Ticker

6/recent/ticker-posts

Yake-Yake da Zaman Lafiya a Cikin Littafin Magana Jari Ce

Citation: Atuwo, A.A. and Faruk, A. (2024). Yaƙe-Yaƙe da Zaman Lafiya a Cikin Littafin Magana Jari Ce. Ginshiƙin Nazarin Salon Waƙoƙin Hausa, 141-154. www.doi.org/10.36349/djhs.2024.v03i01.017.

Yaƙe-Yaƙe da Zaman Lafiya a Cikin Littafin Magana Jari Ce

Abdulbasir Ahmad Atuwo
Sashen Harsunan Nijeriya
Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato
drabdulbasir87@gmail.com
07032492269

Da

Abdurrahman Faruk
Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya
Jami’ar Umaru Musa Yar’adua, Katsina
Abduldaruk232@gmail.com
08065547688

Tsakure: Yaƙi da zaman lafiya kishiyoyin juna ne. Yanaye-yanaye ne na zamantakewar rayuwa. idan al’umma ta yi yawa, akan sami bambancin ra’ayoyi. Ba abin mamaki ba ne ga samun bambancin ra’ayoyi tsakanin al’ummomin da ke zaune a muhalli guda da kuma masu maƙwabtaka da juna. Duk inda rashin jituwa ya ɓulla, lallai ƙarshensa yaƙi ne. Idan aka gwabza, kowa ya ji kowa, sai kuma a dawo a yi sulhu wato a yafe wa juna. Da zaran an yafe wa juna aka manta da baya, sai kuma zumunci mai danƙo ya biyo baya a narke a koma wasa. Wannan zumunci mai danƙo shi ake kira zaman lafiya. Ke nan, da zaman lafiya da yaƙi taubasai ne. Wannan maƙala mai taken, “Yaƙe-Yaƙe da Zaman Lafiya a Cikin Littafin Magana Jari Ce,” sharhi ne dangane da matsayin yaƙe-yaƙe da zaman lafiya da yadda suka zama furen kallo ga marubuta labaran Hausa. An yi garkuwa da littafin Magana Jari Ce na Abubakar Imam. Ke nan maƙalar za ta bayyana yadda yaƙi da zaman lafiya suka zama wasu saƙonni na musamman a cikin littafin na Magana Jari Ce. An karanta littafin Magana Jari Ce da wasu ayyuka na masana, waɗanda suka yi sharhi a kan yaƙi da zaman lafiya, a matsayin manyan hanyoyin da aka bi aka gudanar da binciken. An yi amfani da ra’in karin maganar nan mai cewa, “Idan An Ciza, Sai a Hura” a wajen gudanar da maƙalar. Daga ƙarshe sai maƙalar ta gano cewa yaƙi da zaman lafiya su ne ma manyan ginshiƙan da aka gina littafin Magana Jari Ce da su. Haka kuma, mawallafin ya yi amfani da littafin na Magana Jari Ce don ya nusar da al’umma a kan dalilan da kan haddasa yaƙi, domin a yi taka-tsan-tsan da su da kuma yadda ake tattalin dawo da zaman lafiya idan ya kuɓuce..

Fitilun Kalmomi: Yaƙe-yaƙe, Zaman Lafiya, Magana Jari Ce

Gabatarwa

Adabi dai tumbin giwa ne da har ma wasu Hausawa na yi masa kirari da, “Ka fi giwa nama.” Sannan adabi kamar jakar magori ce, wadda ta ƙunshi abubuwa daban-daban. An siffanta adabi da waɗannan abubuwa guda biyu a cikin karin magana, ganin yadda ya ƙunshi fagagen rayuwar al’umma daban-daban. A wannan maƙala, an binciki adabi, inda aka gano wani giɓi na rayuwar al’umma da ake so a cike. An hango wata matasala wadda ta mamaye rayuwar al’umma da ake so a yi gyara a kanta. Da yake shi adabi madubi ne da akan duba domin a ga inda rayuwara al’ummar ke buƙatar gyara, a gyara. Yaƙi da dalilan da ke haddasa shi, da kuma zaman lafiya da dalilan da ke kawo zaman lafiya aka yi tsokaci a cikin rubutaccen adabin Hausa. Ke nan dai, ana so a yi sharhi kan yaƙe-yaƙen da zaman lafiya a cikin littafin Magana Jari Ce wanda Alhaji Abubakar Imam ya wallafa. An yi wa maƙalar laƙabi da, “Yaƙe-Yaƙe da Zaman Lafiya a Cikin Littafin Magana Jari Ce.

Masana da manazarta sun yi nazarce-nazarce a kan wannan fage na yin tsokaci a kan al’adun zamantakewar rayuwar Hausawa a cikin rubutaccen adabinsu. Misali, akwai aikace-aikace da aka yi da ke da alaƙa da fagen nazarin rayuwar al’umma, musamman abin da ya shafi tsarin zamantakewarsu. Ayyuka ire-iren su Clausewitch (1968) da Fuller (1970) da Fika (1978) da Muri (2003) da Hussaini (2016) da Atuwo (2009) Umar (2017) da kuma Shehu (2018), misalai ne na waɗannan nazarce-nazarce. Wasu daga cikin waɗannan rubuce-rubuce sun yi bayani ne a kan tarihin yaƙe-yaƙe da yadda suka gudana, wasu kuma a kan rikice-rikicen ƙabilanci da na bambancin addini aka gudanar da su. An rubuta wasu daga cikinsu a kan yadda sojoji suka fuskanci matsala da yadda suka sami nasara wajen kare martabar ƙasarsu. Wasu kuma sai suka fuskanci zaman lafiya da yadda ake tattalinsa idan ya kuɓuce wa al’umma da dai sauransu. Ke nan aiwatar da bincike-bincike makamantan waɗannan ba yau aka fara ba.

Kamar yadda waɗannan rubuce-rubuce suka yi tsokaci a kan yaƙi da zaman lafiya, haka ita ma wannan maƙala ta yi nazarin yaƙi da zaman lafiya, bisa la’akari da yadda marubuta labaran Hausa ke sarrafa su a cikin rubuce-rubucensu.

An fara gabatar da maƙalar tun farko, daga baya sai aka biyo da ma’anar yaƙi da zaman lafiya. An kawo taƙaitaccen bayani a kan samuwar littafin Magana Jari Ce. Bayan nan, sai aka kawo matsayin yaƙi da zaman lafiya a cikin littafin Magana Jaru Ce. Bayan an ƙare kawo yadda amai littafin Magana Jari Ce ya yi amfani da yaƙi da zaman lafiya wajen isar da saƙon littafinsa, sai aka kawo sakamakon da maƙalar ta gano. Dagan an sai kammala binciken. An kawo jawabin kammalawa da kuma manazarta, inda aka samu muhimman bayanan da aka gina maƙalar da su.

Ra’in Bincike

An ɗora wannan bincike a kan ra’in karin Magana wadda ke cewa, “Idan An Ciza, Sai a Hura.” Sharhin wannan karin magana shi ne idan aka ɗauki zafi, sai a dawo daga baya kuma a huce. An gina karin maganar daga halin ɓera da kan ciza ƙafar mutum ko hannu musamman wanda ya ci abinci bai wanke ba, idan yana barci. Ɓera kan zo yana jin ƙanshin abincin mutum ya ci bai wanke hannunsa ba. Ɓera kan hura inda ya ciza domin mai ƙafar ko hannun ya ji sanyi-sanyi yadda ba zai kula da cizon ba. Duk inda aka yi amfani da wannan karin maganar, ana nuna wani lamari da ya tsananta, ya sosa zuciya, ya kuma tayar da hankali, to kuma, idan aka yi haƙuri na wani lokaci, lamarin zai wuce har ya kasance an manta da shi, sai dai labari. Da yake yanzu nazarce-nazarce ire-iren waɗannan, akan ɗora su a kan ra’in karin magana. Ita kuwa karin magana wata gajeriyar magana ce mai ɗauke da dogon sharhi idan aka warware ta.

Dangantakar ra’in, “Idan Aka Ciza, Sai a hura” da wannan bincike da ake gudanarwa ita ce, wannan karin magana na nuna cewa, idan aka yi faɗa, sai kuma a yi abota. Karin maganar na bayyana bai kamata ba a riƙa yin faɗa kodayaushe, ba tare da an yi abota ba. Haka shi ma wannan bincike ke yin bayani a kan yaƙi da zaman lafiya. Binciken na nuna cewa bayan an tattauna dalilan da ke haddasa yaƙi, sai kuma a kawo dalilan da ke bunƙasa zaman lafiya a cikin al’umma. Kamar yadda aka siffanta yaƙi da cizo, haka aka siffanta busawa da zaman lafiya. Ke nan takardar ta yi tsokaci a kan yaƙi da sabubbansa, sai kuma zaman lafiya da abubuwan da ke kawo shi.

Taƙaitaccen Tarihin Mawallafin Magana Jari Ce

Wanda ya wallafa littafin Magana Jari Ce shi ne Alhaji Abubakar Imam. Dangane da haihuwarsa da ƙuruciyarsa wato tarihin rayuwarsa, masana sun sha tofa albarkacin bakinsu a kai. Daga cikin ire-iren waɗannan masana akwai: Pweddon (1977) da Mora (1989) da Ibrahim (1990) da Malumfashi (2009) da Guga (2010) da Nafi, u (2012) da Hassan (2013) da Maiyama (2013) da Sani (2013) da dai suransu. Duka waɗannan masana sun tabbatar da cewa, an haifi Abubakar Imam a shekarar 1911, a garin Kagara ta Kwantagora wadda daga baya ta koma cikin jihar Neja (Malumfashi, 2009:13).

