Ticker

6/recent/ticker-posts

Bitar Dalilan Yawaitar Mutuwar Auren Hausawa a Karni na 21

Citation: Abdullahi, I.S.S. (2024). Bitar Dalilan Yawaitar Mutuwar Auren Hausawa a Ƙarni na 21. Ginshiƙin Nazarin Salon Waƙoƙin Hausa, 132-140. www.doi.org/10.36349/djhs.2024.v03i01.016.

Bitar Dalilan Yawaitar Mutuwar Auren Hausawa a Ƙarni na 21

Ibrahim Abdullahi Sarkin Sudan
Sashen Koyar da Harsunan Nigeriya
Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato
ibrasskg@gmail.com
0803 6153 050

Tsakure: Wannan maƙala ta yi ƙoƙarin yin bitar wasu matsaloli a alumar Hausawa waɗanda suke haddasa yawaitar mutuwar aure. Waɗannan matsaloli kamar yadda aka yi nazarinsu, suna da alaƙa ne da zamani. Wato idan aka kwatanta, za a ga a da ba haka rayuwar ta Hausawa take ba. An sami tattara waɗannan bayanai ne ta bin bahasin dalilan mutuwar aurarrakin daga bakin zawarawan da abin ya shafa da kuma mazan da suka yi sakin. Haka kuma an sami wasu bayanan daga dangin waɗanda abin ya shafa da bayanan kotu da na kafafen yaɗa labarai musamman na sadar da zumunta na zamani. Nazarin ya gano cewa, wasu daga cikin matsalolin da suke jawo yawaitar mutuwar aure sun samu ne daga matan. Wasu kuma suna da alaƙa da mazan. Wasu sun shafi dangi ko iyaye na ma’auratan, a yayin da aka ɗora alhakin wasu matsalolin ga gurɓacewar al’uma wadda sauyawar zamani ya kawo. Nazarin ya gano cewa, akwai illoli masu yawa da al’umar Hausawa za ta fuskanta idan aurarraki suka ci gaba da mutuwa kamar yadda abin yake ƙaruwa a wannan zamani.

Fitilun Kalmomi: Matsaloli, Al’umar Hausawa, Mutuwar aure, Ƙarni na 21

Gabatarwa

Zamantakewar aure kamar rayuwa ce ga abu mai rai. Aure yana iya mutuwa a kowane lokaci kamar yadda rayuwar abu mai rai take iya ɗaukewa a duk sa’ilin da ta zo ƙarshe. Ga duk mabiya Musulunci, hukunce-hukuncen rayuwa ko mutuwar aure abu ɗaya ne muddin dai ana bin sharuɗɗan addinin sau-da-ƙafa. To sai dai dalilan da sukan jawo saurin mutuwar aure suna iya danganta daga al’uma zuwa wata ko daga wuri zuwa wuri. Yanayin mutane da tsarin gudanar da rayuwarsu da na muhallin da suke zaune da kuma irin fahimta ko wayewarsu, suna iya yin tasiri dangane da yawaita ko ƙarancin mutuwar aure. Wannan ne ya sa idan aka kwatanta yawaitar mutuwar aure a al’ummomi mabambanta, za a ga sakamakon ya fito kai tsaye. Haka abin dole zai bambanta dangane da matsalolin da al’umma za ta fuskanta na ƙaranci ko yawaitar illolin rayuwa waɗanda suka tuzgo a dalilin mutuwar aure. A cikin nazarin an yi ƙoƙarin bibiyar musabbabin yawaitar mutuwar aure a al’umar Hausawa a wannan zamani (ƙarni na 21). Dalilin karkata linzamin nazarin ga Hausawa bai rasa nasaba da lura da aka yi da ta’azzarar matsalar gare su fiye da yadda abin yake gudana idan an kwatanta da maƙwantansu na kusa da na nesa. Haka kuma, kasancewar zamani abokin tafiya, shi ma ya taimaka wajen yawaitar mutuwar auren Hausawa.

Mutuwar Aure

Rayuwar Hausawa ta gargajiya da ta Musulunci sun aminta da mutuwa a matsayin babban abin da ke raba aure. Da zarar ɗaya daga cikin ma’aurata ya mutu to aure ya ƙare. A duk lokacin da aka sami rabuwa na halaccin zama a tsakanin ma’aurata Hausawa, to akan ce aure ya mutu. Wato babu abin da ake kira aure a tsakanin mata da miji. Wannan kuwa yana faruwa ne idan miji ya sauwaƙe wa matarsa ko idan ita ta nema ya kuma amince da ya yi hakan. A wasu lokutan kuma ana samun shigowar magabata wajen mutuwar aure. Idan aka fahimci zaman auren ba zai iya ɗorewa a tsakanin mata da miji ba ta la’akari da yanayin da ake ciki, sai magabatan kowane ɓangare su aminta a raba auren. Wata hanyar kuma da aure yake rabuwa a tsakanin ma’aurata (Hausawa) ita ce ta hanyar hukuma. Idan aka sami saɓani a tsakanin ma’aurata, aka kasa warwarewa a gida, to abin yakan kai ga hukuma. Galibi irin wannan yana aukuwa ne idan mace ita ke bukatar rabuwar. A gargajiyance, mace tana iya kashe aure ta hanyar barin gidan miji ta koma gidan wani namijin da take so. Shi kuma wanda aka koma gidansa idan ya aminta sai ya biya tsohon mijin dukiyar aurensa (Abdullahi 2008).

