Ticker

6/recent/ticker-posts

Adon Harshe a Waƙar Kirmau Uban Gabasawa ta Aminu Ladan (Alan Waƙa)

Citation: Ali, B.Y. and Danbappa, H.R. (2024). Adon Harshe a Waƙar Kirmau Uban Gabasawa ta Aminu Ladan (Alan Waƙa). Ginshiƙin Nazarin Salon Waƙoƙin Hausa, 550-558. www.doi.org/10.36349/djhs.2024.v03i01.068.

Adon Harshe a Waƙar Kirmau Uban Gabasawa ta Aminu Ladan (Alan Waƙa)

Bilkisu Yusuf Ali
Al-Qalam University, Katsina
bilkisuyusuf64@gmail.com
+2348064159965

Da

Hauwa Rabi’u Danbappa
Aminu Kano College of Islamic And Legal Studies, Kano.
hauwadanbappa200@yahoo.com
+2348035452399

Tsakure: Kiɗa da waƙa abubuwa ne da zai yi wuya a raba Bahaushe da su. Hausawa suna amfani da waƙa wajen faɗakarwa ko wa’azantarwa ko yabo musamman a fada. “Abun da wuya wai gurguwa da auren nesa” a raba fada da makaɗa. Wannan takarda mai taken “Adon harshe a waƙar Kirmau Uban Gabasawa ta bibiyi wasu daga cikin adon harshe da makaɗa Aminu Ala ya yi amfani da su a cikin waƙar. Masana da manazarta kamar Gusau (2014) da Ɗanbappa (2019) sun nazarci adon harshe a fannonin adabi daban-daban. Fannonin sun haɗa da, jawabai na shugabanni da waƙoƙi a matsayin dabarun jawo hankali da sa karsashi. An yi amfani da rain Gusau ( 2008 ). Hanyoyin da aka bi domin gudanar da bincike sune ta sauraron waƙar da kuma bibiyar masana da litattafai da maƙalu domin gano irin adon harshen da aka yi amfani da su a waƙar. An gano yadda Makaɗa Ala ke amfani da ƙwarewar harshe wajen zaƙulo kalmomi cikin hikima domin waƙa ta zama mai sa karsashi da armashi. Makaɗa Ala ya yi amfani da adon harshe na siffantawa da mutuntawa da dabbantawa da abuntarwa da kambamar zulake.

Fitilun Kalmomi: Adon Harshe, Waƙar Kirmau Uban Gabasawa, Aminu Ladan (Alan Waƙa)

Gabatarwa

Wannan Nazarin waƙar Kirmau mai Gabasawa ta Alan waƙa, wadda ya yi wa sarkin Gaya Dr. Aliyu, ya yi ta ne don taya shi murna karɓar sandar sarauta da aka bashi[1] bayan ya zama sarkin Gaya. Waƙar tana da ɗiya goam sha biyar, kuma an yi waƙar ne a shekarar 2022 a watan junairu. Wannan takarda ta kalli adon harshe ne a cikin waƙar ta Aminu Alan waƙa, inda ya nuna fasaharsa wajen fito da manyan nau’oin adon harshe irinsu Kamantawa da siffantawa da alamtawa da dabbantawa da kambamawa. Bayan an kawo ma’anar waƙar baka da waƙar baka ta zamani da kuma ma’anar adon harshe kamar yadda masana suka kalle shi. A ƙarshe takardar ta kawo sakamakon bincike da manazarta.

1.1       Kiɗa da Waƙar Baka

Waƙa tana cikin makarantar farko ta Bahaushe wanda cikinta yakan koyi ilimi na rayuwar yau da kullum. Waƙa a ƙasar Hausa, wani ginshiƙin abu ne da ake aiwatarwa don ilmantarwa da sadarwa ko nishaɗantarwa ko bayar da gudummawa ta musamman a zamantakewa. A gun Bahaushe kiɗa da waƙa yana cikin adabinsa da rayuwarsa har da al’adunsa.

            Gusau (2019:5) ya bayyana cewa “a ilimin fanni waƙar baka , kiɗa yana nuni ne da wani amo ko sauti da ake samarwa ta gwama ko haɗa abubuwa biyu kamar dutsi +dutsi ko tafi +tafi ko baki +ƙahon dabbobi ko ganga +gula (makaɗi) ko wani amo ne wanda yakan shiga jikin mai sauraro , ya sa masa karsashi har ya dinga rausayawa, yana tattakawa ko jujjuyawa. Dumfawa[2] ya ce "Waƙa na daya daga cikin daɗaɗɗan hanyoyin Hausawa na koyar da ilimi a cikin nishadi. Waƙa ita ce hanyar koyar da al'umma tarbiyya da kuma dabarun zaman duniya gabanin zuwan Musulunci da kuma wayewar kai ta hanyar karatu da rubutu"

