Ticker

6/recent/ticker-posts

Wasu Daga Cikin Dabarun Rubuta Gajerun Labarai

An turo waɗannan a matsayin wani ɓangare na bita a zauren WhatsApp na Gasar Gajerun Labarai Ta ACR. Ahmad Musa Dangiwa (2024).

HANYOYIN RUBUTA GAJERUN LABARAI BISA TSARIN MUSULUNCI

Rubuta gajerun labarai bisa tsarin Musulunci yana buƙatar kulawa da wasu ƙa’idoji da suka shafi addini da al’ada.

Duk da cewa kowa da salon rubuta labarinsa,amma da wuya ka gama labarin ka ba kataɓo Adabin Addini ba,walau kai tsaye ko kuma ta hanyar jan zaren labarin ka.

Ga waɗanda su ka hau wannan salon to ga wasu hanyoyin da za a bi:

1. Fahimtar Akidar Musulunci

Aƙida da Tauhidi: Ka tabbatar da cewa labarin ka yana dacewa da ƙa’idojin aƙida da tauhidi. Kada ka rubuta labari da zai saɓawa Addinin ka na Musulunci.

2. Nuna Halaye Masu Kyau

Kyawawan Halaye: Labarin ka ya kamata ya ƙunshi koyarwa ta halaye masu kyau kamar gaskiya, adalci, haƙuri, da taimako.

Misalai na Annabawa da Sahabbai: Yi amfani da misalai daga rayuwar Annabi Muhammad (S.A.W) da Sahabbai don nuna kyawawan halaye da ɗabi'u.Wannan zai ƙawata labarin tare da janhankali.

3. Kyakkyawan Magana

Kalma Mai Dadi: Ka guji kalmomi masu ɓata zuciya ko ƙazantar harshe. Ka yi amfani da kalmomi masu kyau da za su ja hankalin mai karatu cikin alheri.

Bayani Mai Dadi: Rubutu cikin salo mai sauƙi da fahimta, wanda zai kasance mai daɗi ga mai karatu.

4. Girmamawa ga Iyaye da Malamai

Tarbiyya: Ka haɗa darussa da suka shafi girmama iyaye da malaman addini. Wannan yana daga cikin koyarwar Musulunci.

Misalai daga Alkur’ani da Hadisai: Yi amfani da nassosi daga Alkur’ani da Hadisai don tallafawa labarin ka.

Amma da sharaɗin in akwai buƙatar haka,kuma akwai in da ya dace,amma in ba bu to kada kayi.

5. Nuna Mahimmancin Imani da Ƙaddara

Tawakkali: Ka nuna yadda jaruman labarin ka suke dogaro ga Allah (SWT) a cikin rayuwarsu.

Domin duk mai burin wani abu to akwai shi da tawakkali.

Rashin Kiyayya: Ka guji nuna ƙiyayya ko ƙyashi. A maimakon haka, ka bayyana yadda imaninsu ya taimaka musu wajen fuskantar ƙalubale.

6. Nuna Daraja ga Abin da Shari’a Ta Haramta

Ƙiyayya da Ƙazanta: Ka guji labaran da za su ƙunshi ƙazanta, ko wani abu da shari’a ta haramta.

Kamar aikata shan giya,zina ko luwadi.

Tsafta da Tsari: Labarin ka ya kamata ya zama mai tsafta da tsari, kamar yadda Musulunci yake koya tsafta.

7. Addu'a da Tawassuli

Ka haɗa addu’a da tawassuli a cikin labarin ka. Wannan yana koya wa mai karatu muhimmancin addu’a da roƙon Allah.

Ƙarfafa Ruhin Addini:

 Ka ƙarfafa ruhin addini da imani a cikin labarin ka.

8. Sauraron Ra'ayin Malamai

Shawarar Malamai: Ka nemi shawara daga malamai ko masana a fannin rubutu da addini don tabbatar da cewa labarin ka yana kan hanyar da ta dace.

Karɓar Gyara: Ka karɓi gyara da shawarar da za su taimaka wajen inganta labarin ka.

9. Rikewa da Abubuwan Al’ada

Adana Al’adun Hausawa da na Musulunci: Ka ida rubuta labarin ka da wasu hanyoyi da za su taimaka wajen adana

al’adun Hausawa da na Musulunci, kamar yadda ake yin aure, suna, da sauran abubuwan al’ada.

10. Kada ka saki zaren labarin ka yai ta tafiya,ko kamo waɗansu ƙananan jigogi har ka fita ga babban jigon ka.

Misali:Kai ta bada tarihin wani abu,wanda bai da amfani ga Al'ada ko Addinin ka ballantana ma a cikin labarin.

11. Kammalawa

Kammalawa da Hikima:

 Ka tabbatar da cewa labarin ka yana da kammalawa da kuma wata hikima  mai ƙarfafawa ko wa’azi.

Da waɗannan hanyoyin ne,za ka iya rubuta gajerun labarai da za su dace da tsarin Musulunci kuma su kasance masu ƙayatarwa da amfani ga al’umma, matuƙar a wannan layin ka gina labarin ka.

Hanya a buɗe take mai tambaya ko neman ƙarin bayani gami da gyara.

Mal. Abubakar Almustapha Yar'adua (Baba Abu)

*** ***

ADADIN KALMOMI A GAJEREN LABARI

Da yake wasu suna ta ƙorafi a kan kalmomi sun ƙi ba su haɗin kai wajen kammaluwar labarinsu, yana da kyau mu sake lura da wani abu.

Tabbas adadin kalmomi su ne suka fi muhimmanci wajen bambance gajeren labari da dogo. Sannan kuma bin ƙa'idojin gasa suna da muhimmanci wajen kai wa ga nasara a kowace gasa. Don haka sai a kiyaye.

Abin da marubuta za su yi a irin wannan yanayi shi ne, idan labarin bai ƙare ba, kuma an ƙure adadin kalmomin, to sai a cigaba da rubutun har sai an gama.

Idan an gama din sai a dawo a sake karantawa, ana yi ana tsame wasu kalmomin da ba su da muhimmanci, ana rage tsayin jimlolin. Misali,

Yanayin da ta shiga a wannan lokacin da abin ya faru, ya matuƙar tayar mata da hankali ƙwarai da gaske

Idan an lura, wannan jimla ce mai adadin kalmomi 20. Amma za a iya rage adadin kalmomin su koma 12 ba tare da ma'anar ta sauya ba:

Yanayin da ta shiga a lokacin, ya matuƙar tayar mata da hankali

Za ma su iya komawa kalmomi 10 kamar haka:

Lokacin da abin ya faru ta shiga tsananin tashin hankali

Na tabbata idan aka bi wannan dabarar, cikin sauƙi kalmomi dubu biyar za su iya komawa dubu huɗu ko ƙasa da haka.

Sai dai a kiyaye kada garin neman gira a rasa ido. Wato kada a rage wa labarin armashi a ƙoƙarin taƙaita kalmomin. Kada kuma a yarda zaren labarin ya tsinke ko saƙonsa ya sauya fasalin harsashin da aka aza shi.

Mal. Mujahid Abdullahi

Gasar Rubutattun Gajerun Labaran Hausa Ta ARC. Ahmad Musa Dangiwa Literary Foundation

Post a Comment

0 Comments