Tunani da kuma hukunce-hukuncen da sukan biyo bayan mutuwar aure suna da yawa. Daga ciki, dole ma’auratan da danginsu ko makusanta da ma al’uma su yarda:

·         Babu sauran gusar da sha’awa ko saduwa a tsakaninsu a matsayin mata da miji.

·         Babu wajibcin taimakon juna wanda addini ko al’ada suka tanada.

·         Babu gado a tsakaninsu idan ɗaya ya mutu bayan mutuwar aure.

·         Babu tilastawa na bin umurnin da ya shafi hani ko horo.

·         Babu tilastawa na biyayya.

A taƙaice dai, duk abin da ya haɗa su mai alaƙa da aure ya raba su in ban da wasu haƙƙoƙi da aka fayyace kamar kula da kuma shawara a kan ‘ya’ya ko wata dukiya da ta sarƙu a tsakani da dai makamantansu.

Fuskokin Dalilan Mutuwar Auren Hausawa a Ƙarni na 21

Hausawa suna cewa, “Zamani abokin tafiya.” Baya ga abin da aka sani a gargajiyance ko a al’adance masu sa aure ya mutu kai tsaye, zamanin da Hausawa suka sami kansu ya buɗe musu wani shafi na dalilan rabuwa tsakanin mata da miji. Wasu daga cikin waɗannan matsaloli akwai su tun ba yau ba. To, sai dai zamani ya sabunta su. A wannan fasali, an yi bitar dalilan da sukan haddasa mutuwar auren Hausawa a wannan zamanin zuwa ga matsalolin namiji ko mace ko na tarayya (maza da mata) ko na iyaye da dangi da makusantan ma’aurata da kuma na al’umma.

Matsalolin da Suka Shafi Miji

A cikin wannan fasalin, an dubi wasu matsalolin da suke haddasa mutuwar aure a al’ummar Hausawa masu alaƙa da zamani waɗanda suka ta’allaƙa ga maza. Wato aiwatar da su da maza magidanta suke yi, sais u zama musabbabin mutuwar aure.

Neman Matan Banza

Wasu magidanta a wannan zamanin sun ɗabi’antu da cin amanar matansu ta hanyar neman matan banza a waje ba da niyyar auren su ba. Da zarar mace ta sami labari ko ƙwararan hujjoji a kan wannan hali da miji yake ciki, to sai a fara ɗaukar matakai waɗanda za su sa a yi ta fitina har daga ƙarshe idan bai bari ba, sai aure ya mutu. Wasu matan sukan ɗauki matakai ne saboda kare kansu daga kamuwa da cututtuka masu alaƙa da jima’i barkatai.

Kwaɗayin Arzikin Iyayen Mace

Wasu maza sukan auri mace saboda kwaɗayin abin hannunta ko na iyayenta/danginta. Duk wani abu da zai biyo bayan auren na kasa cimma abin da ya sa ya yi shi, to yana iya kawo saɓani. Daga nan sai rabuwa, saboda ba zai iya jure wa zaman ba muddin bai fa’idantu da abin da ta mallaka ko iyayenta suka mallaka ba.

Gurin Auren Mace ‘Yar Boko

Ganin yadda ilimin boko ya zama ado a al’umar Hausawa a wannan zamani, an wayi gari idan mace ba ta yi karatun boko ba to samun miji musamman ɗan bokon yakan yi mata wahala. Ga maza ‘yan boko waɗanda suka riga suka auri mata marasa ilinin boko a can baya, sukan fuskanci matsalar zamantakewar aure a lokacin da suka ƙallafa wa kansu zama da mace ‘yar boko. Duk kyautatawar da matarsa (marar ilimin boko) take yi ba zai gani ba saboda yana ganin bai shiga cikin yayi ba. Wannan yakan sa a yi ta samun matsala har auren ya mutu, ya je ya auro ‘yar bokon don ya sami gamsuwar da zamani ya ƙawata.

Neman Ƙawar Mata ko Ƙanwa ko ‘Yar’aiki

Rashin kunya da iskanci na wasu mazan da suke neman ƙanne ko ƙawaye ko masu aikin matansu. Yawan neman mata barkatai ya zama ɗabi’ar wasu mazaje Hausawa a wannan zamani. Ana samun magidanta da yawa da sukan kasance, ko bayan sun yi aure ba su barin neman mata a waje domin su yi iskanci ko lalata da su. Wannan ƙazantar ba ta tsaya ga neman matan da suke nesa da su ba. Hatta da matan da suke kusa da su ba su bari ba. A irin wannan yanayi, akan sami mazan da sukan jarabtu da neman ƙannen matansu ko ƙawayen matansu ko ma ‘yan aikin gidajensu. Da zarar irin wannan matsalar ta fallasu to nan take aure yakan mutu.