Kamar yadda suka nuna, Abubakar Imam ya fara karatun allo a wurin mahaifinsa mai suna Malam Usman. Daga baya kuma sai ya koma ɗaukar ilmin littattafai na addinin Musulunci a wajen yayansa wato Malam Bello Kagara. A wajen shekarar 1922, Abubakar Imam ya shiga makarantar boko ta Midil, wadda ke Katsina, inda ya ƙare a shekarrar 1927. A wannan makaranta Imam ya riƙe muƙamai da yawa daga cikinsu har da Ma’ajin Ɗalibai. A shekarar 1932 Imam ya kammala karatun Kwaleji. Yana ƙare Kwaleji sai Abubakar Imam ya sami aikin koyarwa a makarantar Midil, wato inda ya yi ken an. A wannan lokaci ne Majalisar Masarautar Katsaina ta ba shi aikin tafinta, a lokacin Sarkin Katsina Dikko (Maiyama, 2013: 415).

A shekarar 1935 kuma, an ɗora wa Abubakar Imam aikin alhakin duba rahotannin da suka shafi shari’ar kisan kai domin a tantance abin da ke cikin harshen Ingilishi da Larabci shi ne a cikin harshen Hausa. Daga cikin muƙaman da Abubakar Imam ya riƙe har da Zama Jami’in Hukumar Bayar da Shawara ta Katsina da Editan Jaridar Gaskiya Ta Fi Kwabo Malumfashi, (2009: 21).

Abubakar Imam ya shiga cikin harkokin siyasa kacokan, inda ya fara shiga cikin Jam’iyyar Mutanen Arewa a cikin shekarar 1948, inda ya riƙe muƙamin Ma’ajin Ƙungiya. A sha’anin siyasa tabbas Abubakar Imam ya taka muhimmiyar rawa wajen ganin an yi siyasa don taimakon ƙasa da al’ummar Nijeriya ba siyasar muzgnawa da danniya ba. Wato dai ya yi siyasa ba da gaba ba (Malumfashi, 2009: 21).

Ta fuskar rubuce-rubuce kuma, an tabbatar da Alhaji Imam ya rubuta littattafai a ƙalla guda goma sha takwas (18) da suka shafi fagagen ilmi da daman gaske (Malumfashi, 2009:21). Daga cikin littafan day a rubuta da hannunsa akwai:

1.      Ruwan Bagaja 1933

2.      Magana Jari Ce I, 1939

3.      Magana Jari Ce II, 1940

4.      Magana Jari Ce III, 1940

5.      Ikon Allah

6.      Tarihin Sayyidina Abubakar Saddik

7.      Tarihin Sahabbai

8.      Tafiya Mabuɗin Ilmi da sauransu ( Malumfashi, 2009)

Wannan littafi na Magana Jari Ce I-III ne wannna maƙala aza ta yi nazarin Yaƙi da Zaman Lafiya a cikinsa. Allah Ya yi wa Abubakar Imam rasuwa a ranan Jumu’a, 19 ga watan Yuni shekarar 1981 Miladiyya, a Asibitin Koayarwa ta Ahamadu Bello da ke cikin garin Zariya. Ya bar matar aure ɗaya da ‘ya’ya goma sha huɗu (14), bakwai maza bakwai mata. Alhaji Abubakar Iman ya bar jikoki a ƙalla guda arba’in da biyu (42) maza da mata (Mora, 1989: 229).

Wanzuwar Littafin Magana Jari Ce

A wajen shekarar 1932-1933, ‘yan ƙasa sun sami ilmin book bakin gwargawado. Da yawansu sun iya karatu da rubutu. Sai dai kash!, ga dai sani ya samu, amma kuma ga ƙishirwar littattafan karantawa. Ga ma littattafan da ake karantawa a makarantu sun yi ƙaranci, ga rashin dacewa ga ɗalibai. Ɗaliban makarantar Elementare sun gaji da karanata su, saboda babu sauyi. Ga littattafan da saurin gundurar mai karatu, saboda babu ɗaya daga cikinsu da ya shafi tantagaryar adabi. Duka-duka ma littattafan da ake koya wa yara karatu da su guda biyu ne: Daga Aljaman Yara, sai Littafin Koyarwa na Karatu da Rubutu (Malumfashi, 2009:52).

Ko da Gwamnatin Arewa ƙarƙashin Hukumar Ilimi ta fahimci wannan matsala ta rashin littattafan karantawa a makarantun Elementare, sai ta sa wani Jami’inta wato Dr.R.M. Esat a ƙarƙashin Hukumar Fassara, ya kewaya cikin ƙasa ya yi yekuwar cewa, Hukumar Ilmi za ta sa gasar rubuta ƙagaggun labarai na Hausa. Kamar yadda sunan littattafan ya nuna, an sanya dokokin gasar waɗanda su ne R.M. East ya kewaya ya shaida wa ‘yan ƙasa da suka ilmanta, cewa ba fa fasssara ake so ba, a wannan karon ana buƙatar ƙagawar mawallafi ne. Duk wanda ya yi nasara, za a ba shi kyauta mai tsoka, kuma a buga masa littafinsa kyauta, littattafan su kuma kewaya cikin ƙasa (Malumfashi, 2019:52).

Bayan an yi wannan gasa a shekarar 1932-1933, sai aka fitar da sakamakon gasar, inda littattafai biyar suka lashe gasar. Ga littaffan:

1.      Ruwan Bagaja na Abubakar Kagara

2.      Ganɗoki na Bello Kagara

3.      Shaihu Umar na Abubakar Bauchi

4.      Idon Matambayi na Sani Gwarzo

5.      Jiki Magayi na R.M. East da John Umaru Tafida Zariya (Malumfashi, 2009: 25).

Wannan nasara da Abubakar Imam ya samu ta sa an buga littafinsa na Ruwan Bagaja a shekarar 1933, kuma sai aka aro shi daga Lardin Katsina inda yake aikin koyarwa ya zo ofishin Hukumar Fassara da ke Zariya don ya rubuta littaffan da za a raba a makarantun da ke Arewacin Nijeriya. Kafin ya fara rubuta komai sai da ya ba da shawarar sauya wa Hukumar fassara suna, wadda aikinta a da fassara ne daga Turanci da Larabci zuwa Hausa. Daga nan sai aka mai da ita Hukumar Talifi, saboda yadda aikin wallafe-wallafen littattafai ya ƙaru ga hukumar (Adamu, 2019:17).

Aikin da Abubakar Imam ya fara yi ƙarƙashin Hukumar Talifi shi ne rubuta littattafan Magana Jari Ce na I-III. Kafin ya fara wannna aiki, sai da uban gidansa wato Dr. R. M. Esat ya tattara masa littattafan labaran Turawa da Larabawa da Mutanen Sin da na Al’ummar Rasha, ya yi ta karantawa. Da yake Abubakar Imam yana jin harsuna da dama. Da ya naƙalci yadda rubuce-rubucen labaran wasu al’ummomi suke, sai ya yi azama ya fara rubuta Magana Jari Ce (Pweddon, 1977: 151).

Kodayake, Pweddon ya tabbatar da ba Abubakar Imam ne ya rarraba littafin Magana Jari Ce littafi-littafi ba, ya faɗa masa haka a hirar da Pweddon ya yi da Imam cewa, dangane da littafin Magana Jari Ce littafi na farko zuwa na uku, sai Abubakar Imam ya tabbatar masa da cewa sam, shi bai karkasa littafin Magana jari Ce littafi na farko zuwa na uku ba. Shi ya ci gaba da rubuta labaransa kara zube. Duk labarin da ya faɗo masa a rai, sai ya rubuta abinsa. A cewar Imam editan littafin ne wato Dr. R. M. Esat ne ya kasarkasa shi zuwa littafi na farko da na biyu da na uku don ya yi daɗin karantawa ga ɗalibai (Pweddon, 1977:151). A cikin wamnan liitafi na Magana Jari Ce wannan maƙaka za ta yi nazarin Yaƙi da Zaman Lafiya da yadda Imam ya sarrafa su a cikin Labaransa.

Ma’anar Fitilun Kalmomi

Akwai kalmomin da suka zama tamkar fitila ga wannan maƙala. Su waɗannan kalmomi su ne suka haɗu suka gina taken wannan maƙala. Idan aka lura da taken, za a ga cewa kalmomi ne guda uku su ne: Yaƙi da zaman lafiya da kuma Magana Jari Ce. Yana da kyau a yi fashin baƙinsu kafin a shiga cikin maƙalar gadan-gadan.

 Yaƙi - Yaƙe

 Yaƙi dai shi ne far wa wasu mutane da faɗa domin a mulke su ba (CNHN, 2006: 477). Ke nan ko ta wace fuska aka far wa mutane da faɗa bayan an laƙume su, a aza musu dokokin bauta, to ana iya cewa an yaƙe su ne. Yaƙi gwagwarmayar siyasa ce wadda ake tunkarar abokan gaba a tursasa musu, su karɓi tayin bin ra’ayoyin abokan gaba. Cakuɗuwar siyasa da kan haddasa ruɗin rayuwa, yaƙi ne (Muri, 2003: 25).

Idan aka dubi waɗannan ma’anoni da (CNHN, 2006) da Muri (2003) suka kawo, za a iya daddagewa da cewa, yaƙi ya ƙunshi faɗa wa mutane da faɗa, ko da sanin mutanen ko ba tare da sanin su ba, da nufin idan an ci galaba a kansu, a mulke su ko a mai da su bayi. Yaƙi ya ƙunshi rikicin siyasa tasakanin al’ummomi guda biyu, wanda kan sa wasu mutane su tasar wa wasu da faɗa su kashe su, su kuma mamaye yankunansu da dukiyoyinsu. Yaƙi tashin hankali ne da rikici da tarzoma da tashin-tashina da zaman doya da manja tsakanin al’ummomi guda biyu ko kuma da yawa da suke yi wa juna kallon hadarin kaji. Yaƙi ya zama wani jigo na marubuta labaran Hausa. Sukan shirya littattafansu da nufin nusar da masu karatu a kan dalilai da dabaru da matsalolin yaƙe-yaƙe.

