Ticker

6/recent/ticker-posts

Kukan Talaka Rabonsa: Muryar Makada Bala Gando Ga Shugabannin Zamani

Citation: Bunza, U.A. and Faruk , A. (2024). Kukan Talaka Rabonsa: Muryar Makaɗa Bala Ganɗo ga Shugabannin Zamani. Ginshiƙin Nazarin Salon Waƙoƙin Hausa, 123-131. www.doi.org/10.36349/djhs.2024.v03i01.015

Kukan Talaka Rabonsa: Muryar Makaɗa Bala Ganɗo ga Shugabannin Zamani

Umar Aliyu Bunza
Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya
Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato
aliyu.bunza@udusok.edu.ng
mualiyubunza@gmail.com
07063532532

Da

 Abdurrahman Faruk
Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya
Jami’ar Umaru Musa Yar’adua, Katsina
abdurrahman.faruk@umyu.edu.ng
08065547688.

Tsakure: Sunan wannan maƙala shi ne, ‘Kukan Talaka Rabonsa: Muryar Makaɗa Bala Ganɗo Ga Shugabannin Zamani. An shirya wannan maƙala ce domin a yi nazarin muryar Bala Ganɗo a cikin wata shahararriyar waƙarsa mai suna, “Ba A Gane Manya Sai Ci Ya Samu”’don a fito da kokawarsa ga wani haƙƙi da aka hana masa. Ita waƙa hanya ce ta bayyana kai da isar saƙonni masu yawa ga jama’a. An zaɓi a yi nazarin wannan waƙar ce saboda kasancewarta mai ɗauke da muhimman bayanai da ke nusar da shugabanni ga irin halin da talaka yake tsintar kansa a duk lokacin da aka hana masa wani rabo da ya dace ya samu. An yi amfani da dabarar kawo ɗiyan waƙoƙin da aka tsinci wata magana mai muhimmanci da kuma kusanci ga shugabanni, sannan aka yi sharhi gwargwado. An ɗora Ra’in Mazhabar Gudummuwar Adabi Ga Al’umma (Psychoanalytical Theory) na Gusau (2015) a kan wannan maƙala. A ƙarshe, wannan takarda ta gano wasu zantuka da talaka yake furtawa a duk lokacin da wani ya hana ya sami rabonsa. Daga cikin ire-iren zantukan da aka gano akwai: ‘Bakin da Allah ya tsaga…’, da ‘kura da shan bugu’ da ‘arziki sai Allah’ da ‘kifi na ganin ka mai jar koma’ da sauransu. Makaɗa Bala Ganɗo ba kanwar lasa ba ne wajen isar da saƙon talaka ta wannan fuska a cikin waƙoƙinsa.

Fitilun Kalmomi: Kuka, Talaka, rabo, murya, shugaba da zamani

Gabatarwa

“Talaka bawan Allah!” Haka Hausawa suke yi wa talaka kirari. A zamantakewar al’umma, talaka shi ne mai ƙarancin hali na dukiya da ƙarfin mulki wanda kodayaushe shi ake mulka da kuma nuna wa fin ƙarfi. A duk lokacin da aka nuna wa talaka fin ƙarfi, yakan yi amfani da hikimar magana wajen yin shaguɓe da bayyana damuwarsa. Yin haka na sa talaka ya  huce haushinsa, ya samu sauƙi ga abin da wani na sama gare shi ya aikata masa.

Waƙa na ɗaya daga cikin hikimomin magana da talaka yake amfani da su don ya yi shaguɓe ga wani da yake ganin ya ci haƙƙinsa. Ita waƙa wata maganar hikima ce da wasu mutane suke amfani da ita wajen isar da saƙo ga al’umma. Bala Ganɗo Ambursa na cikin talakawan da suka yi amfani da waƙa don huce haushinsu da yin Alla-wadai ga wasu da yake ganin sun hana shi samun wani rabo nasa. Manufarmu cikin wannan maƙala ita ce sharhin muryar Bala Ganɗo a cikin wata shahararriyar waƙarsa mai suna, “Ba a Gane Manya Sai Ci Ya Samu”’don fito da kokawarsa da kici-kicinsa ga wani haƙƙinsa da aka hana masa.

