aka yi wa yarinya irin wannan aure, za ta kasance cikin halin damuwa koyaushe. Za ta ci gaba da kuka dare da rana. Duba da irin wannan yanayin aure na nuna wa iyaye cewa, duk halin da ‘yarsu ta shiga su suka jefa ta a ciki.Haka kuma kwaɗayin iyaye ya bayyana kuma auren dole ya tabbata. Wani abin lura a nan, shi ne duk halin da ‘ya ta sami kanta a ciki, karta zargi ko face iyayenta.Idan aka yi rashin sa’a ‘yar ta ƙi zama gidan miji, iyayen ma damuwar za ta komakansu fiye da wadda yarinya ta shiga. Wannan matsala na iya zama lokacin da yarinya ta shiga uwa duniya, karuwanci ya zama sana’arta. Idan aka shiga wannan yanayi to damuwa ta koma ga iyaye, ita kuma yarinya ta ɗauki matakin da take ganin ya fi mata sauƙidon warware matsalarta.

Rashin Ilimi/Jahilci

Hausawa na cewa “Jahilci rigar ƙaya”. Ba wannan kaɗai ba, sun ƙara da cewa “Rashin sani ya fi dare duhu”. Haka kuma sun ƙara da cewa “Ilimi fitilar duniya”.Rashin ilimi da kalmar jahilci kalmomi ne masu waƙiltar junansu ta fuskar bayyana ma’anonin juna.

A cikin wannan takarda rashin ilimi na nufin yanayin da akeaikata wasu ayyuka ba tare da wata madogara a matsayin hujja daga Alƙur’ani ko hadisi ko haɗuwar malumma a kai ba. Jahilci kuma shi ne aikata wani aiki don rayuwa na so kawai ba tare da yin la’akari da abin da yake shi ne daidai ba. Ai shi ya saHausawa suka ce “Jahilci rigar ƙaya”. Manufa, riga ce mai wuyan cirewa bayan an sanya ta. A taƙaice, rashin ilimi da jahilci na nufin yin abin da bai dace ba. Rashin ilimi/jahilci na ɗaya daga cikin dalilan da ke sanya iyaye ɗaura wa ‘ya’yansu auren dole har suna ganin ba su yi laifi ba domin aure suka ƙulla ba saɓon Allah ba.Ga wasu baitoci da Fircin Koko ya tabbatar da iyayen da ke yi wa ‘ya’yansu auren dole aikin jahilci ne suke yi saboda rashin ilimi a kan ayyukan da suke yi:

Ko an yi bai kyau ya kamata ku gane,

Tun fil-azal shirya shi ai wauta ne,

Amma akwai jama’ar da su sun gane,

Su ba su sa ‘ya’yansu auren dole.

(Fircin Koko, Waƙar Auren Dole, baiti na 11)

A baiti na11 ɗango na farko marubucin na jan hankalin iyaye da cewa ya dace su san da cewa ko sun ɗaura wa ‘ya’yansu auren dole aikin banza suka yi domin ba za a yi madalla da auren ba. A ɗango na biyu ma ya ƙara da cewa asalin shirya aure dole wauta ne, wato rashin aiki da ilimi. A ɗango mai bi masa da nahuɗu kuwa, sai ya kawo zancen masu ilimi da ba su yi wa ‘ya’yansu auren dole. Babu shakka ya kawo mutane iri biyu, wato jahilai marasa ilimi da kuma masu ilimi da ba su yin ko kusa ga auren dole balle su yi wa ‘ya’yansu shi.

Bayan haka kuma, Fircin Kokoya kawo bayanin cewa wasu maza ma na da laifi kamar haka:

Kai ko maza wasu na da laifi mai yawa,

Ka nemi mace ta ce abin bai yiyuwa,

In banda hauka sai ka bar ta ka bar zuwa,

Balle a ce an ɗaura auren dole.

(Fircin Koko, Waƙar Auren Dole, baiti na 20)

Akwai baiti na 20 kuma, Sama’ila ya bayyana cewa wasu maza na da laifi mai yawa inda suke nacewa sai sun auri yarinya duk da ta bayyana musu cewa ba su son sa saboda rashin sani ko ilimi. Ya fito da wannan magana a ɗango na uku inda ya ce “In banda hauka” mai nufin in banda jahilci sai ka bar ta ka bar zuwa. A nan, marubucin na zargin masu tsayawa kai da guiwa don ganin cewa sai sun auri wadda bata son su.A cikin wannan lamari akwai jahilci da rashin sanin ya kamata musamman ganin yadda suke fafutukar kawo maƙiyi kusa gare su. Ga wani wuri da jahilci da rashin ilimi ya bayyana kamar yadda Fircin Koko ya bayyana:

21. Wani ko da an ce ba a so nai bai bari,

Ka ga har shi gigice ka gan shi wuri-wuri,

Har sai shi kai kuɗɗi ga ɗibbo gari-gari,

Wai don shi dai aure ta ko don dole.

(Fircin Koko, Waƙar Auren Dole, baiti na 21)

A baiti na 21 Sama’ila ya fito da rashin ilimi/jahilcin wasu maza amasu wautar son auren waɗanda ba su son su a fili inda ko an sheda masa ba a son sa ba ya haƙura, face sai ya bi duk hanyar da za a yi wannan aure. Saboda jahilci za sa ƙafafunsa takalma ya je duk inda za a sami maganin da zai sa yarinya ta amince da shi. Hanyoyin da yake bi ba waɗanda shari’a ta yarda da su ba ne. Yin haka kuwa sai maras ilimi ko wanda ya saki hanyar gaskiya. Tsayawa kai da fata don ganin mutum ya auri yarinya ko ta hanyar yi mata magani ne, aikin rashin ilimi ne kuma jahilci ne. Ba wannan kaɗai ba, ya ɗauki hanyar daba madaidaiciya ba.