Zaman Lafiya

 Kalmomi biyu ne suka haɗu suka samar da zaman Lafiya wato “Zama” da “Lafiya.” Idan aka ce, “Zama,” ana nufin kasancewa zaune kishiyar tsayuwa (CNHN, 2006: 489). Yayin da kalmar, “Lafiya” ke nufin rashin tashin hankali da hargitsi a wuri (CNHN, 2006: 298). Idan aka haɗa kalmomin guda biyu, “Zaman Lafiya,” ana maganar gudanar da rayuwa cikin natsuwa da lumana ba tare da wani ƙalubalen tsaro ba. Kodayake a ra’ayin wani masani, Zaman Lafiya shi ne:

Zama cikin natsuwa da sakewa da rashin fargaba da tashin-tashina ta kowace fuska. Zama ne da ba ka cuta ba, ba a cuce ka ba. Zama ne na aminci ga ƙasa da waɗanda ke cikinta da waɗanda za su ziyarce ta da waɗanda za su fice daga cikinta da waɗanda ke maƙawbtaka da ita. Zama ne da zai bai wa duk wanda ke cikin ƙasa da asalinta da baƙinta na arziƙi da ‘yan gudun hijira da masu zaman mafakar siyasa a cikin natsuwa da kuranye firgita a tsakaninsu. Zaman lafiya zama ne na ɗebe ɗammaha ga duk wata hayagaga da ruɓushi da ta bda zaune tsaye da wata halitta za ta haddasa ga wanda ke cikinta face abubuwan da babu makawa aka ƙaddaro gare ta daga Mai Ƙaddarawa wato Allah (Shehu, 2018: 3-4).

La’akari da wannan ma’ana ta Zaman Lafiya da Shehu (2018) ya bayar, za a iya cewa duk wani yanayi da zai ba mazaunin muhalli ko baƙo ko mutum ko dabba dama su rayu cikin walwala da kwanciyar hankari, shi ake ce wa zaman lafiya. Zaman lafiya kishiyar yaƙi ne, duk inda ɗaya yake, to, ɗaya zai faku. Shi ma zaman lafiya ɗaya ne daga cikin furannin kallon da marubuta labaran Hausa ke amfani da su wajen ƙawata labaransu. Wannan dalili ne ya sa wannan maƙala ta yi tsokaci a kan yaƙi da zaman lafiya a cikin littafin Magana Jari Ce na Abubakar Imam.

 

Yaƙi Cikin Littafin Magana Jari Ce

Yaƙi wani babban tubali ne na gina littafin Magana Jari Ce. Mawallafin littafin Magana Jari Ce ya yai amfani da Yaƙi ya gina wasu labarai na littafin. Kamar yadda Muri (2003) ya nuna, duk inda yaƙi ya auku, yana da ginshiƙai guda goma (10). Waɗannan ginshiƙai na yaƙi su ne ke sa yaƙi ya amsa sunansa, kuma su ne kan kawo nasara. Idan ƙasa ko al’umma suka kauce wa waɗannan ginshiƙai, ko suka sami matsala wajen yin amfani da wasu, to, za su ɗauki kashinsu da hannu daga abokan gaba. Waɗannan ginshiƙai su ne: Manufar yaƙi da tattalin arziƙin dakaru da tarwatsa abokan gaba da nasarar yaƙi da mallakar ƙarfin filin daga da ɓoye sirrin dabarar yaƙi da Tsaro da sanin makamar yaƙi da biyyayyar jagora daga dakaru da kuma iya rarraba dakaru a fagen yaƙi (Muri, 2003: 87. Fassarar mai bincike). Bari a dubi yadda Abubakar Imam ya sarrafa su a cikin labaran da ke cikin Magana Jari Ce.

Manufar Yaƙi

Manufa na nufin inda aka sa gaba. Babban dalilin yin wani abu ma manufarsa ce. Ke nan idan aka ce manufar yaƙi, ana nufin babban dalilin da ya sa aka fito filin daga. Babu abin da za a iya aiwatarwa, ba tare da yana da manufa ba. Dalilin da ya sa aka ko za a ko ake aikata wani abu shi ne manufarsa. Manufar yaƙi na nufin dalilin da ya haddasa yaƙi. Da wuya haka kawai, ba cas, ba as, a tsiri yin yaƙi da waɗansu al’umma. Shi yaƙin ma a karan kansa ba abu ne mai amfani ba. Idan kuwa hali ya ba da sai an yi, to sai a yi shi bisa kan ƙa’ida da dokokin da aka shimfiɗa don haka. A cikin buɗewar Magana Jari Ce littafi na farko, an nuna cewa manufar yaƙin da Sarkin Sinari ke yi ita ce ramuwar gayya. Domin Sarki Abdurrahman ya ci mutuncinsa, don kawai ya aika masa da wasiƙa ta neman shawara a kan su ƙara ƙarfafa zumuncinsu ta hanyar haɗa ‘ya’yansu aure. Ko da Sarki ya karanta takardar sai:

...Ya tashi da faɗa, ya fizge takarda daga hannun Magatakarda ya kekketa. Ya tashi ya kama gemun Wazirin Sinari, ya jefar da shi gefe guda. Sarakunansa suka shiga tsakani, suna, “Hucewa mai duniya! Rashin hankali ne na yara.” Sarki ya ce ko Musa ya lalace ya auri Sinaratu? Me aka yi aka yi Sarkin Sinari, balle ‘yarsa Sinaratu? Ya dubi mutanensa, ya ce, “Ku yi ta dukan su sai sun bar ƙasata!” (Imam, 1939: 4).

Da an karanta wannan bayani na sama, za a fahimci cewa, ba haka kurun Sarkin Sinari ya afka wa mutanen Sarki Abdurrahman da yaƙi ba. An ga yadda Sarki Abdurrahman ya yanke hukunci cikin fushi, ya ci fuskar Sarkin Sinari a gaban manzanninsa. Idan aka lura da dalilin cin fuskar kuma, Sarki Abdurrahman ne ba ya da gaskiya. Shawara ce Sarkin Sinari ya nema, idan bai karɓi shawarar ba, yadda Sarkin Sinari ya aiko da wasiƙa, kamata ya yi shi ma ya sa a mai da masa amsa a rubuce kuma cikin harshe mai laushi kamar yadda aka yi masa. A maimakon haka, sai ya ci wa manzannin mutunci, ya kuma sa aka yi musu ature, suka bar ƙasarsa dutse hannun riga. Duk wanda ya karanta wannan bayani da ke sama, zai gane cewa bai kamata Sarkin Sinari ya sa ido ga wannan cin mutunci ba. Yaƙi ne kawai hanyar warware matsalar.

Tattalin Arziƙin Dakaru

 Idan aka ce, “Tattali,” ana nufin tanaji ko kula ko ajiye wani abu don yin amfani da shi nan gaba (CNHN, 2006: 432). Yayin da “Arziƙi” ke nufin wadata ko sa’a ko kuɓuta ko kirki (CNHN, 2006:19). Dangane da kalmar, “Dakaru” kuma, an bayyana ta dajarumai ko mayaƙa masu tafiya da ƙafa. Matsiyatan mutune ma dakaru ne (CNHN, 2006:88). Idan aka haɗa kalmomin guda uku wuri ɗaya, za su samar da, “Tattalin Arziƙin Dakaru” da ke nufin tanaji don a wadatar da jarumai da wani abu da nan gaba zai taimake su yayin da buƙatarsa ta taso. Idan aka yi maganar tattalin arziƙin Dakaru, ke nan ana maganar wadatar da mayaƙa da jarumai da kayan faɗa ko makaman yaƙi da nufin tunkarar abokan gaba. Wani wani ginshiƙi ne na yaƙi. Shuwagabanni da hukumomi da ma al’umma ne ke da alhakin tanadar wa jarumai makaman yaƙi. Idan aka yi musu haka, za a ƙara musu ƙaimi domin su tunkari abokan gaba kuma su ci galaba a kansu. A cikin littafin Magana Jari Ce, an yi amfani da irin wannan ginshiƙin yaƙi.

A cikin buɗewar littafin Magana Jari Ce littafi na farko, an nuna cewa bayan da rashin jituwa ta auku tsakanin Sarki Abdurrahman da Sarkin Sinari, sai Sarkin Sinari ya aiko da mayaƙa suka nufo garin Sarki Abdurrahman domin su yaƙe su. Ko da wani Bafaden Sarki Abdurrahman ya ga abin da ke faruwa da idonsa, sai ya garzaya ya sanar da Sarki Adurrahaman. Daga nan sai Sarki:

...Ya zaɓi ‘yan ƙwarbai guda ɗari ya aika da su inda aku ya misalta masa. Ya kuma ta da manzanni ya aika da su Kudu da Arewa, Gabas da Yamma, a gaya wa mutane su yiwo harama, su zo maza da shirin yaƙi. Maƙera kuma suka shiga shirin gyara makamai (Imam, 1939: 8).

Dubi yadda bayanin nan na sama ya nuna Sarki ya aika wa mutane a kan su taho da gaugawa, ga yaƙi nan ya same su babu ko shiri, amma bai ce su taho hannu-biyu ba, sai ya ƙarfafa musu tahowa da makamai. An nuna a cikin labarin cewa, an ba maƙera dama su gyara musu makaman da suka dakushe da waɗanda suka kare. Mallaka da gayara makamin yaƙi ko don gudun ta-kwana, wani ginshiƙi ne mai muhimmanci na yaƙi da aka yi amfani da shi a cikin littafin Magana Jari Ce.