Ɗaure Miji a Gidan Yari

Matsalar aikata laifin da zai kai miji gidan yari kamar sata da sauransu. A lokacin da mace da miji suke gudanar da rayuwarsu, sai kwatsam wani abu na ƙaddara ta faru ga miji. Irin waɗannan miyagun ƙaddarori sukan iya sa hukuma zartar da hukunci a ɗaure maigida a gidan yari na wani lokaci. Misalan irin wannan matsaloli su ne a kama shi da laifin sata ko zamba ko damfara da dai sauran miyagun ɗabi’u da zamani ya ɓullo da su. Wannan ɗauri da za a yi wa mai laifin yakan shafi auren. Wato matar ta ga ba ta iya zama a cikin ƙasƙanci na lokacin da mijin yake ɗaure. Tana ganin jama’a za su ta yi mata kallon matar azzalumi. Sakamakon haka sai ita ko iyayenta su nemi a raba auren.

Rashin Aikin yi ga Miji

A duk lokacin da magidanci ba ya da aikin yi, to dole sai iyalinsa sun shiga cikin ƙuncin rayuwa. A taƙaice zai kasa ciyar da iyalinsa. Ita kuma rayuwa ba ta gudana sai da ci. A da magidanci ba ya zama ba aikin yi. Ko da ba ya da shi, ba a rasa rufin asiri daga dangi ko abokan zama. Haka ita ma matar ba za ta rasa ‘yan dabarun da za ta riƙa yi ba musamman na ƙananan sana’o’in mata ana samun abin da aka rufa wa juna asiri. A yanzu, idan mutum ya rasa aikin yi, ba lallai ba ne wani ya ɗauki nauyinsa. Ƙarshen, auren mutuwa yake yi saboda rashin ɗaukar ɗawainiyar iyali.

Rashin Adalci a Tsakanin Matan Mutum Ɗaya

A wannan zamanin ana samun mazan Hausawa da ke auren mata fiye da ɗaya. Zamani ya zo da matsalar rashin nuna adalci a tsakanin matan daga namiji. Kai tsaye za a ga magidanci yana nuna wariya ko cin amanar wasu matan da ba ya ɗasawa da su. Idan cin fuska da walaƙancin ya yi yawa sai ya zama sanadin mutuwar aure. Wasu mazan ma dalili kawai suke nema na rabuwa da mace, shi yakan sa a ɗaukar mata wannan matakin.

Jarabar Son Mata

Tsananin kwaɗayi ko jarabar wasu mazaje na sha’awar mata yakan sa duk wadda suka gani ta ba su sha’awa kuma suna da hali sai su ƙoƙarta auren ta. Irin wanan aure da aka yi da manufar gusar da sha’awa, da zarar an biya bukata ba abin da zai biyo baya sai rabuwa. A wannan zamanin ana saurin jan hankalin matan ne da kuɗi ko wasu abubuwan kamar mota ko gida mai kyau ko alƙawuran ƙarya da dai sauransu.

Ba Mace ‘Yanci Fiye da Kima

A wannan zamani ana samun mazan da suke ikirarin wayewa. Wannan wayewar takan ba su damar ba matansu ‘yanci fiye da kima. Akan wayi gari irin wannan mata ta riƙa yin duk abin da ta ga dama a gidan. A duk lokacin da hankalinsa ya dawo, ya yi ƙoƙarin hana ta, to sai sabuwar fitina ta ɓarke a gidan wanda takan iya kaiwa ga mutuwar aure.

Matsalolin da Suka Shafi Mata

Wannan fasalin ya mayar da hankali ne wajen tattaro matsalolin matan aure da suke haddasa mutuwar aure a al’umar Hausawa a wannan zamanin. Daga cikin waɗannan matsalolin akwai:

Rashin Kunya da Ƙarancin Tarbiyya

Yawancin yara mata a wannan zamanin sukan ɗabi’antu da rashin kunya tun kafin su shigo gidan miji. Wannan ya danganci furta maganganun rashin mutunci ga duk wanda aka ga dama ba tare da ganin girma ko kima ko matsayin mutum ba. Wasu matan suna ganin idan mace ba ta yi rashin kunya ba, ba ta waye ba (Isah, 2013). A irin wannan yanayi ba su fahimtar cewa, mu’amala a gidan miji ba ɗaya take da mu’amala a waje ko a gidan iyaye ba. Idan suka ci gaba da wannan ɗabi’a ta rashin kunya ga mutane a gidan miji to nan take aure yakan mutu, domin ba kowane gida ko kowane namiji yake haƙuri da rashin kunyar mace ba. Galibi irin wannan ɗabi’a ga matan yanzu tana aukuwa ne a sakamakon ƙarancin tarbiyya da suka samu daga iyayensu. Haka kuma akwai mummunar ɗabi’ar nuna tsananin so da ƙauna da iyaye mata suke yi wa ‘ya’yansu ta yadda duk abin da yarinya ta yi ba a ganin laifinta. Idan wannan ɗabi’a ta kai gidan miji ko wani magabaci nasa, nan da nan takan zama sanadin mutuwar aure.

Wulaƙanta Abokan Zama

Al’adar Hausawa ta yi kyakkyawar tanadi a kan yadda matan da ke auren miji ɗaya suke zama da juna ta hanyar girmamawa da mutunta juna. A al’adance akwai wata ‘yar girmamawa da ake yi wa Uwar-gida (Matar farko). Haka abin yake tafiya girma-girma har zuwa ga ta ƙarshe (amarya). A yanzu ba a yawaita samun irin wannan gimamawar daga amare zuwa ga matan auren da suka tarar kamar yadda ake samu a da. A maimakon haka sai walaƙanci da cin fuska musamman in ba a jituwa da juna. Wannan yakan sa a yi ta samun saɓani da faɗace-faɗace har aure ya mutu.