Ma’anar Waƙa

A cikin Sa’id (2006: 466), an bayar da ma’anar waƙa da cewa, “Waƙa wata tsararriyar magana ce da ake rerawa a kan kari ko rauji.” Masana da manazarta da yawa sun tofa albarkacin bakinsu game da ma’anar waƙa. A wannan gaɓa, an kawo wasu kaɗan domin su ba da haske kan abin da ake magana, wato waƙa. Daga cikin waɗannan ma’anoni akwai:

Ɗangambo (2007: 6) wanda ya ce, “Waƙa wani furuci (lafazi ko saƙo) ne cikin azanci da ake aiwatarwa ta hanyar rerawa da daidaita kalmomi cikin wani tsari ko ƙa’ida da kuma yin amfani da dabaru ko salon armashi. Shi kuma Yahaya (1984:3) ya bayyana waƙa da cewa, “Maganar hikima ce da ake rerawa ba faɗa kurum ba wadda ke da wani saƙo da ke ƙunshe cikin wasu kalmomi zaɓaɓɓu tsararru kuma zaunannu.””Shi ma Gusau (2003:4) cewa ya yi, “Waƙa wani zance ne shiryayye cikin hikima da azanci da yake zuwa gaɓa-gaɓa bisa ƙa’idojin tsari da daidaitawa a rere cikin sautin murya da amsa-amon kari da amshi.”

Yahaya da wasu (2007:21) sun bayyana waƙar baka da cewa, “Zance ne sarrafaffe, aunanne wanda ake aiwatar da shi ta bin hawa da saukar murya, mai zuwa a gunduwowin layuka da ake rerawa bisa wani daidaitaccen tsari, wani bi har da kiɗa.”

Ta hanyar lura da waɗannan ma’anoni, wannan takarda na ganin cewa, “Waƙa wata tsararriyar hanyar magana ce da ake isar da saƙonni mabambanta a cikinta ta dabarar saƙar kalmomi da kuma lugudensu.

Taƙaitaccen Tarihin Rayuwar Makaɗa Bala Ganɗo

Cikakken sunan Bala Ganɗo na yanka shi ne Muhammadu, sai dai an fi sanin sa da Bala Ganɗo. Ba kasafai ake jin mai kiran sa Muhammadu ba, domin ba kai tsaye ake gane wanda ake magana kansa ba, sai an ce Bala Ganɗo. An haifi Bala Ganɗo a shekarar 1958 a cikin garin Ambursa na jihar Kebbi a wata unguwa mai suna Shiyar ‘Yan Kurin Haƙo. Bala Ganɗo mutum ne mai matsakaicin tsawo, mai yawan fara’a da wasa da dariya. Ya fara waƙa tun yana matashi, kuma ya yi waƙoƙi da dama. Waƙarsa da ta fi fice ita ce waƙar “Ba A gane Manya…”wato waƙar da wannan maƙala ke nazarin kukan talaka a ciki.[1]

A tsarin waƙa, Bala Ganɗo yana gudanar da waƙoƙinsa ne tare da taimakon masu kiɗa da amshi. Waƙoƙin Bala Ganɗo sun ƙunshi jigogi da mabambanta. Bala Ganɗo ya rasu a gidansa ranar Talala a shekarar 2017 yana da shekaru 65 a sanadiyyar ciwon ciki. Allah ya gafarta masa.[2]

