Ticker

6/recent/ticker-posts

Baramu Hanyar Neman Arziki: Tsokaci Daga Wasu Wakokin Alhaji Musa Dankwairo

Citation: Doguwa, I.H. and Garba, S. (2024). Baramu Hanyar Neman Arziki: Tsokaci Daga Wasu Waƙoƙin Alhaji Musa Ɗanƙwairo. Ginshiƙin Nazarin Salon Waƙoƙin Hausa, 576-582. www.doi.org/10.36349/djhs.2024.v03i01.071.

Baramu Hanyar Neman Arziki: Tsokaci Daga Wasu Waƙoƙin Alhaji Musa Ɗanƙwairo

Ismaila Halilu Doguwa PhD
Kano State Ministry for Local Government
08036961436
doguwaye@gmail.com

Da

Professor Salisu Garba
Department of African Languages and Cultures
Faculty of Arts, ABU Zaria.
08036020230
Sgkargi@Yahoo.com

Tsakure: Wannan maƙala mai taken Baramu hanyar Neman Arziki: Tsokaci daga wasu waƙoƙin Alhaji Musa Ɗankwairo ta fito da tasirin sanaar baramu ne a kan sauran sana’o’i, tamkar yadda Alhaji Musa Ɗanƙwairo ya yi ishara da su a wasu waƙoƙinsa. A wannan makala an mayar da hankali ne a kan wasu daga cikin waƙoƙin Ɗankwairo waɗanda suka haɗa da: Waƙar Yan Arewa da ta Alhaji Bala Ɗan Umaru da ta Gojen Noma Ɗan Musa, wajen zaƙulo alfanun da baramu suke da shi a wajen bunƙasa tattalin arzikin alumma da ƙasar Hausa baki ɗaya. An yi amfani da ingantattun dabarun bincike waɗanda suka haɗa da ziyartar ɗakunan karatu, inda aka nazarci wasu ayyuka da aka gabatar a kan waƙoƙin Alhaji Musa Ɗankwairao. Sannan aka bibiyi ɗakin adana fasahar baka na Sashen Harsuna da Al’adun Afirka, na Jami’ar Ahmadu Bello, Zariya, da kuma sauraren MP3 da CD-CD, sannan aka zaƙulo wuraren da wannan fasihi ya ambaci tarihin waɗannan baramu da tasirinsu ga rayuwar Hausawa ta fuskar ci gaban tattalin arziki. Haka kuma, maƙalar ta gano cewa, sanaar baramu tana da tasiri a kan sanaar siminti da sarrafa ƙarfen tama da sarrafa fatu da ƙiraga da sarrafa kayan ƙyale-ƙyale da kuma sanaar gine-gine, duk sun dogara ne a kan sana’ar baramu. A ƙarshe binciken ya gano cewa, Alhaji Musa Ɗankwairo yana daga cikin shahararrun mawaƙa da suka fito da muhimmancin baramu ta fuskar haɓakawa da ci gaban tattalin arziki a ƙasar Hausa.

Fitilun Kalmomi: Baramu, Neman Arziki, Waƙoƙin Baka, Alhaji Musa Ɗanƙwairo

Gabatarwa

Sanannen abu ne cewa, dukkanin al’umma tana da irin baiwar da Allah ya yi mata wadda take alfahari da ita, musamman wajen gudanar da al’amuran rayuwa na yau da kullum. Misali, yayin da wani Allah ya ba shi dukiya, wani ilimi, wani hazaƙa, wani kuwa ƙwarewa, a wajen gudanar da rayuwa da sauransu. Kasancewar kowa da irin baiwar da yake da ita, don haka a kullum tunanin ɗan’dam, ba ya wuce na wannan baiwar da take tattare da shi, ta wajen cim ma buƙatunsa na yau da kullum. A dalilin haka ne ma yake jajircewa, wajen bijirowa da hanyoyi iri daban-daban domin cin moriyar irin wannan baiwa, domin nema wa kan sa madogarar rayuwa, musamman ta hanyar gudanar da sana’o’i. Sana’ar baramu na ɗaya daga cikin sana’o’i daɗaɗɗu da al’ummar Hausawa suke alfahari da su, musamman ta fuskar dogaro da kai a ƙasar Hausa. Hausawa sun ɗauki wannan sana’a a matsayin wata hanya ta baje kolin samar da kayayyakin amfani na yau da kullum a tsakaninsu da ma sauran al’umma baki ɗaya.