1.2       Ma’anar Waƙar Baka ta Zamani a Taƙaice

A ƙasar Hausa, waƙa wata hanya ce ta isar da saƙo. Hausawa sun riƙeta tun zamani mai tsawo, suna amfani da ita, suna isar da manufofinsu da saƙonninsu ga jama’a, har zuwa lokacin da aka samu sabuwar hanya ta isar da saƙo ta waƙar baka wanda ake amfani da fiyano maimakon kayan kiɗa na zamani da aka sani a baya. Waƙoƙin Fiyano na Hausa su ne waƙoƙin da suka samu bayan da kayan kiɗa na Hausawa suka haɗu da baƙin al’ummu irin Larabawa da Turawa, kuma suka yi tasiri a kan na Hausawa. Waƙoƙin fiyano na Hausa sun wanzu sakamakon tasirin baƙin al’umma ya haifar da samuwar waƙoƙin fiyano na Hausa.

Gusau (2008:6) ya bayyana cewa “Fiyano wani abin kiɗa ne baƙo ga Hausawa da suka samu ta hanyar hulɗa ta Turawa”. Gusau (2011: 8) ya kuma nuna cewa “Daga bisani, bayan Hausawa sun iya karatu da rubutu na ajami da kuma na boko, sai aka samu wasu mutane suna rubuta waƙoƙi, amma sai su ɗora musu rauji na karin murya, sa’an nan su rera su tare da amon kiɗa (sauti na kiɗa)…Har wayau, kayan kiɗan da ake amfani da su wajen rera waɗannan waƙoƙi sun ƙunshi kayan kiɗa na zamani ne kamar mandiri da fiyano da jita da gangunan Turawa da makamantansu”.Ita kuwa a nata ra’ayin Binta (2011:77) ta bayyana cewa “Shigowar kiɗan fiyano zuwa ga Hausawa yana da dangantaka ne da sha’awar kallo da sauraron kaɗe-kaɗen finafinan Indiya da Hausawa suka tsinci kansu a ciki

1.3       Taƙaitaccen Tarihin Mawaƙi

An haifi Aminu Ladan Abubakar Alan waƙa ranar Talata 11/02 a shekarar 1973 a unguwar Yakasai da ke cikin Birnin Kano. Ya yi karatun Muhammadiya kuma ya samu ilimin addini gwargwadon iko. Bayan karatun al-ƙur’ani ya karanta littattafai da dama da a kan saka a makarantun soro da suka haɗa da Al-muktasirul Akdhari da Ƙawa'idi da Ishmawiy da Muktasar da Ta'alimi. a Ɓangaren Lugga ya karanta Su Ishriniya da Ɗanɗarani.A ɓangaren karatun boko Malam Aminu Ala a ɓangaren boko ya yi karatun firamarea Tudun Murtala a tsakanin shekarar 1980 zuwa1986, sannan ya yi makarantar sakandare ta GSS Kawaji a Dakata, Kano ashekarar 1987 zuwa 1992 a shekarar 2004 Ya ci gaba dakaratu a makarantar School of Technology da ke Kano inda ya samishaidar diflomarsa 2007. Daga nan ya koma karatunsa a jami’ar Open University a yanzu haka yana aji uku inda yake karanta Hausa.Aminu Ala ya zama marubucin littafin Hausa inda ya fitar dalittafinsa na farko mai suna Jirgi Ɗaya a shekarar 1999. Sai cin zarafi da baƙar aniya da cin fuska da sawaba da jirwaye da ƙawazuci da tarzoma da ceto ko cuta? Ya riƙe shugabancin ƙungoyoyin marubuta kamar Brigade Authors Forum, da Hausa Authors Forum Association Of Nig. Authors.

A fagen waƙa kuwa Aminu Ala tun filazil mutum ne mai sonwaƙoƙi don haka yake yawan sauraren mawaƙan baka na gargajiyamusamman Musa Ɗanƙwairo da Shata. Haka yana son waƙoƙin begenAnnabi (S.A.W.). Ya fara waƙa tun yana Islamiyya daga nan ya fara. A shekarar 2000-2003 bayan haɗuwarsa da Marigayi Abdullahi Sani Makarantar lungu sai ya kuma gogewa. Gidan Radiyon Kano nan ne ya fito da shi inda ya yi waƙar “BelloƊandago Radiyon Kano da “Gagara-gasa uwa ma-ba-da-Mama” da kuma“FM, AM Radiyon Kano” a shekarar 2003. A shekarar 2004 Aminu Alada “Baubawan Burmi” da “Jamia Gidan Ban kashi” da sauransu.

