Ticker

6/recent/ticker-posts

Bibiyar Al’adun Hausawa a Littafin Gumakan Zamani na Yusuf M. Adamu

Citation: Ammani, M. (2024). Bibiyar Al’adun Hausawa a Littafin Gumakan Zamani na Yusuf M. Adamu. Ginshiƙin Nazarin Salon Waƙoƙin Hausa, 559-566. www.doi.org/10.36349/djhs.2024.v03i01.069.

Bibiyar Al’adun Hausawa a Littafin Gumakan Zamani na Yusuf M. Adamu

Muhammad Ammani
Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero, Kano
mammani.hau@buk.edu.ng
+2347063507090

Tsakure: Hausawa al’umma ce mai tsananin riƙo da aladunsu na gargajiya, musamman abubuwan da suka shafi aure da haihuwa da mutuwa da sutura da bukukuwa da sauran aladun da suka keɓance su ta fuskar zamantakewa. Manufar wannan takarda ita ce, a bibiyi wasu sassan al’adun Hausawa na gargajiya a littafin Gumakan Zamani wallafar Yusuf M. Adamu. Ta haka ne aka lalubo ɗimbin al’adu da suke ɗamfare a labarin kamar; tsarin shugabanci da sana’a da aure da cimaka da karimci da yanayin zamantakewa. An ɗora wannan bincike a bisa ra’in Gudummuwar Adabi ga Al’umma (Functional Theory), wanda yake duba yadda aikin adabi yake tafiya da al’adu na al’umma da yadda suke daɗa inganta rukunonin rayuwa. Hanyoyin tattaro bayanan wannan aiki sun haɗa da; nazartar littafin Gumakan Zamani sau da ƙafa da zimmar kalato wasu aladun Hausawa. An yi bitar ayyukan magabata masu alaƙa kamar; wallafaffun littattafai da kundayen bincike da maƙalu da sauran takardu na ilimi. Binciken lura cewa, mawallafa ƙagaggun labarai na Hausa suna amfani da hikima wajen sakaɗa hoton al’adun Hausawa a littattafansu. Ta haka ne kuma, labaran nasu suke taka muhimmiyar rawa wajen rayawa da taskace al’adun gargajiyar Bahaushe.

Fitilun Kalmomi: Ƙagaggen labari, Al’ada, Adabi, Hausawa, Gargajiya

Gabatarwa

Wanzuwar ƙagaggun labarai na Hausa wata gagarumar dama ce da ta taimaka ainun, musamman wajen fito da wasu manufofi ko saƙonni masu nusar da al’umma darussan rayuwa. Ta haka ne mawallafa da dama suke baje-kolin tunaninsu, ta hanyar yin la’akari da wani yanayi da al’umma ta kasance a ciki, sannan su shirya ƙagaggen labari wanda zai nusar da su. Bisa yawanci, akan gina labaran ne da zummar faɗakarwa, ko ilmantarwa, ko wa’azantarwa, ko kuma wani lokaci a nishaɗantar da su. Madosar wannan takarda ita ce, a nazarci littafin Gumakan Zamani ta hanyar zaƙulo wasu al’adun Hausawa daban-daban kmar zamantakewa da cimaka a yanayin karamcinsu da sauransu. Ta haka ne za a yi tsokaci a kan kowace nau’in al’ada da aka samu, sannan a kafa hujja ta hanyar tsakuro misalai daga matanin labarin domin a inganta sahihancin binciken.

2.0       Hoton Littafin Gumakan Zamani a Taƙaice

Tun asali, an samar da wannan, Gumakan Zamani a sakamakon gasar ƙagaggun labarai na Hausa da aka shirya a shekarar 1992. Amma saboda wasu dalilai da suka bijiro wa mawallafin, sai ya ajiye littafin bai shiga gasar ba. Sai a shekarar 2012 mawallafin ya yi tunanin sauya akalar labarin, daga bisani kuma sai ya bar shi kamar yadda ya ƙage shi tun farko a 1992. Don haka sai ya yi masa wasu ‘yan sauye-sauye, kuma waɗanda ba su shafi ko suka sauya matanin labarin kamar yadda yake tun asali ba[1].

Bisa manufa, an gina labarin wannan littafi ne a bisa “Tasirin kuɗi ga rayuwar al’umma/Ɗan’adam”. Littafin ya nuni tare da faɗakar da jama’a, su kiyaye mummunar ɗabi’ar nan ta mallakar dukiya a bisa ƙazamar hanya. Sannan kuma ya ƙara nusar da mutane su tashi tsaye, domin neman na kansu (dukiya) a bisa tsabtacciyar hanya ba tare da an kauce wa shari’a Musulunci ko dokar da tsarin ƙasa ta tanada ba. Haƙiƙa wannan littafi ya cancanci ƙwaƙƙwƙaran yabo ta wannan fuska.