Ko shakka babu, makaɗa Alhaji Musa Ɗanƙwairo Maradun, ya yi amfani da irin hikimomin da Allah ya yi masa tare da ƙwarewa, wajen fito da wasu kalmomi da suka shafi sana’ar baramu a cikin wasu waƙoƙinsa, a matsayin wani maauni na tsara waƙoƙinsa da faɗakar da Hausawa, domin nuna matsayinsu a ƙasar Hausa da amfanin sanaar baramu a tsakanin alumma. Wannan kuma, wata hanya ce, ta fayyace muhimmancin da ke tattare da sana’ar baramu, musamman ta fuskar haifar da sana’ar dogaro da kai a tsakanin al’umma, musamman wajen samar da kayan amfani na yau da kullum ga masu gudanar da sana’ar ƙira da gini da kayan ƙyale-ƙyale na mata da na noma da sauransu. A ƙarshe, wannan maƙala, ta yi wani yunƙuri na fito da ire-iren sanaoin baramu da fayyace tasirinsu a kan wasu sanaoi na gargajiya, har da na zamani, sannan kuma da irin tasirinsu wajen haɓakawa da bunƙasa tattalin arzikin Hausawa da na ƙasa baki ɗaya.

1.2 Taƙaitaccen Tarihin Marigayi Alhaji Musa Ɗanƙwairo Maradun

An haifi Alhaji Musa Ɗanƙwairo a shekarar 1904 a Bakura cikin yankin mulki na Sakkwato. Daga baya suka yi ƙaura da mahaifinsa mai suna Usman Ɗanƙwaironga zuwa wani ƙauye da ke Birnin Қaya da ke ƙarƙashin Sarkin Ƙayan Maradun.

A wani ƙaulin kuma, an ce an haifi Alhaji Musa Ɗanƙwairo ne a Goran Namaye shekarar 1915. Mahaifinsa, Mallam Usman Ɗanƙwaironga, mutumin wani ƙauye ne da ake kira Bakura a Ɗankadu cikin jihar Sakkwato. Sannan kuma sunan mahaifiyarsa Yarnunu (Inno ‘yar Hasana) mutumiyar ƙauyen Goron Namaye ce.

A wani ƙaulin kuma, an ce an haifi Alhaji Musa Ɗanƙwairo ne a shekara ta 1909 a cikin wani ƙauye da ake kira Ɗankadu da ke ƙasar Bakura ta ƙaramar hukumar Talatar Mafara, cikin jihar Sakkwato. Alhaji Musa Ɗanƙwairo ba shi ne babba ko kuma auta a wajen mahaifinsa ba, domin kuwa yana da yayye da kuma ƙanne. Babban wansa shi ne makaɗa Abdu Kurna wanda ma shi ne ya rene shi ta fuskar kiɗa da waƙa.

Alhaji Musa Ɗanƙwairo ya samo sunansa ne, watau laƙabin Ɗanƙwairo, ta fuska biyu. Akwai masu da’awar cewa an sa masa wannan suna ne saboda zaƙin muryarsa a wurin waƙa, akwai kuma maganar cewa, ya samo sunan ne daga wani ƙanin mahaifinsa da ake kira Ƙwairo, wanda shi ma ya samo wannan suna ne saboda zaƙin muryarsa. Saboda kara irin ta Hausawa, sai ake kiran sa da Ɗanƙwairo. Shi dai Alhaji Musa Ɗanƙwairo ya yi ƙuruciyarsa ne a Birnin Ƙayan Maradun a yayin da mahaifinsa yake yi wa Sarkin Ƙayan Maradun waƙa, a matsayin Ubangidansa.

Alhaji Musa Ɗanƙwairo bai sami damar shiga makarantar allo ko ta boko ba. Amma duk da haka, mutum ne mai fasaha da kaifin basira. Sannan yana da saurin fahimta da kuma ɗauke duk wani tarihin abubuwa da yake ji daga manya.