Daga nan likkafa ta ci gaba inda Freedom Radiyo su ma suka shigasanya waƙoƙinsa, musamman ta “Jamia” da wadda ya yi wa Sarkin Kano ta “Bakan-Dabo”. A fagen waƙoƙin siyasa kuma ya fara jin amonsa a Jamiyyar A.N.P.P. inda ya yi waƙoƙi da dama waƙoƙi da dama ga Gwamnan Kano na wananan lokaci Malam Ibrahim Shekarau da mutuminda ake ganin shi ne ubangidansa a wannan lokaci wato Alhaji Sani LawanƘofar Mata.A shekarar 2012 Aminu Ala ya buɗe sitidiyo nasa na kansa wandaake yin ayyukan da suka shafi waƙoƙi da ɗab’i mai suna “Taskar AlaGlobal”Ya sami shaidar karramawa ta Dakta daga jami’ar Height da ke jamhuriyar Benin a ranar 26/9/2020. Aminu Alan Waƙa ya zama Ɗan amanar Bichi a ranar 12/08/2019.

Sannan ya sake zama sarkin waƙar sarkin Dutse Ranar 15-16/12/2019. Ya zama sarkin ɗiyan Gobir a shekarar 2022. Iyayen gidan Ala akwai Sarkin Kano da Sarkin DutseFarfesa Sa’idu Muhammad Gusau.[3]

1.4       Taƙaitaccen Bayani a Kan Alhaji Dr. Aliyu Ibrahim (Sarkin Gaya)

An haife shi ranar 10/10/69. Ya halarci makarantar firamare ta Kofar Na’isa daga shekarar 1974-1980. Daga nan ya wuce makarantar sakandire ta GSS Gwammaja2 daga 1980-1985. Ya samu shaidar karatun difloma a makarantar Polytechnic wadda ya yi daga shekara ta 1989-1990. Sannan ya kuma yin wata diflomar a ɓangaren Public account and audit a shekarar 1998-1999 sannan ya kammala da adɓance diploma a public administration . ya kuma yin wani kwas din adɓance diploma a bangaren public accountant and audit 2000-2003. Ya kuma HND a bangaren gudanar da harkokin mulki (Public Administration) a kwalejin kimiyya da fasaha ta Kano. Daga nan ya tafi ya yi babbar diploma (PGD) a Banking and Finance 2005-2006 sai wuce ya yi masters duka a jami’ar Bayero ta Kano. Sarkin Gaya Alhaji (Dr) Aliyu Ibrahim ya bayar da gagarumar gudummawa wajen ayyukan gwamnati wanda ya rike inda ta kai har ya zamana ya rike mukaddashin (mai kula da kuɗi) Burser (2005-2009) a kwalejin KAS da ke Kano sai kuma ya zama cikakken mai kula da kuɗi (Burser) (2011-2015). Ya sami sauyin wurin aiki inda ya koma makarantar kula da ayyukan gona ta a shekarar 2019-2021 wanda daga nan ya ajiye aiki don kashin kansa saboda ya mayar da hankali kan kasuwancinsa. lahadi 26/9/2021. Ya zama Sarkin Gaya ranar 22 ga watan Satumba 2021. Inda gwamnan Kano Dr Abdullahi Ganduje ya ba shi sanda a ranar 22/1/2022.[4]

1.0              Ra’in Bincike

Ra’in da aka gudanar da wannan bincike aka kuma ɗora binciken a kansa shi ne, ra’in Gusau Gusau (1993/2003) Jagoran Nazarin Waƙar Baka da Ɗangambo Ɗangambo, A. (2007). Ɗaurayar Gadon Feɗe Waƙa.

1.1              Hanyoyin gudanar da Bincike

Yayin gudanar da wannan nazari, an kai ziyar aɗakunan karatu don yin nazarin wasu littatafai da suka shafi waƙar baka ta zamani. Haka kuma, an tattauana da mawaƙin sannan an tattauna da wasu masana da manazarta waƙa don samun haske da ƙarin bayani don inganta takardar. An saurari waƙar sannan an yi amfani da hanyoyi na zamani don naɗar sauti da juyar waƙar daga saurare zuwa rubutu.