Tarwatsa Abokan Gaba

 “Tarwatsa” na nufin watsa ko barbaza (CNHN, 2006: 430). Tarwatsa abokan gaba ya shafi watsa abokan gaba ke nan ko barbaza su ba tare da suna son haka ba. Idan aka watsa abokan gaba a filin daga, an barbaza su ke nan, kowa ya sa fuskanci alƙiblarsa daban. tarwatsa abokan gaba ya shafi korar su daga fagen yaƙi, su koma a guje, su ji tsoro. Idan abokan gaba suka fahimci babu nasara cikin tunkarar abokan gaba, suka ga alamar idan suka tsaya a filin daga, kila babu mai kai labari gida, to sai su ranta cikin na kare. A irin wannan yananyi, za a ga abokan gaba na ce wa juna, “In ba ka yi ba ni wuri.” Ya kamata kowace al’umma ta kasance kamar haka, wato mai ƙoƙarin ganin ta tarwatsa abokan gaba a wajen yaƙi ce. Ginshiƙi babba a sha’anin yaƙi.

A buɗewar labarin littafi na farko na Magana Jari Ce, an samu irin wannan ginshiƙi na yaƙi. Saboda shawarar da Aku ya ba Sarki Abdurrahman ta yadda za a tunkari mayaƙan Sarkin Sinari, mayaƙan Sarki Abdurrahman sun yi nasarar tarwatsa dakarun Sarkin Sinari. Wannan nasara ta samu ne saboda naƙaltar wannan ginshiƙi da dakarun Sarki Abdurrahman suka yi. Bayan da suka yi aiki da dabarar da aku ya ba su ta yaƙi, sai ga wani daga cikin ‘yan ƙwarban Sarki Abdurrahman ya zo da bushara, sai y ace:

“Shekaran jiya da hantsi muna nan mun yi kwanto inda ka ce mana, sai muka hangi ƙura ta toshe sama, sai tsinin mashi kawai kake gani suna wal wal wal. Ga masu dawaki da dakarai bilahaddin. Muka hanga har iyakar ganinmu, ba mu ga ƙarshensu ba. Muna nan dai sai da muka bari goshin yaƙi ya kawo dab da mu, sa’an nan muka yi ta sako musu kibau kamar ruwan sama. Na gaba suka juya da baya, suka gamu da waɗanda ke biye, abin ya cuɗe. Ga ‘yar hanya ƙarama. Dawaki suka yi ta zallo suna faɗa wa junansu. Mu ko dai sai zuba musu kibau muke. Na bisa na ta sulluɓowa ƙasa, dawaki na tattake su. Cikin na gaban nan sai ɗai-ɗai suka sami komawa ga wajen uwar yaƙi. Jim kaɗan sai kuma ga wasu suka taso wai za su yi mana sukuwar salla. Ba dama, don hanyar ta cika matsatsi tsakanin duwatsu. Muka yi musu yadda muka yi wa na farko. Aka yi ta aiko waɗansu muna yi musu haka nan, har la’asar. Da suka ga ba dama suka koma, suka bar gawawwakin ‘yan’uwansu nan abin sai wanda ya gani” (Imam, 1939:8).

Idan dakaru ko jarumai suak sami wannan yanayi da aka yi bayani a sama, musamman yayin da suka tsakiyar filin daga, sai murna. Nasara ta samu, domin sun tarwatsa abokan gaba. An nuna a cikin bayanin cewa, kwantan ɓaunar da dakarun Sarki Abdurrahman suka yi dakarun Sarkin Sinari ya sa mayaƙan Sarkin Sianari suka yi ta komawa baya, wasu suka faɗi matattu, wasu cikin miyagun raunuka, wasu kuma sun sami nasarar ranta cikin na kare. Irin wannan yanayi shi ma ginshiƙi ne mai matuƙar muhimmanci a sha’anin yaƙi. Idan dakaru suka san yadda za su yi wa abokan gaba ƙofar raggo, su rutsa da su, su kuma fatattake su, to sauran al’uumomin da ke son tsokanar su, za su shiga taitayinsu.

Kamar yadda ya faru ga dakarun Sarkin Sinari, haka lamarin ya kasance ga mutanen Suraida da suka kai yaƙi ga mutanen Niraini da ke cikin labarin, “In Ajali Ya Yi Kira, Ko Ba Ciwo A je.” Na cikin littafin Magana Jari Ce na farko. A cikin labarin an bayyana yadda mutanen Suraida suka ɗauki kashinsu da hannu daga mutanen da suka kai wa yaƙi wato mutanen ƙasar Niraini. Ga yadda fafatawar ta kasance:

Wata rana mutanen ƙasar Suraida suka kai yaƙi ƙasar Niraini. Mutanen Suraida suka kori na Niraini suka kashe musu jama’a mai yawa. Suna murna za su shiga garin, ashe sarkin Yaƙin Niraini ya shirya waɗansu dakarai, suka biyo jama’ar Suraida suka yi musu zobe, suka hana su gaba suka hana su baya. Da wani dakaren Suraida wai shi Barde, ya ga za a halaka su nan tsaye da yunwa ma kaɗai, sai ya ce wa ‘yan’uwa, “Ya kamata mu yi ƙunar Baƙin Wake, kada mu mutu nan mu bar wa na baya abin faɗi.” Suka tasar ma mutanen Niraini, Barde ya fara kai wa ya soki wani ɗan saurayi ya mace. Mutanen Niraini suka kashe yawancin mutanen Suraida aka kama barde, har an fara sassare shi za a kashe, Sarki ya ce a ƙyale shi (Imam, 1939: 57).

Idan aka bi wannan bayani na sama, za a ga cewa, mutanen Suraida da suka fara kai farmaki ga jama’ar ƙasar Niraini, su ne kuma suka ranta cikin na kare. An nuna yadda suka riƙa ganin kamar sun laƙume mutanen Niraini, amma da yake yaƙi ɗan yaudara ne, sai ga shi mutanen Niraini sun mai da biki, sun yi wa mutanen Suraida ɓarna mai yawa suka kashe wasu suka tarwatsa wasu, suka jinyata wasu. Ba kome ya sa haka ba, saboda sanin yadda yaƙi kan kasance tamkar hawainiya. Tarwatsa abokan gaba, babban ginshiƙi ne na yaƙi da aka amfana da shi wajen ba da labarin Magana Jari Ce.

Nasarar Yaƙi

 Samun sa’a ko samun biyan buƙata shi ne nasara. Cin galaba ma nsara ce (CNHN, 2006: 357). Nasarar yaƙi ke nan na nufin samun sa’ar yaƙi ko cin galaba a wajen yaƙi. Ginshiƙin yaƙi ne mai girma da ya fi kowane ginƙishi muhimmanci da ƙarfi. Hausawa kan ce, “Sa’a ta fi manyan kaya.” Sukan ce kuma, “Amfanin zunubi, romo.” Duk irin yadda aka sha wahala a fagen daga, idan dai har an yi nasara, to an sami galabar yaƙi ke nan. Wannan ginshiƙi ya yi tasiri a cikin littafin Magana Jari Ce na Abubakar Imam. A cikin buɗewar littafi na ɗaya na Magana Jari Ce an ga yadda aka fafata tsakanin dakarun Sarki Abdurrahman da na Sarkin Sinari, amma dai suk da cewa mutanen Sarki Abdurrahaman aka kawo wa hari, su ne kuma suka sami nasara a yaƙin. Ga albishir da wani ɗan ƙwarbai ya kawo wa Sarki Abdurrahman, yana gaya masa nasarar da aka samu:

Ana nan kamar kwana biyar, sai ga wani daga cikin ‘yan ƙwarbai da sarki ya aika, ya zo a sukwane da bushara, ya ce wa Sarki, “Allah Ya ba ka nasara, ai wannan dabara da ka yi ta fita...” (Imam, 1939: 8).

Muhimmancin da nasara ke da shi ga yaƙi ne ya sa, a cikin albishir wanda ɗan ƙwarbai ya yi wa Sarki. Kafin ya faɗa masa yadda aka yi nasara ta samu, da yadda aka yi gwagwarmayar samuwarta, sai da ya fara kwaɗaita wa Sarki cewa nasara gare su take. Daga nan sai ya zarce ga ba Sarki labarin yadda aka yi aka samu nasarar. Saboda muhimmancin nasara a wajen yaƙi ga kowane shugaba, ya sa a ƙasar Hausa ake yi wa sarakunansu inkiya da, “Allah Ba Ka Nasara.” Idan nasara ta yi wa basarake nisa, to, gaf yake da komawa bawa.

A cikin labarin, “In Ajali Ya Yi Kira, Ko Ba Ciwo A Je,” an nuna nasara ce ta fi komai muhimmanci a sha’anin yaƙi. Mutanen ƙasar Niraini ne suka kawo musu hari. Bayan sun yi wa mutanen Nirini ɓarna mai yawa sun kakkashe musu jama’a, suna ƙoƙarin su kutsa cikin gari, su kwashi ganima:

Ashe Sarkin Yaƙin Niraini ya shirya wasu dakarai, suka biyo jama’ar Suraida suka yi musu zobe, suka hana su gaba, suka hana su baya. Da wani dakaren Suraida wai shi Barde ya ga za a halaka su nan tsaye da yunwa ma kaɗai, sai ya ce wa ‘yan’uwansa, “Ya kamata mu yi ƙunar Baƙin Wake” (Imam, 1939: 57).

Bayan dakarun Niraini sun mai da martini a kan dakarun Suraida, sai suka yi nasara a kan mutanen Suraida da suka kawo musu hari. Ashe nasara ba gare su take ba, tana nan wurin mutanen Niraini. Daga baya mutanen Niraini suka sake shiri, suka far musu, kuma suka sami galaba a kansu.