Dangane da wurin wanda ya fara waƙa, bincike ya gano cewa Ɗanƙwairo ya koyi waƙarsa ne wajen babban wansa Abdu Kurna har ya kai ga fara cin gashin kan sa. Amma ko kusa bai koyi waƙa a wajen mahaifinsa ba, domin kuwa lokacin mahaifinsa ya tsufa har ma ya daina yawon kiɗa. A wani binciken kuwa an ce, Alhaji Musa Ɗanƙwairo ya fara koyon kiɗa da waƙa ne daga mahaifinsa tun yana ɗan shekara bakwai, sai dai a daidai wannan lokacin mahaifinsa ya tsufa, saboda haka babban wansa Abdu Kurna ya ci gaba da tafiyar da al’amuran kiɗa. Don haka lokacin da mahaifinsa ya ajiye kiɗa sai ya koma wajen babban wansa ya ci gaba da bin sa yawon kiɗa da waƙa wurare daban-daban, suna yi wa Sarakuna waƙa. (Yahaya, 1991:8-11).

Alhaji Musa Ɗanƙwairo ya fara kiɗa da waƙa ne, tun yana ƙarami lokacin da yake bin wansa Abdu Kurna suna zuwa yawon kiɗa gidajen Sarkuna, a lokacin kiɗan kanzagi yake yi, daga nan ya koma amshi. Ɗanƙwairo ya fara yin waƙoƙin noma na kan sa ne, lokacin da yake bin ƙauyuka, kuma da wannan kiɗan ya shahara.

A shekarar 1962, Musa Ɗanƙwairo ya fara waƙar Sarauta tasa ta kan sa, wanda ya fara yi wa waƙar sarauta shi ne Sardaunan Sakkwato, Alhaji Ahmadu Bello. Waƙar kuma da ya fara ita ce:

Kada Marake Giwa,

Ba a haye ma Barde,

Amadu ɗan Ibrahimu,

Ba ka ya da Gudun Arna ba”

(Ɗanƙwairo: Waƙar Sardauna).

Ɗanƙwairo ya yi masa waƙar ce a lokacin Sardauna ya kai rangadin siyasa zuwa Maradun. Alhaji Musa Ɗanƙwairo yana ɗaya daga cikin makaɗan fada kuma shi makaɗin ‘Yandoton Tsafe ne. (Ibrahim, 1986:111).

Maƙaɗa Alhaji Musa Ɗanƙwairo ya yi matan aure guda uku da yaya goma sha bakwai, maza guda goma da mata guda bakwai. Allah ya yi wa makaɗi Musa Ɗanƙwairo rasuwa ranar jumaa 13 ga watan Satumba, 1991 a gidansa da ke Gidan Kano. (Gusau, 2005:115).

2.1 Baramu a cikin waƙoƙin Alhaji Musa Ɗanƙwairo

Sana’a ginshiƙi ce ta gudanar da rayuwar kowacce alumma ta duniya. Kowacce alumma tana da hanyoyin da take bi wajen gudanar da sanaoi iri daban-daban domin kyautata rayuwarta da kuma tsare mutuncinta, a ƙasa ko a ruwa ko a tsaunuka da sauransu. Manazarta al’ada irin su Ibrahim, (1981) da Yahaya da wasu, (1992) da Almajir, (2010) da sauransu, sun haɗu a kan cewa, sana’a tsari ne na hikima da ake sarrafa albarkatun ƙasa da sauran niimomin da Allah ya yi wa ɗan’adam domin samar da muhimman abubuwan buƙata da rarraba su ga jama’a masu buƙata. Sanaoin gargajiya na Hausawa sanaoi ne da aka daɗe ana aiwatar da su a ƙasar Hausa, kuma suna da matuƙar muhimmanci ga alummar Hausawa. Sanaa alamari ne da ya shafi wani tafarkin rayuwa da mutum kan zaɓa ya rinƙa aiwatar da shi domin samun hanyar biyan buƙatun rayuwarsa. Sanaar baramu sanaa ce, da ake haƙo albarkatun ƙasa masu darajar gaske, daga ƙarƙashin ƙasa ko a ruwa ko a cikin duwatsu waɗanda suka haɗa da: tama da kanwa da zinare da hoge da farar ƙasa da ɓakuwa da kuza da sauransu. Sannan ana sarrafa baramu domin samar da kayan noma da wanzanci da fawa da kayan kwalliya na mata da yi wa gidaje ado da sauransu. Ibrahim, (2002) wanda ya kira baramu da sunan ma’adanai a cikin aikinsa, ya bayyana cewa, ma’adanai (baramu) wasu abubuwa ne da ake samu da launuka da kuma siffofi iri-iri wasu ana samun su da siffar dutse mai garai-garai, wani dutsen mai duhu, wani kuma mai sumul-sumul, kamar akwamari da hanta. Akwai kuma masu nauyi kamar azurfa, sannan kuma akwai marasa nauyi irin su farar ƙasa.

