Citation: Adamu, A.I. and Buhari, A.T. (2024). Habaici Cikin Waƙar “Kowa Ya Yi Maka Kan Kara” Ta Alhaji Garba Gashuwa. Ginshiƙin Nazarin Salon Waƙoƙin Hausa, 155-160. www.doi.org/10.36349/djhs.2024.v03i01.018.
Habaici Cikin Waƙar “Kowa Ya Yi Maka Kan Kara” Ta Alhaji Garba
Gashuwa
A’ishatu Isma’il Adamu
Sashen Koyar da Haus
Jami’ar Ilimi ta Sa’adatu Rimi,
Kumbotso, Kano State
aishaismailadamu@gmail.com
08065525769
Da
A’ishatu Tukur Buhari
Sashen Koyar da
Hausa,
Jami’ar Ilimi ta
Sa’adatu Rimi,
Kumbotso, Kano State
aishatutukurbuhari@gmail.com
07067337655
Tsakure: Wannan nazari
mai suna “Habaici Cikin Waƙar Kowa Ya Yi Maka Kan Kara” ta Alhaji
Garba Gashuwa. Babbar manufar nazarin ita ce fito da habaici ta hanyar zaƙulo ire-iren hikimomi da basirori da dabaru na sarrafa harshe da
mawallafin ya yi amfani da su a cikin waƙar domin ya
jawo hankulan jama’a zuwa ga manufa. An kalli yadda marubucin ya yi amfani da dabarar
sanya habaici a waƙar
cikin hikima domin ya isar da saƙonsa.
An ɗora wannan nazari a bisa mazahabar Abdulƙadir Ɗangambo
(2007) ta Ɗaurayar Gadon Feɗe Waƙa. Dabaru da hanyoyin da aka bi wajen gudanar da
wannan nazari sun haɗa da samo matanin waƙar daga hannun marubucin a kuma rubuce tare da
tattaunawa da shi. A nazarin kuma an gano marubucin ya yi amfani da dabarar
sarrafa harshe ta sanya habaici a cikin waƙar don
ya mayar da martani ga abokin adawa. Gudunmawar da nazarin ya bayar ita ce zai
zama jagora ga manazarta da ɗalibai ta yadda za su nazarci
habaici a rubutacciyar waƙa,
musamman waƙoƙin siyasa a fannin adabin Hausa.
Fitilun
Kalmomi: Salo, Habaici, Waƙoƙin Hausa, Alhaji Garba Gashuwa, Sarrafa harshe
Gabatarwa
Marubuta wakokin Hausa sukan yi amfani da salo daban-daban a wajen tsara
baitocin wakokinsu domin jawo hankulan masu sauraro zuwa ga manufarsu. Habaici
na ɗaya daga cikin hanyoyin
da mawallafa waƙoƙin siyasa kan yi amfani da shi wajen isar da saƙonsu
ga abokan adawa domin su munana su ko su dakusar da su a wajen al’umma. A
wannan nazari an kawo yadda Alhaji Garba Gashuwa ya yi amfani da wannan dabara
ta sarrafa harshe na habaici a waƙar siyasa mai suna “Kowa Ya Yi Maka Kan Kara” inda
aka fito da misalansa tare da yin sharhi a kansu.
Taƙaitacen Tarihin Garba Gashuwa
Alhaji Garba Gashuwa shi ne mawallafin waƙar Kowa Ya Yi Maka Kan
Kara ta siyasa. An haife shi a ƙasar Bade ta tsohuwar jihar Borno wadda a yanzu ƙaramar
hukuma ce a jihar Yobe, a cikin shekara ta 1957. Bayan ya kammala karatun Alƙur’ani
mai girma da fiƙhu da hadisai sai kuma ya shiga harkokin
kasuwancin sayar da littattafai kamar su Ƙawa’idi da Yasin Arshada da Iza-Waƙa da
Dala’ilul-khairati da makamantan su a garin Bade.
