Ticker

6/recent/ticker-posts

Harshe Makamin Siyasa: Nazarin Yabo da Suka Cikin Wakokin Siyasa

Citation: Yusuf, J. (2024). Harshe Makamin Siyasa: Nazarin Yabo da Suka cikin Waƙoƙin Siyasa. Ginshiƙin Nazarin Salon Waƙoƙin Hausa, 567-575. www.doi.org/10.36349/djhs.2024.v03i01.070.

Harshe Makamin Siyasa: Nazarin Yabo da Suka Cikin Waƙoƙin Siyasa

Jibril Yusuf
Department of Nigerian Languages and Linguistics
Kaduna State University, Kaduna
Phone no: +2347030399995
Email: jibreelzango@gmail.com

Tsakure: Harshe yana ɗaya daga cikin tarin baiwar da Allah (S.W.T) ya hore wa ɗan Adam, wanda ake amfani da shi wajen sadarwa musamman ta hanyar yin magana ko waƙa ko hira da dai sauransu. Harshe yana daga cikin muhimman abubuwan da ake amfani da su a fagen siyasa, wanda hakan yakan taimaka wurin samun nasara ko akasin haka. Mawaƙan siyasa da dama sukan yi amfani da irin baiwar da Allah ya ba su na iya sarrafa kalmomi a waƙe wajen yabon jamiyyarsu ko yayanta, domin ɗaga su da tallata su ga sauran jama’a. Haka kuma da irin wannan baiwar ce suke amfani wajen sukar ‘yan adawa da jam’iyyar adawar domin dusashe haskensu. Wannan takarda ta yi nazarin yadda ake amfani da waƙoƙin siyasa wajen yabon jamiyya da shugabanninta da kuma ƙoƙarin daƙushe hasken jamiyyar adawa da magoya bayanta. A ƙarshe binciken ya gano cewa harshe wani ginshiƙi ne wajen tafiyar da alamuran siyasa domin da shi ne ake tallata jam’iyya ko ɗan takara har su karɓu ga jama’a, kuma da shi ne ake kushe su ta hanyar suka wanda hakan kan rage musu farin jini ko ya janyo su rasa magoya baya. A cikin nazarin an riƙa kawo misalai daga baitocin waƙoƙin siyasa domin kafa hujja.

Fitilun Kalmomi: Harshe, Siyasa, Yabo, Suka da Waƙa

Gabatarwa

Nazari da bincike a kan waƙoƙin siyasa ba sabon abu ne ba a fagen nazarin Hausa, musamman idan aka yi la’akari da irin rawar da masana da manazarta suka taka wajen fito da muhimman abubuwan da waɗannan waƙoƙi suka ƙunsa. Masana irin su Hiskett, (1975) da) Birniwa, (1987) da Funtua, (2003) da Ɗangulbi, (2003 da 2016) da Ɗan’illela, (2010) da Sani, (2012) sun yi waɗannan nazarce-nazarce ne ta la’akari da yadda marubuta waƙoƙin suka baje kolin basirarsu ta hanyar jeranta zance cikin hikima da basira wanda suka kira shi zubi da tsari da kuma nazarin harshen waƙa, wato salo, sai kuma nazarin irin saƙon da mawaƙi ke son isarwa ga al’umma, wanda a harshen nazari aka kira shi jigo. Sai Idris, (2016) wanda ya yi nazarin bijirewa a waƙoƙin siyasa da  Yusuf, (2018) wanda shi ya dubi abin da ya shafi tarihin wata jam’iyyar ne a cikin waƙoƙin siyasa.

A cikin wannan nazari za a dubi yadda mawaƙan siyasa suke amfani da harshensu wajen yabon ko dai jam’iyya ko shugabanninta ko kuma ‘yan takaranta domin fito da su da tallata su ga jama’a don neman goyon bayansu. Da kuma yadda mawaƙan a wasu lokuta kan yi amfani da harshen nasu wajen sukar ‘yan adawa ta hanyar kushe su don jama’a su ƙaurace musu, don dai su tabbatar ba su samu wani tagomashi ba. Za a yi wannan nazari ne ta hanyar kawo misalai daga wasu baitocin waƙoƙin siyasa.       

2.0 Tsakanin Harshe Da Siyasa

Harshe yana ɗaya daga cikin ɗimbin baiwar da Allah ya hore wa ɗan Adam. Yana daga cikin manyan abubuwan da suka bambanta shi da dabba.  Masana sun bayyana cewa harshe ba shi da wata gamammiyar ma’ana ta bai ɗaya, sai dai harshe wata ɗabi’a ce wadda tun fil azal ɗan Adam kan samu ta haihuwa da koyo a dalilin cuɗanya da masu harshen (Ɗangulbi, 2016: 185).

A ganin Crystal (1987: 19) harshe wani abu ne ko alamomi da ake magana ko rubutawa da manufar isar da saƙo. Harshe shi ne ke bayyana matsayin kowace al’umma ta duniya, al’adunsu da muhallansu. Haka kuma, harshe shi ke tsara wa kowace al’umma hanyar da take gudanar da tunaninta da kuma tantance matsayi da darajar kowace al’umma a duniya.

Dangane da kalmar siyasa kuwa Balarabiyar kalma ce, asali ta samu ne daga kalmar Larabci “saasa”, amma saboda ƙa’idar tasarifi ta nahawun Larabci sai kalmar ta koma “siyaasa”, wadda ke nufin juyawa a kan wani lamari ko kuma yarda da wani ko jiɓintar al’amarin al’umma tare da saninsu ko ba tare da saninsu ba. Dar-Elmashreq a cikin Idris, (2016:49).