Alhaji Musa Ɗanƙwairo, makaɗi ne kuma masani na tattalin arzikin ƙasar Hausa, mai riƙo da aladun Hausawa na gargajiya da kuma faɗakarwa wajen rungumarsu da kyautata su, tamkar yadda haka ta bayyana a cikin waƙoƙinsa. Kasancewar haka ne, ta ba Ɗanƙwairo damar cusa wasu daga cikin sanaoin gargajiya na Hausawa, waɗanda suka haɗa da sana’ar baramu a cikin wasu waƙoƙinsa. A wannan maƙala an duba wasu daga cikin ɗiyan waƙoƙin Alhaji Musa Ɗanƙwairo an nazarce su, sannan an fito da wasu sana’o’in baramu da ya ambata a cikinsu tare da sharhi a kan su kamar haka:

2.2 Kuza

A National Museum Jos, (1979) an bayyana cewa, kuza tana kama da baƙar ƙasa amma ta fi ƙasa nauyi. Ba a samun ta a matakin amfani kai tsaye, har sai an sarrafa ta, ta hanyar haɗa ta da iskar gas (oɗygen) da sauran nau’o’in ma’adinai, mafi yawa ana samun kuza a matsayin dutse. A wasu wuraren kuma a kan sami kuza a cikin ruwan rafi ko yashi ko dutse ko a shimfiɗe a kan ƙasa, musamman da damina idan ruwa ya sauka.

Daga cikin waƙoƙin Alhaji Musa Ɗanƙwairo, akwai waɗanda ya ɗora su a kan haɓakawa tare da bunƙasa sanaoin gargajiya, ta hanyar tsayuwa a kan sanaa tare da ci gaban masanaantu a yankunan ƙasar Hausa.

 Makaɗin ya yi ƙoƙarin nuna wa alumma matsayin jajircewa da mai da hankali a kan kowace irin sana’a a ƙasar Hausa. Ga dai abin da yake cewa a cikin waƙar Yan Arewa:

 Jagora: Mun zama lafiya ‘yan arewa godiya ɗai mukai,

‘Y\Amshi: Allah Ya maimaita mana ga jihar arewa mai halin girma.

 Jagora: Wajen fuskar sana’a,

‘Y/Amshi: Ka ga arewa ba a tsere min ba,

Jagora: Wajen fuskar sana’a,

‘Y\ Amshi: Ka ga arewa ba a tsere min ba.

Jagora: Sakkwato akwai siminti.

: Kamfanin Abdallah Gusau,

: Akwai wurin gyaran mota,

: Abin da yai mana nisa

‘Y\Amshi: Yanzu arewa ya zan ga ya kusa

Jagora: Abin da yai mana nisa

‘Y\Amshi: Yanzu arewa ya zan ga ya kusa

Jagora: Kano ake jiman fata

: Kano ake yin tayoyi

: Kano ake yin ƙarufa irin na har da kujeri

: Kano ake yin kwanoni irin na gyaran gidaje

: Kuma Kano ake yin kwanoni irin na cin abinci

: Kano ake yin alawar lemo

‘Y\Amshi: Abubuwan jin daɗi ka ga arewa ba a tsere min ba

Jagora: Kano ake yin turare

: Abubuwan jin daɗi

‘Y\Amshi: Ka ga arewa ba a tsere min ba

Jagora: Ƙaruffan yin famfo

: Kano wurin narke kuza

Jagora: Fayafayan garmaho tin da

 ........................................