Tauye Haƙƙin ‘Ya’ya

A tawa fahimta tauye haƙƙi na nufin hana wa mutum haƙƙinsa ƙiri-ƙiri saboda dalilin rinjaya ko wani dalili mai kama da wannan kamar hana ‘ya zaɓa wa kanta mijin aure ko hana su ‘yancinsu ba domin jahilci ba kamar yadda yake a bayanin daya gabata na jahilci. Fircin Koko ya kawo misalai ta fuskokin da iyaye ke tauye haƙƙoƙin ‘ya’yansu ta hanyar yi musu auren dole kamar haka:

Wasu sai su zagi ɗiyansu har duka sukai,

Wai don ta yarda da wane don so nai sukai,

Auren ga ko da ta ƙi ɗaurawa sukai,

Daɗa sai su tilasta ta auren dole.

(Fircin Koko, Waƙar Auren Dole, baiti na 38)

Allah ya hore wa wasu iyaye ‘ya’yansu ta fuskar jin maganar da suka yi da kuma aminta da ita ko da rayuwarsu ba ta so. Haka kuma wasu daga cikinsu na tsoron fushin iyayensu ba don komai ba sai don darajar haihuwa da ke tsakanin ‘ya’ya da iyayensu; wasu kuma an halicce su da tsoron duka.Wannan na ɗaya daga cikin dalilan da ke sanya iyaye na yi wa ‘ya’yansu auren dole. Ba wannan kaɗai ba, ladabi da biyayyan ‘ya’ya ga iyaye na daga cikin abubuwan da ke sanya a yi wa ‘ya’ya auren dole, kuma da jin auren dole, za a fahimci akwai tauye haƙƙin ‘ya’ya da iyaye ke yi ta fuskar tilasta su auren dole. Duk abin da aka ce an tilasta mutum yin sa ko aka yi masa shi, ba shakka akwai tauye haƙƙi da fin ƙarfi a ciki. Baiti na 38 marubucin ya nuna ƙarfin iyaye a kan ‘ya’ya ta hanyar sanya su auri wanda suke so, ba wanda’ya’yan ke so ba. An nuna cewa idan dai iyaye na son mutum ko ‘ya’ya ba su so, ɗaura aure ake yi. A cikin wannan yanayi idan aka lura sosai akwai danne haƙƙi da nuna fin ƙarfin ‘ya’ya mata daga iyayensu.

A wani baiti na daban, Fircin Koko ya ƙara tabbatar da tauye haƙƙin ‘ya’ya da iyaye ke yi kamar haka:

Ƙyale ta ko ta je tana dawowa,

Tunda munka yi babu mai tayarwa,

Kwanan ga sai ta gane ko mu aw wa,

Domin muna maishe ta ko don dole.

(Fircin Koko, Waƙar Auren Dole, Baiti na 41)

A baitin marubucin ya ƙara jaddada tauyije haƙƙin ‘ya’ya da iyaye ke yi ta fuskar nuna sun fi ƙarfin kowa ga sha’anin aurar da ‘ya’yansu ga duk wanda ransu ke so, ba wanda ‘ya’yan ke so ba. Wannan ya tabbata a wurin da suke cewa: “Tunda munka yi babu mai tayarwa” da kuma “Kwanan ga sai ta gane ko mu aw wa”. A ƙarshe suka biyo da cewa “Domin muna maishe ta ko don dole”. A cikin waɗannan maganganu akwai nuna fin ƙarfi da danniya daga iyaye zuwa ga ‘ya’yansu a wurin da suka nuna yin abin da suke so shi ne dole, baabin da ‘ya’yansu ke so ba. Idan aka lura da irin izzar da iyaye ke nunawa a cikin sha’anin aurar da ‘ya’yansu akwai matuƙar cutarwa a ciki da nuna na isa, ba wanda ya isa. A ƙarshe, takardar na da fahimtar cewa, babu abin da ya kawo wannan sai rashin sanin haƙƙin ‘ya’ya a kan na iyaye. Da an san haƙƙin ‘ya’ya da ba a mayar da su tamkar bayi ba, ana azabtar da su ba bisa haƙƙi ba.

Wasu atsalolin Auren Dole Ga Al’umma

Kamar yadda tsarin takardar ya nuna wannan babban ɓangare ne da take ɗauke da shi, wato illolin da auren dole ke tattare da shi. Babu shakka akwai waɗannan illoli da za a yi Magana kansu domin marubucin ƙasidar ya faɗi wasu da Allah ya nufi ya tuna da su a lokacin da ya rubuta ƙasidarsa. Za a ga hakan a cikin wasu misalai da za a kawo daga baitocin waƙar.

Rusa Zumunta

Akan yi aure domin haɗa zumunta tsakanin al’umma, amma ba auren dole ba. Duk auren da aka yi ba a zauna lafiya ba tsakanin miji da mata, ba a samu zumunci mai kyau ba a nan. Auren dole na da illoli da yawa, sai dai za a tsaya ga waɗanda marubucin waƙar ya kawo domin yi wa al’umma gargaɗi da a guje shi. Daga cikin illolinsa akwai ɓata zumuntar da ke tsakanin iyayen miji da na mata. A mahangar marubucin, ga abin daya kawo da ke lalata zumunta tsakanin dangin miji da na mata a cikin baitoci masu zuwa kamar haka:

 Auren da duk aka yi shi ba soyayya,

 Ƙarshe kana ishe shi ya zama kunya,

 Sai a ɗunguma kotu gun jayayya,

 Ka san akwai kunya ga auren dole.