2.1 Wane ne Mawallafin Littafin?

Mawallafin wannan littafi shi ne Farfesa Yusuf Muhammad Adamu. An haife shi ranar Alhamis, 9th ga Maris a shekarar 1968 a cikin birnin Katsina. Ya yi karatun allo da na Islamiyya, daga nan kuma ya ci gaba da ɗaukar karatun littattafai da suka danganci addini a wajen wasu malamansa. Ya yi karatun boko a Giginyu Primary School daga shekarar 1975-1980, sai Government Secondary School, Koko, a shekarar 1982, sai Government Science Secondary School, Zuru, a 1985. Ya samu digirinsa na farko a fannin labarin ƙasa (Geography) a Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo da ke Sakkwato a shekarar 1990, sai Jami’ar Ibadan, inda ya yi digiri na biyu (M.Ssc) a shekarar 1994, sai Jami’ar Bayero, Kano, inda ya samu digiri na uku (PhD) a 2003.

Ya fara aiki da Jami’ar Bayero, Kano, a shekarar 1995, a halin yanzu kuma Farfesa ne a Jami’ar ta Bayero, Kano. Ya riƙe muƙamai da dama kamar; shugaban Sashen labarin ƙasa a shekarar 2018, sai Darakta a Maɗaba’ar Jami’ar Bayero[2], Kano, daga shekarar (2015-2019). Ya shugabanci Ƙungiyar Marubuta ta Ƙasa (ANA) reshen jihar Kano har sau uku. Ya ba da gudummuwa sosai wajen ciyar da adabin Hausa a gaba, inda ya wallafa jerin littattafai da dama masu ɗauke da muhimman saƙonni daban-daban ga al’umma. Daga cikinsu akwai: Idan so Cuta ne da Ummal-Khairi da Maza Gumbar Dutse da Son Zuciya da Dukan Ruwa da sauransu.

3.0       Hausawa da Al’adunsu

Ayyukan masana da manazarta dangane da al’adun Hausawa suna da yawan gaske, don haka mawuyacin abu ne a iya ƙayyade su a cikin ƙanƙanin lokaci. A bisa wannan tafarki ne masana kamar Gusau (2010: 2) ya bayyana ma’anar al’ada kamar haka, “ita ce tafarki wanda wata al’umma take rayuwa a cikinsa angane da yanayin abinci da tufafi da muhalli da rayuwar aure a haihuwa da mutuwa da wasu hulɗoɗin rayuwa kamar maƙwabtaka da sana’oi da kasuwanci da shugabanci da bukukuwa da sauran abubuwa waɗanda suke da alaƙa da haka”.

Dangane da yanayin zamantakewar rayuwar kowace al’umma na yau da kullum kuwa, masana al’adun al’ummu daban-daban na duniya sun yarda cewa, kowace al’umma da ta wanzu a doron ƙasa tana da nata nau’in al’adun. Ta haka ne kuma take gudanar da wasu kevavvun tsare-tsare da suka shafi gaba ɗayan rayuwarsu, musamman abubuwan da suka shafi aure, ko haihuwa, ko mutuwa, ko sana’o’i, kasuwanci, ko kuma tsarin tattalin arziki da sauran makamantansu. Saboda haka ne ne Gusau (2012: 3-4) ya nuna ce, “kowace al’umma ta duniya tana da wasu al’adu waɗanda takan kevanta da su, waɗanda takan tanada wa kanta lokaci bayan lokaci, waɗanda kuma ta haka suke zama daɗaɗɗu da kuma sababbi. Irin waɗannan al’adu ne sukan zama alƙibla na al’umma waɗanda ake sanin ta da su, ake rarrabe ta da su, ake fahimtar ta da su, kuma ake kiyaye mutuncincinta da su. Haka kuma da su ne ake kaɗa wa al’umma takenta, kuma da an gano su a nuna na al’umma kaza ne.

Har wa yau kuma, Mu’azu (2006: 205-206) ya yi ƙarin haske cewa, su kuwa Hausawa mutane ne masu tsananin riƙo da al’adunsu na gargajiya, musamman abubuwa irin su tufafi da abinci da sauran al’amuran a suka shafi aure da haihuwa da mutuwa da makamantansu waɗanda suke gudana a tsakanin’yan’uwa da abokan arziki. Haka kuma, Hausawa mutane ne masu girmama shugabanni, suna gudanar da sana’o’i da sauran hanyoyin mu’amala na rayuwar yau da kullum.