Daga nan ne sai ya shiga harkokin waƙe-waƙe na addinin Musulunci kamar su Isra’i da
Mi’iraji da Mu’ujizar Annabi Muhammad (S.A.W.) da tauhidi da wafatin Manzon
Allah (S.A.W.) da makamantansu.
Alhaji Garba Gashuwa ya fara waƙoƙin siyasa a shekarar 1978 lokacin da
marigayi Malam Aminu Kano ya je yaƙin neman zaɓe na jam’iyyar PRP a garin Gashuwa da kewaye. Jin
irin fasahar da Allah ya yi wa wannan bawan Allah shi ne dalilin da ya sa
marigayi Malam Aminu Kano ya neme shi da ya dawo Kano ya zauna domin ya ci gaba
da bayar da gudummawarsa a cikin harkokin siyasa kamar yadda ya saba. Tun daga
wannan lokaci ne Alhaji Garba Gashuwa ya shiga harkokin siyasa tsundum tare da
wallafe-wallafen waƙoƙin siyasa. Ire-iren waƙoƙin da ya wallafa a
shekarar 1979-83, sun haɗa da;
“Ina Gizon Yake?” da “Mai Ƙuri’a Ta fi Kai Tunani PRP Za Ka Zaɓa.” Bugu da ƙari, mawallafin bai
tsaya a waƙoƙin siyasa kaɗai ba,
ya ma wallafa waƙoƙi masu ɗimbin yawa a kan harkokin ilimi da addini da
al’adun gargajiya da yaɗa
manufofin gwamnati da faɗakarwa
tare da wayar da kan al’umma dangane da sauran al’amuran yau da kullum.
Hazaƙar Alhaji Garba Gashuwa musamman wajen raya al’adun gargajiya ya jawo
hankalin Gwamnatin jihar Kano a ƙarƙashin Gwamnan jiha na wancan lokacin, Marigayi
Alhaji Sabo Bakin zuwa ta ɗauke
shi aiki a gidan talabijin na Jihar Kano (CTV 67) a ɓangaren al’adun gargajiya a shekarar 1963.
Ya zauna gidan talabijin na CTV 67 har zuwa shekarar 1989. Daga nan sai
gwamnatin mulkin soja ta Jihar Kano a ƙarƙashin Kanal Idris Garba (mai murabus) ta
nemi Alhaji Garba Gashuwa da ya zo ya taimaka mata da shawarwari a Ma’aikatar
Tarihi da Al’adu ta Jihar Kano (History
and Culture Bureau). Ya ci gaba da zama da wannan hukuma yana bayar da
gudummawarsa har sai da ta kai ya sami cigaba zuwa matsayin mamba a Hukumar
Daraktocin wannan ma’aikata daga 1989 zuwa 1995.
Tun daga shekarar 1995, har ya zuwa yau Alhaji Garba ya fi mayar da
hankalinsa a kan wallafa waƙoƙin faɗakarwa
da wayar da kai da addini da al’adu da kuma siyasa. Zuwa yanzu dai Alhaji Garba
Gashuwa ya wallafa waƙoƙi kimanin 600. amma saboda wasu dalilai waƙoƙin da
suke a rubuce a hannunsa a halin yanzu, adadinsu bai wuce ɗari huɗu ba, kuma yana rubuta su ne cikin Hausar
ajami.
Har ila yau kuma, Alhaji Garba Gashuwa ya sami shaidar takardu na girmamawa
daga gwamnatin jihar Kano da kuma wasu ma’aikatun gwamnatin Kano.
A halin yanzu Alhaji Garba Gashuwa yana zaune a unguwar Sheka da ke ƙaramar
hukumar Kumbotso a jihar Kano, tare da matan aure guda biyu da kuma ‘ya’ya goma
sha ɗaya. Yana nan kuma yana
ci gaba da rera waƙoƙinsa a fannoni daban-daban. Kamar addini da siyasa
da faɗakarwa.