Taƙaitaccen tarihin waƙar Ba A Gane Manya Sai Ci Ya Samu

An fara aza harsashin wannan waƙa ce a shekarar 1997 lokacin mulkin tsohon gwamnan Kebbi Abubakar Musa Garkuwan Yawuri. A wannan shekarar ce gwamnatin Kebbi ta shelanta rabon takin zamani a garuruwa da dama, ciki kuwa har da garin Ambursa. Mutane da yawa suka fita wajen neman takin, ciki har da Bala Ganɗo da abokansa: Abdu Fati da Bala Haske. A can wajen rabon takin ne wani abu na rashin jituwa ya ratsa tsakanin su Bala da masu rabon taki abin da ya kawo suka fara furta kalmomin arashi kai tsaye. Bala Ganɗo ne ya fara kawo arashi a sigar waƙa, shi ma Abdu Fati ya jefo nasa, sai Bala Haske ya ƙarasa. Daga wannan ne Bala Ganɗo ya faɗaɗa arashin nasu, ya gina cikakkiyar bakandamiyar waƙarsa da ya kira, “Ba A Gane Manya Sai Ci Ya Samu.”’A yau waƙar ta yaɗu ko’ina a cikin jihar Kebbi har ana sanya ta a gidajen rediyo da talabijin na jihar Kebbi. A cikin wannan waƙa, Bala Ganɗo ya kawo wasu ɗiyan waƙa da ya nuna yadda talaka ke kallon yadda shugabannin zamani ke zaluntarsa. A wannan takarda an yi sharhin wasu ɗiyan waƙar domin bayyana saƙon Bala Ganɗo ga al’umma baki ɗaya.[3]

 

Ra’in da Aka Ɗora Maƙalar

An ɗora wa wannan maƙala a kan Ra’in Gudummuwar Adabi ga Al’umma (Psychoanalytical Theory) na Gusau (2015). Mazahabar tana koyar da yadda adabi ke taka muhimmiyar rawa dangane da zamantakewar rayuwar al’ umma. A cikin wannan mazhaba, ana bayyana yadda adabi ke da tasiri sosai a kan ala’adun al’umma da ma fasahohinsu da kuma yadda adabin yake shafar rukunonin rayuwa (Gusau, 2015: 41). Dangantakar wannan Ra’i na Mazhabar Gudummuwar Adabi Ga Al’umma (Psychoanalytical Theory) da wannan maƙala ita ce ta fuskar yadda mazhabar ke fayyace rawar da adabi kan taka wajen bunƙasa zamantakewa da fasahohi da al’adun al’umma. Wannan maƙala ma ta waiwayi yadda adabin waƙar baka ya yi ruwa da tsaki wajen bayyana zamantakewar da ke tsakanin talakawa a ƙasar Hausa da kuma shugabanninsu a wannan zamani. An yi haka ne ta hanyar nazarin gudummuwar da waƙar Makaɗa Bala Ganɗo ta bayar wajen fito da huce haushin talakawa a kan hana su wani haƙƙi da shugabanninsu suke yi. Ke nan da Ra’in Mazahabar Gudummuwar Adabi da wannan maƙala duk jirgi ɗaya ya ɗauko su. 

Muryar Makaɗa Bala Ganɗo Ga Shugabannin Zamani

Yanayin sautin magana ko kuma yanayin amon ganga ko wani abin kiɗa shi ne murya (Sa’id, 2006: 353). Murya har wa yau na nufin saƙon da kan fita daga bakin wani mutum ko rukunin wasu mutane mai ɗauke da ra’ayinsa ko ra’ayoyinsu.[4]. Yayin da shugaba ke nufin jagora ko ja gaba wanda ya ɗau nauyin ragamar jama’a ko wata ƙungiya ta mutane (Sa’id, 2006: 415). Idan shugaba ya wuce ɗaya ya kai biyu ko fiye da biyu sai a ce shugabanni. Dangane da kalmar zamani kuwa, ana iya cewa yayi ke nan ko lokaci ko lokacin da ake ciki ko mai ci (Sa’id, 2006:489). Kodayake Ilyasu (2020) ya ce zamani na nufin lamarin da ke gudana yanzu na yayi da ya shafi almundahana da cuta. Ke nan idan aka ce shugabannin zamani, ana nufin shugabannin wannan lokaci marasa tausayi. A wannan fasali an bi wasu kalamai da muryoyin Makaɗa Bala Ganɗo da nufin nazarin saƙon da suke bayyanawa na huce haushinsa a matsayinsa na talakan Nijeriya da aka hana shi takin zamani.