Cin Amanar Aure

A wannan zamani, akan sami yawaitar mu’amalar iskanci na matan aure da wasu mazajen na waje. Wasu matan aure sukan yi amfani da damar da suka samu na wayewa, ci gaban zamani da sakewa a gidan miji su ƙulla hulɗar iskancici da wasu mazaje ana haɗuwa ana fasiƙanci. Duk lokacin da asirin wannan cin amanar ya tonu, sai fitina ta kunno kai har auren ya rabu.

Rashin Haƙuri a kan Karyewar Arzikin Miji

Matan aure da yawa a wannan zamanin ba su yin haƙuri da karyewar arzikin miji. Wasu suna yin auren ne a dalilin arzikin da mijin ya mallaka. Idan kuma arzikin ya karye su ma sai su fice, su nemi wani mai arzikin kuma. Irin haka ya fi faruwa ne da matan da iyayensu attajirai ne ko masu tsananin kyau ko masu surar jiki mai jan hankali.

Kishi a kan Ƙarin Aure

Matan yanzu sun fi son su zauna su kaɗai daga su sai miji sai ‘ya’yansu a gida. Da zarar miji ya yi yunƙurin ƙaro wata mata, an fara fitina ke nan har maganar rabuwa ta kunno kai. Wasu matan sun fi sha’awar aurensu ya mutu da su zauna da kishiya. Wasu kuma sun fi ƙaunar mijin ya yi ta bin matan banza a waje da ya ƙaro wata.

Ɗabi’ar Sata

Wasu matan a wannan zamanin sukan auri namiji ne da niyyar arzuta kansu ko samun abin duniya. Idan suka yi rashin sa’a mijin ya ƙi sakar musu bakin aljihunsa, sai su shiga satar masa duk abin da suka gani mai amfani. Tun ana yi wa miji har a fara kaiwa ga sauran mutanen gida. Sannu a hankali abin ya kai ga maƙwabta da gidayen buki ko inda ta je baƙunta. Duk ranar da dubu ta cika ko mijin ya gaji da wannan mummunar ɗabi’ar, sai auren ya mutu.

Shiga Bokaye da Malaman Tsibbu

A wannan zamani ana samun mata da yawa da suka mayar da hankali wajen shiga bokaye ko malaman tsibbu. Akasari suna yin haka ne domin su mallake miji ko dukiyarsa ko kuma gidan, sai abin da suka ce. Duk da yake wasu sukan yi ikirarin yin nasara, amma ba a kallon mace mai wannan ɗabi’ar da daraja. A ƙarshe irin wannan aure yakan mutu.

Ƙazanta

Akwai maza da yawa da ba su sha’awar ƙazanta ko kaɗan. Idan Allah ya jarabe su da mata ƙazama, to sai zaman ya ƙi yin daɗi. Irin wannan mace za a ga ba ta damu da kulawa da tsabtar muhalli da yara da abinci da ma ita kanta ba. Tun ana haƙuri, har a wayi gari mijin ya kasa zama da ita saboda wannan mummunar ɗabi’a. Daga ƙarshe wasu mazan sukan zaɓi rabuwa da mace ƙazama.

Aikin Gwaunati da Kasuwanci.

Mata da yawa a wannan zamani musamman waɗanda suka yi karatun boko sukan so a ce suna aikin gwaunati ko wani kasuwanci ko ma su haɗa duka biyun. Zamani yakan ba irin waɗannan mata sa’a mazansu su amince da abin da suke so. Irin yadda aikin ko kasuwancin suke ɗauke wa matan hankali sai a wayi gari suna watsi da al’amurran kulawa na iyali. Irin wannan yanayi ya sha haifar da matsala ta yadda har yakan zama sanadin mutuwar aure.

Shigar Matan Aure Kafafen Sada Zumunta na Zamani

Hausawa sukan ce ‘Zamani Riga.’ Matan aure Hausawa sun tsunduma a cikin harkar sadarwa na zamani kamar Facebook da WhatsApp da Twitter da sauran su ta hanyar amfani da wayar hannu. Wannan yanayi ya zama wa wasu matan jaraba ta yadda har ya kawo musu fitintinu iri-iri a rayuwar aure. Maza da yawa sukan zargi matansu da wuce gona da iri a wajen mu’amala da waɗanda ba muharramansu ba ta hanyar amfani da waɗannan kafafe na sada zumunta na zamani. Haka kuma waɗannan kafafe suna ɗauke hankalin matan aure daga kula da yara ko mantawa da girki a kan wuta ko wasu haƙƙoƙi na zamantakewar aure. Idan lamarin ya yi ƙamari, sai aure ya mutu.