3.1       Adon Harshe

Adon harshe dabara ce da marubuta kan yi amfani da ita don ƙawata ayyukan na adabi. Wurn (1991:281) ta bayyana adon harshe da cewa, shi ne amfani da kalma ko furuci ba da ma’anarsu ta asali ba , ta hanyar amfani da idon zuci (imaginatiɓe way) don kaiwa maƙura wajen ƙayatarwa. Gusau (1983:54) cewa ya yi adon harshe wata dabara ce wadda ake yi wa harshen kwalliya. A wajen adonta harshe akan zaɓo wasu kalmomi ne a zayyana waƙa da su, a ƙawata ta sosai ta yadda za a burge mai sauraro a kuma jawo hankalinsa. Ɗangambo (2007:39) ya kira da sauran dabarun sarrafawa in da ya ce su waɗannan yawanci dabaru ne jawo hankali ta hanyoyi iri daban-daban kuma don dalilai daban-daban. Sarɓi (2007:153) shi ma ra’ayinsu ɗaya da Ɗamgambo in da ya ce hanyoyi ne da marubuta waƙoƙi suke amfani da su ta hanyar sarrafa kalmomi da maganganu domin cusa sha’awa da jin daɗi ga mai karatu ko mai sauraren waƙoƙinsu. Bisa waɗannan ma’anoni za a iya cewa, adon harshe sinadari ne da ke ƙara wa magana ɗanɗano, ta yi zaƙi a kuma dinga ɗokin saurare ba tare da gajiyawa ba. Tamkar yadda gishiri ya ke a cikin miya, waɗannan dabaru suna taimakawa duk wani zance ko jawabi ko waƙa armashi tare da jan ra’ayin mai sauraro cikin sauƙi, ta amfani da kalmomi masu mabanbanta ma’ana, sukan kuma taimaka wajen zurfafa tunani domin gano abubuwan da suka ƙunsa.

3.2       Nau’o’in Adon Harshe

Masana da manazarta da dama, sun kawo nau’o’in adon harshe kamar Tsoho (1987) da Dija (1997) da Yahaya (2001) da Ɗangambo (2007) kamar haka:

Kamantawa ko Tamka:

Kamance na fifiko

Kamance na daidaito

Kamance na kashi ko gazawa.

Jinsirtawa

Mutumtarwa

Dabbantarwa

Abuntarwa

Kambame

Alamtarwa

Jerin sarƙe da sauransu.

3.2.1    Kamantawa

Tsoho (1987) ya kira kamantawa da tamka inda ya ce ‘tamka na nufin kwatanta wani abu da wani ta hanyar yin amfani da kalmar kwatantawa. Shi ma kamar takwarorinsa ya bayyana cewa ana amfani da kalmmomi wajen tamka da suka haɗa da:kamar da tamkar da kwatancin da daidai da ya fida ya kasa da sauransu. Akwai kamace na daidaito da kamance na fifiko da kamance na gazawa. A wannan waƙa mawaƙin ya kawo kamance na fifiko inda yake cewa:

Jagora: Goron gudu a Kai wa barewa jaki ya na tsaye.

:Mai sanya ‘yan maza sui raki.

(Aminu Ala: Ɗa na 1)

A nan, makaɗa Aminu Ala ya nuna yadda idan ana maganar gudu ba za a gayyaci barewa ba. Duk da cewa dukkaninsu dabbobi ne amma a wajen gudu ba za a haɗa barewa da jaki ba. Mawakin ya yi amfani da kaifin basirarsa wajen nuna barewa ta fi jaki a fagen gudu, an yi amfani da hikima wajen nuna yadda sarkin Gaya ya fi sauran sarakuna a fagen jarumta. Wannan ya nuna kamance na fifiko duk da cewa suna da sarauta ɗaya amma ya fi su.Sannan an nuna yadda yake a fagen jarumta duk da shi namiji ne amma ya fi sauran maza. Don haka a wannan ɗiyar waƙar an fito da kamanci ne na daidaito yace:

Jagora:            Da kan cika uba kan dauka.

(Aminu Ala: Ɗa na 1)

A nan makaɗin ya nuna kamanci na daidaito inda ya nuna sarkin Gaya Aliyu da mahaifinsa duka sun yi sarki don haka duka sun gaji sarautar Gaya.

3.2.2    Siffantawa

Siffantawa dabara ce ta amfani da wasu kalmomi domin bayyana wasu ta amfani da halayya ko yanayi ko kuma ɗabi’a domin ƙara wa zance armashi. Ɗangambo (2007:43) ya ce siffantawa kamar kamantawa ce, sai dai kamance ne na kai tsaye, akan ɗauki darajar wani abu ko halayyarsa, a ɗora wa wani kai tsaye, wato a ce kaza ko kaza kaza ne. Shi ne kaza. Ya kuma kasa ta gida biyu da doguwar siffantawa da gajeriyar siffantawa’’ Aminu ya kawo siffantawa a ɗiyan waƙarsa yana cewa :

Jagora: Kirmau Ubangidan Gabasawa dabbar Wahabu taken Giwa

:Ka zama damunar al’umma sauka da lullumi

:Ka zama inuwa ta kadaura mai ba da ilimi

:Ka zama rahamar al’umma inuwar tsane gumi

(Aminu Ala: Ɗa na 9)

A nan, makaɗa ya yi amfani da siffantawa wajen siffanta sarki da damina mai lullumi, abun nufi kowa ya na amfana da shi da mai ƙaunarsa da makiyinsa. Sannan ya zama ni’ima ga al’ummar Gaya. A dai ɗiyan waƙar makaɗin ya ƙara siffanta Sarki da Kadaura wato babbar bishiya mai yalwa. Makaɗin ya ƙara siffanta sarkin Gaya da inuwar tsane gumi. Wannan hikima ce ta makaɗin wajen siffanta sarkin da nuna cewa shi ne mai taimakon talakawa mai wadata su. A nan makada ya yi amfani da siffantawa wajen siffanta Sarki da damina mai lullumi abun nufi kowa ya na amfana da shi da mai kaunarsa da makiyinsa Sannan ya siffanta shi da Kadaura babbar bishiya mai yalwa. Makaɗin ya kuma siffanta sarkin da inuwar tsane gumi. Wannan wata hikima da zalaka wajen nuna cewar sarki uban talakawa ne ya na taimakon na ƙasa da shi.