Kukan Talaka Rabonsa

Talaka shi ne mutumin da bai riƙe da wani muƙami na sarauta ko kuma maras wadata (Sa’id, 2006: 423). Talaka ya haɗa duk mutumin da ba shi da wata kafa ta faɗa a ji a hukumance. Yana kuma ɗaukar mai ƙaramin ƙarfi da ba ya da isasshiyar wadata ta dukiya.  A zamantakewar al’umma, talaka yana damuwa ne da abin da yake rabonsa. Rabo a nan yana nufin wani abu da mutum ya cancanta ya samu. Kowane talaka yana kwaɗayin samun abin da ya cancance shi cikin abin da hukuma ko wani mutum ke rabawa. A duk lokacin da talaka ya nemi wani abu da ya dace ya samu, sai kuma wani mutum ya zama sanadiyyar talakan ya rasa wannan abu, to, yakan ji ciwon lamarin ya kuma tsani wanda ya hana ya sami abin. Wannan kan sanya talaka ya koka, ya ji takaici, wani lokaci ma har a sami yankewar hulɗa tsakaninsa da wanda ya yi masa wannan shiga hanci da ƙudundune.

Bala Ganɗo Ambursa ya yi amfani da basirarsa ta waƙa ya bayyana takaicinsa kan yadda aka hana shi samun takin zamani alhali kuwa ya cancanci ya sami nasa rabon. Ga abin da ya faɗa a wannan ɗan waƙa:

Jagora: Ai farko abin da yas sa ni ni aza waƙag ga,

Ni dai abin rabo shi yas samu da haƙƙe nau,

Sai nig ga an rabe an ce ni ban samu ba,

Wai su wane had da cewa mi nika dibin su.

A wannan ɗan waƙa Bala Ganɗo ya nuna sanadin aza harsashin wannnan waƙa “Ba A Gane Manya Sai Ci Ya Samu’ Bala mutum ne ma’aboci wasa da raha cikin mutane. A wannan shekara ta 1997 gwamnatin jihar Kebbi ta fitar da takin zamani domin a raba wa manoma. An kai buhuhuwan taki masu yawa a kowace gunduma, sannan aka shelanta ranar da za a yi rabon takin. A garin Ambursa, tun da sanyin safiya mutane suka hallara a wurin rabon takin a unguwar Tudun Wada kusa ga sabon ofishin ‘yan sanda da ke kan hanyar zuwa filin jirgin sama. Bala yana cikin waɗanda suka yi sammako zuwa can. Ya ci gaba da kai-kawonsa yana masha’a da mutane da zaton zai sami taki. Can zuwa yamma sai jami’an rabon takin suka sanar da taron jama’a cewa taki ya ƙare. Wannan abu fa ya ba mutane mamaki da haushi. Jama’a suka shiga watsewa cikin ɓacin rai, wasu kuma suna Alla-ya-isa. Shi kuma Bala wannan lamari ne ya sa ya assasa wannan waƙa. Wannan abu ne sananne duk lokacin da aka taɓa mai ƙaramin ƙarfi, sai ya yi amfani da harshensa ya furta magana mai zafi domin rage raɗaɗi na abin da wanda ya fi shi ƙarfi ya yi masa.

Bakin Da Allah Ya Tsaga, Bai Hana Shi Abinci

A halin zaman tare, mutane sun bambanta dangane da zaɓen abokan mu’amala. Yawancin lokuta, zamantakewar tana kasancewa ne ta ƙwarya ta bi ƙwarya. Talaka na kallon masu mulki da masu hannu da shuni a matsayin waɗanda ba su buƙatarsa sai dole. Duk wata kafa ta samu da walwala suna katange talaka, su tanada wa kansu kawai. Irin wannan yanayi yana sa talaka ya furta kalamai iri-iri da ke nuna ya ji takaicin an hana shi ya sami wani abu. Duk da kuwa ya yi imani da cewa, ba mai hana wani samun arziƙi sai Allah. Shi ma Bala Ganɗo irin wannan furuci ne ya yi lokacin da aka tabbatar masa da cewa taki ya ƙare. Ga shi kuwa ya kwaɗaita wa ransa za ya samu. Ga abin da ya ce:

Jagora: Allahu Ƙadirun wasu dai ba su buƙatam mu,

Kowa da inda Allah yay yi abincinai.