An yi wannan waƙar a
shekarar 2003. Mawallafin ya bai wa
wannan waƙar
suna “Kowa Ya Yi Maka Kan Kara”, saboda ya mayar da martani ga wani babban jigo
a cikin jam’iyyar APP. A sakamakon
wani saɓani da
aka samu a tsakaninsa da mawaƙin, a kan an umarce shi da ya yi masa waƙa,
hakan ba ta samu ba.
Waƙar “Kowa Ya Yi Maka Kan Kara” tana ɗauke da baituka 28, kuma kowanne baiti yana ɗauke da ɗangwaye biyar-biyar, amma tana ɗauke da taƙadarin baiti ƙwaya ɗaya wato baiti na 24. A wannan baiti ya zo
da ɗangwayensa daban a cikin
waƙa, wato mai ƙwar bakwai ne. Yawanci idan aka samu taƙadarin
baiti a waƙa, mawallafan sukan ƙara jaddada manufarsu a ciki.
Ma’anar Habaici
Masana da manazarta da dama sun
bayyana ma’anar habaici kamar haka:
Ita ce furta
wata kalma ta suka ko zagin wani a fakaice, kuma a gaban idonsa, ta yadda wani
daban ba lalle ya gane da wanda ake ba. Amma idan aka ambaci wani abu da yake
da dangantaka da mutum, to ba makawa zai fahimci da shi ake. Wani lokaci shaguɓe ko gugar zana suna iya ɗaukar ma’anar habaici.
Galibi an fi yiwa abokan hamayya ko maƙiyi habaici domin a tunzura shi ko a
tsokane shi ko kuma a ɓata
masa rai Sa’id, (2002:231:1).
An kuma bayyana ma’anar da cewa.
Habaici wasu
kalmomi ne da ake faɗa a fakaice don a ɓata wa wani mutum rai ba tare da an bayyana mutumin da ake nufi ƙuru-ƙuru ba. Habaici
ya fi zambo sauƙi domin akwai sakaya zance a cikinsa wato ba a fitowa fili ƙarara a yi wa
mutum shi, kuma ba a fadin wata fitacciyar siffar mutum ko wani fitaccen
halinsa. Kalmomin sakaya wa da ake amfani da su a yi habaici sun haɗa da ‘wane’ ko
‘wagga’ ko ‘wadanga’ da sauransu. Domin haka ake cewa, habaici riga ce duk
wanda ya sa za ta shige shi Gusau, (2002:37).
A wata ma’anar kuma.
Habaici magana
ce mai ɓoyayyar
manufa. Akan yi magana da niyyar ko nufin wani abu ga wanda aka yi habaicin
dominsa. Idan ba mutum ya san kan zance ba, ba kasafai yake gane wanda aka yi
habaicn dominsa ba. Domin shi habaici ana laƙaba shi ne da wani abu da yake ba mai
kyau ba. Saboda haka shi habaici zagi-zagi ne na rara-gefe. Habaici yana da
ma’ana kusan iri ɗaya
da gugar zana ko shaguɓe.”
Ɗangambo,
(2008:72-73).
A wata ma’anar dai kuma, an
bayyana shi kamar haka:
Hausawa na cewa
“Habaici da kamar faɗa”
magana ce za a yi ta gugar zana, domin mayar da martani ga wani da ya ɓata ma rai. Ba a gane wanda
aka yi wa habaici sai an san abin da ya haifar da habaicin. Sarɓi, (2007:145).
A taƙaice za a iya kallon
habaici da cewa magana ce da ta ƙunshi zagi ko suka a fakaice da nufin
bayyana wani saƙo kamar ga wani domin a munana mishi/masa ko a wulaƙantar
da shi.