4.0       Lalubo Wasu Al’adun Hausawa a Littafin Gumakan Zamani

Wannan bincike ya bi diddigin al’adun Hausawa a wannan littafi. A sakamakon haka ne aka lalubo wasu rukunonin al’adun nasu, musamman waɗanda suka shafi yanayin zamantakewar yau da kullum da tsarin dogaro da kai da yanayin cimaka da kyautatawa da sauran makamantansu kamar haka:

4.1 Sana’o’in Hausawa

Ƙamusun Hausa (2006: 387) ya ba da ma’anar sana’a kamar haka, “aikin da mutun yake yi don samun abinci”. A fahimtar Auta (2006: 195) kuwa ya nuna cewa, “sana’a ita ce wani tafarkin rayuwa da mutum kan ɗauka ya bi shi domin ya samun samun abin biyan buƙatunsa na yau da gobe.

Saboda muhimmancin sana’a ga rayuwar Bahaushe, yakan sa a gaje su daga wajen iyaye da kakanni, kuma al’adarsa ba ta yarda ya zauna haka nan ba tare da aiwatar da sana’a ba. Domin kuwa, ta hanyar sana’ar ce zai riƙa biya wa kansa buƙatun yau da kullum, kuma ya taimaka wa ‘yan’uwansa wajen magance wasu buƙatun rayuwa da suka taso.

Ga misalan wasu sana’o’in Hausawa na gargajiya a wannan littafi, da yadda suke gudanar da su domin magance zaman kashe-wando da samun abin da za su vatar. Misali,

Ɗan kasuwa ne babba, kuma manomin gaske. Aƙalla kowace shekara ya noma buhun dawa ɗari biyu, buhun masara ɗari, buhun gero ɗari ko ma fiye da haka. In ya yi wake kuma, yakan noma wajen buhu arba’in. Gonakinsa manya guda uku ƙanana biyu, kuma yana tava kiwo ko da yake shanun nasa ba su wuce hamsin ba.” (shf: 7-8, sl: 3).

A nan za a ga yadda mawallafin ya fito da wasu daɗaɗɗun sana’o’in Hausawa na gargajiya. Misali, ya nuna cewa Alhaji Mustafa ya kasance mutum mai matuƙar gudanar da sana’o’in noma[3] da kiwo[4], waɗanda a sanadiyyar haka ne arzikinsa ya bunƙasa.

Ga wani ƙarin misalin mai ɗauke da wata sana’ar gargajiya a littafin kamar haka:

“Alhaji Murtala sun buɗe gidan dambe a nan Marmaro, a Sarari kuwa wani babban otel suke ginawa.” (shf: 45, sl: 3).

Shi kuwa wannan misali da aka bayar a sama, ya fito da wata sana’ar gargajiya da Hausawa suka ɗauki lokaci mai tsawon gaske suna aiwatar da ita. Bisa asali, ita wannan sana’a ta dambe[5] akan yi ta ne tsakanin mutane guda biyu, a gefe ɗaya kuma ɗimbin mutane (‘yan kallo) suna kallo a yi masu kirari.

4.2 Tsarin Shugabanci

Sha’anin shugabanci a ƙasar Hausa daɗaɗɗen al’amari ne wanda Hausawa suka ɗauki lokaci mai tsawon gaske suna gadanar da shi a tsakaninsu. Domin kuwa, ta haka ne suke samun tsararriyar hanya wadda al’umma za ta riƙa kai buƙatunta ga shugabanninsu kamar su; Sarki da Hakimi da Dagaci da Mai’unguwa.     

Misali, Zaruk (1990) ya nuna cewa, ana tunanin sarauta ta samo asali ne daga kan maigida wato mai shugabantar iyalansa, daga nan sai yaɗuwar al’ummar Hausawa ta yawaita mai kawo sulhu, tsakanin wannan gida da wancan gida wato mai unguwa. Daga nan kuma, ganin rigingimu na ƙara yawaita, sai suka yi tunanin samun shugaban ƙauyen da suke zaune wato dagaci, domin ƙoƙarin kawo masu sulhu da kuma yin hukunci ga dukkanin mai kawo ruɗani a cikin Hausawa mazauna wannan yanki, da tafiya ta yi tafiya kuma har zuwa Sarki.

Ga hoton wasu sarautun gargajiya na ƙasar Hausa, waɗanda suke nuna yadda masu riƙe da sarautun suke kulawa da talakawansu. Haka su ma talakawan, suna nuna matuƙar biyayya da ladabi da kiyaye dokokin shuwagabanninsu. Misali,

“Lokacin da Murtala ya isa garinsu, bai zame ko’ina ba sai gidan hakiminsu, ya je ya yi gaisuwa kuma ya yi wa hakimin alheri. Daga nan sai gidan Liman, nan ma ya yi masa alheri.”(shf: 26. Sl: 1).