Duba Wayar Miji

Aurarraki sun sha mutuwa a wannan zamani a sakamakon fifintunun da suka taso bisa dalilan duba wayoyin mazaje ko ɗaukar wayar miji idan an kira da matan aure suke yi. Tsananin kishi ko zargi ko karanbanin son sanin abin da miji yake ciki na mu’amala da wasu a waje musamman mata, shi yakan ja wasu mata su riƙa leƙa wayoyin mazajensu. Idan suka ga abin da bai gamsar da su ba sai fitina. Haka shi ma mijin idan ba ya jin daɗin wannan ɗabi’ar to sai ta zama sanadin rabuwa.

Yawaitar Ciwon Iskoki

A yanzu mata da yawa suna haɗuwa da jarabawar iskoki su hana mace zama gidan miji. Wasu Iskokin sukan hana mace haihuwa ko haddasa husuma da miji ko mutanen gida. Wasu kuma sukan cusa wa mace matsanancin rashin lafiya ko ƙyamar zama da mijin da dai sauran fifinfinu. To idan wannan yanayi ya yi tsanani ba abin da kan biyo baya sai rabuwa.

Rashin Iya Girki

Zamani bai ba wasu iyaye sukunin samun lokaci ko yanayin koya wa ‘ya’yansu mata girki ba. An wayi gari a wannan zanamin akan kai yara mata gidan miji ba su iya girka abincin da za a ci ba. Wato har yarinya ta gama zaman gidan iyayenta, ba ta san yadda ake girki ba. Tunanin irin waɗannan mata shi ne, idan miji yana da hali, ya samo mata mai yi mata girki. In kuma ba a yi haka ba, to a rinƙa sawo dafaffen abinci a ci a gidan. In an yi rashin sa’ar da mijin bai yarda da wannan tsarin na ƙarya ba, to sai auren ya mutu.

Rashin Laƙantar Ladubban Aure ko Zama a Gidan Miji

Irin rayuwar da wasu Hausawa suke gudanarwa a yanzu na tsarin zaman bariki, yara mata da yawa sun rasa samun horo ko tarbiyar yadda ake zama a gidan miji. Ba su tashi da sanin yadda ake aikace-aikace na gida ba kamar shara da wanke-wanke da daka da sauran su. Haka kuma ba su ilmantu da ladubban yadda ake gayar da mutane a gida ba, idan gari ya waye. Ba su san ladubban zamantakewar aure ba. Irin wannan matsala takan sa auren ya sukurkuce har ya mutu idan mijin ya gaji da sakarcin mace.

Matsalolin Maza da Mata

Baya ga matsalolin maza da na mata, akwai wasu da ake samu daga duk ɓangarorin biyu. Wato mata da mata sukan yi ruwa da tsaki wajen aukuwar su, kuma su haddasa mutuwar aure a wannan zamanin. Ga wasu daga ciki:

Ƙarya a Lokacin Neman Aure

Samari da ’yanmata sukan yi wa juna ƙarya kafin a yi aure. Bayan an yi auren sai a yi ta samun matsalolin a sakamakon fahimtar cewa an gina soyayyar ne a kan ƙarya. Ire-iren ƙaryayyakin da aka fi yi sun haɗa da yanayin ƙarfin arziki, nasaba, wurin zama, aikin yi, matsayin iyaye da dai sauransu. Aure yakan yi saurin mutuwa da zarar ɗaya daga cikin ma’auratan ya fahimci an yaudare shi da ƙarya gabanin ƙulla auren.

Rashin Haihuwa

Matsalar rashin haihuwa ba sabuwar aba ba ce a tsakanin ma’aurata a al’umar Hausawa. To sai dai haƙuri da irin wannan yanayi shi ne abin da ya ƙaranta a wannan zamanin. Ma’aurata da danginsu sukan sa ran a haihu a cikin shekarar farko da yin aure. Idan aka sami akasin haka, sai a fara neman dalili. Idan matsalar ta fara ɗaukar lokaci mai tsawo to akan shiga binciken inda take, wato ta ɓangaren namiji ko ta matar. Namiji yakan fara neman aure idan ya fahimci matsalar ba daga gare shi ta fito ba. Wannan aure da zai ƙara yakan kawo taƙaddamar da za ta sa matar da ke da lalurar rashin haihuwar ta fice kafin ko bayan an yi auren. Idan kuma matsalar daga namijin ne, to ita matar takan kasa zama a irin wannan yanayi. Ƙarshenta dai sai aure ya mutu.

Shaye-shayen Miyagun Ƙwayoyi

 Maza da matan aure Hausawa a wannan zamanin sun tsunduma a kan harkar shan miyagun ƙwayoyi. Wasu ana sane za a ɗaura aure da tunanin ai auren zai iya natsar da mutum ya daina. Wasu kuma za a yi auren ba tare da mace ko mijin ko iyayensu sun san halin da wani daga cikin ma’auratan yake ciki na ɗabi’ar shaye-shaye ba (Umar 2020). Sai bayan tafiya ta fara nisa sai komai ya bayyana. A irin wannan yanayi, aure yana mutuwa saboda rashin natsuwa da shaye-shayen abokin zama.