Ƙamusun Almunjid Wasiɗ a cikin Idris, (2016:47) ya bai wa siyasa ma’anoni guda biyu. Ma’ana ta farko ya bayyana siyasa da cewa ingantar da al’umma da shiryar da su zuwa ga tafarkin tsira. Ma’ana ta biyu kuwa cewa ya yi, siyasa na nufin gudanar da fannin mulki da ayyukan ƙasa a cikin ƙasar ko a wajenta, inda ta haka ne ake samun siyasar cikin gida da ta ƙasashen waje.

Shi kuwa Idris, (2016:49) ya bayyana siyasa da cewa hanya ce ta tafiyar da mulkin jama’a a zamanance ko a gargajiyance. Ko kuma dabara ce ta jawo hankalin mutane ta hanyar karkata ta inda suka sa gaba a kowane fage. Misali idan ɗan siyasa ya lura da abin da mutane suka fi so, to shi ma sai ya karkata ta can ko da kuwa da gaske har cikin zuciyarsa ba yana nufin hakan ne ba. A cewar Idris, (2016:49) idan aka yi la’akari da waɗannan halaye na ‘yan siyasa za a iya cewa duk wanda ya iya shan kan mutane, da lallaɓa su da iya jan ra’ayinsu ko da kuwa ta hanyar yaudara ce za a iya cewa ya iya siyasa.

Ta la’akari da waɗannan ma’anoni da bayanai da aka kawo, an lura cewa dangantakar harshe da siyasa tamkar irin ta hanta da jini ce, domin kuwa an nuna cewa siyasa tana buƙatar tausasawa, da iya magana da jan hankali da iya amfani da kalamai na jan hankali da dai sauransu. Ke nan za a iya cewa siyasa ba za ta yiwu ba in ba tare da harshe ba.

3.0 Matsayin Waƙa A Siyasa.

Waƙa aba ce da fasihai suke amfani da ita domin isar da wata manufa cikin sauri ga jama’a. Waƙa ta fi saurin karɓuwa ga jama’a fiye da wa’azi, wannan ne ma ya sa yawan ayyukan malaman jihadi waƙoƙi ne, (Adamu, 2015:128). Samuwar waƙoƙin Hausa na siyasa abu ne mai daɗaɗɗen tarihi wanda aka nuna cewa sun fara samuwa tun lokaci mai tsawo bayan bayyanar addinin Musulunci a ƙasar Hausa, inda aka samu rubuce-rubuce na waƙoƙi da suka shafi sarakunan Musulunci a cikin littattafan adabin Larabci, (Hiskett, 1975:92). Haka kuma a ƙasar Hausa an samu waƙoƙin Hausa na siyasa da dama waɗanda aka rubuta tun a wuraren ƙarni na 19, waɗanda aka alaƙanta su da Shaihu Usmanu Ɗanfodiyo da almajiransa. Waɗannan bayin Allah sun rubuta waƙoƙi game da yadda sarakunan Haɓe suke tafiyar da mulkinsu a ƙasar Hausa. Sun rubuta waƙoƙi daban-daban waɗanda suke ɗauke da bayani kan irin tsarin mulkin da Musulunci ya zo da shi. Ga misali, waƙar Abdullahin Gwandu mai suna “Tsarin Mulki Na Musulunci.” Yawancin waɗannan waƙoƙi da ake kira waƙoƙin masu jihadi suna ƙunshe ne da bayanai kan yadda za a gudanar da mulki bisa adalci. (Ɗangulbi, 2003:81-82).

Bayan zuwan Turawan mulkin mallaka a ƙarni na ashirin, an samu sabon tsarin siyasa wanda Turawan suka zo da shi, inda daga ciki aka samu siyasar jam’iyyu waɗanda aka kakkafa domin gudanar da zaɓuɓɓuka ƙarƙashinsu. An samu marubuta da dama waɗanda suka rubuta waƙoƙi domin faɗakarwa ga jama’a, game da muhimmancin shiga harkokin siyasa da jam’iyyar da ta dace.

 ‘Yan kishin ƙasa waɗanda suka samu ilimin zamani su ne suka yi hoɓɓasa wajen ganin an samu ‘yancin kai, wanda bayan samuwar hakan kuma su ne suka zama jagororin siyasar jam’iyyun da aka kafa. Bugu da ƙari kuma, wasu daga cikinsu ne suka rubuta waƙoƙin siyasa tun a karon fari. Misali; Malam Sa’adu Zungur ya rubuta waƙoƙi, daga ciki akwai, “Arewa Jumhuriya ko Mulukiya” wadda ba waƙar siyasar jam’iyya ba ce. Daga bisani, sai ya rubuta Waƙar “Jihadin Neman Sawaba” wadda waƙar siyasar jam’iyya ce, a matsayinsa na ɗan jam’iyyar NEPU wanda yake yin tir da ‘yan jam’iyyar NPC mai mulki. Shi ma Mudi Sipikin ya rubuta waƙar “Arewa Jumhuriya Kawai” wadda ba ta shafi wata jam’iyya ba, amma daga bisani bayan kafa jam’iyyu, ya rubuta waƙoƙin siyasar jam’iyyu musamman ma na jam’iyyar NPC. Mawaƙa irin su Gambo Hawaja Jos da Aƙilu Aliyu da Lawal Maiturare da Yusuf Kantu da sauransu duk sun rubuta waƙoƙin siyasa a wannan lokaci waɗanda kusan za a iya cewa, su ne mabuɗin samuwar waƙoƙin siyasar jam’iyya a Arewacin Nijeriya. (Ɗangulbi, 2003:84). An kuma ci gaba da rubuta waƙoƙin siyasa har zuwa wannan zamanin siyasa da muke ciki.