Shi kuwa misalin da aka fitar a sama, yana nuna yadda al’umma (talakawa) suka ɗauki shuwagabanninsu da ƙima da daraja. Misali, saboda matsayin da Hakimi[6] da Liman[7] suke da shi a cikin al’umma, shi ya sa a lokacin da Murtala ya dawo garinsu na Marmaro bai je gida ba, sai da ya fara zuwa gidajensu ya gaishe su tare da yi masu alheri (kyauta) kafin ya shiga gidansu.

4.3 Abincin Hausawa na Gargajiya

Wannan kalma daidai take da kalmar Cimaka ko Cima. Kalmar suna ce kuma ta mata, tana nufin abinci, musamman wanda aka dafa (Gusau, 2009: 115).

Dangane da ma’anar abinci kuwa, masana kamar Lawal (2018: 217) ya ba da ma’anar abinci kamar haka, “duk wata cimaka ta ci, ko sha, wadda al’umma ta saba da ita a tsarin gudanar da rayuwarta ta yau da kullum, kuma a bisa tsarin addininta”.

Wasu daga cikin cimakar Hausawa na gargajiya da aka samu a wannan littafi, akwai waɗanda suka danganci ajin abinci mai ƙara ƙarfi da abinci mai ruwa. Misali,

“Shigowar wani abokinsa ta tashe shi firgigit. “Dirhami!” Choka ya kira shi da ƙarfi. “Choka yaya gari?” “Lafiya ƙalau, ba ka rage ‘yar fura ba?” (shf: 2, sl: 2).

Misali na sama yana ɗauke da ajin abincin Hausawa na gargajiya mai ruwa wannan littafin. Mawallafin ya ambaci fura[8] a matsayin ɗaya daga cikin cimakar Hausawa, musamman a lokacin da Choka (abokin Murtala) ya shigo ɗakinsa yana ya nemi ya ba shi sauran fura idan ya rage domin ya sha.

4.4 Aure

Gusau (2012: 18) ya ce, “aure wata alaƙa ce halattacciya, wadda ta halatta zaman tare tsakanin ma’aurata guda biyu, wato miji da mata. Ana yin sa ne, saboda abin da aka haifa ya samu asali da mutunci da kiyayewar iyaye.

A wannan littafi, an nuna yadda aure yake da matuƙar fa’ida ga rayuwar ɗan A dam. Shi ya sa mawallafin ya ambaci yadda wasu matasa suke tattaunawa a tsakaninsu, tare da yi junansu nasiha cewa ya kamata su yi aure. Ga abin da ya ce,

Ƙwarai kuwa. Ni na ma fara tunanin komawa gida, a can nake son in yi aure. Dama akwai wata yarinya da na tava so, an ce har yanzu ba ta yi aure ba, wai makaranta take yi” (shf: 25, sl: 3).

A tattaunawar da Murtala yake yi da abokinsa Choka, za a ga yadda yake nuna masa cewa, a halin yanzu yana buƙatar ya yi aure domin cikar ƙima da kamalarsa. Ta haka ne yake ganin dacewar ya koma wa wata tshohuwar budurwarsa, wadda suka yi soyayya domin an ce ba ta yi aure ba har yanzu.

4.5 Tsarin Zamantakewa

A gargajiyance, kalmar zamantakewa kamar yadda Adamu (2008: 21) da Ammani (2013: 481) suka bayyana, tana nufin zama wuri ɗaya tare da wasu mutane daban, a ƙarƙashinka suke ko kuma zaman wuri ne ya haɗa kamar mawabtaka, ko unguwa ɗaya. Haka kuma za ta iya yiwuwa zama ne tare a dangi, ko zama na tare da iyali, ko kuma yadda iyalin suke yin zama a tsakaninsu.

An samu misalin yadda Hausawa suke gudanar da kyakkyawar al’ada ta zamantakewa, musamman wadda ta shafi zaman aure a tsakanin mata (kishiyoyi) guda biyu ko fiye.

“Ai dole ne Hajiya Maryam ta yi hawaye. Ko ba komai ai Murtala ɗanta ne, domin sun yi zaman arziki da Hajiya Ramatu, Hajiya Ramatu ba ta yi zaman kishi da ita ba, sai zaman mutunci da amana. Kuma ma ko mene ne, ai Murtala ɗanta ne domin ta auri ubansa kuma ɗiyarta Habiba ƙanwarsa ce” (shf: 13, sl: 4).