Dabarun Gudanar Da Bincike
Duk wani bincike na ilimi da za a gudanar
yana da dabaru da hanyoyi da mai yin nazarin kan zaɓa domin ya bi wajen cimma nasarar wannan
bincike. An ɗora
wannan bincike bisa ra’in Abdulƙadir Ɗangambo (2007) ta Ɗaurayar Gadon Feɗe Waƙa. Dabaru
da hanyoyin da aka bi wajen gudanar da wannan nazari sun haɗa da samo matanin waƙar kai tsaye daga wurin
marubucin, an kuma same ta a rubuce da kuma cikin kaset, sannan an sami
cikakkiyar waƙar a cikin kundin binciken Adamu, (2012:228-232)
domin samun sauƙin nazari. Haka kuma an tattauna da marubucin
dangane da tarihinsa da kuma ita kanta waƙar.
Habaici a Waƙar Siyasa “Kowa
Ya Yi Maka Kan Kara” Ta Alhaji Garba Gashuwa
Alhaji Garba Gashuwa ya yi amfani da habaici mai yawa a cikin waƙar,
kasancewar waƙar an gina ta ne a kan mayar da martani ga wani
babban jigo, a cikin jam’iyyar. Saboda rashin jituwa da suka samu a tsakaninsu
da mawallafin, wanda ya samo asali a sakamakon wani taro da jam’iyyar ta
gudanar a Damaturu. Domin haka mawallafin ya yi amfani da hikimar da yake da
ita a matsayinsa na mawaƙi, inda ya juya harshe cikin hikima ya sulluke
shi.
Baitocin Habaici a Waƙar Kowa Ya Yi
Maka Kan Kara
Ga yadda ya kawo baitukan habaici a cikin waƙar.
Baiti na 16,
Ranar zaɓe ku daina shakka bari fargaba,
Ba mu fa san fargaba ba kuma mu ba mu san
ta ba,
Duk mai kishin ƙasa ba zai mata tuggu
ba,
Yaro ya san ubansa tun ma bai tashi ba,
Jallah taimaka taimaki jam’iyyarka APP.
(Garba Gashuwa, waƙar “Kowa Ya Yi Maka Kan
Kara” bt na 16)
A wannan baiti ya bayyana wannan babban jigon da mai yin tuggu, wato mai
shirya zagon ƙasa a cikin jam’iyya. Haka kuma a cikin baitin
mawaƙin ya nuna cewa ya san duk mai son sa da mai son ci gabansa, sannan kuma ya
san wanda ba ya son sa da kuma ƙin ci gabansa a cikin jam’iyyar APP inda ya kawo
maganar kamar haka: “Yaro ya san ubansa tun ma bai tashi ba”. Wato shi mawaƙin ya
san ba ya son sa a cikin jam’iyyar.
Sai ya kuma faɗin a baiti na 17,
Ga albishiri ku ɗan ba ni goro fari na ci,
Yau kuma zan tona duk bayaninka magulmaci,
Ga ma zogale gandi[1] ya fi hulɗa da maƙaryaci,
Ga kuma jama’a suna ta fama da kici-kici,
Daina bimbimi ka faɗi mai ku kai wa APP.
(Garba Gashuwa, waƙar “Kowa Ya Yi Maka Kan
Kara” bt na 17)
A wannan baitin mawallafin yana jan hankalin ‘yan jam’iyya domin bayyana
musu halayyar wannan babban jigo, inda yake bayyana shi da matsayin magulmaci,
ya kuma kira shi da “zogale gandi”.
Haka ma a Baiti na 18,
Na washi na ga shugaba da hali yana raƙumi,
Sai a maƙa mai yugwai a ja ko
bisa sansami,
Sai yai lagado ya kama baki ya na raƙumi,
Tsuntattar mage ba ta bin dunka a ƙorami,
Daina bimbimi ka faɗi mai ku kai wa APP.