Idan aka duba za a ga cewa waƙa tana taka muhimmiyar rawa a siyasa, domin kusan ma a iya cewa ta zama gishiri in ba kai ba miya, kasancewar kusan duk jam’iyyun siyasa a yanzu suna da waƙoƙinsu, haka ma ‘yan takara da shugabannin jam’iyyu duk akan yi musu waƙoƙi domin tallata su.

4.0 Yabo A Waƙoƙin Siyasa

Kalmar yabo na nufin faɗar wata kalma mai daɗi ga wani abu ko wani mutum da ya aikata wani kyakkyawan abu. Yabo a waƙoƙin siyasa ya shafi yadda mawaƙan siyasa suke faɗin abubuwan alherin wasu ‘yan siyasa ko jam’iyyarsu da shugabanninta. Mafi yawan mawaƙan siyasa sun fi amfani da yabo a cikin waƙoƙinsu, domin da yabon ne ake fito da irin abubuwan alherin da jam’iyya ko ɗan takara ko shugabannin jam’iyya ke da shi, wanda zai sa jama’a su gamsu da su zaɓe su. A wannan nazari an raba yabo a waƙoƙin siyasa zuwa gida uku kamar haka:

-                      Yabon Jam’iyya

-                      Yabon shugabannin jam’iyya.

-                      Yabon ‘yan takara.

4.1 Yabon Jam’iyya

A nan mawaƙi kan mayar da hankali ne kacokam wajen yabon jam’iyyar da yake waƙewa, ta hanyar fito da manufofi da tsare-tsaren jam’iyyar, wanda idan har ta kai ga lashe zaɓe al’umma za su amfana. Dubi abin da wani mawaƙi yake cewa wajen yabon jam’iyyar ‘Peoples Democratic Party’ (PDP):

 

Jam’iyya masoyan Allah ka zo al’umma ga ta,

Jam’iyya a kan manufar alheri ta yi tsarinta,

Jam’iyyar da babu ruwanta da zaluncin mazalunta,

PDP farar aniya ta zo domin mazanmu da mata.

(Shu’aibu Idris ‘Yammedi; waƙar Bakandamiya).

A wannan baitin, mawaƙin ya yabi jam’iyyar da yake waƙewa ne, inda yake nuna cewa, ai jam’iyyar ta masoyan Allah (mutanen kirki) ce, kuma tana da manufofi da tsare-tsare waɗanda ta shirya su domin jin daɗin al’ummar ƙasa baki ɗaya, don haka mawaƙin ya nuna cewa, aniyar jam’iyyar fara ce tas, babu niyyar zalunci a tare da ita. Don haka ya kamata ‘yan ƙasa su fito su rungume ta domin kuwa da manufar alheri ta zo.

Haka kuma, a wurin yabon jam’iyyar mawaƙan kan nuna irin kyawawan manufofin da jam’iyya take da su ga al’umma, wanda za ta yi ƙoƙarin samar musu idan suka zaɓe ta. Misali;

Aƙidarmu ta kyautata wa mutane,

Ya sa ‘yanci har ta karɓu sosai ga mutane,

Idan ba ita jam’iyyar ƙasar duk matsala ne,

A yau mun muku tanadin ta kowa ya riƙe ta.

(Haruna Aliyu Ningi; waƙar Iyata Sarauniya)

A nan mawaƙin ya tallata jam’iyyarsa ne da cewa, aƙidar jam’iyyar PDP ce kyautatawa ga kowa. Wannan ya sa jam’iyyar take da manufar samar da, yanci ga kowa domin samun kyautatuwar rayuwa da kuma kauce wa matsalolin rayuwa, wanda mawaƙin ya ce jam’iyyar ta yi wa ‘yan ƙasa tanadin wannan ‘yancin. Har ma ya nuna cewa idan ba wannan jam’iyyar jama’a suka zaɓa ba, to fa ba za a rabu da matsala ba.

4.2 Yabon Shugabannin Jam’iyya.

Kamar yadda mawaƙa kan yabi jam’iyyarsu don samun tagomashi, haka ma sukan fito da shugabannin jam’iyyar su yabe su, su nuna wa duniya cewa shugabanninsu nagartattu ne waɗanda za su iya kai jam’iyya da al’umma ga tudun mun tsira. Mawaƙa kan yabi shugabanni ne ta hanyar  nuna wa mutane alherinsu, da ƙwarewarsu wajen sanin makamar mulki da shugabanci da adalcinsu da dai sauran abubuwan yabo. Misali, dubi abin da wani mawaƙi yake cewa:

Ya jama’a ku zo ga gwanin da ake tunani,

Mai son jam’iyya magani mai warke rauni,

Mai ɗimbin basira gwanin zurfin tunani,

Shi ne Audu Ogbeh ya zam nashinal ciyaman.

(Haruna Aliyu Ningi; waƙar Audu Ogbeh National Chairman)

A nan mawaƙin ya nuna shugaban jam’iyyar PDP a matsayin gwani wanda ke da ƙwarewa a fagen shugabanci, sannan kuma yana da son jama’a, kuma zai iya share musu kukansu, kasancewarsa mutum mai basira da zurfin tunani.