3.2.3    Abuntarwa

Abuntarwa ta ƙunshi siffanta abu mai rai da wanda ba shi da rai. Kamar yadda Dija (1997) ta bayyana cewa abuntarwa shi ne a mayar da mutum ko dabba ko tsuntsu ko wani abu mai rai ya zama abu mara rai, wato a kwatanta shi ko a yi magana da shi kamar wani abin da ba shi da rai.”Bunza (2014) ya bayyana cewa« abuntarwa ya saɓa wa dabbantarwa, domin shi akan ɗauki mutum ko dabba ko wani abu mai rai a ba shi matsayin wani abu maras rai, ko a ɗauki wani abu maras rai a ba shi matsayin wani abu maras rai ba shi ba, duk abuntarwa ne, ya ƙara da cewa asalin salon abuntarwa ya samo asali daga kalmar “abu”

Kai ne awartakin gasa karfe ja ragamar Gaya.

Jagora: Yau ka zam uban al’umma sautin amon Gaya,

:Kai ne awartakin gasa ƙarfe ja ragamar Gaya,

:Mai ƙin ya ji ni dole ya kauce ko dai ya zagaya,

:Ka zama ginshiƙin al’umma bangon mutan Gaya,

(Aminu Ala: Ɗa na 6)

A wannan ɗiyan waƙar, makaɗin ya abuntar da sarkin Gaya inda ya kira shi da amo wato sauti wanda yana nufin shi ne muryarsu a kowane wuri da kowane lokaci. Shi ne wakilinsu da zai nema musu ‘yanci ya karɓo musu damarsu. Ya kira shi da awartaki[5] inda yake nufin jigo na al’ummar Gaya wanda yake ɗauke da gaɓaren duka al’amuran Gayawa.

3.3.4    Mutuntarwa

Dabarar mutuntarwa dabara ce da ta danganci ba wa wani abu hali ko wani aiki na mutum. Ɗangambo (2007:45) ya bayyana ma’anar mutuntarwa da cewa: A ɗauki wasu halaye kosiffofi ko darajojida sauransu da mutum ne kawai aka sani da su, a laƙaba wa wani abu mara rai ko dabba ko tsuntsu ko ƙwaro da sauransu, wato abubuwan da ba mutum ba.Shi kuwaBunza(2014:76)cewa ya yi:“A tsarin mutuntarwa, za a ɗauki wani abu da ba mutum ba, a ba shi duk wata sifa da dabara da basira da aiki irin na mutum abar mai sauraro ko mai karatu da mamaki.” A taƙaice dabarar mutuntarwa dabara ce da ta danganci ba wa wani abu hali ko wani aiki ko sifa da aka san mutum ne kawai ke da ita.

Jagora: Lale maraba da Ali zaki,

:Lale maraba da Ali zaki,

:Lale maraba da ‘yan sarki,

:Zakin ƙasar Gaya yai sarki,

:Uban dawa da birni sarki,

:Ga mai ƙasar Gaya yai sarki,

:Zaki irinka ba ya raki,

:Dabbar Wahabu taken giwa.

(Aminu Ala :Ɗa na 14)

A ɗiyan wannan waƙar an kira sarkin Gaya da zaki kai tsaye wanda wannan dabbantarwa ne. Amma wata hikima ce ta nuna fasaha da adon harshe. An kira shi da zaki ne don nuna cewa yana da ƙarfi na jarumta da iko da isa da mulki kamar dai yadda zaki yake a cikin dawa ba a iya tunkararsa. Makaɗin ya kuma kiran Sarkin Gaya da giwa. Ita ma giwa a dawa ba dabbar da ta fi ta girma da kwarjini kamar zaki ba mai ita tarar giwa.

3.2.5    Kambame

Kambamawa shi ne kuranta abu afaɗeshi wanda a zahiri ba lallai ne hakan ya faru ba. Ɗangambo ( 2007:43) ita wannan wani lafazi ne ko furici da mawaƙa kan yi wanda sai a ga abu ne mai wiuya haka ta auku. Wannan dabara ce ta kambamawa don jawo hankali” A wannan waƙar makaɗa Aminu Ala ya yi amfani da wannan dabara inda yake cewa:

Jagora: Rana fito gari ya waye dubu jiran guda,

:Yau ka zamo uban al’umma dubu jiran guda,

Sarki ka ke ga Gaya ta Kanawa tushen gari guda,

:Haske na haskake al’umma yardar gwani guda,

:An yi dare gari ya waye buɗe muke yi wa sarkina.