‘Y\Amshi: Abubuwan jin daɗi ka ga arewa ba a tsere min ba

Jagora: Kayan ƙyaleƙyale na ban shaawa

: Hoda da gazal da jan baki duk Zariya ake yin su

‘Y/Amshi: Abubuwan jin daɗi ka ga arewa ba a tsere min ba

(CD-CD).

Gaba gaɗi a cikin ɗiyan wannan waƙa, Alhaji Musa Ɗanƙwairo ya jero irin abubuwan da ake samarwa a kuma sarrafa a yankunan jahohin arewa, inda ya yi ishara da cewa ana narka kuza a wasu yankuna na arewacin Nijeriya, musamman ƙasar Hausa. Wannan ya tabbatar da cewa, akwai kuza a ƙasar Hausa kuma ana cinikayyarta, sannan tana ɗaya daga cikin baramun da ake alfahari da su a ƙasar Hausa. Haka kuma, tana da matuƙar tasiri wajen bunƙasa tattalin arzikin alumma, musamman a tsakanin matasa. A cikin waɗannan ɗiyan waƙa, ya nuna yadda ake sanaar siminti da sarrafa shi a yankin sakkwato da ke arewacin Nijeriya, wanda yana ɗaya daga cikin baramu da ake alfahari da su a ƙasar Hausa, musamman ta wajen samar da aikin yi tare da bunƙasa sanaar gine-gine, bayan hada-hadar cinikayyarsa. Duk da wannan matsayi na siminti ga alumma, ba don sanaar baramu ba da ba a same shi ba.

Haka kuma, ya kawo cewa, ana sana’ar gyaran mota a yankunan ƙasar Hausa, inda ya ba da misali da kamfanin Abadallah na Gusau. Wannan wani babban ci gaba ne wajen haɓaka tattalin arziki, musamman ta hanyar samar da sana’ar dogaro da kai ga matasa, misali, kanikanci, bayan hada-hadar cinikayyar motoci. Ɗanƙwairo, ya kuma bayyana ƙarfe na kujeru da kwanoni na gyaran gidaje da na cin abinci da na yin famfo, a matsayin abubuwan da ake samarwa a sarrafa su a yankunan Arewacin Nijeriya. Dukkanin waɗannan, daga karfe dangin tama ake samar da su. Sannan kuma ana amfani da kuza, a matsayin sinadarin da yake hana ƙarafa yin tsatsa bayan an samar da su. Saboda haka, ba don sanaar baramu ba, da ba a sami irin waɗannan kayayyaki ko kuma inganta su ba. Har ila yau, ya kawo tasirin baramu a ƙasar Hausa, inda a waƙar ya ambata cewa, ana yin jimar fata a garin Kano. Hakan ya nuna cewa, a Arewacin Nijeriya ana alfahari da sana’ar jima, musamman yadda ake sarrafa ta a samar da takalma da jakunkuna da sauransu. Amma duk da haka, sana’ar baramu ta yi tasiri a cikin sana’ar jima, musamman ta fuskar kayan jimar fata irin su: wuƙa da kartaji da sauransu, duk waɗannan ana samar da su ne daga ƙarfe dangin tama. Bugu da ƙari, mawaƙin ya nuna cewa, ana samun kayan ƙyale-ƙyale na ban shaawa, sannan ana samun kayan kwalliya irin su hoda da gazal da janbaki a Zariya. Waɗannan duk sun taimaka wajen samarwa tare da ci gaban sana’ar koli da makamantansu a yankunan Arewacin Nijeriya. Sannan kuma suna da alaƙa ta kusa da kaya dangin baramu da ake samu a ƙasar Hausa. Misali, ana sarrafa zinare wajen samar da kayan ƙyale-ƙyale na sarƙa da ɗankunne da zobe da sauransu. Sannan ana sarrafa koya wajen samar da hoda da gazal da janbaki da sauransu. Dukkanin waɗannan, suna taimakawa wajen samar da kayan kwalliya musamman ga mata, wanda ba don sana’ar baramu ba, da ba a same su ba. Saboda haka, samar da waɗannan abubuwa ko sarrafa su a ƙasar Hausa yana da muhimmanci ta wajen ginawa da haɓaka tattalin arziki a tsakanin al’umma da ƙasa baki ɗaya.