 Abu an yi don nasara a ce ya ɓaci,

 Shi wanga aure shi ka ɓata zumunci,

 Daɗa kai da dangi ba shiri sai ɓaci,

 Don kun riga kun ƙulla auren dole.

(Fircin Koko, Waƙar Auren Dole, baiti na 53 da 54)

Duk abin da aka yi domin samun cigaba, kuma ya kasance ba a samu cigaban basai cigaba, buƙata bata biya ba. Haka kuma, duk abin da aka yi domin gyara zumunta kuma ba a kai ga nasarar yin hakan ba, to an sami akasi wato lalacewa. Idan aka haɗa aure tsakanin ‘ya’ya, babu shakka an haɗa zumunta ta alheri. Dogewan auren shi ke tabbatar da ƙulluwar zumunta. Watsewar auren kuwa, yana tabbatar da lalacewar zumuncin da aka ƙulla. A baiti na 53 marubucin ya faɗi cewa, duk auren da aka ƙulla ba tare da ma’aurata na son juna ba, an yi aikin banza kuma, ƙarshen al’amari za a tarar da an ji kunya haɗa auren saboda lalacewarsa. Bashi kaɗai ne kunya ba in ji marubucin. Ya Ce, zuwa kotu wurin alƙali domin ya raba auren, kuma a je a rinƙa jayayya tsakanin mata da miji da iyayensu, shi ma abin kunya ne. Babu shakka mai yiwuwa ne alƙali bai ko san da an yi auren ba, amma an kai masa shari’ar kashe shi, tare da lissafa abin da kowa ya kasha domin a biya kowa nasa, kunya ce babba ba ƙarama ba. A fahimtar maƙalar auren dole na ɗaya daga cikin abubuwan da ke kawo lalacewar zumuntar aure tsakanin ma’aurata. A baiti na 54 marubucin ya ci gaba da cewa, duk abin da aka yi domin a samu nasara kuma ba a samu ba, an samu akasi ke nan. A layi na biyu da ke cikin baitina 54 marubucin ya faɗi cewa auren dole na ɓata zumunci, kuma daga nan tsakanin dangin miji da na mata babu mutunta juna, sai zagin a sanadiyyar lalacewar auren dolen da suka ƙulla. Bayanin marubucin da ke cikin baitoci biyu da ke sama gaskiya ne domin irin haka ya sha faruwa tsakanin ma’aurata ta inda aure ke lalacewa, ita ma zumuntar da ke tsakani ta lalatace.

Sanya ‘Ya’ya Karuwanci

Karuwanci wata ɗabi’a ce da mata ke aikatawa kuma abin ƙyama ga addini da kuma al’adun al’ummomi. Babu iyayen da ke son ‘yarsu ta zama karuwa, sai dai abin na faruwa ta tsinkan cewa ko yarinya tace bata son wanda aka haɗa ta aure dashi, mai yiwuwa idan aka yi auren ta sauya tunani. Ana samun irin haka jefi-jefi a ɓangaren yaran da ke yi wa iyayensu biyayya ga abubuwan da suka umurce su da yi. Tare da haka, an sha samun ‘ya’ya mata na faɗawa tarkon karuwanci a sanadiyyar yi musu auren dole. Ga abin da marubucin ya kawo dangane da karuwancin ‘ya’ya a sanadiyyar auren dole da aka yi musu:

Ku ke da ‘yarku ku zo ku sa ta ta nakkasa,

Har sai ta tashi tana ta dandi ƙasa-ƙasa,

Duk ko ɗiyar da ka dandi ai ta nakkasa,

 Sanadin zama haka gunta auren dole.

(Fircin Koko, Waƙar Auren Dole, baiti na 17)

A cikin baitin da ya gabata marubucin ya nuna iyaye na daga cikin waɗanda ke sanya ‘ya’yansu shiga karuwanci ta hanyar yi musu auren dole. Tabbas, sun yi musu auren ba domin su zama karuwai ba, sai dai domin su zauna gidajen aurensu. Bayan yin auren ne abubuwan da ake ƙyama ke faruwa bada sani da son iyaye ba.Wannan ne dalilin da ya sanya Koko faɗin cewa, “Ku ke da ‘yarku ku zo ku sa ta ta nakkasa” a ɗango na farko. Nakkasa a nan karuwanci yake nufi. Idan an ce yarinya ta nakkasa, ana nufin ta hau turbar daba ta dace ta hau ba, irin sata da karuwanci da shaye-shaye da sauransu. A ɗango na biyu marubucin ya ɗan bayyana abin da ke faruwa bayan mace ta fara karuwanci na cewa, za ta kama dandi (Yawon banza/iska), ba ta nan ba ta can. Ya yanke hukuncin cewa duk ɗiyar da ke yawon dandi babu shakka ta nakkasa a ɗango na uku. A ɗango nahuɗu kuma, ya kawo dalilin da ya sanya ta nakkasa, kuma shi ne auren dole.

Ita ba ta kunya ko a ce mata karuwa,

Mi ad dalili wai kuke haka ‘yan uwa?

Ku sani fa auren dole ba wata ƙaruwa,

 Sai dai wulaƙanci ga auren dole.