Haka kuma a wasu baitoci Dauda Kahutu Rarara ya yabi shugaban jam’iyyar APC ta hanyar nuna cewa shi ne jagora, kuma sama yake da kowa a cikin jam’iyyar. Dubi abin da ya ce:

Mun ƙara gode sarki Allah Ganduje ne uban fati,

Shugaban jam’iyya uban kowa mana kowa ya adane kati,

An ƙara gyara jam’iyya maza Isah ka ƙara yo sauti,

Kowa ya yi sahu jiran liman Baban Abba za ya ja sallah.

Ga national ciyaman ya zo kowa ya zo ya hau layi,

Ganduje shugaban jam’iyya ƙaryarku ‘yan a sha shayi,

Baba girma ya ishe girma jagoran arziƙi abin koyi,

Yau Ganduje na cikin ofis gyan-gyan babu ƙila ko ƙala.

(Dauda Kahutu Rarara Waƙar Ganduje Shugaban Party)

Idan aka dubi waɗannan baitoci za a ga cewa, yabo ne yake yi wa shugaban jam’iyyar, inda yake nuna cewa shi ne shugaban jam’iyya kuma uba ga kowane ɗan jam’iyya. A cikin baitocin ya nuna cewa, bai wa Ganduje shugabancin jam’iyyar ma gyara jam’iyyar da ƙara mata ƙima ya yi. Don haka kowa ya adana katinsa shaidarsa na zama ɗan jam’iyya kuma ya yi shirin yi wa shugaban jam’iyyar biyayya, sannan duk wasu masu ƙananan maganganu su kauce, don dai ta Allah ba tasu ba. Idan aka duba za a ga cewa wannan duk yabo ne ga shugaban jam’iyyar APC mawaƙin ya yi.

 

4.3 Yabon ‘Yan Takara

Yabon ‘yan takara ya shafi yadda mawaƙa ke faɗin wasu abubuwa masu nagarta wanda ‘yan takara suke da su, waɗanda kuma za su birge mutane har su ji sun aminta da su a matsayin waɗanda za su zaɓa su shugabance su. Da yawa waƙoƙin siyasa na wannan ƙarnin (Ƙ 21) mawaƙan sun fi mayar da hankali wajen yabon ‘yan takara saɓanin waƙoƙin ƙarni na 20 waɗanda suka fi mayar da hankali kan jam’iyya da tallata ta. Kusan ma idan aka ce duk ‘yan takara a wannan zamanin babu wanda ba a yi masa waƙar tallata shi ba, ba a yi ƙarya ba. (Yusuf, 2018:125). Yawanci mawaƙan sukan riƙa ambaton halayen kirki ga ɗan takara kamar; riƙon amana da hakuri da tausayi da son jama’a da dai sauransu ko da bay a da su. Misali, dubi abin da Dauda Kahutu Rarara ya ce;

Mun gamsu da kai Janaral domin baka mana ƙarya,

Gaskiyarka guda ɗaya ka riƙe yara ka riƙe manya,

Burinka a gyara ga wasu na juya maka baya,

Allahu guda ɗaya shi ne ke dafa maka kafi wulaƙanci.

Gaskiya da amana to wannan sai Baba Buhari,

Kowa ka gaya masa in ya taho turkenmu da ƙwari,

Bin Baba Buhari ibada ne mun gamsu da sauri,

Ku gaya musu su ma to su taho don ga mu da jirgin adalci.

(Waƙar Sai Baba Buhari  ta Dauda Kahutu Rarara).

A nan mawaƙin yana yabon halayen ɗan takararsa ne, wato Janar Buhari, inda yake nuna cewa shi mutum ne mai gaskiya, domin ba ya ƙarya, kuma in ya faɗa sai ya cika. A cikin baitukan ya nuna cewa, shi burinsa shi ne a gyara ƙasa domin ingantacciyar rayuwa. A baiti na biyu kuma, ya nuna cewa mutum ne mai riƙon amana, har mawaƙin yana ganin cewa ai bin sa ma ibada ne don gaskiya da riƙon amanarsa.

Bugu da ƙari, dubi abin da mawaƙi Garba Gashuwa ke cewa wajen yabon ɗan takarar gwamnan Kano na wancan lokaci Malam  Ibrahim Shekarau:

Ibrahim Gwamnan gaskiya,

Ya ƙi jininka marar gaskiya,

Idan ka yi Allah saka masa.

Ibrahim Gwamnan mutan Kano,

Ga mu da ɗa mai ƙaunar Kano,

Ɗan jabu ke goranta masa.

Ibrahim ba zai ƙwange ba,

Ba kuma zai so mai coge ba,

Idan ka yi Allah saka masa.

Ibrahim Allah ya tsare.

Tuntuni bai son yai kuskure, 

Idan ya yi Allah yafe masa

(Mulki Na Allah ne; Garba Gashuwa).

A nan mawaƙin yana yabon halayen ɗan takarar ne ta hanyar nuna cewa shi mai gaskiya ne, kuma babu abin da ya tsana kamar rashin gaskiya da masu aikata shi. Ya kuma nuna cewa ai shi mai ƙaunar Kano ne da mutanenta, don haka babu wanda zai ƙi shi sai “ɗan jabu” kamar yadda ya kira shi, wato wanda ba ɗan halal ba, ko kuma ba cikakken ɗan Kano ba.

A nan mun ga yadda mawaƙa ke amfani da harshe wajen yabon gwanayensu a siyasance domin haska su don jama’a su amince da su. Bari mu ga kuma yadda suke amfani da harshen domin sukar ‘yan adawa da jam’iyyarsu.