Ɓoye Sirrin Fasahar Yaƙi

Kalmar “Asiri” ce ake kan sauya riga ta koma kalmar “Sirri” saboda wata ƙa’ida ta nahawun harshen Hausa). Yayin da “Fasaha ke nufin, “Gwaninta ko ƙwarewa” (CNHN, 2006: 136). Idan aka yi maganar ɓoye sirrin fasahar yaƙi, ana nufin sakaya ƙwarewa da tanaje-tanajen da aka yi domin tunkarar abokan gaba. Wannan hali, wani ginshiƙi ne mai matuƙar muhimmanci ga harkar yaƙi. An yi amafani da wannan ginshiƙi aka bayar da labarin da ke cikin buɗewar littafin Magana Jari Ce littafi na farko. Lokacin da labari ya zo wa Sarki Abdurrahman cewa ga dakarun Sarkin Sinari can za su far wa mutanensa, sai aku ya ba shi shawara a kan dabarar da ya kamata ya yi don ya ci galaba a kansu:

Aku ya ce, “Yanzu Sarkin Sinari ya kusa kawowa kadarkon Kimba, nufinsa ya biyo ta tsakanin dutsen Kimba da Ubandawaki ya kewayo ta Gabas ya faɗa wa birni ta inda ba a tsammaninsa. Sarki ya ce, “Cikin ‘yan gari ma akwai wani mahalukin da ya san wannan wuri balle Sarkin Sinari? Aku ya ce, “Kai dai ka ji abin da zan gaya maka. Yanzu maza ka koma gida ka aika da ‘yan ƙwarbai su tsare makurɗin nan da ke tsakanin dutsen Kimba da Ubandawaki kome yawan rundunarsa, ko mutum goma masu ƙarfin zuciya sa iya mai da shi baya a wannan wuri, kafin ya kewayo ma ka shirya uwar yaƙi” (Imam, 1939).

Wannan shawara da aku ya ba Sarki, asirce aka bayar da ita ba tare da sanin kowa ba, hatta wazirinsa ma bai sani ba, Sarki bai kuma faɗa masa ba, saboda an ɓoye waɗannan bayanai masu muhimmanci. Sarki yana gani cewa bai kamata ya faɗa wa kowa wannan sirri ba. Ya bar wa kansa sani. Daga shi sai ɗansa Musa da ya tabbatar ba zai faɗa wa kowa ba. Da Waziri ya ji wannan sirri, da ya yi amfani da damar, ya ɓata shirin. Hujjar da ya sa aka ce Waziri bai san da wannan sirri ba, ita ce, yadda aka nuna ya ta da Barakai takanas-ta-kano ya ce zai yi masa kyauta mai tsoka ya kuma ‘yanta shi idan ya tafi ya shaida wa sarkin Sinari a kan ya zo ya yaƙi Sarki Adurrahman. Da Barakai aka tafo domin a murƙushe sarki Abdurrahaman. Da suka ƙare ƙulle-ƙullensu, sai ba su sami nasara ba, Kwatsam!

Sai ga Barakai ya komo domin ya gaya wa waziri abin da ya faru, ya ce, “Mu ke kan gaba, sai kawai muka ga ana ta zubo mana kibau, har aka sami dokina ban sani, sai na ga kawai mun zube. Ni kuwa da na ga haka sai na kwanta ƙarƙashinsa kamar na mutu. Na yini nan ba motsi. Ana ta yaƙi bisa kaina. Da dare ya yi tsaka, na ji sun yi shiru, sai na sulale na dawo. Waziri ya yi masa barka, ya ce, “In ji ba a gane kai ne ba?” Barakai ya ce, “Na tabbata ba wanda ya gane ni.” Waziri ya ce to madalla, amma ina mamakin yadda Sarki ya gane ta nan za su ɓullo. Barakai ya ce, “Ni ma haka nan, bakina dai ban yi da kowa ba.” Waziri ya ce, “Lalle mutanen Sinari akwai munafukai, amma ba kome gobe ma rana ce.” (Imam, 1939: 9)

A cikin wannan bayani na sama, an ji inda waziri da Barakai suke tattaunawa suna mamakin yadda aka yi Sarki Abdurrahman ya gane ta inda Sarkin Sinari zai biyo, a zargin da suke yi wasu mutanen garin Sinari ne suka yi fitar ƙafa suka lallaɓo suka zo suka sanar da Sarki Abdurrahman. Ke nan waziri bai san cewa aku ne ya yi duba irin tasu ta tsuntsaye ya gano wannan sirri ba. Da aku ya faɗa wa sarki Abdurrahman, sai ya bar wa kansa sani bai sanar da Wazirinsa ba. Ɓoye sirrin dabarun yaƙi yana da matuƙar muhimmanci kuma ginshiƙin yaƙi ne mai muhimmanci.

Bin Umurnin Jagoran Yaƙi

Shugaba ko jami’i ko madugu shi ne jagora (CNHN, 2006:211). Jagoran yaƙi na nufin madugun yaƙi ke nan. Shi ne shugaban rundunar yaƙi. Shi ke ba sauran dakaru unurni da doka. Ya zama wajibi ga dakaru su bi umurnin madugun yaƙi ko suna so ko ba su so. Dalili kuwa shi ne, shi ke da ilmin dabarun yaƙi. Hausawa na cewa, “Yaƙi ɗan zamba ne.” Yadda dakaru suke ganin wasu lamurra za su kasance ko su tafi daidai, ba shi madugun yaƙi ke duba ba. Shi ya sa a tsarin dokokin yaƙi, ba a yi wa madugu ko jagoran yaƙi gardama. Duk inda aka taras an faye samun rashin nasara a wajen yaƙi, babu jituwa tsakanin jagora ko madugun yaƙi da dakarunsa. Wannan rashin jituwa ne ke jawo dakaru su riƙa yi wa Madugu gardama.

Bin umurnin jagoran yaƙi wani ginshiƙi ne babba da ke tallafe da harkokin yaƙi. An yi amfani da wannan ginshiƙi a cikin littafin Magana Jari Ce, inda aka fito da dakarun da sarki Adurrahman ya sa su tsare tsakanin dutsen Kimba da na Ubandawaki da ake tsammani Sarkin Sinari zai biyo. A nan Sarki Abdurrahman ne ya kasance jagoran yaƙi saboda shi ya tura su ya kuma faɗa musu ga inda kowanensu zai tsaya:

...Suka koma gida, ya zaɓi ‘yan ƙwarbai guda ɗari ya aika da su inda aku ya misalta masa, ya kuma ta da manzanni ya aika da su Kudu da Arewa, Gabas da Yamma a gaya wa mutane su yiwo harama, su zo maza da shirin yaƙi. Maƙera kuma su shiga gyara makamai (Imam, 1939: 8).

Da ‘yan ƙwarban nan da Sarki Abdurrahaman ya wakilta su tsaya bakin rai bakin fama, ba su bi umurnnin Sarki ba, da ba a sami nasarar da aka samu ba ta mai da rundunar Sarkin Sinari baya. Kasancewar dakarun sun bi umurnin Sarki da sarkin Yaƙi wanda shi ne jagoransu. Kuma shi ya tsara komai, shi ya sa aka yi nasarar fatattakar dakarun Sarkin Sinari.

Ƙwarewa Wajen Rarraba Wa Dakaru Matsayi a Filin Daga

Gwaninta ko iya wani abu sosai ita ce ƙwarewa (CNHN, 2006: 292). Kalmar “Raba” na nufin kasa abu gida-gida ko datsa abu gida biyu ko fiye (CNHN, 2006: 362). Ƙwarewa wajen rarraba dakaru a fagen daga, na nufin gwaninta wajen ba dakaru matsayin ko rawar da za su taka a filin daga da nufin a samu nasara ta yaƙi. Kowane madugun yaƙi da aka zaɓa, musamman sarautun yaƙi waɗanda masarautun ƙasar Hausa kan yi wa wasu mutane saboda cancantarsu, misali, Sarkin Yaƙi da Ga Yaƙi da Mai Yaƙi da sauransu. Ƙwarewa a kan yadda ake rarraba dakaru na yaƙi ake dubawa a bayar da ire-iren waɗannan sarautu, ba wani abu daban ba. Idan madugun yaƙi ya ƙware wajen raba wa dakaru ayyuka ko matsayi ko rawar da kowanensu zai taka a fagen daga, to nasara za ta samu ba tare da wata wahala ba. Idan madugu ya kasa samun irin wannan ƙwarewa, tabbas, za a yi ta cin galabar mutanensa. Ke nan ƙwarewa wajen rarraba dakarun yaƙi a filin daga wani ginshiƙi ne na yaƙi.

A cikin buɗewar littafin Magana Jari Ce, an nuna yadda aku ya ba Sarki Abdurrahaman shwarar yadda za a rarraba ‘yan ƙwarbai (Dakarun yaƙi) a tsakanin dutsen Kimba da Ubandawaki. Aku ya kuma fasalta wa Sarki yadda za a ajiye dakarun da abin da ya kamata su yi, da dama lokacin da za su faɗa wa abokan gabarsu wato mayaƙan Sarkin Sinari:

Ka koma gida ka aika da ‘yan ƙwarbai su tsare makurɗin nan da ke tsakanin dutsen Kimba da Ubandawaki. Kome yawan rundunarsa, ko mutum goma masu ƙarfin zuciya sa iya mai da shi baya a wannan wuri kafin ya kewayo ma ka shirya uwar yaƙi (Imam, 1939: 8).

Wannan shawara ta aku, ta nuna yawan ‘yan ƙwarban da za a aika da su. A cikin bayanin nansa ya auna wurin da za a kai dakarun ne kafin ya ba da lissafin dakarun da za a kai. Bayan haka, aku ya sake auna matsatsin da ke tsakanin dutsen Kimba da Ubandawaki da kuma yawan tawagar Sarkin Sinari idan aka ce ta tsakanin duwatsun nan za su biyo. Haka kuma ya sake auna tazarar da ke akwai idan Sarkin Sinari ya koma baya da nufin ya kewayo ya shigo ta ƙofar gari. Matsalolin da Sarkin Sinari zai fuskanta a wannan wuri su ne aku ya yi amfani da su ya yi hasashen nasarar da sarki Abdurrahman zai samu a kan Sarkin Sirika. Kwarewa ga aikinsa ya sa duk shawarawarin da ya bayar, sun yi amfani domin an samu nasara.