A al’ummar Hausawa, talaka yana da yaƙinin abincin kowane bawa ba ya wuce shi. Yana sane da karin maganar da ke cewa rabon kwaɗo, ba ya hawa sama. Talaka na sane da cewa, a cikin jama’a ana samun rashin jituwa tsakanin wasu mutane. Wasu kan bi kowane mataki don ganin sun hana wani samun wani abu. Su kuma hanyoyin samun abinci suna da yawa. Haka kuma hanyar abincin wani, ajalin wani ce. Shi ma Bala irin wannan ne ya kawo a wannan ɗan waƙa. A ɗan waƙar ya nuna Allah ne kaɗai mai ƙarfin iko da bukatar wasu ba ta hana ikonsa. Ke nan hana shi taki da jami’an rabon suka yi, ba ya hana shi samun wasu hanyoyi na samun abinci tun da Allah ba ya barin wani bawa ya rayu ba tare da abin da zai ci ba.

 

 

Kura Da Shan Bugu , Gardi da Karɓe Kuɗi

A tsarin zaman duniya, mutane kashi biyu ne. Akwai waɗanda suke wahala domin samar da abin da zai inganta zaman jama’a. Akwai kuma rukunin waɗanda suke cin moriyar wahalar wasu (Ewa-Udu, 2008).  A al’ummar Hausawa ma, masu ƙaramin ƙarfi-talakawa suke nemo abin da yake ƙarfafa ɗorewar ci gaban al’umma. Su ke ainihin ayyukan ƙarfi masu wahala kamar noma da kiwo da dako da sauransu. A ƙarshe kuma, su suke rasa walwala ko madafa daga yawancin abin da suka sha wahala kansa. Talakawa su ke siyasa da agaza mata, su ke yin tururuwa wurin jefa ƙuri’a don fatar su sami shugaba mai tausayin su. Da zarar aka kammala zaɓe, aka rantsar da waɗanda suka lashe zaɓe, suka samu suka haye madafun iko, sai kuma talaka ya tashi a tutar babu.

Daga ɓangaren masu hali da masu mulki da attajirai, yawancin lokuta suna cikin inuwa sukan sanya talakawa aiki ko a bisa tsarin yarjejeniyar jinga ko gayya da makamantansu. Abin da suke yi kawai shi ne su sanya ido da ba da umurni, sai kuma ba da shawara. A ƙarshe kuma su suke kwashe amfani na abin da talakawa suka sha wahalarsa ta hanyar sayewa ko yaudara da sauransu. Irin wannan yanayi yana sanya talakawa su riƙa furta kalamai da suke bayyana damuwarsu ga abin da musamman shugabanninsu suke yi musu. Bala Ganɗo ya nuna irin wannan damuwa inda ya ce: 

Jagora: Kai ai ‘yan yara suka yaƙin kamun ‘yan kaji,

Haƙ ƙarƙashin rihewa ‘yan yara ka kurɗawa,

Kai hac cikin haki wasu‘’yan yara ka sa kansu,

To had da tuntuɓe wasu ‘yan yara ka rabkawa.

Kai hak kututturu wasu ‘yan yara ka takawa,

Kai hac cikin ƙaya wasu ‘yan yara ka hwaɗawa,

‘Kai wane kai taro dac can na tare wajjen ga,’

Suna ta yin hwaɗa wa juna ba su kame ba.

 Sui ƙoƙari su kame ‘yan yara su jinƙe cab,

A zo wurin a yanke ‘yan yara ka taushewa,

A zo wurin a hige ‘yan yara ka higewa,

A zo wurin rabo hihhike suka samowa.

Jagora: Su ko manya-manya su ke taushe guraye.

Jagora: Yaro wanda ad da tsoka ɗan gata na shi.