5.0 Suka A Waƙoƙin Siyasa

Kalmar Suka a nan tana nufin faɗar wasu kalmomi marasa kyau ga wani mutum ko wasu mutane, dangane da yadda yake tafiyar da wani aiki na ƙashin kansa ko kuma na jama’a (Ɗangulbi, 2016:186). Ita wannan suka ga ‘yan siyasa tana shafar wasu abubuwa da suke gudanarwa ne cikin ayyukansu, waɗanda jama’a ba su gamsu da su ba.

5.1 Sukar Jam’iyyar Adawa.

Wannan ya shafi yadda mawaƙan siyasa suke yin amfani da harshe wajen sukar abokan adawa na jam’iyyun adawa, domin nuna wa duniya illolinsu. Wannan ne ya sa da zaran mawaƙan sun tashi yin wata waƙa ga jam’iyyarsu sai su soki jam’iyyar adawa ta hanyar ambaton gazawarta ta wani ɓangaren domin dusashe haskenta. Misali, dubi yadda Haruna Aliyu Ningi ya soki Jam’iyyar PDP a waƙarsa ta “PDP Jam’iyyar ‘Yan Boko Haram”:

PDP jam’iyyar cin hancin tsiya jam’iyyar da ke da cin rashawa ƙatuwa,

PDP jam’iyyar tashin hankali su ne masu cin amana ƙato kuwa,

Ta bar jam’iyyar mutunci ko tausayi PDP a yanzu ta koma karuwa,

Ga sake ƙa’ida da ƙin bin dokar tsiya ta maishe ƙasarmu har ta zama gurguwa,

Sha shida ta fi sha tara wannan miskila sai ta kar ƙasarmu in dai ba mu kar ta ba.

(Haruna Aliyu Ningi; Waƙar PDP Jam’iyyar ‘Yan Boko Haram).

A wannan baitin mawaƙin yana sukar jam’iyyar PDP ne da cewa, ai ita ce ƙungiyar ‘yan ta’addan Boko Haram. A cikin baitin ya soki jam’iyyar da cewa jam’iyyar cin hanci da rashawa ce. Kuma jam’iyya ce ta tashin hankali da cin amana ba kaɗan ba. Ya ci gaba da sukar jam’iyyar PDP da cewa a da ita jam’iyya ce mai mutunci, amma yanzu ta lalace. A cewar mawaƙin jam’iyyar ta saki duk ƙa’ida da dokar da aka gina ta a kai, wanda hakan gurgunta ƙasa yake yi.

Haka kuma wani mawaƙi ya soki jam’iyyar PDP kamar haka:

Jam’iyyar lema yanzu ta zubar da mutuncinta,

Birni da karkara al’ummaramu duk mun gane ta,

Ba ta da alƙibla shi ya sa muke nisantar ta,

Wannan yana cikin abin da yau ya wargaza tsarinta,

Hanya da sarƙaƙiya ina gani ba za fa na kutsa ba.

(Waƙar APP Zaɓin Kowa ta Bashir Sani Basharawa Ringim)

A nan mawaƙin ya nuna cewa an riga an fahimci cewa jam’iyyar ba ta da sauran mutunci a idon ‘yan ƙasa,  domin ba ta da alƙibla kuma hakan ne ma ya sa ta rasa tsari sai ‘yan ƙasa suka guje ta. Don haka ya soke ta da cewa ita jam’iyyar PDP tamkar hanya ce mai sarƙaƙiya da bai kamata a bi ta ba.

Bala Ibrahim Ringim a waƙarsa ta “Bakandamiya” ya soki jam’iyyar adawa ta ANPP, inda a farkon baitin ma ya nuna cewa sukar jam’iyyar zai yi. Dubi abin da ya ce:

 

 

 

ANPP a yau fa dole in ɓata ki,

Ba wani mai bin ki sai fa mai ra’ayin jaki,

Sai wanda uwa mahaifiya tai mai baki,

Yau ba mai gaskata ki kan bisa tsarinki,

In ba mai son ya ja da ikon Allah ba.

(Waƙar Bakandamiya ta Bala Ibrahim Ringim)

A cikin baitin ya nuna cewa duk wanda ya bi jam’iyyar ANPP tamkar jaki yake,wato ba shi da tunani da lissafi, kuma bai san inda kansa yake masa ciwo ba. Haka kuma babu mai bin ta sai mai bakin uwa, wato wanda mahaifiyarsa ta masa baki. Ke nan ba mutanen kirki ba ne a cikinta, wannan ya sa jam’iyyar ta rasa kyakkyawan tsari. Don haka bin jam’iyyar ma kamar ja da ikon Allah ne.

5.2 Sukar Shugabannin Jam’iyya

Mawaƙa kan soki shugabannin jam’iyyar adawa ne ta hanyar nuna gazawarsu. Sukan nuna rashin ƙwarewarsu a fili ta yadda jama’a ba za su amince su danƙa amana a hannunsu ba. Ba za su faɗi wani abin kirki nasu ba ko da kuwa suna da shi, sai dai su yi ƙoƙarin nuna kuskurensu domin al’umma su guje su. Misali, Dauda Kahutu Rarara ya ce;

A ran nan muka gane matsayin kowane ɓangare.

Shugaban jam’iyyarsu ga shi ya tafka uban kure.

Yanzu komai ya tonu talakawa sun ankare.