(Fircin Koko, Waƙar Auren Dole, baiti na 18)

A baiti na 18 kuma marubucin ya faɗi cewa, idan wadda aka yi wa auren dole ta shiga uwa duniya, bata jin kunyar a ce mata karuwa domin a ganinta, ba laifinta ba ne, laifin iyayenta ne da suka yi mata auren dole. Ya tambayi al’umma a kan me ke sanya suna yi wa ‘ya’yansu auren dole? Bayan haka ya ja kunnensu cewa idan ba su sani ba, su san da cewa raguwa ke tattare da auren dole ba ƙaruwa ba. A ƙarshe, duk wadda ba ta daina ba, wulaƙanci zai biyo bayan ta zama karuwa. Wulaƙancin da ake nufi a nan shi ne, da ita da iyayenta da sauran danginta duka za a rinƙa yi musu faɗe cewa ai sun yi abin faɗi domin ‘yarsu karuwa ce. Da ‘yar da iyayen duka ba wanda ke farin ciki da maganar da aka yi masa. A ƙarshe idan ta kamu da wani ciwo ko kuma ta yi rashin sa’ar samun haihuwa a wajen karuwanci, shi ne ƙarshen wulaƙanci.

Matsalar ƙiyayya mun jiba ƙarama ba ce,

Auren da anka yi in akwai ta yakan mace,

Wata sai ta salwance tazan dai ta wuce,

 Wai don ta tsira ga wanga auren dole.

(Fircin Koko, Waƙar Auren Dole, baiti na 39)

Baiti na 39 da ke sama marubucin na jan hanklin iyaye dasu fahimcicewa, ƙiyayya na iya haddasa komai ba karuwanci kaɗai ba. Ya ƙara da cewa,duk auren da aka yi idanakwai ƙiyayya za a kai ranar da za a rabu ba cikin mutunci ba. Haka kuma, wata ma kan shiga uwa duniya a rasa sanin inda take sanadiyyar auren doleda aka yi mata. Ta zaɓi yin haka ne domin ya fi zamanta a gidan da aka yi mata auren dole.

Ƙiyo Da Kisan Kai

Rashin so tsakanin saurayi da budurwa ke kawo ƙiyo. Ƙiyo na nufin inda za a sami mata na guje wa miji don ba ta buƙatar saduwa da shi sanadiyyar rashin ƙauna a tsakaninsu. Wannan ke sanya miji na cikin ɗaki, mata na waje ko ɗaya na ciki ɗaya na waje. Wani lokaci ma matar kan ƙi shiga ɗaki da dare sai dai ta je wani wuri ta kwana don rashin buƙatar saduwa da mijin da aka aurar mata. Wannan na faruwa ne saboda aurar da yarinya ga wani a kan tilas ba da son ranta ba. Marubucin ya kawo ƙiyayya da ƙiyo a cikin waƙarsa domin ya nuna illar auren dole, kamar yadda ya ambata a cikin baitoci masu zuwa kamar haka:

 Ka taho kana zance tana tsokin ka,

 Shirme kake ita ba ta ko ƙaunar ka,

 Nan sai ta juya ba ta ko duban ka,

 Ni ba ni son ka ka bar ni ya zama dole.

(Fircin Koko, Waƙar Auren Dole, baiti na 25)

A baiti na 25 marubucin ya fito da ƙiyayya tsakanin miji da mata a fili sanadiyyar ƙulla auren dole. Idan aka sami miji na magana matarsa ba ta amsawa akwai dalilin daya sa hakan. Idan aka sami haka, marubucin ya ce shirme mijin ke yi, domin matar bata ƙaunar sa. Haka kuma, duk lokacin da aka samu mata na ba miji baya bata ƙaunar fuskantar sa akwai matsalar rashin so, wato ƙiyayya. Hasali ma idan matar tabuɗa baki ta yi magana, abin da take ce wa mijin shi ne, ba ni son ka don haka tilas ka rabu da ni, kamar yadda marubucin ya kawo a layi nahuɗu da ke cikin baitin da aka kawo a sama. Ga abin da matar ta ci gaba da faɗa in ji marubucin a biti na 26 kamar haka:

 Ban son ka ban son wanda ke ƙaunar ka,

 In ko da bashi yau faɗar shi na ba ka,

 Na tabbatar maka ba ni dai auren ka,

 Shi ko shina tsaye ya maƙe ya ƙyale.

(Fircin Koko, Waƙar Auren Dole, baiti na 26)

A cikin baitin da ke sama marubucin ya kawo maganar da mata ke gaya wa mijinta cewa, ba ta son sa, kuma ba ta son duk wanda ke ƙaunar sa. Tunda ba ta son mai ƙaunar mijin ta, ai mijin ne ba ta ƙauna kai tsaye. Wannan ya tabbatar da ƙiyayya tsakanin mata da miji sanadiyyar auren dole. Ta ci gaba da gaya masa cewa, ta riga ta ba shi tabbacin ba za ta aure shi ba saboda ba ta son sa. Matar ta ci gaba da magana har ta kai inda take gaya wa mai neman ta aure cewa, idan yana bin ta bashi ya faɗa ta biya shi. Haka ta ƙara da cewa, ta tabbatar masa ba za ta aure shi ba. Duk waɗannan magnganu da yarinyar ke yi, marubucin ya nuna cewa, yana nan tsaye tare da yarinyar bai ce uffn ba, kuma ya ƙi canza ra’ayi zuwa ga wata. Wannan baiti na nuna ko aure ba a yi ba, a wurin zance ne take gaya masa waɗannan maganganu, ba ma tare da an yi aure ba. Wannan ya yi daidai da abin da Hauswa ke faɗa na cewa, “Son masoyin wani ƙoshin wahala”. A cikin baitoci masu zuwa kuma, marubucin ya komo ga maganar miji bayan an ƙulla masa aure da wadda ba ya so kamar haka:

Wani har shi ce ke wance ban ƙaunar ki,

Ko can da Inna da Baba ke ƙaunar ki,

 In don ta ni ne ba ni dai auro ki,

 Ni yau da ke harakag ga ta zama dole.