2.3 Farar ƙasa

Farar ƙasa, ƙasa ce fara wadda ake shafe da ita. (CNHN, 2006:134). Farar ƙasa wata ƙasa ce fara wadda ake haƙowa a ƙasa a matsayin gari ko guda-guda, idan an buge tana zama gari da ake yin fenti na shafen ɗaki ko a yi wa ƙwarya ado da ita. Sannan ana sarrafa farar ƙasa a haɗa takin zamani da ita. (Doguwa, 2023:136). Alhaji Musa Ɗanƙwairo ya waiwayi sana’ar farar ƙasa wadda take ɗaya daga cikin nau’o’in sana’o’in baramu da ake da su a yankunan ƙasar Hausa. Misali, ya kawo yadda magina suke sarrafa farar ƙasa, sannan su ƙawata ɗakuna da gidaje da ita, a cikin sana’arsu, wanda hakan, ya ƙara tabbatar da sana’ar baramu a matsayin wani tsani da yake taimakawa wajen cicciɓa sana’ar gini a ƙasar Hausa. Dubi dai abin da Alhaji Musa Ɗanƙwairo Maradun yake cewa a cikin waƙar da ya yi wa Alhaji Bala Ɗan Umaru:

 .....................................

Jagora: Wanda ba ya zaɓen kyauta,

: In kana da shi ya ba ka,

: In ba ka da shi ya ba ka.

 ‘Y/Amshi: Haka Allah ya yo halinai.

 Jagora: Kowa da wadda Allah ya yi shi,

 ‘Y/Amshi: Duniya ba a zo ta ba.

 Jagora: Wani na da gidan kwano,

: An sa siminti an gyara,

: Ga farar ƙasa duka an goge,

: Wani na da gidan laka,

(CD-CD).

A cikin ɗiyan wannan waƙa, an fahimci farar ƙasa na ɗaya daga cikin baramu da ake samu a kuma yi sana’arsu a ƙasar Hausa, don haka tana da muhimmancin gaske, musamman wajen ginawa da haɓaka tattalin arzikin al’umma da ƙasa baki ɗaya, ta hanyar haifar da sana’o’in dogaro da kai a tsakanin al’umma. Misali, masu sana’ar fenti suna amfani da farar ƙasa domin yi wa gidaje shafe (fenti), sannan ana amfani da farar ƙasa a matsayin wani sinadari da ake haɗa taki na zamani da ita, domin zuba wa amfanin gona. Haka kuma, ana inganta sana’ar gyaɗa da farar ƙasa ta hanyar amfani da ita wajen soyawa, domin ƙara mata karɓuwa wajen sayarwa. Mata masu ciki suna tauna farar ƙasa ko tsotsa a matsayin maganin tashin zuciya da sauransu. Amma duk da wannan matsayi na farar ƙasa a cikin al’umma, ba don sana’ar baramu ba, da ba a same ta ba. Saboda haka, farar ƙasa na ɗaya daga cikin sana’o’in baramu da ake alfahari da su ta wajen haɓaka tattalin arzikin al’umma da ƙasa baki ɗaya. Domin tana samar da aikin yi tare da abin dogaro da kai a tsakanin al’umma a ƙasar Hausa.

2.4 Hoge

Hoge wani ɗan ƙaramin dutse ne ko tubalin ƙasa busasshe. (CNHN, 2006:201). Hoge shi ne duk wata dunƙulalliyar ƙasa wadda sai an sara ƙasa ake samun ta kuma a dunƙule take zuwa ko kuma asalinta daga ƙasa take.

Har ila yau, a cikin waƙoƙin Alhaji Musa Ɗanƙwairo, ya waiwayi ɓangaren hoge wanda yana ɗaya daga cikin baramu da ake amfani da su wajen inganta sana’ar noma da gine-gine a ƙasar Hausa. Wannan mawaƙi, a cikin ɗiyar waƙar da ya yi wa Gojen Noma Ɗanmusa, ya kawo yadda manoma suke amfani da hoge a wajen inganta sana’ar noma, ta hanyar ɗaure (huɗa) amfanin gona da shi, wanda hakan, babban cigaba ne a sana’ar noma musamman ta fuskar haɓakawa da kawo ci gaban tattalin arzikin al’umma. Alhaji Musa Ɗanƙwairo ya ce:

 Jagora: Je ga magajin Abdu,

 Y/Amshi: Jajema na Sale gwarzon Sani.