Za a ga hoton zamantakewar aure a tsakanin mutane guda biyu ko fiye a misalin da aka bayar a sama. Wato yadda Hajiya Maryama ta tabbatar cewa ta yi zaman arziki da mutunci da amana tsakaninta da Hajiya Ramatu (mahaifiyar Murtala) a lokacin da suka auri miji ɗaya, kafin Allah (SWT) ya yi masa rasuwa a sakamakon hatsarin mota suka yi shi da matarsa.

4.6 Kayayyakin Hausawa na Gargajiya

Su ne ire-iren kayayyakin da Bahaushe yake amfani da su a harkokin rayuwarsu na yau da kullum. Za a iya yin amfani da wasu daga cikin waɗannan kayayyaki a cikin gidan Bahaushe, ko a gona, ko a fagen fama (faɗa/farauta) da sauran makamantansu.

Wasu kayayyakin gargajiyar Bahaushe da aka samu a cikin wannan littafi, suna da alaƙa da yadda Hausawa suke tafiyar da huɗoɗinsu na cikin gida, ko na waje, ko a gona, ko a lokacin faɗa (kare kai), ko kuma a lokacin farauta.

“Mutane sun taru wasu da gorori, wasu da wuƙaƙe, wasu da sanduna da dai sauransu, a wata sabuwar unguwar Marmaro” (shf: 55, sl: 4).

Wannan misali na sama ya fito da wasu kayayyakin amfanin Bahaushe a wurare daban-daban. Misali, wuƙa[9] akan yi amfani da ita a cikin gida, ko a fagen farauta domin a yanka abin da aka kama. Haka kuma akwai sanda[10] da gora[11], waɗanda ake amfani da su a wajen farauta da kuma faɗa domin ba wa kai kariya daga abokan gaba

4.7 Karamci

Ma’anar karamci kamar yadda Ƙamusun Hausa (2006: 233) ya nuna ita ce, “kyautatawa ko kuma nuna alheri”. Shi kuwa Zabi (2018: 508) yana ganin cewa, karamci baiwa ce da Allah (SWT) yake ba wa wasu mutane na musamman. Kuma hanyoyin karamci suna da yawan gaske, kama daga zumunci da kyauta da saukar baƙi da kuma girmama magabata da sauransu.

Ke nan a iya cewa karamci sanannen abu ne tun asali a ƙasar Hausa, kuma al’ummar Hausawa suna aiwatar da shi ta fuskoki daban-daban kamar kyauta da girmama baƙo[12] da sauran makamantansu.

Ga misalin yadda aka fito a al’adar karamci, musamman yadda ake girmama baƙo a wannan littafi. Ga abin da mawallafin ya ce, a lokacin da Murtala ya ziyarci gidan Hajiya Maryam a matsayinsa na baƙo.

“Hankalin Hajiya Maryam ya ya ƙara dugunzuma, ta lura Murtala yana cikin wani mawuyacin hali. “Murtala za ka ga ɗaki na nan a waje, ka je ka zauna, in ka ci abinci ka huta sai mu yi magana (shf: 13, sl: 2).

A nan, an nuna yadda aka yi karamci ta fuskar girmama baƙo. Wato yadda Hajiya Maryam ta karrama baƙonta (ɗanta) Murtala. Ta haka ne ta tarbe shi hannu bibiyu, inda ta ba shi masauki (ɗaki) domin zauna tare da kwana a ciki. Haka kuma ta nuna masa cewa, bayan wurin kwana akwai abinci da za ta sa a kawo masa domin ya ci kafin ta yi magana da shi a kan dalilin zuwansa.

4.8 Al’adar Saye

Salim (1978: 92) ya bayyana cewa, saye shi ne ƙin kiran abu da sunansa ta hanyar sayawa, a yi amfani da wasu kalmomi da suke da kusan ma’ana ɗaya da shi, amma kuma aka ɗauka cewa su waɗannan kalmomi an yarda da amfani da su a wannan waje.

Binciken da Lawal (2019: 12) ya yi, ya ba da ma’anar saye kamar haka, “ƙin faɗar wani abu da sunansa na asali, a maimakon haka sai a yi amfani da wata Kalmar ko kalmomi waɗanda al’adar al’umma ta yarda da su da za su iya bayyana wancan abin don kyautata tarbiyyar al’umma ”.

Don haka a iya cewa, saye daɗaɗɗiyar al’ada ce da aka san al’ummar Hausawa da ita, musamman a tsarinsu na cuɗe-ni-in-cuɗe-ka da wasu ƙabilu, ko a mu’amalar zaman iyali, ko kuma a sauran harkokin da suke gudanarwa da danginsu na kusa da na nesa.