(Fircin Koko, Waƙar Auren Dole, baiti na 62)

A baiti na 62marubucin ya bijiro da maganganun da miji ke yi wa matar daba ya so bayan an ƙulla aure. Kai tsaye yake buɗa baki ya ce mata ni fa ban ƙaunar ki, da ma Inna da Baba ne ke ƙaunar ki ba ni ba. Yakan ƙara mata da cewa, idan da sonsa ne, ba za a ƙulla aure tsakaninsu ba domin ba ya ƙaunar ta. A ƙarshen baiti ya faɗa mata cewa tsakaninsa da ita haraka ce kawai ta tilas, saboda Inna da Baba sun tsoma baki a cikin sha’anin auren, aka yi shi a kan tilas. A baiti mi zuwa marubucin ya waiwayo zuwa ga iyaye yana nuna musu abin da suka yi na ƙulla auren dole kuskure ne kuma babbar illa ce ga ma’aurata baki ɗaya. Ga abin da ya ce:

 Ku sani ɗiya kan damu in an yi shi,

 Kullum su kasa zama gida sai tashi,

 Shi ko miji su zamo suna ƙyamar shi,

 Nan kun ga illa ce ta auren dole.

(Fircin Koko, Waƙar Auren Dole, baiti na 12)

Marubucin na faɗa wa iyaye cewa ‘ya’ya na samun damuwa mai tsanani saboda yi musu auren dole. Maimakon suna zaune a gidajen aurensu, a’a. Kullum mace na kan hanya zuwa gidansu ko gidan ‘yan uwa da zancen yaji. Haka kuma, da mata da miji babu mai ƙaunar juna sai ƙyama a tsakani. Marubucin na jan hankalin iyaye tare da nuna musu illar haɗa auren dole da suka yi, kamar yadda tun farko aka ambata cewa, wannan ɓangare zai yi magana kan illolin auren dole.

A ɓangaren kisa kuwa, an sha samun kisan kai saboda ƙulla auren dole, ko mata ta yi sanadiyyar mutuwar miji ko kuma ita kanta ta yi sanadiyyar mutuwar kanta. A binciken da maƙalarar ta yi, mata sun fi maza alwashi da kashe mazansu na aure sanadiyyar auren dole ko wani dalili na daban, duk da yakeakan samiwasu daga cikinsu su faɗawa cikin rijiya ko wata hanyar halaka irin wannan. Akan sami mace ta sha wani magani ko guba domin ta huta da azabar auren dole. Marubuci waƙar ya ambaci kisan kai a cikin waƙarsa da auren dole ya sha haddasawa a lokaci mai ɗan tsawo daya wuce. Ga abin da ya faɗa dangane da hakan:

Duba a kainai mun ji har wasu kan mutu,

 Ko ko su ce wa mijinsu kai sai ka mutu,

 Duk yadda zan yi inai yazan dai ka mutu,

 In bar ganin ka saboda auren dole.

(Fircin Koko, Waƙar Auren Dole, baiti na 19)

A cikin baiti na 19 da ke sama marubucin yace sun ji wasu mutane (miji da mata ko mata ko kuma miji shi kaɗai), ko mata tace wa mijinta sai ta kashe shi saboda aurar da ita da aka yi ba tare da tana son sa ba. Wannan ya nuna a fili cewa auren dole ne aka yi mata ba tare da son ranta ba. Ɗango na uku matar ta faɗi cewa duk yadda za ta yi sai ta yi domin ganin mijin ya rasa ransa. A ɗango na ƙarshe sai marubucin ya kawo dalilin matar na yin tsaye kai da fata don ganin mijin ya rasa ransa. Dalilin da tabayar kuwa, shi ne auren dole. Babu shakka an sha samun matan da aka yi wa auren dole su yi sanadiyyar mutuwar miji ko su kashe kansu ta wata hanyar daba a sani ba. Wasu na shan magungunan kwana fiye da kima, idan ya rinjaye su sai mutuwa. Wasu kuma kai tsaye su sha guba su sheƙa lahira tsammanin hakan ya fi musu sauƙi da zama tare da wanda ba su so. Wasu kuma kan faɗa rijiya sai in lokaci bai yi ba, a yi jinya a warke. Dangane da hakan ga abin da marubucin ya ƙara kawowa a wani baitin waƙa na daban kamar haka:

Mata sukan kashe ma miji in basu so,

 Wasu ko su nakkasa shi mijin in ba su so,

 Kai kar ku shirya abin da kun san babu so,

 Domin akwai wahala ga auren dole.

(Fircin Koko, Waƙar Auren Dole, baiti na 49)

Ya fitofili ya nuna cewa mata kan kashe miji matuƙar ba su son sa, wasu kuma su nakkasa shi idan ba su son sa ta hanyar da suka yi tunanin nakkasa shi. Sanin haɗarin da ke tattare da rashin so ya sa marubucin ya tsawata wa iyaye cewa kar su yarda su ƙullaaure matuƙar babu so tsakanin ‘yarsu da saurayi domin guje wa kisa.