(Aminu Ala: Ɗa na 7)

A wannan ɗan makaɗin ya yi amfani da kambamawa ga sarkin Gaya inda ya ambace shi yadda rana take fitowa da yadda al’umma kan jira fitowar rana don cigaba da al’amuransu na yau da kullum. Sannan ya kuma jaddada maganarsa da shi fa sarkin Gaya haske ne shi mai haskaka al’umma. Wannan wata dabara ce ta kambamawa.

Sakamakon Bincike

Wannan nazari mai suna Adon harshe a waƙar Aminu Ala ta Kirmau Uban Gabasawa ya gano fasaha da azanci na makaɗan baka na zamani inda suke amfani dabarar saka adon harshe a waƙoƙinsu don ƙawata waƙoƙinsu da jan ra’ayin mai sauraro da kambama sarakuna da suke yi wa waƙa. Kamar makaɗan dauri, makaɗan baka na zamani suna amfani da fasaharsu wajen kambama sarakunan da suke tare da su ta hanyar fasahar da suke da ita da kalamai masu cike da balaga da jan hankali don ƙara fito da martabar da sarakunan da suke yi wa waƙa. Makaɗan baka na zamani sun ɗau salon a makaɗan baka na gargajiya a yau don ƙara assasa wannan ɓangare na waƙoƙin fada kuma suka yi fice a wannan fage kamar dai shi (Dr) Aminu Ladan Abubakar (Alan waƙa)

Kammalawa

Wannan takarda mai suna adon harshe a waƙar Kirmau uban Gabasawa ta kalli adon harshe da Aminu Ladan Abubakar (Alan waƙa) ya kawo a cikin waƙar. Dafarko an kawo gabatarwar takarda inda a ciki aka fito da taƙaitaccen tarihin waƙa da wanda ya yi waƙar da wanda aka yi wa waƙar. An kawo ma’anar waƙar baka a taƙaice da kuma ma’anar waƙar baka ta zamani an kawo ma’anar adon harshe da nau’oinsa. Daga ciki an kwao kamantawa da siffantawa da alamtawa da dabbantawa da kambamawa tare da fito da misalansu daga cikin waƙar.

Manazarta

Abdullahi, B. (2014). Kwatanta Salon Harshe A Littattafan Wani Hanin Ga Allah Da Na Budurwar Zuciya. Kundin Digiri Na Biyu: Jami''ar Bayero, Kano

Binta, A.S (2011) “Tasirin Kayan Kiɗan Zamani A Kan Kaɗe-Kaɗen Hausawa Na

Gargajiya” Kundin Digiri Na biyu. Sashen Koyar Da Harsunan Nijeriya DaKimiyyar Harshe. Jami’ar Bayero, Kano.

Dija, Ɗ.(1997). Adon Harshe A Cikin Rubutaccen Adabin Hausa. Kundin Digiri Na Biyu: Jami’ar Bayero Kano.

Bunza, A. M. (2014). In Ba Ka San Gari ba Saurari Daka. Muryar Nazari Cikin Tafashen Gambo. Kano: Darul'umma Printing Press .

Ɗangambo, A. (2007). Ɗaurayar Gadon Feɗe Waƙa. Kaduna: Baraka Press & Publishers Limited.

Gusau, S.M (2008) Waƙoƙin Baka a Ƙasar Hausa Yanaye-Yanayensu da Sigoginsu Kano: Benchmark Publishers Limited

Gusau, S.M (1993/2003) Jagoran Nazarin Waƙar Baka Kano: Benchmark Publishers Limited

Gusau , S.M (2014) Waƙar Baka Bahaushiya (The Hausa Oral Song) Bayero University , Kano Inuaugral Lecture Series NO.14. Kano : Bayero University

Gusau, S.M (2019) Diwanin Waƙoƙin Baka Juzu’i na Huɗu Kano: Centurey Research And Publishing Limited

Tsoho, M. Y. (1987). Tarkakken Matanin Waƙar Kanzil Azimi ta Aliyu Namangi. Kundin Digiri Na Biyu: Jami'ar Bayero Kano.

Yahya, A. B. (2001). Salo Asirin Waƙa. Kaduna: Fisbas Media Services.

Rataye

G/Waƙa: Ali gadanga ɗan Ibrahim,

:Sarkin Gayan mu ne,

:Kirmau Ubangidan Gabasawa dabbar Wahabu ta zam giwa.