(Dauda Kahutu Rarara, Waƙar Zuwan Mai Malfa Kano)

Mawaƙin a nan ya nuna cewa ai shugaban Jam’iyyar PDP ya yi kuskuren da ya tona wa jam’iyyar asiri, kowa ya fahimci halin da suke ciki. Har ya nuna yadda talakawa suka gane duk irin maguɗin da jam’iyyar take yi a baya, da yadda take sayen ƙuri’u da kuɗi. Ya dai soki shugaban jam’iyyar da rashin iya aiki ne inda har ya nuna cewa ya tafka kuskure.

A wata waƙar kuma Bashir Sani Basharawa Ringim ya soki shugabannin jam’iyyar PDP ba wai ta hanyar nuna gazawarsu kaɗai ba, sai da ya nuna cewa ma su suka kashe jam’iyyarsu murus da kansu. Dubi abin da ya ce:

Mr. Audu Obe shi ya sa hannunsa ya naushe ta,

Atiku abubakar ya sa ƙafarsa ya make ta,

Sani Garka Ɗambatta ya cicciɓe ta ya ka da ta,

Sannan Musa Gwadabe ya sa wuƙa wuyanta ya yanka ta.

(Waƙar APP Zaɓin Kowa ta Bashir Sani Basharawa Ringim)

A wannan baitin mawaƙin yana sukar shugabannin jam’iyyar ne da cewa sun kashe jam’iyyar babu sauranta, a ƙoƙarinsa na nuna cewa jam’iyyar APP ce ake yayi. Ya kawo sunayen jiga-jigan jam’iyyar ya nuna irin gudummawar da kowanne ya bayar wajen kisan jam’iyyar adawa.

5.3 Sukar ‘Yan Takara

‘Yan takara su ne waɗanda suka fito neman a zaɓe su a wani matsayi don su wakilci jama’a. Sukan fita yaƙin neman zaɓe, inda sukan riƙa lallaɓar mutane da kalmomi masu daɗi haɗe da alƙawuran da zai ja hankalin masu zaɓe su zaɓe su. Mawaƙa kan yi amfani da waƙoƙinsu wajen sukar ‘yan takara da nuna illar zaɓensu a wani matsayi, ta hanyar kushe su da faɗin waɗansu abubuwa da ba a son jama’a su ji su, domin kawai su ɓata alaƙar su da mutane don kada su zaɓe su. Misali, dubi wannan baiti:

Wasu sun yi ginin toka sun tabbata lallai za ya baje,

Ƙoƙarinsu wajen ɓuya sun kwashi daloli za su guje,

Jama’a ku tare ku tare ɗakin ɓeraye za mu baje,

Mu fatattaki PDP, APC sak sama har ƙasa.

(Dauda Kahutu Rarara, Waƙar Mai Malfa Ya Karaya).

A wannan baitin mawaƙin ya soki ‘yan takarar jam’iyyar adawa ta PDP ne da cewa, jama’a fa su lura, yanzu ba ma lashe zaɓen ne ya fi damun su ba, a’a, wurin ɓuya suke nema domin irin almundahanar da suka tafka. Inda mawaƙin ke nuna cewa a tare su kada su gudu, domin sun sace dukiyar ƙasa. Ke nan idan aka duba wannan sukar ‘yan adawa yake yi domin ya tabbatar wa al’umma da cewa ba su fa cancanta a zaɓe su ba.

Akan kuma soki ‘yan takara ta hanyar alaƙanta su da wani mummunan abu wanda al’umma suka ƙayamata ko kuma suke ganin gazawa ce ga mutum domin a nuna gazawar ‘yan takara. Alal misali, dubi baitin da ke ƙasa:

Limami jahili ba za na bi sallarka ba,

Domin bai san haƙƙi na gyaran salawati ba,

Ga ba’adiyya da ƙabli na ga fa bai san su ba,

Don haka ba zai shige gabana fa na bi shi ba.

(waƙar Bulaliya ta Bala Ibrahim Ringim)

A nan mawaƙin ya kwatanta ɗan takara da jahilin limami wanda bai san ƙabli da ba’adi ba. ke nan idan sallah ta ɓaci bai san yadda zai yi ya gyara ta ba. A nan mawaƙin ya soki ɗan takara ne da rashin cancanta, domin bai ma san makamar aiki ba, kuma idan aka samu matsala bai san yadda zai warware ta ba don ba shi da ilimin shugabanci.

A wani baitin kuma mawaƙin ya soki ɗan takarar da cewa;

Yau kai ɗan mai a ce ba zan bi ɗabi’arka ba,

Ɗan baubawa ba zan bi hanyar da ka bi ta ba,

Ko gobe ba za na taka titin da hau shi ba,

Na san fa halinka shi ya sa fa ba zan bi ka ba.

(Waƙar Bulaliya ta Bala Ibrahim Ringim)

A nan ya nuna cewa ba zai bi ɗabi’ar wannan ɗan takarar ba, domin shi ba ma cikakken Bahaushe ba ne, kuma ya san halinsa ba mai kyau ba ne, don haka ba zai haɗa hanyar da shi ba, wato ba zai zaɓe shi ba.

Dangane da bayanan da suka zo a baya za a fahimci cewa mawaƙa suna amfani da harshe wajen ɗaukaka ɗan takara, su haskaka shi ta hanyar koɗa shi da yabon kyawawan abubuwa dangane da shi. Sannan sukan yi amfani da harshe wajen kushe abokan adawa ta hanyar fito da wasu munanan abubuwa waɗanda za su sa al’umma su tsane su ta amfani da suka.