Duka

Akan sami mijina dukan matarsa saboda rashin son da ke tsakaninsu. Haka akan sami wani lokaci miji ke dukanmatarsa, wani lokaci kuma, mata ke dukan miji sanadiyyar rashin so da kuma rinjayar miji da ƙarfi. A wasu lokuta akan sami faɗa tsakanin mata da miji, kuma a sami matace ke dukan miji ba mijin ke dukan ta ba.Babu shakka duka na daga cikin matsalolin da auren dole ke haddasawa, kamar yadda marubuci waƙar ya ambata a cikin baiti mai zuwa:

Laifi kaɗan sai ɗai shi zazzage ta,

Wata ran a iske har shina kilmat ta,

In ɗan kure ta yi saishi mammare ta,

 Daɗa kun ji illa nan ta auren dole.

(Fircin Koko, Waƙar Auren Dole, baiti na 61)

Idan aka yi wa namiji auren dole da wata mace, miji ya fi nuna zafin rai sosai sama ga matar.Duk lokacin da matar ta yi masa laifi zai ɗauki matakin da zai kai ya duke ta. Matakin da ke kai miji ya doki matarsashi ne zagin da yake yi mata, idan aka yi rashin sa’a ta rama sai ya duke ta. Idan ta yi haƙuri ba ta rama ba, ƙilan ta guje wa dukan. Marubucin ya nuna cewa wata rana za tarad da yana kilmar ta (kilma na nufin dukan kowane sashen jikin mutum ta hanyar fusata mai iya kai ga a yi wa mutum rauni). Ya kawo wannan magna a ɗango na biyu da ke cikin baitin dake magana kansa.Haka ma a cikin layi na 3 marubucin ya ƙara kawo cewa, in ɗan kure ta yi wa miji sai ya mammare ta, mai nufin ba mari ɗaya ko biyu ba, mari da yawa na ɗibar haushi. Irin wannan mari ne za a tarad da fuskar mce ya kumbura sosai, harda sauran sashen jikinta da duka ta kai gare shi. Idan haka ya faru, an samimatsalar da Fircin Koko ke bayani a cikin baitocin waƙarsa. Duk lokacin da aka samu irin wannan al’amari ya faru, an yi kusa kai ga samun rabuwar aure.

Nadama

Akan sami yin nadama ta ɓangaren waɗanda suka yi tsaye sai an yi auren da yarinya ko yaro ba ya so. Hausawa na cewa, “Da-na-sani ƙeya ce”. Duk wanda ya yi tsaye sai an yi auren dole, su ke shiga cikin da-na-sani bayan ƙulla auren da ɗaya daga cikin ango ko amarya ke ƙyama. A nan, za a gano da-na-sanin da takardar ke magana a kai ta fuskar samuwar abubuwan da suka biyo baya da suka ci wa waɗanda suka ƙulla auren dole tuwo a ƙwarya. Ga wasu baitoci da ke tabbatar dada-na-sani ga iyaye ko waɗanda aka yi wa auren kamar haka:

Ku sani ɗiya kan damu in an yi shi,

Kullum su kasa zama gida sai tashi,

Shi ko miji su zamo suna ƙyamar shi,

 Nan kun ga illa ce ta auren dole.

(Fircin Koko, Waƙar Auren Dole, baiti na 13)

A wannan baiti mawaƙin ya yi gargaɗi ga iyayen ‘ya’ya baki ɗaya da cewa kar su kuskura su sanya su auren dole. Yi wa ‘ya’ya auren dole sanya su cikin tsaka mai wuya ne. Mace ba za ta zauna gidan aurenta ba matuƙar bata son mijin da aka haɗa su, sai yawan yin yaji har sai an gaji an raba auren. Ba wannan kaɗai ba, za su yi ta ƙyamar mijin aurensu, idan miji na cikin ɗaki, mata na waje. Ba su zama wuri ɗaya koyaushe, balle su yi zance ko shawara. Marubucin ya sheda wa iyaye cewa, bayanin daya yi ga iyaye, duk illoli ne na auren dole domin su kiyaye.Daga cikin illolin auren dole tsakanin mata da miji akwai abubuwan da marubuci waƙar ya kawo kamar haka:

Ka taho kana zance tana tsokin ka,

Shirme kake ita ba ta ko ƙaunar ka,

Nan sai ta juya ba ta ko duban ka,

 Ni ba ni son ka ka bar ni ya zama dole.

(Fircin Koko, Waƙar Auren Dole, baiti na 25)

A baiti na 25 akwai miji ya yi zance matar ta ƙyale shi saboda rashin ƙauna. Hasali ma idan suna zaune wuri ɗaya, baya take ba shi saboda rashin ƙauna kuma, komai daɗewa rabuwa za a y a kan rashin ƙaunar. Idan aka rabu akwai yiwuwar lalacewar dangantakar da ke tsakanin dangin miji da na mata. Ba wannan kaɗai ba, marubuci waƙar ya ƙara bayyanawa a baiti na 26 cewa, matar za ta kai fagen gaya wa miji cewa bata son sa bale ƙauna. Za tace masa idan yana bin ta bashi sai ya faɗa ta biya shi. A cikin zance ma takan sheda masa bata son sa, don haka ba za ta aure shi ba. Duk maganganun da take gaya masa ba ya cewa uffan domin yana son a yi. Wata matsala da ake haɗuwa da ita kuma ita ce, mata ta ƙi dafa abinci ba domin bata iyawa ba, sai domin tsananin rashin son mijin, sai kuma yawan zagin sa. Babu abin daya sanya ta yin haka face rashin son sa da ba ta yi, su kuma iyaye sun tilasta sai an yi auren. Idan aka yi la’akari da abin da aka faɗa a baya, babu tantama domin an ce auren dole na da illoli ba ma illa kaɗai ba.

A ci gaba da kawo illolin auren dole marubucin waƙar ya ƙara bayyana su kamar haka:

Wata ko ta ɗau kayan mijinta ta ƙone,

Ko da shina goya ta duk banza ne,

Zancen da yay yi gare ta duk shirme ne,

 Kai ko gani nai gunta sai dai dole.