Rashin Gamsuwa Wajen Kwanciya Tsakanin Ma’aurata

Wannan matsala ce da ake haƙuri da ita a al’umar Hausawa. Ba a ma so abin ya shiga kunnen jama’a har a ji kunya. Akan shiga neman magani idan ana ganinn matsalar rashin lafiya ce, ko kuma a haƙura idan yanayin mutum ne. To amma a wannan zamani, ma’aurata ba su cika yin haƙuri da rashin gamsuwa da juna wajen kwanciya ba. Tsoron gudun kada mace ta rinƙa bin maza a waje saboda rashin gamsuwa yakan sa miji ya saki matar. Shi kuma namiji yakan samu mafitar ƙara aure, wanda hakan yana iya jawo wata fitinar da za ta kashe auren matar da ke da matsala.

Rashin Lafiya

Rayuwar aure a wasu lokuta takan haɗu da jarabawar rashin lafiya. A da ma’aurata sukan yi haƙuri a duƙufa wajen neman magani. Duk da yake a yanzun ma ana samun masu haƙurin, amma akasarin matasa ba su iya jimirin rashin lafiyar abokan zama. Misali, ga macen da ta sami matsalar yoyon fitsari (VVF) takan fuskanci matsalar tsangwama da ƙyama daga miji. Daga ƙarshe ya rabu da ita ya yi wani auren. Haka ma abin yake ga rashin lafiyar da ke da alaƙa da cutar da ke karya garkuwar jiki (HIV/AIDS). Nan ma ma’aurata ba su haƙura da ɗorewar aure. Hasali ma akan ƙare da zargin juna.

Luwaɗi da Maɗigo

A wannan zamani, matasa maza da mata suna shiga cikin mummunar ɗabi’ar luwaɗi ga maza da kuma maɗigo ga mata. Idan aka yi rashin sa’ar daura aure da ɗaya daga cikin masu wannan ɗabi’ar (mace ko namiji), to auren yakan yi saurin mutuwa da zarar an fahimta. Gambo (2013) ya tabbatar da cewa, idan mace ta ɗabi’antu da harkar maɗigo ba yadda za a yi ta daraja aure. Al’umar Hausawa tana ƙyamar waɗannan munanan ɗabi’u ta yadda babu mai son haɗa zuri’arsa da masu yi in ba a tsakaninsu ba.

Ƙayyade Iyali

Tunanin ma’aurata a wannan zamanin yakan bambanta a kan ƙayyade yawan ‘ya’yan da za a haifa ko tsayar da haihuwa a wani lakaci. Idan aka sami irin wannan matsala yakan sa sa a ja daga kuma daga ƙarshe aure ya mutu.

Rashin haƙuri

Rashin haƙuri ga mata da maza a wannan zamani musamman masu ƙananan shekaru abu ne da ya yawaita. Ba su ladabtu da jure wa kwaramniyar aure ba. Da zarar an ɗan sami saɓani sai su harzuƙa. Ammani (2013) yana da tunanin cewa, rashin uzurin ma’aurata ga juna idan an yi kuskure shi ke haifar da rashin haƙuri. Yawaitar rashin haƙuri ga mace ko magidanci a lamarin aure, abu ne da yake haifar da saurin mutuwar aure. Daga baya kuma a yi nadamar rashin hakurin da aka yi.

Matsalolin Iyaye da Dangi da Makusanta

Bayan matsalolin da ma’aurata suke haddasawa waɗanda kan sa aure ya mutu a wannan zamanin, akwai tarin wasu da suka shafi mutanen da ke da alaƙa da auren musamman makusanta. Waɗannan sun haɗa da iyaye da dangi maza da mata da kuma sauran makusanta. Wannan fasalin zai yi bitar rawar da suke takawa.

Son Abin Duniya

A wannan zamani, son abin duniya yakan yi tasiri wajen ƙulla aure. Iyaye ko dangin mace ko namiji sukan sa ido ga abin da za su samu ko za su riƙa samu albarkacin auren da suka ƙulla a tsakanin ‘ya’yansu. Idan suka kasa cimma wannan burin sai auren ya fara sukurkucewa. Wasu iyayen idan suka aurar da ‘yarsu ga mai arziki, sukan yi mata huɗubar ta yi ƙoƙari ta tara abin duniya ta hanyar kisisina ko yaudara ga miji. Haka su ma dangin namiji talaka idan ya auri mai hali ko ‘yar mai arziki, sukan so yin amfani da wannan dama su tara abin duniya albarkacin auren. Idan hakan bai samu ba to ba za a ba auren goyon bayan da yake bukata ba. Wannan yakan iya jawo mutuwar aure.

Sa Ido ga Ma’aurata

Wasu iyayen miji ko na mata da ‘yan’uwansu ko masu “shige-da-fice” (Ammani, 2013) a wannan zamani sukan sa ido a kan duk abin da mace ko namji suke yi ko da ba a muhalli ɗaya suke zaune ba. Wannan ya saɓa wa irin zaman da ake yi a da na jin kunyar juna da kawar da kai ga abin da kowa ke aikatawa. Duk abin da mace ta yi ko miji ya yi ga matarsa suna lura. Idan bai gamshe su ba sun kama jinini ke nan. Ta haka za a yi ta yaɗa gulma da tsegumi da zuga wani sashe don ya ƙi yarda da ra’ayin ɗaya. Idan ma aka sami dama har cin fuska iyayen miji ke yi wa mata ko iyayen mata su yi wa miji. Idan irin wannan matsala ta yi yawa sai fitintinu su fara kunno kai. Auren da ke cikin irin wannan yanayi yakan mutu ne idan matar ta ƙi yin abin da ake so ko mijin ya ƙi yarda da manufofin ‘yan sa ido.