 Jagora: Mai galmar maɗan gabas,

: Wata huɗa yakai,

: Yana kuyye manya-manya,

 Y/Amshi: Hoge ya aza shi saka-saka.

 Jagora: Mai galmar maɗan gabas,

: Wata huɗa yakai,

: Yana kuyye manya-manya.

 Y/Amshi: Hoge ya aza a shi kata-kata.

 Jagora: Mai galmar maɗan gabas,

: Wata huɗa yakai,

: Yana kuyye manya-manya,

 Y/Amshi: Hoge ya aza shi mara-mara.

(Gusau, 2009:445)

A nan Alhaji Musa Ɗanƙwairo ya yi amfani da irin ƙwarewarsa ta amfani da kalmar hoge wanda yana ɗaya daga cikin baramun da ake sarrafawa a ƙasar Hausa. Mawaƙin ya tabbatar da cewa hoge yana da matuƙar amfani ga sanaar noma domin da shi ake amfani a lokacin damina (faɗuwar ruwa) a huɗe gona a yi shuka. Haka kuma, a duk lokacin da yabanya (shuka) ta fara girma, a kan ba ta hoge ta hanyar yin safce (huɗa/ban ƙasa) domin a ƙara inganta amfanin da aka shuka, saboda ya ƙara samun kariya daga iska. Ana kuma amfani da hoge a fitar da wuriya ko ganɗo domin fitar da iyakar gona ko a kare gona daga matsalar ambaliyar ruwa ko zaizaya. Saboda haka, an gano hoge yana da matuƙar amfani wajen haɓaka sana’ar noma, wanda hakan ya taimaka wajen bunƙasa tattalin arzikin alummar ƙasar Hausa, ta fuskar noma. Haka kuma, ana amfani da hoge wajen samar da muhalli ko inganta shi a ƙasar Hausa. Misali, ana sarrafa hoge a yi amfani da shi domin samar da gidaje ko yin gyaransu (misali, yaɓe). Wannan wata babbar hanya ce ta samar da aikin yi tare da bunƙasa tattalin arziki a tsakanin alumma a ƙasar Hausa. Saboda haka, duk da matsayin hoge a wajen inganta sana’ar noma da gine-gine, ba don sana’ar baramu ba, da ba a sami hoge ba, har a kai ga sarrafa shi domin inganta sana’ar noma da samar da muhalli a tsakanin al’umma a ƙasar Hausa.

3.1 Sakamakon Bincike

A wannan bincike an gano muhimman abubuwa masu dama ta hanyar tsokaci da fasahar makaɗi Musa Ɗanƙwairo a cikin waƙoƙinsa. Daga ciki makaɗa Alhaji Musa Ɗanƙwairo Maradun ya fito da wasu daga cikin sanaoin baramu a ciki domin fayyace muhimmancinsu wajen ginawa da haɓakawa, tare da bunƙasa tattalin arziki a tsakanin al’umma da ƙasa baki ɗaya. An gano wasu ɗiyan waƙoƙi da mawaƙin ya ambaci baramu a ciki, waɗanda suka haɗa da kuza da tama da farar ƙasa da hoge. Sannan an gano irin gudunmuwar da suke bayarwa ta fuskar haɓaka tattalin arziki da ci gaban al’umma da ƙasa baki ɗaya. Haka kuma, an gano mawaƙin ya kawo wasu ɗiyan waƙoƙi da suke nuni da waɗansu abubuwa waɗanda ba don sana’ar baramu ba, ba za a same su ba. Misali: ƙarafa da kayan ƙyaleƙyale da hoda da sauransu. Har ila yau, maƙalar ta iya gano cewa, makaɗa Alhaji Musa Ɗanƙwairo na ɗaya daga cikin waɗanda suka iya zaburar da al’umma domin su farka wajen jajircewa a kan sana’o’in gargajiya musamman waɗanda suka shafi baramu a ƙasar Hausa saboda yadda ya fito da su a idon duniya.