Ga misalin al’adar saye a wannan littafi, inda Murtala ya je gidan su Hajiya Maryam ya gabatar mata da wasu matsalolinsa na rayuwa, kuma ta yi alƙawari taimaka masa. Ga abin da ta ce masa kamar haka:

“Can ta ce wa Murtala, “Ba komai Murtala, ka yi haƙuri zan yi wa Malam (mai gidanta) magana in sha Allahu zai samar maka aikin yi tunda ka yi makaranta” (shf: 14. Sl: 2).

Wannan furuci da Hajiya Maryam ta yi wa Murtala, ya fito da misalin al’adar saye na suna[13]. Wato ta sakaya sunan mijinta Alhaji Usman, inda ta kira shi da Malam saboda alkunya da ke akwai a tsakanin mata da miji.

4.9       Zaman Makoki

Zaman makoki shi ne zaman da ake yi bayan an binne mamaci, sai duk jama’a su taru a gidan da aka yi mutuwar a ɗan zauna na ‘yan wasu lokuta, ana yi wa ‘yan’uwansa gaisuwa ta nuna juyayin rashin da aka yi. Daga nan sai wasu su waste, sai abar ‘yan’uwa na jini da abokan arziki su ci gaba zaman makokin. A tsarin irin wannan zama, maza sukan zauna ne a ƙofar gida suna karvar gaisuwar, su kuwa mata suna cikin gida suna karvar gaisuwar ‘yan’uwansu mata. Hikimar yin hakan ita ce, yin taka-tsantsan dad a Musulunci ya wajabta a kan haɗuwar maza da mata a bigire ɗaya.

A ƙa’idar zaman makoki, akan kwashe aƙalla kwana uku ana karvar gaisuwa. Wasu wuraren kuwa sukan yi kwana bakwai idan wani babban mutum mai muhimmanci ya mutu a cikin zuri’a, ta la’akari da irin jama’ar da ke zuwa daga kusa da nesa (Gulbi, 2013: 182-183).

Marubucin littafin ya kawo misalin yadda Hausawa suke gudanar da al’adar zaman makoki. Misali, inda ya bayyana yadda aka kawo gawauwakin su Alhaji Mustafa (mahaifin Murtala) da Hajiya Ramatu (mahaifiyar Murtala) gida, sannan aka yi masu sutura aka kai su maƙabarta.

“Ko da yake dai shi ma hawaye sun cika masa ido, ga dukkan alamu ɗan mai Gidan ne. Bayan an yi musu wanka, aka fito da su aka yi musu sallah, aka je aka binne su. Aka dawo aka ci gaba da zaman makoki” (shf: 7, sl: 2).

A nan kuma za a ga yadda mawallafin ya fito da al’adar nan ta zaman makoki bayan mamaci ya mutu. Ta haka ne ya bayyana cewa, bayan an yi wa Alhaji Mustafa da matarsa Hajiya Ramatu sutura, sai ‘yan’uwa da sauran abokan arziki suka dawo gida suka ci gaba da yin zaman makoki (karvar gaisuwa).

5.0       Kammalawa

Wannan takarda ta kawo bayanai a kan wasu al’adun Hausawa a ƙagaggun labarai na Hausa. Ta haka ne aka bibiyi sawun wasu al’adun Hausawa daban-daban a littafin Gumakan Zamani wallafar Farfesa Yusuf M. Adamu. An yi sharar fage inda aka kawo saƙon littafin a taƙaice, sai bayani a kan Hausawa da al’adunsu tare da lalubo wasu sassan al’adun nasu a wannan littafin. Misali, an fito da sana’o’in Hausawa na gargajiya da tsarin shugabancinsu kamar hakimi da liman, sai yanayin cimakarsu ta gargajiya da kuma sha’anin aure. Har wa yau kuma, an zaƙulu wasu sauran al’adun gargajiyar Bahaushe kamar yanayin zamantakewarsa da yadda yake nuna karamci da al’adar saye da zaman makoki da wasu kayayyakin amfani na Hausawa a cikin gida, ko lokacin farauta, ko kuma a lokacin faɗa (domin kare kai).