6.0 Tasirin Yabo da Suka cikin Waƙoƙin Siyasa.

Siyasa wata aba ce da ta shafi rayuwar al’umma, kuma ta yi tasiri matuƙa a zukatansu. Haka ne ma ya sa mawaƙan siyasa su ma ba a bar su a baya ba, domin su ma suna da irin wannan tasirin a cikin jininsu da rayuwarsu ta yau da kullum. Wannan tasirin ne, ya sa waƙoƙin siyasa da ma ‘yan siyasar suka zama tamkar jini da tsoka da ba a raba su. Don haka ne waƙa a ƙasar Hausa ta zama tamkar ruwan dare, sannan kuma ta zama babbar hanyar tallata jam’iyyu da shugabanni da sauran ‘yan siyasa. Ke nan, ana iya cewa, ana amfani da waƙa a matsayin wata kafa ta yaɗa manufa cikin gaggawa kamar yadda iska ke kaɗawa, ta game ko’ina cikin ƙanƙanin lokaci. Wannan na iya kasancewa babban dalilin da ya sa ‘yan siyasa suke amfani da waƙoƙi masu ɗauke da yabo da suka wajen tallata manufofinsu da kawunansu. (Adamu, 2015:127).

A ganin Funtua, (2003:48-51) waƙoƙin siyasa sun kasance tamkar zuciya ko ruhin siyasa, waɗanda idan babu su to tabbas siyasa ba za ta yi armashi sosai ba domin kuwa an rage mata karsashi matuƙa. A cewarsa, tasirin waƙa a fagen siyasa tamkar tasirin gishiri ne a cikin miya, domin kuwa waƙoƙin siyasa masu ɗauke da yabo da suka sukan sa jam’iyyu karɓuwa ƙwarai ga al’umma. Ta hanyar yabo, mawaƙan kan riƙa faɗin alherai da lagwadar da ke tattare da jam’iyya matuƙar dai alumma suka amince, suka rungume ta.

Ta fuskar suka kuwa, waƙoƙin sun yi tasiri wajen faɗakar da al’umma illolin miyagun shugabanni da salon shugabanci maras inganci, wanda hakan yakan sa al’umma su gane shugabannin da ya kamata su zaɓa da kuma waɗanda bai kamata su zaɓa ba. Wannan wayar da kai da waƙoƙi kan yi wa al’umma suke sanya har al’ummar su gane jam’iyyar da ta fi kyawawan manufofi da ingantattun tsare-tsare, da kuma nagartattun ‘yan takara waɗanda akan riƙa faɗin alherinsu ga al’umma ta hanyar waɗannan waƙoƙin.

Bugu da ƙari, waƙoƙin siyasa masu ƙunshe da yabo da suka a wannan zamani kusan su ne ƙashin bayan samun nasarar ɗan takara ko kuma rashin nasararsa, musamman idan aka dubi yadda al’umma suka rungumi waƙoƙin kuma suke sauraron su a kullum. A yanzu, musamman wannan Jumhuriya ta biyar da ake ciki, akwai alamun duk jam’iyyar da ta fi yawan waƙoƙi da mawaƙa to ana sa rai ta fi yawan mabiya, duk jam’iyyar kuwa da ta fi yawan magoya baya, to ana sa rai cewa ita ce za ta yi nasara. Tabbas! Harshen yabo da suka a waƙoƙin siyasa suna taka muhimmiyar rawa wajen samun karɓuwar ko rashin karɓuwar jam’iyyu da ‘yan takara ga jama’a.

A yau waƙoƙin siyasa masu ƙunshe da yabo da suka sun kasance tamkar ma siyasar ba ta yiwuwa sai da su, domin ko a yawon kamfe duk inda za a shiga to amon waƙoƙin ne suke fara sallama ga al’ummar wannan wuri tun kafin ma a ji abin da ya kawo su. Ke nan waƙoƙin sun zama tamkar wasu jakadu ne na ‘yan takara da ‘yan siyasa waɗanda suke wakiltarsu har a inda gangar jikinsu ba ta kai ba. Sun kuma kasance wata kafa ta tallata jam’iyyu da ‘yan takara har su sami karɓuwa ba tare da wakilan wannan jam’iyyar sun je ko da sau guda sun kai ziyarar neman goyon baya ba. Idan aka bugi ƙirji a wannan zamanin aka ce babu ɗan takarar da ba a yi masa waƙar yabo ko suka ba, to ba zai zama kuskure ba, domin kuwa su kansu ‘yan siyasar da ‘yan takarar suna ganin cewa, waƙar ta fi saurin yin tasiri fiye da duk wani jawabi da ɗan siyasa zai tsaya ya yi ga taron jama’a.

Baya ga tasirin da yabon ‘yan siyasar yakan haifar na samuwar ayyukan cigaba, suka da mawaƙan kan riƙa yi don nuna rashin amincewarsu ga wani tsari da shugaba ya kawo shi ma yana yin tasiri ƙwarai wajen kawo gyara ga lamarin shugabanci. Misali, abin da ya shafi gudanar da mulkin adalci, ta hanyar kula da ginin ƙasa, da ba da muhimmanci wajen kiwon lafiya da ilimi da tattalin arziki da sauransu.

Haka kuma idan ba a yi wa shugabanni da gwamnati adawa ta hanyar suka ba, to ba za su kula da yi wa jama’ar ƙasa ayyukan cigaba da ya kamata ba. Domin a siyasa, suka da yabo su ne gishirin siyasa musamman a mulkin dimokuraɗiyya, wanda sukan taimaka wa shugabanni su yi adalci da ayyukan gina ƙasa a lokacin da suke gudanar da mulki. Ke nan, waƙoƙin siyasar da suke fitowa da wannan salon na yabo da suka suna da tasiri ƙwarai wajen daidaituwar al’amuran shugabanci.