(Fircin Koko, Waƙar Auren Dole, baiti na 50)

A baiti na 50 marubucin ya bayyana cewa za a sami mata ta ɗauki kayan mijinta ta ƙona, sannan ko goya ta yake yi a baya aikin banza ya yi in ji marubucin. Haka kuma duk zancen daya yi mata, a wurinta shirme ne yake yi kawai. Ba wannan kaɗai ba, ta tayar da kai ta dube shi sai dai a kan kuskure kurum saboda rashin so. Haka kuma miji ba ya da daraja a wurin matar. A baiti na 51 kuma, marubucin ya ƙara da cewa mijin ya san da cewa baya da daraja a wurin matar, sannan duk maganar daya yi mata bata ɗaukar maganar da muhimmanci saboda rashin so. Marubucin ya ƙara da tambayar mijin cewa yana son ya ji dalilin daya sanya har ya bari aka ɗaura aure bayan yana sane da yarinya ba ta son sa.Allah Sarki! Duk wulaƙanta miji da mata ke yi a kan rashin so, ashe kaɗan ne idan aka kwatanta da idan aka sami rashin son daga miji ne. Don tabbatar da hakan, ga abin da marubucin ya faɗa:

Ga maza idan an sa su auren dole,

Nan mace za ta ganin wuya don dole,

In ta yi zance sai mijinta shi ƙyale,

 Samun irin haka sai ga auren dole.

(Fircin Koko, Waƙar Auren Dole, baiti na 59)

Baiti na 59 marubucin ya faɗi ƙololuwar illar auren dole da cewa, idan aka tilastamiji sai ya auri mace a kan tilas, mace za ta sha wuya a hannun mijin fiye da yadda miji ke sha a wajen matar idan itace bata son sa. Zancen da miji ke yi mata ta ƙyale bai kai zafin wanda mata ke yi miji ya ƙyale ba. Wannan ya nuna cewa, kuskure ne ga iyaye na kowane ɓangare su haɗa auren dole tsakanin ‘ya’yansu. Wannan ya yi daidai da maganar da ake faɗa cewa, kowa ya dafa mugun tuwa, da shi za a ci shi. Ma’anaidan iyaye suka yi wa ‘ya’yansu auren dole, duk masifar da ta biyo baya, za ta shafe su kamar yadda idan aure ya yi daɗi su ma za su yi farin ciki.

Sakamakon Bincike

A cikin ɗan binciken da wannan takarda ta yi ta gano a zamanin da (musamman lokacin da ake cikin ƙarancin wayewar addinin Musulunci an samu iyaye ko dangi na ƙulla auren dole tsakanin wata da wani domin kwaɗayin ƙarfafa zumuntar da ke tsakaninsu ta ɗan uwantaka ko ta abokantaka da sauran dangantakar da ke sanya a haɗa yara aure. Daga cikin auren dole da aka haɗawa, da wuya ƙwarai ake samun biyu a cikin goma da ke ƙarko ya kasance an samu zaman lafiya tsakanin ango da amaryarsa. Wasu iyaye na yi wa ‘ya’yansu mata auren dole saboda kwaɗayin da kegare su na abin duniya da ya haɗa da kuɗi da sauran irinsu. Kafin yanzu, iyaye na haɗa ‘ya’yansu auren dole saboda rashin sanin illarsa, wato jahilci. Buƙatar kowane uba itace ya yi wa ‘yarsa aure ta je ta zauna lafiya. Maimakon hakan sai iyayen su rinƙa tauye haƙƙin ‘ya’yansu domin ganin ‘ya’yan sun bi inda suke so basu bi inda ‘ya’yansu ke so ba. Takardar ta gano cewa, duk auren da aka yi batare da ma’aurata na so ba, ƙarshensa ya lalace a gaban kotun alƙali ko kuma a gida.

Bawaɗannan kaɗai ba, takardar ta gano cewa akwai illolin da auren dole ke kawowa tsakanin miji da mata, a ƙarshe abin ya kawo da-na-sani ga iyaye. Haka kuma auren dole na sanya ‘ya’ya mata shiga uwa duniya da nufin yin karauwanci fiye da zama gidan miji a sanadiyyar auren dole. Ba wannan kaɗai ba, auren dole na sanadin mata ta kashe kanta ko kuma ta kashe mijin da aka aurar da ita gare shi domin rashin so da ƙauna. Haka kuma takardar tagano akan samu miji ya yi wa mata dukan daba ya da makari ta hanyar kilmar ta da mammaran ta saboda takaicin ƙiyayyar da matar ke yi masa. Ɓangare ɗaya kuma, matar na ɗaukar matakin ganin ta yi sanadiyyarrasa ran angonta ta kowane halin da bai dace ba idan ta sami damar yin haka. Duk inda aka samu waɗannan abubuwa tsakanin miji da mata na zaman kurege da bushiya, tilas akwai dalilin rashin so da rashin ƙauna tsakaninsu. Wani abu da takardar ta ƙara ganowa shi ne, alherin da ke cikinsa bai kai sharrinsa yawa ba. A taƙaice, waɗannan ne abubuwan da takardar ta hango a matsayin sakamakon binciken da ta gano.