1.                  Jagora: Goron gudu akai wa barewa jaki yana tsaye,

:Ɗa kan cika uba kan ɗauka salkar giye uba gun giwa,

:Tushen Kano ga ‘ya’yan Sarki,

:Lale maraba da Ali zaki,

:Lale da maraaba ‘yan sarki,

:Zakin ƙasar Gaya yai sarki,

:Uban dawa da birni sarki,

:Ga mai ƙasar Gaya yai sarki,

:Zaki irinka ba ya raki,

:Mai sanya ‘yan maza sui raki,

:Mai sa mutan gari su ɗoki,

:Azarɓaɓi na zallar shauƙi,

:Ɗa kan cika uba kan ɗauka,

:Salkar giye uba ɗan giwa.

:Ali gadanga ɗan Ibrahim dabbar Wahabu taken giwa

2.                  Jagora: Ali gadanga ɗan Ibrahim Sarkin Gayan mu ne,

:Kirmau uban gidan Gabasawa,

:Dabbar Wahabu taken giwa,

:Ali gadanga ƙusar yaƙi,

:Sarkin Gayar mu ne,

:Kirmau Uban gidan gabasawa,

Dabbar wahabu taken giwa,

:Ali gadanga ɗan Ibrahim,

:Sarkin Gayan mu ne,

:Kirmau Ubangidan Gabasawa dabbar Wahabu taken giwa.

‘Y/Amshi: Ali gadanga ɗan Ibrahim,

:Sarkin Gayan mu ne,

:Kirmau Ubangidan Gabasawa dabbar Wahabu taken giwa.

3.                  Jagora: Allahu rahimun mabuwayi Na zo a durƙushe,

:Bawanka ne aminun Ala yai zaune durƙushe,

:Na nemi taimako a gareka don kar na dakushe,

:Karawa karsashin fikirata don kar ta murƙushe,

:Kai min tagomashi na basira don kar ta dallashe,

:Sarkina.

‘Y/Amshi: Ɗa kan cika uba kan ɗauka,

:Sarkin Gayan mu ne,

:Kirmau Ubangidan Gabasawa dabbar Wahabu taken giwa.

4.                  Jagora: Nai tsani ga shugaba na halitta manzo abin yabo,

:Nuril huda a bi ka a huta haske na mai rabo,

:Khairil wara abin dubana Annabi sha yabo,

:Tsani na yin a istisgasa domin biɗar rabo,

:Ɗaha sha yabon al’umma datar da ni gwani sarkina

‘Y/Amshi: Ali gadanga ɗan Ibrahim

:Sarkin Gayan mu ne,

:Kirmau Ubangidan Gabasawa dabbar Wahabu taken giwa.

5.                  Jagora: Bayan yabo na sarki Allah zan hau tudin yabo,

:Bayan yabo na manzon Allah zan je fagen yabo,

:Sarkin Gaya uban al’umma shi zan yi wa yabo,

:Murna ta lokacin koronashan hujjar shirin yabo,

:Dafawa baitukan da na tsara Allah mamallaki sarkina.

‘Y/Amshi: Ali gadanga ɗan Ibrahim ,

:Sarkin Gayan mu ne,

:Kirmau Ubangidan Gabasawa dabbar Wahabu taken giwa

6.                  Jagora: Rana fito gari yaw aye dubu jiran guda,

:Yau ka zamo uban al’umma dubu jiran guda,

Sarki ka ke ga Gaya ta Kanawa tushen gari guda,

:Haske na haskake al’umma yardar gwani guda,

:An yi dare gari ya waye buɗe muke yi wa sarkina.

‘Y/Amshi: Ali gadanga ɗan Ibrahim,

:Sarkin Gayan mu ne,

:Kirmau Ubangidan Gabasawa dabbar Wahabu taken giwa

7.                  Jagora: Ka zama damunar al’umma sauka da lullumi,

:Ka zama inuwa ta kadaura mai ba da ilimi,

:Ka zama rahamar al’umma inuwar tsane gumi,

:Zaki ka ke uban duka dauji sai dai da lallami,

:Alhamdu zaka yi da daɗawa godewa Rabbana Sarkina.

‘Y/Amshi: Ali gadanga ɗan Ibrahim ,

:Sarkin Gayan mu ne,

:Kirmau Ubangidan Gabasawa dabbar Wahabu taken giwa.

8.                  Jagora: Ƙarni na shiga tun tale-tale zan biya,

:Tun zamanin ana karafkar matafiya,

:Ƙasar Gaya anan zango ne, zangon matafiya,

:Tun daga Habasha , Tumbuktu zangon su ne Gaya,

:Ta nan suke shiga duka saƙon birnin Kano a kowace rana.

‘Y/Amshi: Ali gadanga ɗan Ibrahim,

:Sarkin Gayan mu ne,

:Kirmau Ubangidan Gabasawa dabbar Wahabu taken giwa.