A dunƙule, an gano cewa, idan har manazarta za su mai da hankali wajen nazartar irin waɗannan waƙoƙi tare da zaƙulo irin hikimomin da mawaƙa suke sarrafawa wajen ginawa da ɗora waƙoƙinsu, ko shakka babu ƙwalliya za ta biya kuɗin sabulu wajen gano abubuwan sana’o’i na dogaro da kai a yankunan ƙasar Hausa, tamkar yadda ya jibge su a waɗannan waƙoƙi nasa da aka nazarta.

4.1 Kammalawa

A wannan maƙala mai taken Baramu Hanyar Neman Arziki: Tsokaci Daga wasu Waƙoƙin Alhaji Musa Ɗanƙwairo. Bayan gabatarwa, tare da kawo taƙaitaccen tarihin mawaƙi, Alhaji Musa Ɗanƙwairo da kuma tarihin samuwa da haɓakar sana’o’in gargajiya, musamman sana’ar baramu, maƙalar ta ambaci wasu nauoin baramu da suke jibge a ƙasar Hausa. Sai kuma aka zayyano wasu ɗiyoyi daga cikin waƙoƙinsa,Yan Arewa da ta Bala Ɗan Umaru da ta Gojen Noma Ɗanmusa, domin fito da misalan wuraren da ya ambaci wasu daga cikin baramu a cikinsu. Bayan haka kuma, sai aka fayyace irin gudunmuwar da baramu suke bayarwa wajen samarwa da bunƙasar sauran sanaoin ƙasar Hausa tare da haɓaka tattalin arziki ga al’ummar ƙasar Hausa da kuma ƙasa baki ɗaya.

A ƙarshe sai aka ambaci kaɗan daga cikin sakamakon binciken da wannan maƙala ta gano domin jan hankalin alumma da ƙara musu ƙarfin gwiwa game da mayar da hankali wajen zaƙulo ire-iren waɗannan muhimman sana’o’i na gargajiyar Bahaushe domin cin moriyarsu da kuma rufe bakin ‘yan gaza-gani, masu ganin cewa ‘yan arewa cima-zaune ne.

Manazarta

Almajir, T.S. (2010). Hikimomin Hausa: Littafi Don Ƙananan Makarantun Sakandire na uku. Kano: Fidan Publishers.

CNHN, (2006). Ƙamusun Hausa na Jamiar Bayero. Zaria: Ahmadu Bello University Press.

Doguwa, I.H. (2023). Sana’ar Baramu da Al’adunta a ƙasar Hausa. Kundin Digiri na uku, Sashen Harsuna da Al’adun Afirka. Zariya: Jami’ar Ahmadu Bello.

Gusau, S.M. (2005). Makaɗa da Mawaƙan Hausa. Kano: Benchmark Publishers Limited.

Gusau, S.M. (2009). Diwanin Waƙoƙin Baka Zaɓaɓɓun Matanoni na Waƙoƙin Baka na Hausa. Kano: Centuary Research and Publishin Limited.

Ibrahim, B. (2002). Ma’adinai: Hanyoyin Sarrafasu da Ayyukansu a Ƙasar Hausa. Kundin Digiri na Biyu, Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya. Kano: Jamiar Bayero.

Ibrahim, M.S. (1981). Tattalin Arziƙin Hausawa na Gargajiya. Kanao: Jami’ar Bayero.

Ibrahim, R. (1986). Gudummuwar Makaɗan Fada wajen yaɗa Fannonin Addinin Musulunci. Kundin Digiri na Ɗaya, Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya. Kano: Jamiar Bayero.

National Museum, (1979). The History of Tin Mining in Nigeria. Jos: Federal Department of Antiquities.

Yahaya, D.H. (1991). Alhaji Musa Ɗanƙwairo: Makaɗin Fada ko na Jama’a. Kundin digiri na Ɗaya, Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya. Kano: Jamiar Bayero.

Yahaya, I.Y da wasu. (1992). Darussan Hausa Don Manyan Makarantun Sakandire. Ibadan: Ride Print..

Post a Comment

0 Comments