Auren Dole

Auren dole ya daɗe yana kawo illoli ga zamantakewar Hausawa. Duk da yake Hausawa sun waye, amma ana samun birbishin wannan lamari inda akan rinjayi yarinya ko yaro a tilasta musu auren waɗanda ba su so. A yanzu hakan ya fi faruwa ne a gidajen masu arziki ko idan ana son ƙulla alaƙar ta aure da mai arziki ko sarauta ko wani matsayi a al’umma. Akan sami rashin natsuwa ga duk namiji ko macen da aka yi wa auren dole. Wannan yakan jawo rashin walwala da gudanar da ibadar cikin jin daɗi da sakewa. Idan yanayin ya tsananta to sai rabuwa ta biyo baya ko da kuwa an sami zuri’a.

Matsalolin Al’uma

Yanayin da al’uma yake ciki a wannan zamani yana taimakawa wajen yawaitar mutuwar auren Hausawa. A wannan fasali, an bibiyi halayen da aure yakan shiga har ya kai ga mutuwa a sakamakon matsalolin da al’umar ta haifar.

Bambancin Ra’ayin Siyasa

A wannan zamani, ra’ayin siyasa yana shiga zukatan mutane ya yi tasiri matuƙa ta yadda har yakan shafi mu’amala da zumunci da ke tsakaninsu. Idan bambancin ra’ayin siyasa mai tsanani da shiga cikin lamarin zamantakewar aure to takan sa ya mutu. Ana samun irin wannan yanayin ne ga misali idan aka sami saɓanin ra’ayin siyasa tsakanin iyayen miji da na mata ko tsakanin miji shi kan sa da iyayen mata ko ‘yan’uwanta. Zafafan kalamai da wulaƙanci suna iya bijirowa ta yadda sukan shafi auren ya mutu ko da kuwa akwai zuri’a.

Mutuwar Magabata

A al’umar Hausawa, magabata suna taka muhimmiyar rawa wajen ɗorewar zamantakewar aure. A wasu lokutan, su ne suke assasa auren ta hanyar zaɓa wa ɗansu ko ‘yarsu miji ko mata. Bayan an yi auren kuma su yi ta shiga tsakani suna tsawatawa ko sasantawa idan an sami saɓani ko sun ga an saki hanya. To idan irin waɗannan magabata ko iyaye suka rasu, sai ma’auratan su kasa warware matsalolinsu na aure ko su kasa sauraron waɗanda suke kusa. Wannan yakan sa aure ya yi saurin mutuwa.

Bambancin Aƙidar Addini

Tsananin soyayya da ƙauna da ke shiga tsakanin mace da namji takan sa a kasa lura da duk wani abu da zai iya kawo matsala a zamantakewar aure. Sai bayan an yi aure, an zauna aka fahimci juna sai a rinƙa samun tashintashina. Bambancin aƙidar addini tsakanin miji da mata ko tsakanin miji da iyayen mata yakan iya haifar da saɓanin da jawo mutuwar aure. A wasu lokuta, sai bayan an yi auren, miji yakan tsiri wata aƙida ta addini wadda takan sa a ji ƙyamar ɗorewar zama tare da shi. Aurarraki sun sha mutuwa a wannan zamani a kan wannan dalilin. Daga cikin aƙidojin addini da akan sami matsala a tsakani akwai ɗariƙa da izala da shi’a.

Amfani da Sihiri Wajen Raba Aure

Ba tun yau ba, Hausawa suna amfani da hanyoyin sihiri wajen warware matsalolinsu ko da kuwa sakamakon abin sharri ne ga wasu. Irin wannan tunani har yanzu yana da tasiri kuma yana ɗaukar sabon salo wajen wargaza zamantarewar aure. Galibi ana amfani ne da sihiri wajen lalata auren da ba a so. Masu adawa da wannan auren kamar kishiyoyi ko waɗanda aka yi kasayya da su ba su yi nasara ba, sun fi amfani da wannan dabarar wajen raba aure. A taƙaice dai, hanyoyi ne da Bokaye ko Malaman tsibbu suke amfani da iskoki wajen raba mata da miji.

Rashin Jituwa Tsakanin Matar Uba da ‘Ya’yan Miji

A gidajen Hausawa da dama akan sami rashin jituwa a tsanin mutane daban-daban. Wanda ya fi tsananta da illa a wannnan zamanin ba kamar tsakanin matar uba da ‘ya’yan miji. Ita tana alfahari ko gadarar mata ce ga ubansu, su kuma suna ganin su ‘ya’ya ne ba bayi ko barori a gidan ba. An fi samun irin wannan matsala a gidan da uwar ‘ya’yan ta mutu ko aurenta ya ƙare, aka damƙa su a hannun matar uba. Hakan kuma yana faruwa ne a inda matar uba take nuna son rai da son zuciya wajen mu’amala da ‘ya’yan miji (waɗanda ba ita ce uwarsu ba). Haka kuma yana iya kasancewa ‘ya’yan ne suka ɗabi’antu da rashin kunya ga matar ubansu. To ko dai yaya lamarin yake kasancewa, akwai tabbacin yana kawo sanadin mutuwar aure a wannan zamani, musamman idan ba a kai zuciya nesa ba.