Irin wannan ƙwarewa ce Sarkin yaƙin Niraini yake da ita, shi ya sa da tawagar Sarkin Suraida ta far jama’arsa ba zato ba tsammani, ya yi maganinsu. Ga yadda suka yi:

Wata shekara mutanen ƙasar Suraida suka kai yaƙi ƙasar Niraini. Mutanen Suraida suka kori na Niraini suka kasha musu jama’a mai yawa. Suna murna za su shiga garin, ashe sarkin Yaƙin Niraini ya shirya waɗansu dakarai, suka biyo jama’ar Sarkin Suraida suka yi musu zobe, suka hana su gaba, suka hana su baya. (Imam, 1939:57)

Duk wanda ya karanta farkon bayanin nan na sama, zai fahimci ƙwarewar da Sarkin Yaƙin Niraini yake da ita. Ƙwarewarsa ce ta sa yake da ƙarfin zuciya da sanin makamar yaƙi. Ya fahimci cewa don sun kashe mutanen Niraini da yawa har sun tunkari shiga garin domin su sami ganima, ba shi ne ke nufin sun ci galaba a kansu ba. A maimakon haka, sai Sarkin Yaƙi ya sake dabara, inda ya haɗa wata uwar yaƙi ta gaugawa ya kuma ba da umarnin a yi wa dakarun Suraida zobe. Haƙarsa ta cim ma ruwa domin kuwa, sun ci galaba a kan mayaƙan Suraida har suka kama Barde.

 Zaman Lafiya a Cikin Littafin Magana Jari Ce

Marubucin littafin Magana Jari Ce, wato Abubakar Imam, ya yi amfani da tubalin Zaman Lafiya wajen gina labaran da ke cikin littafin nasa. Masana ilmin Fagen Zaman Lafaiya, sun tabbatar da cewa, zaman lafiya tumbin giwa ne. Abubuwan da ke ƙunshe a cikinsa suna da yawa. Kafin zaman lafiya a ɗore a cikin al’umma, dole sai an sami amana da aminci da lumana da natsuwa da tausayi da adalci da ƙauna da soyayya da zumunci da kuma auratayya (Francis, 2006; Bachaka da Aliyu, 2013). Bari a bi waɗannan kayan cikin Zaman Lafiya ɗaya bayan ɗaya domin a ga yadda mawallafin littafin Magana Jari Ce ya warware su a cikin labaransa.

Amana

Idan aka ce, “Amana,” ana nufin ba mutum ajiyar kaya ko wani abu yadda zai adana shi kamar nasa ba tare da wani abu ya salwanta, ko wani abu ya same shi ba. Amana wani lokaci na nufin yarda (CNHN, 2006:15). Ba dole sai wani abu ake ba mutum amanar sa ba, akan ba da har amanar abin da ba a iya gani balle a taɓa da hannu, kamar magana ko soyayya. Babu yadda za a yi zaman lafiya ya samu a cikin al’umma idan har babu yarda da amana tsakanin mutane. Duk al’ummar da ta kasance ba ta da amana, to za ta rasa zaman lafiya. Da wuya a ba wani amanar wani abu ya ci amana, kuma wanda ya ba shi amanar ya ƙyale shi, ba tare da ya bi haƙƙinsa ko da ta hanyar kai wa ƙara ga hukuma ba. Idan lamari ya kai ga alƙali, to an sami rikici ke nan. Rikici kuma shi ne kishiyar zaman lafiya.

A cikin littafin Magana Jari Ce, an yi amfani da amana wajen warwarar wasu labaran. Misali, a labarin, “Girman Kai Rawanin Tsiya” da ke cikin littafi na biyu na Magana Jari Ce. A cikin labarin an kawo yadda M. Sidi Ibrahim, mahaifin Wowo, ya tattara dukiyarsa ya zuba cikin akwatin ƙarfe ya binne a rami. Ya kira wani amintaccen almajirinsa wai shi Ɗan’inna, ya nuna masa wurin, ya ce masa:

“Ga amanar Allah da ma’aiki nan na ba ka. Domin ka san rai kwakwai, mutuwa kwakwai. In Allah Ya sa na riga ka mutuwa, ina son ka ba Wowo su, amma kada ka gaya wa kowa wannan al’amri. Ko shi yaron kuwa ma kada ka nuna masa ko alamar akwai waɗannan, sai ka ga ya shiryu (Imam, 1940: 25)

Zaman lafiya da amincewa da juna ya sa Malam Sidi Ibrahim ya danƙa wa Malam Ɗan’inna dukiyarsa. Malam Sidi ya gargaɗe shi kada ya nuna wa kowa har da Wowo, sai ya natsu. Da babu zaman lafiya tsakanin Malam Sidi da Malam Ɗan’inna, da wuya amana mai ƙarfi haka ta shiga tsakaninsu. Ke nan amana ma ginshiƙi ne babba na zaman lafiya.

Aminci

Aminci na nufin abota ko yarda (CNHN, 2006: 16). Idan akwai aminci tsakanin mutane guda biyu, sai a ce aminan juna ne. Idan aka ce aminan juna ne, to tabbas akwai yarda sosai a tsakaninsu. Irin wannan yarda ce Bahaushe kan ce, “Fara ɗaya suke rabawa.” Duk inda aka ji maganar aminci a cikin al’umma, to, tabbas zaman lafiya ya wuri ya zauna. An yi amfani da tubalin aminci a cikin Magana Jari Ce. A cikin labarin, “In Maye Na da Hankali, Ba Ya Fid da Maitarsa a Fili” da ke cikin littafi na farko. A cikin labarin, an nuna cewe domin tsananin amincin da ke tsakanin manyan taurarin labarin wato Jatau da Ɗansanda ya sanya da Jatau ya tsinci dame a kala, bai tasar wa ko’ina ba, sai gidan amininsa Ɗansanda:

Yana cikin tafiya har ya isa daji. Can ya miƙa cikin daji, sai ya ga akwati a wani kogon itace, ya jawo shi ya buɗa, sai ga kuɗi cunkus, ɓarayi sun sato sun ɓoye. Ya tsaya ya yi godiya ga Allah, ya ɗauka ya rufe da ‘yan ƙirare, ya komo gida. Da isarsa gari sai ya tasam ma gidan abokinsa Ɗansanda, ya iske har ya komo, ya ba shi ajiyar kayan, saboda shi gidansa babu wurin ajiya (Imam, 1940: 175).

Ga alama, Ɗansanda kuɗi ne ya tsinta wuri na gugar wuri. An kuma san yadda kuɗi suke a zuciyar bawa, idan ya same su, ɓoyon su yake yi. Shi ma Jatau, ga yadda bayanin nan na sama ya nuna, sai da ya sa ƙirare da ciyawa ya ɓoye akwatin kuɗin nan, yana tsoron kada wani ya gani. Da yake akwai abota tsakaninsa da Ɗansanda, Jatau ko gidansa bai nufa da waɗannan kuɗi ba, sai ya nufi gidan abokinsa Ɗansanda ya ba shi ajiya. Amincin da ke tsakanin Jatau da Ɗansanda ne ya sa Jatau ya ba shi ajiyar kuɗi. Aminci kuma yana ƙara samar da zaman lafiya da lumana a tsakanin mutane.

Lumana

Lumana na nufin zaman lafiya da aminci (CNHN, 2006: 309). Ke nan, wasu kalmomi da ake ƙara bayyana zaman lafiya da su, su ne lumana da aminci. Zaman lumana ma hoto ne na ɗararren zaman lafiya a cikin al’umma. A cikin zaman lumana, za a samu cewa al’ummar da ke da yawan jama’a masu addinai da ƙabilu da tsarin al’adu mabambanta, suna zaune lafiya, ba tare da tsangwama ko ƙyama tsakaninsu ba. Suna gabatar da komai tare ta hanyar ganin mutunci da daraja da martabar juna. Da an sami al’umma cikin irin wannan yanayi, sai a ce suna zaman lumana. An yi amfani da wannan turke a cikin littafin Magana Jari Ce. A labarin, “Kama da Wane Ba Wane Ba Ne” da ke cikin littafin Magana Jari Ce na uku. A cikin labarin, an nuna irin yadda talakawan ƙasar Nisau suke zaune lafiya tsakaninsu da yadda suke son sarkinsu saboda halaye na gari da yake da su. Ga yadda aka tsara shi a cikin labarin:

A ƙasar Nisau an yi wani babban Sarki wanda ake kira Nasiru. Mutanen ƙasar ba wanda suke so da gani kamar sarkin nan nasu. Ga shi dai da kyau, ga fuska, ga haƙuri sai ka ce kasa. Wajen wayo da hankali kuma kamar a ce ya fi kowa. In ko fagen fama aka fita, ko Ɗanwaire ya san da shi (Imam, 1940: 132).

Da jin yadda Sarkin Nisau wato Nasiru da talakawansa suke zaune da juna, abin akwai burgewa. Irin wannan zama ne da ke cike da gamsuwa da yadda ake tafiyar da zamantakewar rayuwa, ake kira zaman lumana. Da aka ce Sarki Nasiru yana da fuska, ana nufin yana da fara’a da haba-haba da talakawansa. An yabe shi da haƙuri, wato yana da juriyar halayen da ba ya so da talakawa ke aikatawa. Ire-iren waɗannan halaye na sarki Nasiru, su ne kan sa zaman lumana, kuma suna ƙara inganta zaman lafiya a cikin al’umma.