Binciken ya fahimci cewa, Hausawa mutane ne masu riƙo da al’adunsu na dauri[14]. Saboda haka ne wasu daga cikin ɗaɗaɗɗun al’adun Hausawa kamar sana’o’in gargajiya suke ƙara ƙarfafa masu guiwa a kan yin dogaro da kai, maimakon su zauna haka nan su zama ci-ma-zaune[15] a cikin al’umma. Haka kuma, an lura Hausawa sun kasance mutane masu kunya sosai. Ta haka ne suke aiwatar da wata kyakkyawar al’ada da ake kira saye, wadda ta shafi nuna kunya da girmamawa ga wasu sunayen da ake sakayawa, saboda wasu dalilai da addini ko al’ada suka tanadar. Wannan ne ya sa ake kiran wannan al’ada da ‘alkunya’. Har wa yau kuma, an gano cewa ƙagaggun labarai na Hausa sun zama tamkar wata muhimmiyar taska da take adanawa tare da bayyana hoton al’adun Hausawa iri daban-daban. Alal misali, an baje-kolin wasu nau’o’in al’adun Hausawa a wannan littafi na Gumakan Zamani irin su; sana’o’in noma da kiwo da zaman makoki da tsarin zamantakewar aure da karamci da tsarin shugabanci da yanayin cimakar Hausawa da sauran makamantansu.

Manazarta

Adamu, M.I. (2008). “Jigon Zamantakewar Aure a Cikin Wasu Waƙoƙin Finafinan Hausa”. Kundin Digiri na Ɗaya. Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero, Kano.

Aliyu, L. (2017). “Nazari a Kan Matsayi Tsakanin Sarki da Hakimai a Fadar Katsina”. Kundin Digiri na Uku. Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero, Kano.

Ammani, M. (2013). “Zamantakewar Auren Hausawa a Yau: Tsokaci a kan Wasu Matsalolin Aure da Hanyoyin Magance su”. A Cikin Tavarvarewar Al’adun Hausawa a Yau (The Deterioration of Hausa Culture). Zaria: Ahmadu Bello University Press.

Auta, A.L. (2006). “Tattalin Arzikin Al’umma: Nazarin Sana’o’i da Kauwancin Hausawa”. A Cikin Algaita Journal of Current Research in Hausa Studies Vol. 1, No. 4. Kano: Benchmark Publishers Limited.

CNHN, (2006). Ƙamusun Hausa na Jam’iar Bayero. Zaria: Ahmadu Bello University Press Limited.

Ɗanmaigoro, A. (2010). “Sana’o’in Hausawa da Fulani”. A Cikin Al’adu da Ɗabi’un Hausawa da Fulani. Kaduna: El-Abbas Printers Media Concept.

Gulbi, A.S. (2013). “Zaman Makokin Bahaushe a Yau”. A Cikin Tavarvarewar Al’adun Hausawa a Yau (The Deterioration of Hausa Culture). Zaria: Ahmadu Bello University Press.

Gusau, S.M. (2009). “Jirwayen Cimakar Hausawa ta Gargajiya a Waƙoƙin Baka na Hausa”. A Cikin Proceeding of 2nd International Conference on Hausa Studies: African and European Perspectives. Napoli: Universita Degli Studi di ‘Oli’ Orientali.

Gusau, G.U. (2012). Bukukuwan Hausawa. Gusau: Ol-Faith Prints Limited.

Gusau, S.M. (2010). “Al’adun Hausawa a Taƙaice”. A Cikin Al’adu da Ɗabi’un Hausawa da Fulani. Kaduna: El-Abbas Printers Media Concept.

Gusau, S.M. (2012). “Al’adun Hausawa da Wasu Hanyoyi na Bunƙasa su”. Takardar da aka Gabatar a Taron Gidauniyar Daɗa Ginawa da Rayar da Rugar Al’adun Hausawa da Fulani ta Fatima Shema Katsina: Kwalejin Ilimi ta Tarayya.

Imam, R.S. (2018). “Nazarin Jigo da Yanayin Taurari a Littafin Gumakan Zamani na Yusuf Muhammad Adamu”. Kundin Digiri na Ɗaya. Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero, Kano.

Lawal. N. (2019). “Nazarin Saye a Al’ummar Hausawa”. Kundin Digiri na Uku. Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero, Kano.

Mu’azu, A. (2006). “Matsayin Al’adu Baƙi a Ƙagaggun Labaran Hausa”. A Cikin Algaita Journal of Current Research in Hausa Studies Vol. 1, No. 4. Kano: Benchmark Publishers Limited.

Salim, B.A. (1978). “Saye a Hausa”. A Cikin Harsunan Nijeriya. Vol. Viii. Kano: Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero.

Sallau, B.A. (2010). Wanzanci da Muhimmancinsa ga Rayuwar Hausawa. Kaduna: M.A. Najiu Professional Printers.

Yahaya, N. (2013). “Sayen Suna a Ƙasar Hausa Jiya da Yau”. A Cikin Tavarvarewar Al’adun Hausawa a Yau (The Deterioration of Hausa Culture). Zaria: Ahmadu Bello University Press.