9.                  Jagora: Kafin a kai hakanga da fari tushem makirkira,

:An ce Abagayawa da farko sune maƙirƙira ,

:A sanadin Kanonki Maƙeri kaya na ƙirƙira,

:Hujjar haƙar tama da ƙarafa ta sa ya ƙirƙira,

:Ya yada sasani na maƙera a Dalar Kano a yau birnina.

‘Y/Amshi: Ali gadanga ɗan Ibrahim

:Sarkin Gayan mu ne,

:Kirmau Ubangidan Gabasawa dabbar Wahabu taken giwa.

10.              Jagora: Uum kan bayyana ta Annabi Isa wannan batun yake,

:Kafin zuwan masihu batun nan ya wanzu faɗake,

:Tun ba lissafi na masihu gurigu wuri ake,

:Tushen Kano fa Abagayawa sai an yi bincike,

:In an yi bincike a sanar min sakamako na makwancina.

‘Y/Amshi: Ali gadanga ɗan Ibrahim

:Sarkin Gayan mu ne,

Kirmau Ubangidan Gabasawa dabbar Wahabu taken giwa.

11.              Jagora: Sunan Kano a bayyane yake, Kanoki shi ne sila,

:Kanoki shugaban ‘yan ƙira shi ne ya zam sila,

:Amma a wani ƙaulin an ce sarkin Kano sila,

:Ni na fi gamsuwa da Kanoki shi za ya zam sila,

:Allah ya san haƙiƙar zance kun dai ji talifi bakina.

‘Y/Amshi: Ali gadanga ɗan Ibrahim,

:Sarkin Gayan mu ne,

:Kirmau Ubangidan Gabasawa dabbar Wahabu taken giwa.

12.              Jagora: Ja ragamarka Ali gadanga sarkin gayan Kano,

:Ali gadanga ɗan Ibrahim sarkin Gayar Kano,

:Taka a hankali huriminka ne mai Gayar Kano,

:Gatanka Rabbana Mabuwayi ga ka na San Kano,

:Alan Kano ka yi maka waƙa Na Nuhu Sunusi Sarkina.

‘Y/Amshi: Ali gadanga ɗan Ibrahim,

:Sarkin Gayan mu ne,

:Kirmau Ubangidan Gabasawa dabbar Wahabu taken giwa.

13.              Jagora: Yau ka zam uban al’umma sautin amon Gaya,

:Kai ne arotakin gasa ƙarfe ja ragamar Gaya,

:Mai ƙin ya ji ni dole ya kauce ko dai ya zagaya,

:Ka zama ginshiƙin al’umma bangon mutan Gaya,

:Alan Aminu Mai Kano ne ke sautin sarkina.

‘Y/Amshi: :Ali gadanga ɗan Ibrahim,

:Sarkin Gayan mu ne,

:Kirmau Ubangidan Gabasawa dabbar Wahabu taken giwa.

14.              Jagora: Abagayawa nai muku murna wannan tagomashi,

:Abagayawa har da maɗatai suna ta karsashi,

:Yau ga wuƙa a kwiɓin sarki sannan ta mokashi,

:Wuƙa ta kwiɓi yanke hukunci sannan tamokashi,

:Wannan tamokashin taya yaƙi Ali gadanga ka ji batuna.

‘Y/Amshi: :Ali gadanga ɗan Ibrahim,

:Sarkin Gayan mu ne,

:Kirmau Ubangidan Gabasawa dabbar Wahabu taken giwa.

15.              Jagora: Don dole ne wajen silar waƙa ta na yi gaisuwa,

:In gai da ma’ajin HausawaAhmadu gaisuwa,

:Ahmad Idris Akanta ga taka gaisuwa,

:Ya ɗau gaɓar in tsira waƙa gun Ali gaisuwa,

:Allah ƙara so da biyayya Alan Kano na kai saƙona.


 



[1] Bikin bayar da sanda ga sabon sarki yana cikin muhimman bukukuwa da ake yi bayan an tabbatar da sabon sarki. Ma’anarsa sarki zai shia ofis ya fara gudanar da harkoki na mulki. Wannan biki an fara shi a qasar Hausa ayan zuwan Turawa. Ma’ana Turawa ne suka kawo shi.

[3] Hira da (Dr) Aminu Ladan Abubakar Sarkin ɗiyan Gobir. Ranar 29/8/2023 a ofishinsa da ke kan titin gidan zoo, da qarfe 10 na safe.

[4] Takardar da aka gabatar a filin taron ranar bayar da sanda wadda wazirin Gaya SSG na Kano ya karanta Alh Usman Alhaji Usman

[5] Awartaki makama zafi. Wani qarfe ne da maƙera suke amfani da shi don dauko ƙarfe daga wuta. Kuma shi ne qashin bayan ƙira.

 

Post a Comment

0 Comments