Natsuwa

An bayyana, “Natsuwa” da tara hankali wuri guda (CNHN, 2006: 459). Idan aka tara hankali wuri guda a kan wani abu, tabbas za a nazarci yadda yake sosai. Idan kuma aka nazarce shi aka gane yadda yake, to za a saba da shi, a kuma iya sakankancewa da shi. Al’ummar da ta sakankance da mutanenta, tabbas ta sami natsuwa da su ke nan. Samun natsuwa ta fuskar sakankancewa kuma zaman lafiya ne. An amfana da natsuwa wajen gina wasu labaran Magana Jari Ce. Misali, a labarin, “Yaro Ɓata Hankalin Dare Ka Yi Suna” da ke cikin littafi na uku na Magana Jari Ce. Abin da ya faru a labarin shi ne, an mutu an bar wa wasu yara maza gadon raƙuma goma sha bakwai. Kafin mahaifin nasu ya rasu, ya faɗa musu darjar rabon da kowanensu zai samu daga raƙuman nan, abin da kawai ya rage a sami malami ko alƙalin da zai aiwatar da rabon gadon. Ga yadda mahaifin nasu ya fasalta yadda yake so a raba wa yaransa raƙuma:

“Niyyata in sun yi yawa in ba babban ɗana nusufi, mai bi masa sulusi, ɗan autan nan nawa kuwa tusu’insu. To ga shi ba su yi yawa ba, amma duk da haka, sai su raba abin da aka samu haka nan. Kada ko wani malami ya ce zai sake mini abin nan da na yi niyyar yi, ya ce ba halas ba ne, ni na san abin da na yi nufi a raina.” (Imam, 1940:80)

Raƙumi sha bakwai ne bawan Allan nan ya yi wasicin yadda za a raba su ga yaransa uku haka. Idan aka tsaya tsaf aka dubi yawan raƙuman, da yawan yaran, da abin da mahaifin ya bari wasici a ba kowanensu, tabbas, ba su rabuwa daidai yadda yake so. In kuwa za a raba su bisa ƙa’idar da ya faɗa, sai an yanka raƙumi guda, shi kuma bai faɗi haka ba. A wannan gaɓa, natsuwa da tara hankali wuri guda kaɗai ne za su sa a yi rabon gadon nan daidai yadda mai mutuwa ke buƙatar sa. Haka kuma idan babu natsuwa da zaman lafiya, da wuya hankali ya tattara ga wannan rabon gado, hasali ma, wani na iya samun dama ya cinye wa yaran nan gadonsu, daga ƙarshe a yi ta rikici.

Tausayi

Sai da zaman lafiya, san nan har za a ji tausayin juna. Shi tausayi jin ƙai ko nuna damuwa kan abin da ya sami wani na rashin jin daɗi ne (CNHN, 2006: 434). Ana buƙatar mai ƙarfi ya ji tausayin marar ƙarfi. Ana son mawadaci ya ji tausayin matalauci. Abu ne mai kyawu, matashi ya ji tausayin tsoho, ko babba ya ji tausayin yaro, ko namiji ya tausaya wa mace, malami ya ji tausayin ɗalibi. Kai! Duk dai wanda Allah Ya ɗora shi a kan wasu mutane da yake sama da su, to kada ya zalunce su, ya dai ji tausayinsu. Idan wannan tsari ya tabbata a cikin al’umma, tabbas zaman lafiya mai ɗorewa zai samu. Mawallafin Magana Jari Ce ya ci moriyar wannan tubali lokacin da yake warawarar labaran littafin. A labarin, “Hassada Ga Mai Rabo Taki” na cikin littafi na uku, an gina shi da tubalin tausayi, inda bayan ‘yan doka sun jefa Bawan Kare cikin ƙaton rami, sai karensa ya riƙa shiga kasuwa yana sato masa ruwa da abinci.

Da ya ga rana ta yi, sai ya sato waina ya rugo, aka biyo shi ya tsere. Da ya zo bakin ramin, sai ya yi haushi, da ya ji na fara ba shi haƙuri, ya ji muryata, sai ya sako mini wainan nan. Na ji wani abu tif ya faɗi, na lalaba, sai na ji waina ce na ɗauka na ci. Tausayinsa kuma ya sake kama ni (Imam, 1940: 171)

Tausayi yakan shiga tsakanin dabba da mutum. Dubi yadda karen nan ke tausayin ubangidansa wato Bawan Kare. Ya tafi kasuwa ya sato masa waina, ya zo har bakin ramin da ya ga an jefa shi, ya jefa. Karen nan yana tausayin Bawan Kare a kan yunwa da ƙishirwa da ya san za su gallabe shi. Haka kuma, shi ma a ɓangaren Bawan Kare yana jin tausayin karensa, ganin ya rasa mai kula da shi, ga shi kuma yana ta ɗawainiyar kula da shi. Zaman lafiyar da ke tsakaninsu ne ya sa suke tausayin juna.

Adalci

Tausayawa ko yin hukunci bisa gaskiya shi ne adalci. Rangwantawa ma adalci ne (CNHN, 2006: 2). Babu abin da ke saurin haɓaka zaman lafiya a cikin al’umma kamar yin hukunci da adalci. Idan wani ya karya doka, dole ne doka ta hukunta shi, ko wane ne ko ɗan wa. Idan hukunci ya kasance babu adalci, talaka kawai ake hukuntawa, to, al’umma za ta shiga cikin halin yaƙi. Idan shugaba ya zama mai adalci ne, mabiyansa za su ƙaunace shi. Haka nan, idan ana yi wa kowa hukunci daidai laifinsa, al’umma za ta rayu cikin lumana da yarda da juna, babu jin haushin juna, babu ƙyashi. Adalci wani furen kallo ne a cikin labaran littafin Magana Jari Ce. Da wannan fure ne aka ƙawata labarin, “Ɗan Hakin da Ka Raina Shi Ke Tsone Ma Ido” da ke cikin Magana Jari Ce littafi na uku. Shari’ar da Sarki ya yi wa Anunu da Bamaguje da Sarkin Fawa, cike take da adalci.

Anunu ya haɗa kai da Sarkin Fawa suka cuci wani Bamaguje. Sun sayi sansa ɗauke da kayan hatsi arha tuɓus, ba ma tare da yardarsa ba. Da Allah Ya ara masa rana, shi ma sai ya sayi kan Anunu ya kuma sa wuƙa ya fara yanka. Anunu ya ƙetare rijiya da baya-baya. Magana ta girma, sai gidan Sarki. Bayan da Sarki ya sa kowa ya mai da zance, sai:

Sarki ya ɓingire da dariya ya ce, “A gaishe ka namiji!” Ya dubi Sarkin Fawa ya ce, “Tun da yake kai ka yi waccan shari’ar ta farko, yanzu sai ka je ka kawo fam goma sha biyu a ba Bamaguje. Anunu kuwa da yake koyaushe kuna tare, ka bi shi bashi. In ko ba ku yarda ba Bamaguje ya yanke kansa.” (Imam, 1940:51)

Wannan hukunci da sarki ya yanke cike yake da adalci. Bamaguje ba Bahaushe ba ne. Anunu da Sarkin Fawa da Sarki duk Hausawa ne. Idan wani Sarki marar adalci ne, zai goyi bayan Hausawa ‘yan’uwansa. Da yake Sarkin adali ne sai ya yi shari’ar bisa gaskiya da adalci. Wannan adalci da ya yi, shi ya sa mutanen gari suka ga girman Sarki, suka yi ta yi wa Anunu dariya. Daga nan sai mutane suka shiga taitayinsu game da yin zalunci, kowa ya guji zaluntar wani, saboda ya san Sarki zai yi masa hukunci. Wannan ya sa suka zauna lafiya.

Ƙauna

Ƙauna ɗorarren zaman lafiya ne tsakanin mutum biyu masu ƙaunar juna. An bayyana ƙauna da son wani abu (CNHN, 2006: 279). Ƙauna tsananin yarda da amincewa da soyayya ke kawo ta. Duka waɗannan kalmomi da aka ambaci ƙauna da su, babu wadda za ta samu idan babu zaman lafiya. Ƙauna na iya shiga tsakanin mutane ko da ba kishiyar jinsi ba. Ke nan aboki na iya ƙaunar abokinsa, ƙawa ta ƙaunaci ƙawarta, iyaye su ƙaunaci ‘ya’yansu, miji ya ƙaunaci matarsa, bara ya ƙaunaci ubangidansa, Shugaba ya ƙaunaci mabiyansa da dai sauransu. Ƙauna taɓarya ce da ake luguden zaman lafiya da ita a cikin rubutattun labaran Hausa. An yi amfani da ita aka nannagi wasu labaran da ke cikin littafin Magana Jari Ce. Misali, a labarin, “Amjadu da Asadu” na cikin littafin Magana Jari Ce na farko.

A cikin labarin, an nuna cewa Amjadu da Asadu mahaifinsu ɗaya, amma kowa da mahaifiyarsa. Suna ƙaunar juna sosai. Ko da Sarki wato mahaifinsu ya yi tafiya, sai makullan (Ƙawararai) na Sarki suka so su shiga tsakaninsu. Yaran suka gane makaircinsu suka ƙi yarda. Da suka ga ba su ci galaba ba, sai suka bari sai da Sarki ya dawo, suka tafi suka yi musu shaida. Sarki ya sa Hauni ya tafi da su daji ya ce ya sare su, ya kashe su kowa ya huta. Akwai ƙauna ƙwarai tsakanin yaran nan, saboda haka sai:

Hauni ya ce, “To ku raba, wa zan fara kansa?” Amjadu ya ce, “Sai ka fara kaina, ba ni ne babba ba?” Asadu ya ce, “A’a in an fara kanka, wata ƙila in ji tsoro in motsa in ta kawo kaina. A dai fara kaina don kada in yi fargaba.” Amjadu ya ce, “Ba na iya ganin an sare ka, tun kafin a zo gare ni ma baƙin ciki ya kashe ni” (Imam, 1940: 152)

Irin wannan ƙauna da Amjadu da Asadu suka nuna wa juna, ita ce wadda ke tsakanin ɗan’uwa da ɗan’uwansa. An ga yadda su Amjadu da Asadu kowa ke begen ɗan’uwansa yana son sa, har ya zaɓi ran ɗan’uwansa fiye da nasa. Ba komai ke sa haka ba, sai wanzajjen zaman lafiya. Babu yadda za a yi a sami zaman lafiya, sai da ƙaunar juna.