A waɗannan ɗiyan waƙa, Bala ya yi amfani da yara da wani aiki da galibi ya rataya ga yara ne. Ya yi haka ne domin ya wakilci talakawa da ayyukan da suke yi. Kamun kaji a yanka domin wata hidima yara suke yi. A wajen kamun kaji, yara kan yi iya ƙoƙarinsu, su shiga lungu da saƙo, su yi nan, su yi can, su mayar da abin raha har su kama. Wani lokaci har sukan yi faɗa a tsakaninsu. A ƙarshe, rabon yaro zai samu cikin naman kajin nan bai taka kara ya karya. Mai uwa a bakin murhu daga cikin yaran, shi yake samun rabo mai tsoka. Su kuma manya da ba su yi ɗawainiyar kamun kajin ba, su ne ke samun babban rabo kamar cinya da haƙarƙari ko awaza.

Idan aka kwatanta waɗannan ɗiyan waƙa da zamantakewar jama’a, za a ga haka talakawa suke rayuwa. Ga misali, a fagen siyasa, talakawa ne ke kuwwa, su suke taruwa cikin rana, su suke banga, su suke layin jefa ƙuri’a, su suke faɗa da hayaniya tsakaninsu, amma kuma abin da suke samu kaɗan ne. Manyan ‘yan siyasa da aikinsu bai wuce ba da umurni ba, su suke cin moriyarta, su kuma suke samun amfani mai yawa daga gare ta.

Kifi Na Ganinka Mai Jar Koma

Ita ma wannan karin magana, Ganɗo ya yi amfani da ita don ya koka dangane da halin da akan saka talaka a ciki a ƙasar nan. A halin rayuwa, ana samun wani rukuni na mutane da suke aikata wani abu maras kyau da ba su so a sani, kuma suna ganin ba a sani ba. Wani lokaci ana sane da abin da suke aikatawa, illa an yi biris ne kawai, aka ƙyale su. Talaka na duban manyan mutane da sukunin aikata wasu ayyuka waɗanda idan ba manyan ba ne ba, babu wanda ya isa ya aikata. Yawanci, manyan suna amfani da damar da suke da ita ta hali da matsayi na mulki wanda yake hana a nuna musu yatsa a sarari. Ganin cewa sun sami wannan tikiti, sai wasu daga cikinsu su riƙa aikata abubuwan da suka ga dama.

Talakawa a lokuta da dama sukan yi kamar ba su san abin da shugabanni suke aikatawa ba. Idan wata dama ta samu, to nan suke jifar su da habaici da zambo domin su huce haushin abin da ake yi musu. Irin wannan yanayi ne Bala Ganɗo ya yi amfani da shi har ya kawo ɗan waƙa inda ya ce:

 Jagora: Abin da yay yi min ciyo Gamɗo uban Mansur,

Yak koma yay yi min zahi Gamɗo Uban Mansur

Wai sai ina ta kuwwa taki ya samu,

Wai sai ina ta murna taki ya samu,

Mun tai wurin rabon taki can aka tara mu,

Mun sha baƙar wuya rana sai taw watce mu,

To munka zo cikin inuwa sai muka zazzauna,

Kowab biyo shinai muna kallon hadarin kaji,

Saboda ba mu ‘yam mata ba su buƙatam mu.

A wannan ɗan waƙa Bala ya bayyana jin takaicinsa na abin da aka yi musu a filin rabon taki. Unguwar Tudun Wada a wancan lokaci fili ne da ke da ƙarancin bishiyoyi na samun inuwa. Fili ne fayau, rana tana haskawa sosai. Ba wani dausayi na samun sanyi. A irin wannan yanayi Bala Ganɗo da sauran talakawa suka yi cincirindo, suka taru a wurin tun da sanyin safiya har yamma. Idan zafin rana ya dame su, sai su taru a ƙarƙashin wata ‘yar bishiya. Haka mutane suka kasance ƙungiya-ƙungiya.

Ana cikin wannan hali ne, sai jami’an rabon taki suka iso. A maimakon su tausaya wa jama’a, sai ya zama babu wata kulawa ta kirki da suka nuna musu. Wannan halin ko-in-kula  ashe ya yi wa Bala zafi, ya kuma riƙe lamarin a zuciyarsa. Wannan ya sa ya soki jami’an rabon takin a ɗangonsa na ƙarshe na wannan waƙa. A ɗangon Bala ya aibata su da son mata.