Zabi, M.A. (2018). “Tubalin Karamci a Ginin Wasu Waƙoƙin Mamman Shata Katsina”. A Cikin Studies in the Songs of Dr. Mamman Shata Katsina. Katsina: Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Umaru Musa Yar’adua.



[1] Hira da Farfesa Yusuf M. Adamu, ranar 04/12/2019 a ofishinsa da ke Sashen Labarin Qasa (Geography) Jami’ar Bayero, Kano.

[2] Bayero University Press

[3] Noma shi ne qashin bayan tattalin arzikin kasar Hausa, kuma ana yin sa ne don a sami abincin da za a ci da kuma wanda za a sayar don yin hidimomin yau da kullum. Haka kuma sana’a ce da xaukacin al’ummar Hausawa suke yi, kamar Sarakai da talakawa da attajirai da maza da mata da manya da yara. A gargajiyar Bahaushe, yana yin noma iri biyu; akwai na abin ci irin su gero da dawa da masar. Kuma akwai noma na sayarwa irin su auduga da gyaxa da rixi (Sallau, 2010: 14).

[4] Kiwo sana’a ce da akan yi gidan gona a samar wa dabbobi wuri tsabtatacce da kuma abinci wadatacce. Ta haka ne wasu suke yin kiwon awaki da tumaki, domin su riqa haihuwar ‘ya’ya daga lokaci zuwa lokaci. Haka kuma akwai Fulanin daji (makiyaya) waxanda suke gudanar da kiwo (nema wa dabbobinsu abinci) ta hanyar tafiya da garken shanunsu. Bisa al’ada, sukan yada zango su yi ‘yan bukkokinsu su saka tabarminsu a ciki zuwa wani xan lokacinsu su qara gaba. Sana’ar kiwo tana wadatar da al’umma abubuwa irin su nama da madara da qwai (Xanmaigoro, 2010: 127-128).

[5] Sana’a ce da ake dukan juna da dunqulallen hannu da zimmar wasa ko faxa (Qamusun Hausa, 2006: 92).

[6] Hakimi shi ne wanda yake da riqe da gundumar mulki a qasarsa, sannan kuma shi ne yake wakiltar Sarki da kuma gudanar da kevevvun ayyukan mulki irin na sarauta da kuma aiwatar da umarnin sarki (Aliyu, 2017: 72).

[7] Liman shi ne mutumin da yake yi wa Musulmi jagora wajen salla da sauran wasu ayyukan addini. A tsarin tafiyar da mulki, hakimi ne yake naxa Liman a qasarsa kuma zai umurce shi ya riqa bin wasu dokoki da sauran hukunce-hukuncen da tsarin mulki ya tanada (Qamusun Hausa, 2006: 306; Aliyu, 2017: 85).

[8] Ita ce abin sha wanda ake yi da gero (Qamusun Hausa, 2006: 203). Ana samar da fura ne daga dangin hatsi musamman gero ta hanyar surfawa, sannan a daka tare da kirvawa sai a dama da kindirmo domin a sha.

 

[9] Qarfe mai tsawo da faxi da aka koxa gefensa ya yi kaifi, ana maqala masa qota don yanka abubuwa da shi, ko a yi makami da shi (Qamusun Hausa, 2006: 203).

[10] Itace da aka karya ko aka sara, daga jikin bishiya don yin amfani da shi kamar a makami na dukan wani abu, ko kuma don dogarawa (Qamusun Hausa, 2006: 203).

[11] Wata irin sanda mai kai kwagiri-kwagiri da gajajjeru, ko dogayen gavovi da ake yin makami da ita ko kuwa a yi sangwami da ita (Qamusun Hausa, 2006: 203).

[12] An yi zamanin da a qasar Hausa duk wani baqo da ya zo, fada yake tafiya kai tsaye nan ne gidansu. Kuma a nan ne za a ba shi muhalli da abincin da zai ci, wani lokaci ma har da wurin noma da matar da zai aura (Zabi, 2018: 508).

[13] Sayen sunan yanka a qasar Hausa wata sananniyar al’ada ce da ta shafi nuna kunya da girmammawa ga sunayen da aka saya. Wannan ne ya sa ake kiran wannan al’ada da ‘alkunya’, kuma dalilai da dama kan sa a saya sunan yanka. Daga cikin dalilan, akwai kunya, wadda kan sa a saya sunan miji, ko mata, ko kuma xan fari (yahaya, 2013: 261).

[14] Zamani mai nisa day a shuxe (Qamusun Hausa, 2006: 100).

[15] Malalacin mutum wanda a koyaushe yake jiran al’umma su yi masa hidima.

Post a Comment

0 Comments