(Garba Gashuwa, waƙar “Kowa Ya Yi Maka Kan
Kara” bt na 18)
A nan mawallafin yana nuna shi wannnan babban jigo bai cancanta ya yi jagoranci
ba, saboda ya siffanta shi da raƙumi da akala wanda sai yadda aka yi da shi. Haka
kuma mawallafin, ya kira shi da “tsuntattar mage”, wato wanda ba a san daga
inda ya fito ba.
Baiti na gaba ma:
Baiti na 20,
Duk ɗan Sarkin da ke siyasa ba taƙama,
Ɗan mai
kuɗɗin da ke siyasa bai taƙama,
Don ga su da ɗan talaka su uku ba mai zama,
Duk hanƙoro muke mu kamo harshen
duma,
Jallah taimaka taimaki jam’iyyarka APP.
(Garba Gashuwa, waƙar “Kowa Ya Yi Maka Kan
Kara” bt na 20)
A nan mawallafin yana nufin cewar ita siyasa ko jam’iyya idan an shige ta
ana neman matsayi ko mulki, to ba bambanci tsakanin talaka da mai kuɗi ko mai sarauta. Domin ita jam’iyya tana
neman haɗin kan
kowa da kowa ne domin ta kai ga nasara.
A wani baitin kuma sai ya ce:
Baiti na 21,
Kyawun ɗan sarki mu gan shi can fada da al’umma,
Sannan mu ishe gabanshi fadawa na zama,
Mu ko faɗa mai Yarima[2] ba ai mana gardama,
Kai ko ɗan ka-yi-na-yi sai hargitsa al’umma,
Daina bimbimi ka faɗi mai kukai wa APP.
(Garba Gashuwa, waƙar “Kowa Ya Yi Maka Kan
Kara” bt na 21)
Idan aka kalli wannan baiti ma, za a ga wani saƙo ne yake isarwa ga
wannan babban jigo na irin halayyar da yake nuna wa na iko da isa, wanda mai
neman al’umma kuma cikakken ɗan
siyasa, bai kamata ya nuna ba, saboda siyasa ƙungiya ce ta kowa da
kowa, don haka mawaƙin ya yi masa shaguɓe da gugar zana idan har ba zai daina iko
da isa ba, to ya daina siyasa, domin a cikin siyasa mutum ba ya yin yadda yake
so, sai ya nemi haɗin kan
mutane.
A waƙar tasa dai a baiti na 22, ga abin da ya ce:
Baiti na 22,
Daga yau ɗan kasuwa ba zai jagoran mu ba,
Mu mu yi wahala ya sai da mu ba zai damu
ba,
Ba dan ya ga ci gabanmu ba ba zai jagoran
mu ba,
Ko
ta watse a gun shi shi ba zai dame mu ba,
Daina bimbimi ka
faɗi mai kukai wa APP.
(Garba Gashuwa,
waƙar
“Kowa Ya Yi Maka Kan Kara” bt na 22)
Mawallafin yana nuna rashin
kishin shi wannan babban jigon jam’iyya na rashin kulawa da hakkin ‘yan
jam’iyya tare da yin zagon ƙasa a cikin jam’iyya.
Sai ya ƙara da cewa:
Baiti na 24,
Ka ce mini ba na yin biyayya ban bi ka ba,
Yaya za ai na bi ka ni bam ma san ka ba,
Idan na bi Najeriya nake bi ko can gaba,
A tsarin fasalinka ba ruwan nan aka yi ka
ba,
Sakkwato Gobir da Zamfarawa wa ke gaba,
Tun da a zanan ka ɓad da
ni ban gane ka ba,
Daina bimbimi ka faɗi mai kukai wa APP.