7.0 Sakamakon Bincike

Dangane da abin da wannan takarda ta tattauna a kai na abin da ya shafi yadda mawaƙa ke amfani da yabo da suka wajen tallata ko kushe ‘yan takara, nazarin ya gano cewa, harshe yana da matuƙar tasiri a siyasa, inda ya kasance kusan in ba tare da gudunmawarsa ba ma siyasar ba za ta yi armashi ba.

Nazarin ya gano cewa, yabo da suka a waƙoƙin siyasa suna tafiya ne kafaɗa da kafaɗa, ta yadda ɗaya ba ya tafiya sai da ɗan’uwansa. Domin kuwa duk inda za a yabi wani abu don a ɗaukaka shi akan yi amfani da nuna gazawar kishiyarsa. Don haka akan fara gudanar da ɗaya ne kafin ɗaya, wato ko dai a fara da sukar ‘yan adawa kafin a yabi wanda za a yi wa yabo. Ko kuma a fara da yabo kafin suka.  A takaice dai yabo da suka sun zama ƙashin bayan waƙoƙin siyasa. Sannan harshe ya kasance tubalin gina yabo da suka a cikin waƙoƙin, domin ta amfani da shi ne ake sarrafa kalmomin yabon da kuma na sukar.

8.0 Kammalawa

Daga bayanan da aka kawo, an nuna cewa harshe makami ne a siyasa. Domin kuwa, maimakon yin amfani da makamin da zai ji wa abokin hamayya rauni na zahiri, sai a yi amfani da kalmomi masu sosa rai da ratsa zuciya a waƙe, domin jan hankalin jama’a don su so ko su ƙi wani ɗan siyasa ko jam’iyya. Takardar ta tattauna irin tasirin da yabo da suka suke da shi a cikin waƙoƙin siyasa. Tunda farko an kawo an yi bayanin dangantakar harshe da siyasa inda aka nuna yadda harshe yake taka muhimmiyar rawa wajen isar da saƙon siyasa ga al’umma. Haka kuma an kawo bayani kan irin muhimmancin da waƙa take da shi a cikin siyasa. Daga nan kuma sai aka tsunduma cikin nazarin inda aka riƙa kawo misalai na baitocin suka da na yabo ko dai ga jam’iyya ko ‘yan siyasa ko kuma ‘yan takara.

Manazarta

Adamu, M. (2015). “Yabo Tubalin Ginin Tallata ‘Yan Takara cikin Waƙoƙin Ƙarni na Ashirin da Ɗaya: Nazari Daga Wasu Waƙoƙin Siyasar Jumhuriya ta Huɗu”. A cikin ALGAITA Journal of Current Research of Hausa Studies. Vol.1 no.(1), 2015. Shafi na 121-132.

Birniwa, H.A (1987). “Conservatism and Dissent: A Comparative Study of NPC/NPN and NEPU/PRP Hausa Political Verse from Circa 1946 tTo 1983”. Kundin digiri na Uku. Sashen Harsunan Nijeriya,. Sokoto: Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sokoto.

Crystal, D. (1987). An Encyclopedia Dictionary.

Ɗan’illela, A. (2010). “Rubutattun Waƙoƙin Siyasa: Nazari a kan Jihohin Sakkwato da Kebbi da kuma Zamfara”. Kundin Digiri na Biyu, Sashen Harsunan Nijeriya. Sokoto: Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sokoto.

Ɗangulbi, A. B. (2003). “Siyasa a Nijeriya: Gudunmawar Marubuta Waƙoƙin Siyasa na Hausa ga Kafa Dimokaraɗiyya a Jumhuriya ta Huɗu Zango na Farko”. Kundin Digiri na Biyu. Sashen Harsunan Nijeriya. Sokoto: Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sokoto.

Ɗangulbi, A. B. (2016). “Tasirin Baitocin Suka da Mai da Martani a cikin Rubutattun Waƙoƙin Siyasa a Ƙasar Hausa.” A cikin The Hausa People Language and History: Past, Present and Future. Shafi na 185-200.

Funtua A. I. (2003). “Waƙoƙin Siyasa Na Hausa A Jumhuriya ta Uku: Yanaye-Yanayensu da Sigoginsu” Kundin Digiri na Biyu. Sashen Harsunan Nijeriya,. Kano: Jami’ar Bayero, Kano.

Gashuwa, G. (B.S.). Fasahar Garba Gashuwa: Wasu Rubutattun Waƙoƙinsa Daga Ajami Zuwa Boko. Babu maɗaba’a.

Hiskett, M. (1975). A History of Hausa Islamic Verse. London: University of London SOAS, Malet Street.

Idris, Y. (2016). “Bijirewa a Waƙoƙin Siyasa: Bincike kan Waƙoƙin 1903-2015”. Kundin Digiri na uku. Sashen Harsuna da Al’adun Afirka,. Zaria: Jami’ar Ahmadu Bello, Zariya.

Sani, M. M. (2012). “Tunanin Siyasa a Waƙoƙin Malam Hassan Nakutama”. Kundin digiri na Biyu. Sokoto: Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sokoto.

Yusuf, J. (2018) “Tarihin jam’iyyar PDP a Bakin Marubuta Waƙa”. Kundin Digiri na Biyu, Sashen Harsunan Nijeriya. Sokoto: Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.

Post a Comment

0 Comments