Kammalawa

A wannan nazarin, an yi ƙoƙarin bibiyar dalilan mutuwar aure waɗanda zamani ya assasa ko ya samar wa sabon salo a al’umar Hausawa. Waɗannan dalilai sun kasu a rukuni biyar. Rukuni na farko shi ne wanda ya shafi gefen miji ta inda aka dubi yadda maza suke zama musabbabin mutuwar aure. Rukuni na biyu ya danganci ɓangaren mata waɗanda nazarin ya gano suka fi yawa wajen haddasa rabuwar auren Hausawa a wannan zamani. Nazarin ya gano akwai matsalolin da maza da mata suka yi tarayya wajen samar da su. Sai kuma rukunin matsalolin da suke raba aure masu alaƙa da iyayen ma’aurata ko danginsu ko makusantansu. Daga ƙarshe aka kawo rukunin da ya shafi al’uma gaba ɗaya. Nazarin ya sami jimillar matsaloli arba’in. Muhimmin abin lura da wannan bita shi ne, ba waɗannan dalilai ne kaɗai suke jawo mutuwar auren Hausawa a wannan ƙarnin ba. Su ne dai wannan nazarin ya iya hangowa. Haka kuma za a iya fahimtar cewa, yawaitar waɗannan matsaloli a wannan zamanin a al’umar Hausawa ya ɗara abin da yake faruwa a sauran al’umomi musamman maƙwabta. Akwai tunanin wannan bitar za ta taimaka wajen nazarta da kuma samar da hanyoyin warware matsalar. Haƙiƙa matsalar yawaitar mutuwar aure tana da illa ga al’uma a wannan zamani musamman idan aka yi kirdadon rayuwar da za a fuskanta nan gaba kamar yawaitar fitsaranci da munanan ɗabi’u daga matasan da abin ya shafa waɗanda ake sa ran su zama mayan gobe.

Manazarta

Abdullahi, I. S. S. (2008). ”Jiya Ba Yau Ba: Waiwaye a Kan Al’adun Matakan Rayuwar Maguzawana Aure da Haihuwa da Mutuwa”. Kundin Digiri na Uku. Sakkwato: Jami’ar Usmanu Danfodiyo.

Abdullahi, M. B. (1997). “Yanayi da Tsarin Al’adun Aure a Birnin Kebbi”, Kundin Digiri na Farko (B.A. Hausa). Sakkwato: Jami’ar Usmanu Danfodiyo.

Adamu, M. (2013). “Taɓarɓarewar Al’adun Aure a Al’ummar Hausawa: Dalilansu da Hanyoyin Magance su”. A Cikin Excerpts of International Seminar on The Deterioration of Hausa Culture. Zaria: Ahmadu Bello University Press Limited.

Ammani, M. (2013). “Zamantakewar Auren Hausawa a Yau: Tsokaci a kan Wasu Matsalolin Aure da Hanyoyin Magance su”. A Cikin Excerpts of International Seminar on The Deterioration of Hausa Culture. Zaria: Ahmadu Bello University Press Limited.

Anchau, M. D. (1986). “Tasirin Zamani da Illolinsu Kan Al’adun Auren Hausawa a Lardin Zazzau, Kundin Digiri na farko (B.A. Hausa). Sakkwato: Jami’ar Sakkwato.

Elias, T. O. (1957). “Hausa Marriage” In Nigeria, A Quarterly Magazine of General Interest No 53. Lagos: Published by the Federal Government of Nigeria, Exhibition Centre, Marina.

Furniss, G. (1999). Poetry, Prose and Popular Culture in Hausa. London: Edinburgh University Press.

Gambo, R. (2013). “Lesbianism in Northern Nigeria: An Assessment of its Causes and Cataclysmic Consequences in Katsina Metropolis”. In Excerpts of International Seminar on The Deterioration of Hausa Culture. Zaria: Ahmadu Bello University Press Limited.

Gwarjo, Y. T. da wasu (2005). Aure a Jihar Katsina. Katsina: Hukumar Binciken Tarihi da Kyautata Al’adu ta Jihar Katsina.

 Ibrahim, M. S. (1985). Auren Hausawa: Gargajiya da Musulunci, Cyclostyled Edition. Zaria: Hausa Publications Centre.

Isah, S. S. (2013). “Taɓarɓarewar Kunya ga Matan Hausawa”. A Cikin Excerpts of International Seminar on The Deterioration of Hausa Culture. Zaria: Ahmadu Bello University Press Limited.

Madauci I. da wasu (1968). Hausa Customs. Zaria: Northern Nigerian Publishing Company.

Mainasara, A. (1985). “Al’adun Aure da Canje-canjensu a Katsina,” Kundin Digirin Farko (B.A. Hausa) Sakkwato: Jami’ar Sakkwato.

Umar, H. A (2020). “Matan Hausawa da Shaye-Shayen Zamani”. A Cikin Bunza, M. U. (et al) Nigeria In Search of Stability The Relevance of History, Language and Religion. Sokoto: Faculty of Arts and Islamic studies.

 

Post a Comment

0 Comments