Ticker

6/recent/ticker-posts

Allah Sarki Sayyidina Usmanu (RA): Sahabi Mai Kunya Kuma Khalifa Mai Hakuri!

Imamul Bukhari ya ruwaito hadisi daga Usman bn Mauhab ya ce:

جاء رجل من أهل مصر حج البيت، فرأى قوما جلوسا، فقال: من هؤلاء القوم؟ فقالوا هؤلاء قريش، قال: فمن الشيخ فيهم؟ قالوا: عبد الله بن عمر، قال: يا ابن عمر، إني سائلك عن شيء فحدثني، هل تعلم أن عثمان فر يوم أحد؟ قال: نعم، قال: تعلم أنه تغيب عن بدر ولم يشهد؟ قال: نعم، قال: تعلم أنه تغيب عن بيعة الرضوان فلم يشهدها؟ قال: نعم، قال: الله أكبر، قال: ابن عمر: تعال أبين لك، أما فراره يوم أحد، فأشهد أن الله عفا عنه وغفر له، وأما تغيبه عن بدر فإنه كانت تحته بنت رسول الله صلى الله عليه وسلم، وكانت مريضة، فقال له رسول الله صلى الله عليه وسلم: «إن لك أجر رجل ممن شهد بدرا، وسهمه» وأما تغيبه عن بيعة الرضوان، فلو كان أحد أعز ببطن مكة من عثمان لبعثه مكانه، فبعث رسول الله صلى الله عليه وسلم عثمان وكانت بيعة الرضوان بعد ما ذهب عثمان إلى مكة، فقال رسول الله صلى الله عليه وسلم بيده اليمنى: «هذه يد عثمان». فضرب بها على يده، فقال: «هذه لعثمان» فقال له ابن عمر اذهب بها الآن معك

صحيح البخاري (5/ 15)

"Wani mutum daga cikin mutanen Misra ya zo aikin Hajji, sai ya ga wasu mutane suna zaune, sai ya ce: Su wanene wadannan mutanen?

Sai suka ce masa wadannan Quraishawa ne.

Sai kuma ya ce: Wanene dattijon da yake cikinsu?

Sai suka ce: Abdullahi bn Umar (ra) ne.

Sai ya ce: Ya kai Dan Umar, zan tambayeka a kan wani abu, sai ka bani amsa.

Shin ka san cewa Usman (ra) ya gudu a ranar yakin Uhudu?

Sai ya ce: Eh na'am.

Sai ya ce: Shin ka san ba ya nan a yakin Badar bai halarceta ba?

Sai ya ce: Eh, na'am.

Sai ya ce: Shin ka san ba ya nan a Bai'ar Ridhwan bai halarceta ba?

Sai ya ce: Eh na'am.

Sai mutumin ya yi kabbara ya ce: Allahu Akbar!

Sai Ibnu Umar (ra) ya ce: zo, zo, kar ka tafi, zo in yi maka bayani.

Amma guduwan da ya yi a ranar Uhudu, na shaida Allah ya yi masa afuwa, kuma ya gafarta masa.

Amma rashin halartansa ga yakin Badar lallai 'yar Manzon Allah (saw) ce ta kasance a karkashinsa (matarsa), sai ta kasance ba ta da lafiya, sai Manzon Allah ya ce masa:

"Lallai kana da ladan mutumin da ya halarci Badar da kasonsa (a rabon ganima)".

Amma rashin halartansa ga Bai'ar Ridhwan kuwa, da ace akwai wani mutum da ya fi izza wanda kabilun Makka suke ganin girmansa fiye da Usmanu (ra) da Annabi (saw) ya aika shi a maimakonsa, amma sai Manzon Allah (saw) ya aika Usmanu (ra) (saboda babu wanda ya kai Usmanu (ra) izza a cikin kabilun Makka, shi ne wanda zai shiga Makka ya fito ba tare da an taba shi ba), to Bai'ar Ridhwan kuwa ta kasance ne bayan Usmanu (ra) ya tafi Makka, sai Manzon Allah (saw) ya ce da hanunsa na dama:

"Wannan hanun Usmanu ne", sai ya buga shi a hanunsa (na hagu), sai ya ce: "Wannar (Bai'ar) ta Usmanu ce)".

Sai Ibnu Umar (ra) ya ce wa mutumin: Yanzu kam tafi da wadannan bayanan a tare da kai".

Abin lura:

1- Afuwa da gafaran da Abdullahi bn Umar (ra) yake nufin Allah ya yi wa Usmanu (ra) a kan guduwa da ya yi a ranar yakin Uhudu shi ne wanda ya zo a cikin fadin Allah (T):

{إِنَّ الَّذِينَ تَوَلَّوْا مِنْكُمْ يَوْمَ الْتَقَى الْجَمْعَانِ إِنَّمَا اسْتَزَلَّهُمُ الشَّيْطَانُ بِبَعْضِ مَا كَسَبُوا وَلَقَدْ عَفَا اللَّهُ عَنْهُمْ إِنَّ اللَّهَ غَفُورٌ حَلِيمٌ } [آل عمران: 155]

"Lallai wadanda suka juya baya (guduwa) daga cikinku a ranar da rundunoni guda biyu suka hadu, lallai Shedan ne ya zamar da su ga aikata kuskure, saboda wani abu da suka aikata na laifi, hakika Allah ya yi musu afuwa, lallai Allah mai yawan gafara da hakuri ne".

2- A karshe Ibnu Umar (ra) ya ce wa mutumin:

"Yanzu kam tafi da wadannan bayanan a tare da kai".

Ibnu Hajar ya ce:

اقرن هذا العذر بالجواب حتى لا يبقى لك فيما أجبتك به حجة على ما كنت تعتقده من غيبة عثمان

فتح الباري لابن حجر (7/ 59)

"Ma'ana; Ka hada wannan uzurin da na yi maka bayani da amsar da na baka a farko, don kar ka samu wata hujja a amsar da na baka a kan aqidarka ta aibanta Usmanu (ra) don rashin halartansa ga yakukuwan Annabi (saw)".

3- Bayan Ibnu Umar (ra) ya amsa wa mutumin da "na'am" a kan dukkan tambayoyinsa guda uku, sai mutumin ya yi kabbara ya ce: Allahu Akbar!

Wannan shi yake nuna duk mai bin son zuciya da kakale - kakalen laifukan mutane ba ya neman bayani a kan abin da ya ji na kuskuren mutum bare kuma ya yi masa uzuri.

Allah Sarki Sayyidina Usmanu (RA): Sahabi Mai Kunya Kuma Khalifa Mai Hakuri!

✍️ Dr. Aliyu Muh’d Sani (H)

Daga zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

Post a Comment

0 Comments