Shawara

Hausawa na cewa ba domin kifin da ya wuce ake yin saba ba, domin mai dawowa. A fahimtar maƙalar babu waɗanda suka fi dacewa da a ba shawara fiye da iyaye. Haka ma akan ba ma’aurata shawarar abin da ya fi dacewa su yi baabin da rayukansu suka zaɓa musu ba. Farko yana da kyau iyaye su rinƙa bincike kafin su haɗa ‘ya’ya aure, idan suna son juna sai a ƙulla auren, idan kuma ba su da ra’ayin juna kar a yarda a ƙulla auren domin maganar Hausawa da suka ce, “Son masoyin wani ƙoshin wahala”. Haka kuma su daina nuna ‘ya’ya nasu ne, don haka sai sun yi yadda suke buƙata, wanda duk yayi abin da yake so zai ga abin da bay a so. Bayan haka su tashi tsaye ga neman ilmin addini da na zamani don ganin ba a bar su a baya ba. Abu ne mai kyau iyaye su rinƙa shawara da ‘ya’yansu a kan abin daya shafi wasu balle ‘ya’yansu. Su san da cewa, yi wa’ya’ya auren dole ba shari’a ce ba, idan aka nemi amincewarsu ya fi kawo zama lafiya da biyan buƙatar iyayen tare da samun farin ciki.

A ɓangaren ‘ya’ya kuma, yana da kyau idnana son a haɗa su auren daba su son wanda za a haɗa su, su je wajen ‘yan uwan mahaifinsu ko na mahaifiya su kai koke da cewa ba su ra’ayin wanda aka haɗa su ko ake son a haɗa su, amma ba ƙara ba. Wannan na da muhimmanci domin zaman aure ba zaman wasa ba ne, ana yin sa har ƙarshen rayuwa idan ba wata matsala ta faru ba. Haka kuma suna iya kai koke ga abokan mahaifnsu ko ga hakimai ko sarakunansu ko limaman garinsu kan kowace matsala ba sai ta auren dole da ake son yi musu ba.

Kammalawa

An samar da maƙalar ta hanyar farawa da gabatarwa da bayanin fitillun kalmomin da ke cikin takenta da suka haɗa da aure da dole da kuma auren dole. An kawo wasu kirarin da ake yi wa aure tare da taƙaitaccen tarihin marubucin waƙar auren dole. An fara tattauna taken takardar ta fuskar kawo dalilan da ke sa iyaye nayi wa ‘ya’yansu auren dole da suka haɗa da kwaɗayin ƙarfafa zumunta da kwaɗayin abin duniya da rashin ilmi da sauransu. A ɓangare na biyu kuwa, an kawo wasu illolin da marubucin waƙar ya hango wa al’umma, ita kuma maƙalar ta fito da su a fili ta bayyanawa al’umma.Daga cikin matsalolin akwai rusa zumunta da sanya ‘ya’ya karuwanci da ƙiyo mai haddasa kisa (mata ta kashe miji ko ta kashe kanta ta fuskar ɗaukanwani mataki ko abin da yayi kama da haka). Akwai duka ko bugun da miji ke yi wa mata ko su bugi juna har ya kai ɗaya ya halaka ɗaya ko duk su alaka. Haka ma akwai nadamar da ke biyowa bayanyin auren dole. An biyo da nadamar da ke ƙara biyowa baya daga cikin illolin auren dole da sakamakon bincike da shawarwari tare da kammalawa a ƙarshe.

Manazarta

Bargery, G.P. (1933). A Hausa-English Dictionary And English-Hausa Vocabulary: Ahmadu Bello University Press, London.

CNHN, (2006). Ƙamusun Hausa, Kano. Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya.

Gobir A.Y. (1993). Malam Muhammadu Umar Kwaran-Gamba da Waƙoƙinsa. Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato.

Koko L.A. (2004), ‘Malam Samaila Abdullahi Fircin Koko Da Waƙoƙinsa’ Kundin Digirin BA Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato.

Koko A.S. (2007), ‘Waƙoƙin Madahu Na Malam Sama’ila Abdullahi Fircin Koko’. Kundin Digirin BA Jmi’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato.

Usman, B.B. (2008), ‘Hikimar Magabata: Nazari A Kan Rayuwar Malam (Dr.) Umaru Nassarawa Wazirin Gwandu (1916-2000) da Waƙoƙinsa’. Kundin Digirin Ph D, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato.

Yahya A.B. (1989), ‘The Verse Category of Madahu With Special Reference To Theme, Style And Background Of Islamic Source And Belief’ Kundin Ph D, U.D.U. Sokoto

Yahaya A.B. (1995), ‘Kwatancen Jigo Tsakanin Waƙoƙin Sarauta Na Baka Da Rubutatun Cikin Harsunan Nijeriya’, 17.34-56. CNHN Jami’ar Bayero, Kano.

Yahya, A.B. (1997) Jigon Nazarin Waƙa. Kaduna Fisbas Media Service.

Yahaya A.B. (2001), ‘Dangantakar waƙa Da Tarbiyar ‘Ya’yan Hausawa’ Cikin Harsunan Nijeriya XIX” 94-108, CNHN Jami’ar Bayero, Kano.

Yahya A.B. (2010), ‘Waƙa: Ma’ana Da Ɗabi’a Da Gimshiƙinta’. Takardar da aka gabatar a taron ƙara wa juna sani da Cibiyar Nazarin Hausa ta jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo,Sakkwato ta gudanar a ranar 27/7/2010.

Yahya A.B. (2014). ‘Rubutattun Waƙoƙin Nasiha: Wani Ɓangare Ko Kuma Sauyin Salo A Cikin Rubutattun Waƙoƙin Hausa Na Wa’azi’ Cikin Algaita, Jami’ar Bayero, Kano.

Yahaya A.B. (2021),Salo Asirin Waƙa, Sabon Tsari. FISBAS Media Service, Kaduna.

 

Post a Comment

0 Comments