Ticker

6/recent/ticker-posts

Siffofin Gajerun Labarai

An turo waɗannan a matsayin wani ɓangare na bita a zauren WhatsApp na Gasar Gajerun Labarai Ta ACR. Ahmad Musa Dangiwa (2024).

SIFFOFIN GAJERUN LABARAI

An daɗe ana gina labaran Hausa a siffar dogayen labarai, kuma kowane labari yakan zo da wasu sigogi masu kamanceceniya da juna ta fuskar jigo(saƙo) da salo da zubi da tsari. Sai dai wani abin lura shi ne, gajeren labari a karan kansa salo ne, saƙo ne kuma tsari ne. Shi ya sa abubuwa huɗu suke da muhimmanci ga mai rubutun gajeren labari da kuma manazarcinsa. Waɗannan batutuwa kuwa su ne:

1. Gajarta ko Taƙaituwa

Gajarta ita ce siffa ta farko kuma mafi muhimmanci da ta bambanta gajeren labari da dogo. Gajeren labari, labari ne wanda za a iya bayarwa ko karantawa a zama ɗaya. Gajartar tana kasancewa ne saboda taƙaitattun kalmomin da aka gina gajeren labarin da su, da kuma taƙaita taurari. Galibi an fi gina gajerun labarai ƙunshe da taƙaitattun taurari. Wani lokacin ma tauraro guda ɗaya, cikin kalmomin da ba su gaza dubu ɗaya (1,000) ba, kuma ba su wuce dubu bakwai da ɗari biyar (7,500) ba. Ana kuma la’akari da zaɓen suna, wato kamar yadda labarin yake gajere, sunan labarin ma ya kasance gajere, ƙunshe da kalmomi masu jan hankali da ba su wuce biyu ko uku zuwa biyar ba. Ke nan, abubuwa uku ne suke fayyace wannan sigar, wato taurari da adadin kalmomi da sunan labari.

2. Daidaituwa

Daidaituwa siga ce ta gajerun labarai wadda take nuna yadda aka tsara labarin tun daga farko zuwa ƙololuwarsa. Yawanci gajerun labarai suna da sassauƙan zubi da tsari, saboda ba su da tsawo sosai, kuma ba su da babi-babi ko yanki-yanki, sai dai kawai taƙaita bayanai zuwa ɓangarori ɗaya ko biyu zuwa uku. Sannan kuma, wuri da taurari da sauransu, dole ne su tafi cikin jituwa da saƙo a ginin gajerun labarai.

3. Saƙo

Duk gajeren labari yana ƙunshe da wani saƙon da yake son isarwa. Shi ya sa gajerun labarai sukan ƙunshi batutuwa na gaskiya ko abin da ke zuciyar marubucin ko ƙirƙirarrun batutuwa ko kuma gamaɗen waɗannan batutuwan. Sai dai, ba wai abubuwan da suka faru a cikin ƙunshiyar labarin suke da muhimmanci ba, aa, saƙon da marubucin gajeren labarin yake so ya isar ga masu karatu.

4. Riƙe mai Karatu

A nan, ana duba yadda aka riƙe mai karatu ne ta hanyar gina labarin cikin hawa mai jan hankali wadda take sanya mai karatu cikin shauƙin me zai faru ne a ƙarshe? A gajerun labarai, ana warware ƙulli cikin sauri wasu lokutan kuma a ƙare shi a buɗe, a bar mai karatu da yanke hukunci. Saboda haka, a wasu gajerun labaran, saƙo mai muhimmanci ma bai fitowa sai a sakin layin ƙarshe na labarin, wato a rufewar labarin.

Mal. Mujahid Abdullahi

Gasar Rubutattun Gajerun Labaran Hausa Ta ARC. Ahmad Musa Dangiwa Literary Foundation

Post a Comment

0 Comments