(Garba Gashuwa, waƙar “Kowa Ya Yi Maka Kan
Kara” bt na 24)
Idan aka kalli wannan baitin, mawallafin yana bayyana saƙonsa a
kan abin da ya faru tsakaninsu shi da Bafarawa a kan zargin da yake yi masa na
rashin biyayya wanda ya kawo saɓani da
rashin fahimta a tsakaninsu. A kan shugaban jam’iyya na ƙasa a wancan lokaci ya
umarci mawallafin ya yi wa wani babban jigo waƙa wanda hakan ba ta samu
ba, domin haka yake jin haushinsa. Hakan ce ta sa mawallafin ya tsara wannan waƙa,
inda yake nunawa a cikin wannan baitin ya juya masa da habaici cewar yaya za a
yi ya bi shi bai ma san shi ba, inda yake nuna cewar shi ba ɗan ƙasa ba ne.
A baiti na 25 sai ya ci gaba da cewa:
Baiti na 25,
Garba ka san baki gare ni cau-cau tamkar
aku,
To tun da ka ja ni yau gwabna kai za ka
shiga uku,
Nai maka yasin da ƙulhuwallahu hawa uku,
Sai nai ƙullin da za ka ma ji ka
a kurukuku,
Daina bimbimi ka faɗi mai kukai wa APP.
(Garba Gashuwa, waƙar “Kowa Ya Yi Maka Kan
Kara” bt na 25)
Mawallafin ya nuna a zahiri ba zai iya rigima da wannan babban jigon ba,
amma saboda baiwar da Allah ya yi masa ta waƙa yake ganin zai iya
amfani da ita domin ya rama abin da ya yi masa.
Sai ya kuma faɗi a
baiti na gaba:
Baiti na 26,
Da ka yo mini kan kara itace zan yi maka,
Ba na shakkar karo da kai ko zan hallaka,
Mai na ci na ashan ka sa ni ramkon azumi duka,
Tun da kana ja da ni kana dab da ka hallaka,
Daina bimbimi ka faɗi mai kukai wa APP.
(Garba Gashuwa, waƙar “Kowa Ya Yi Maka Kan
Kara” bt na 26)
Idan muka lura da wannan baiti za mu ga irin ɓacin ran da mawallafin ya nuna, saboda
adawar da take tsakaninsu yake ganin bai kamata wannan babban jigo ya yi adawa
da Garba Gashuwa ba, domin ƙasa yake da shi. Saboda haka mawaƙin
wannan baitin ya nuna ba ya tsoronsa, a matsayinsa na mawaƙi domin yana ganin zai
iya ramawa da bakinsa.
Sai ya ƙara da cewa:
Baiti na 27,
Ba don gwamna guda ba mai zan yi a yamma ni?,
To
fa sai fa ganin wata na juya don in gani,
Ko ko Ramadan in ya kama don in sani,
Da zai yiwu kai da yin gabas sai in babu
ni,
Daina bimbimi ka faɗi mai kukai wa APP.
(Garba Gashuwa, waƙar “Kowa Ya Yi Maka Kan
Kara” bt na 27)
Wannan baitin ya nuna tsananin adawa tsakaninsa da
wannan babban jigo. A nan ya nuna hidimar da yake yi wa jam’iyya ba don shi
yake yi ba. Yana yi domin kishin jam’iyya kuma domin wasu jiga-jigai na
jam’iyya musamman gwamnan Zamfara a wancan lokaci.
Kammalawa
A taƙaice wannan takarda, an fahimci Alhaji Garba Gashuwa marubuci ne da yake da
ƙwarewa da basira wajen iya sarrafa harshe ta hanyar habaici a waƙarsa
ta “Kowa Ya Yi Maka Kan Kara” ta siyasa. Nazarin kuma ya gano amfani da habaici
a cikin waƙa musamman ta siyasa, hanya ce ta jawo hankalin mai saurare ko mai karatu
don riƙe tunanin mai karatu ko mai sauraro da sa waƙa armashi da kwalliya da
kuma nuna gwanintar harshe. Har ila yau kuma, nazarin ya gano irin dimbin
hikimomin da mawallafin ya yi amfani da su a cikin waƙar na yin amfani da ɓoyayyar manufa da nufin sakaya wani abu ga
wani don ya munana mishi ko ya wulaƙantar da shi ta hanyar sarrafa harshe,
domin ya bayar da saƙo zuwa ga masu saurare ko karatu. A ƙarshe
wannan nazari zai ba da gagarumar gudunmawa ga manzarta da ɗaliban ilimi wajen ƙara fahimtar habaici ta
yadda za a nazarce shi da yi masa sharhi a rubutacciyar waƙa musamman ta siyasa.