Soyayya

Soyayya ta ɗan sha bamban da ƙauna. Ita soyayya nuna ƙauna ce daga ɓangarori biyu masu ƙaunar juna musamman mace da namiji (CNHN, 2006:398). Daga cikin alamun zaman lafiya da juna su ne a sami soyayya tana ratsawa tsakanin samari da ‘yanmata ko Bazawari da Bazawara. Ita soyayya kamar yadda aka ambata, ta fi fito da ƙaunar da ke akwai tsakanin namiji da mace. An ari soyayya an yafa wa wasu labaran da ke cikin littafin Magana Jari Ce na biyu, a labarin, “Ƙamaruzzaman Ɗan Sarki Shahruzzaman,” an nuna tsantsar soyayya tsakanin Ƙamaruzzaman da Badura ‘yar Sarkin Ƙasar Sin.

A labarin an nuna cewa aljannu ne suka sato Badura da Ƙamaruzzaman lokacin da kowanensu ke barci. Sun haka don su raba gardamar da aljannun suke yi a kan wanda ya fi kyau tsakanin Badura da Ƙamaruzzaman. Za a iya gane matsayin soyayyar da suke yi da juna bayan an ji kalaman da kowanensu ya furta a kan ɗan’uwansa. Da suka ta da Ƙamaruzzaman daga barci, ya ga Badura kusa da shi tana ta sharar barci, sai kawai ya ce:

“Da wannan za a aura mini da na yarda.” Ya yi kamar ya tashe ta da ita, ya ji tsoron ko a kawo ta ne don ta ɗauke hankalinsa, saboda haka ya kanne, ya haɗe begensa. (Imam, 1940:141).

Wannan shi ne kalmomin soyayyar da Ƙamaruzzaman ya furta ga Badura bayan an ta da shi daga barci ya gan ta. Daga ɓangaren Badura ma, da aljannu suka ta da ita suka sa Ƙamaruzzaman ya yi barci, ita kuma sai cewa ta yi:

 “A’a’a’a! In dai wannan Baba yake so ya aurar da ni ga shi, na yarda. Ta fa kafa masa ido ba ta ko ƙiftawa, sai ta zare zoben hannunta ta sa masa, ta zare nasa ta sa hannunta” (Imam, 1940:141).

Waɗannan kalamai na soyayya da masoyan suka furta wa junansu, sun nuna cewa akwai soyayya mai danƙo tsakaninsu. Babu yadda za a yi a sami soyayya ba tare da samun zaman lafiya ba. soyayyar ma ai wani ginshiƙi ne na zaman lafiya.

Sakamakon Bicike

Wannan maƙala ta gano cewa, yaƙi da zaman lafiya wasu sinadarai ne da marubuta labaran Hausa kan sarrafa wajen rubuta labaran da ke cikin littattafansu. Mawallafin littafin Magana Jari Ce, kamar sauran marubuta labaran Hausa, ba a bar shi a baya ba wajen cin gajiyar yaƙe-yaƙe da zaman lafiya a cikin littafin na Magana Jari Ce. Za a iya naƙaltar makamar yaƙi da abubuwan da ke kawo zaman lafiya a cikin al’umma, musamman idan aka karanta labaran cikin Magana Jari Ce. Idan zaman lafiya ya yi ƙaranci a cikin al’umma, ana iya karanta labaran cikin Magana Jari Ce domin a farfaɗo musu da shi, domin akwai hanyoyin tattalin zaman lafiya sosai a cikin Magana Jari Ce.

Kammalawa

Wannan maƙala ta yi tsokaci ne a kan yaƙe-yaƙe da ginshiƙansu tare da zaman lafiya da rassansa a cikin littafin Magana Jari Ce. An buɗe maƙalar da jawabin gabatarwa inda aka kawo ma’anonin kalmomin da suka gina taken maƙalar. An kawo taƙaitaccen tarihin rayuwar Alahaji Abubakar Imam, wato mawallafin littafin Magana Jari Ce. Daga nan, sai aka tafi kai tsaye wajen bayanin yadda aka yi littafin Magana Jari Ce ya samu. Bayan an gama wannan bayani, sai kawai aka shiga cikin littafin Magana Jari Ce, aka yi sharhin labaran da suke ɗauke da sinadarin yaƙi da zaman lafiya. An riƙa tsakuro wuraren da yaƙi da zaman lafiya suka ɓulla daga matanonin labaran. Sakamakon maƙalar ya biyo baya, kafin a yi jawabin kammalawa da kuma manazarta, wato wuraren da aka samo muhimman bayanan da aka amfana da su wajen gina maƙalar.

Manazarta

Atuwo, A. A. (2009). Ta’addanci A Idon Bahaushe: Yaɗuwarsa Da Tasirinsa A wasu Ƙagaggun Rubutattun Labarun Hausa. Kundin Digiri Na Uku. Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya. Sakkwato: Jami’ar Usmanu Danfodiyo.

Bunza, A. M. (2021). “Cecekucen Taɓarɓarewar Tsaro a Nijeriya Ta Arewa: (Da Gara Jiya da Ya, Gara a Gyara Yau Don Gobe). Maƙalar da Aka Gabatar a Taron Gasar Ƙasa da Ƙasa ta Rubutattun Waƙoƙin Hausa Mai Take, “Tsaro a Nijeriya ta Arewa” Wadda Hukumar jami’ar Usmanu Danfodiyo Sakkwato ta Tsara. Ranar 15/07/2021. A Babban Ɗakin Taro na Jami’ar, da ƙarfe 11 na safe.

C.N.H.N, (2006). Ƙamusun Hausa na Jami’ar Beyero. Zaria: Ahmadu Bello University Press.

Clausewitch, C. V. (1968). On War. Vol. II. London: Rutledge and Keegan Poul.

Fika, A. M. (1978). The Kano Ciɓil War and British Overrule (1982-1940). London: Oxford University Press.

Fuller, J. F. C. (1970). The Conduct of War (1789-1961). London: Routledge.

Guga, S. B. (2010). Yanayin Sarauta a Cikin Magana Jari Ce. Kundin Digiri na Farko. Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya da Afirika. Zaria: Jami’ar Ahmadu Bello.

Hassan, S. (2013). Nazari Kan Mutuntaka da Adabi: Tasirin Abubakar Imam a Cikin Magana Jari Ce. Kundin Digiri na Uku. Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya da Afirika. Zaria: Jami’ar Ahmadu Bello.

Ibrahim, I.S. (1990). Morality in Imam’s Magana Jari Ce. Maƙalar da Aka Gabatar a taron Ƙara Wa Juna Sani, Wanda Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya da Afirika ya Shirya. Zaria: Jami’ar Ahamdu Bello.

Imam, A. (1939). Magana Jari Ce Littafi na Farko. Zaria: Northern Nigeria Publishing Company.

Imam, A. (1940). Magana Jari Ce Littafi na Biyu. Zaria: Northern Nigeria Publishing Company.

Imam, A. (1940). Magana Jari Ce Littafi na Uku. Zaria: Northern Nigeria Publishing Company.

Jibrin, H. (2016). Demobilisation Policies and Challenges Faced by Nigerian Army, 1970-1983. Ph.D Thesis, Submitted to the Department of History. Sokoto: Usmanu Danfodiyo University.

Maiyama, U. H. (2013). Jigon Sata a Wasu Littattafan Hukumar NORLA. Kundin Digiri na Uku. Sashen Koyar da Harsuanan Nijeriya. Sakkwato: Jami’ar Usmanu Danfodiyo.

Malumfashi, I. A. M. (2018 Ed.). Labarin Hausa a Rubuce (1927-2018). Zaria: University Press and Publishers.

Malumfashi, I. M. (2009). Adabin Abubakar Imam. Sokoto: Garkuwa Media Services.

Mora, A. (1989). Abubakar Imam’s Memoirs. Zaria: Gaskiya Cooporation Limited.

Muri, A. M. (3003). The Defence Policy of the Sokoto Caliphate, 1804-1903. Ph.D Thesis. Department of History. Sokoto: Usmanu Danfodiyo University.

Nafi, u. A. A. (2012). Magana Jari Ce (1-3): Nazarin Salo da Sarrafa Harshe. Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya da Kimiyyar Harsuna. Kano: Jami’ar Bayero.

Pweddon, N. (1977). Thematic Conflict and Narrative Techniques in Abubakar Imam’s Ruwan Bagaja. Ph.D Thesis. Madison: University of Wiscosin.

Sani, I. (2013). Ingenuity of Narratiɓe in Abubakar Imam’s Ruwan Bagaja. In Humanities in Sub-Saharan World. Ruwan Bagaja in Perspective, Eight Decades of a Hausa Masterpiece in Prose (1933-2013) Edited by Bunza, Noofal and Zaria. Zaria: Ahmadu University Press Limited.

Shehu, M. (2018). Zama Lafiya Ya Fi Zama Ɗan sarki: Tunanin Bahaushe a Kan Zaman Lafiya da Sasantawa. Kundin Digiri na Uku. Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya. Sakkwato: Jami’ar Usmanu Danfodiyo.

Umar, A. A. (2017). A History of Communal Cinflicts in Ebiraland, C. 1979-2012. Ph.D Thesis Submitted to the Department of History. Sokoto: Usmanu Danfodiyo University.

Post a Comment

0 Comments