Manazarta
Adamu, A. I. (2012) “Salo da
Sarrafa Harshe a cikin Wasu Waƙoƙin Jam’iyyun ANPP da PDP a Jihohin Kano
da Jigawa”. Kundin Digiri na Biyu. Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya. Kano:
Jami’ar Bayero.
Birniwa, H.A. (1987) “Conservatism and
Dissent: A Comparatiɓe Study of NPC/NPN and
NEPU/PRP Hausa Political Verse From Circa 1946-1983”
Ph.D Thesis, Department of Nigerian Languages. Sokoto: Usmanu Ɗanfodiyo
University.
Bunguɗu, A. I. (2017) “Tarken Rubutattun Waƙoƙin
Siyasa na Kabiru Yahaya Kilasik” Kundin Digiri na Biyu. Sashen Koyar da
Harsunan Nijeriya. Kano: Jami’ar Bayero.
C.N.H.N. (2006) Ƙamusun
Hausa na Jami’ar Bayero Kano. Zaria: Ahmadu Bello University Press.
Dan’iya, D. (1997) “Adon Harshe Cikin Rubutaccen Adabin Hausa”. Kundin
Digiri na Biyu, Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Kano: Jami’ar Bayero
Ɗangambo, A. (1980) "Hausa Wa'azi Verse
From CA 1800 to CA 1970: A Critical Study of form, Content, Language and
Style". Ph.D. Thesis School of Oriental and African Studies, University of
London.
Ɗangambo, A. (1981) “Rikiɗar
Azanci: Siddabarun Salo da Harshe a Cikin Tabarƙoƙo, Tahamisin Aliyu Ɗansidi
Sarkin Zazzau”. Cikin Studies in
Hausa Language, Literature and Culture, CNHN, Kano: Jami’ar Bayero
Ɗangambo,
A. (2007) Ɗaurayar Gadon Feɗe Waƙa (Sabon tsari) Kaduna: Amana
Publishers Limited.
Ɗangambo, A. (2008), Rabe-Raben Adabin Hausa
da Muhimmancinsa ga Rayuwar Hausawa (Sabon tsari) Kaduna: Amana Publishers
Ltd.
Gusau, S.M. (2002) Sarkin Taushi Salihu Jankidi Kaduna: Baraka
Publishers Limited.
Sa’id, B. (2002) “Rubutattun Waƙoƙin Hausa na Ƙarni na Ashirin a
Jihohin Sakkwato da Kabi da Zamfara”. Kundin Digiri na Uku, Sashen Koyar da
Harsunan Nijeriya, Kano: Jami’ar Bayero.
Sarɓi,
S. A. (2007) Nazarin Waƙen Hausa, Samrib Publishers Sallari
Babban Giji, Kano.
Yahya, A. B.
(1997) Jigon Nazarin Waƙa. Kaduna: Fisbas Media Service.
[1] Zogale gandi: Bishiya ce da ake
shukawa ko asawa a gida ko a gona, wadda ake tsigar ganyenta ana dafawa a
kwaxanta a ci ko a yi dambu ko fate-fate ko a yi miya da shi. Ana yi masa
kirari da “zogale gandi samarin danga”. Dubi Qamusun Hausa na Jami’ar Bayero
(2006:494).
[2] Yarima: na nufin (Xan sarki) Xaya
daga sarautun gargajiya wanda ya samo asali daga sarautar Borno. Dubi Qamusun
Hausa na Jami’ar Bayero (2006:480).
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.