A zamantakewar Hausawa, ana bai wa mata kulawa fiye da maza saboda tausaya wa ga rauninsu ko kuma sha’awarsu da ake yi. Da yawa ana lura da manya suna kula ‘yan mata ne saboda sha’awa ba don tausayi ba. Irin wannan wannan kuma yana ba maza haushi ainun. Wannan lamari ne ya sa Bala ya yi furucin, ya nuna idan da ‘yan mata ne suka zo wurin da jami’an rabon takin sun ba su kulawa ta musamman.

 

 

Arziki Sai Allah

Wannan zance ma talakawa kan yi amfani da shi da nufin su nuna wa azzaluman shuwagabanni cewa, babu mai azurtawa sai Allah. Duk wani abu na alheri da mutum yake samu, Allah ne ke bayar da shi. Kowane mutum yana son ya sami arziki. Wannan ya haɗa da lafiya da ‘’ya’ya da dukiya da sauransu. Kowane talaka yana faɗi-tashi domin samun arziki, musamman na dukiya. Wani kan sami dukiya ta hanya mai sauƙi, wani kuma sai ya sha matuƙar wahala kafin ya sami gwargwadon arzikinsa. Talakawa na gudanar da sana’o’i mabambanta domin neman nasu arzikin.

A duk lokacin da wani talaka ya kama hanyar samun wani abu na arziki, ya kuma hangi wani mutum musamman daga cikin shugabanni yana ƙoƙarin toshe hanyar, yakan ji babu daɗi. Wani lokaci akan sami wani babba ya ɗauki alwashin toshe hanyar da wani talaka zai sami wani abin alheri na arzikin. Akan sami wasu daga cikin talakawan waɗanda sukan mayar da lamari ga Allah, su nuna ba mai iya hana su samun arziki sai Allah. Irin wannan tauhidi abu ne sananne a bakunan Hausawa da yawa. Wasu kuwa sai su ƙullaci shuwagabanni a kan haka. Shi dai Bala Ganɗo yana cikin masu mayar da lamari ga Allah. Ya yi wannan furuci lokacin da aka shelanta cewa taki ya ƙare, bayan sun yi jira na tsawon yini guda. Ga yadda ya koka:

Jagora: Nic ce to shi minahikin mi shika wa tsuki?

Wai ba a ba ni taki ban shiga layi ba.

Jagora: Allah ka yin hatci ko da ban sa taki ba,

Na saba yin hatci ban ko sa taki ba.

Jagora: Sai in tallabo dame in kai haƙ ƙofata.

Jagora: In Allah shina ruwa komi zan samu nai.

Noma babbar sana’a! Noma na nufin sana’a ta karta ƙasa da fartanya don a raba shuka da haki. Idan aka shuka kayan amfanin gona, sai a ce an yi noma. Noma dai ya ƙunshi karta ƙasa da ta da ta da yin kuyya don gyaran shuka (Gusau, 1983; Alhassan da Wasu 1988; Yahya 1984;  Garba; 1991; Gumel 1992; Safana 2007; Idris 2009; Rima da Wasu 2000 da Ado da Ibrahim, 2021). Dukkan waɗannan manazarta sun yarda da cewa, noma sana’a ce ta karta ƙasa da fartanya don a raba shuka da haki. Idan aka shuka kayan amfanin gona, sai a ce an yi noma. Noma ya haɗa da yanayin kiwon dabbobi da tsuntsaye da ƙwari don samun wani biyan buƙata daga gare su. Ke nan, noma gyaran gona ne tare da aiwatar da wasu zayyanannun shirye-shirye a lokacin damina ko rani da aka tsara kuma aka tanada da nufin samar da abinci da sauran kayayyakin masarufi da rayuwa ke buƙata.

Noma daɗaɗɗiyar sana’a ce a ƙasar Hausa, shi ya sa ma Hausawan ke yi mata kirari da, “Na duƙe tsohon ciniki, kowa ya zo duniya kai ya taras.” A taƙaice, noma sana’a ce ta karta ƙasa, a zuba wata ƙwayar abinci da nufin idan ruwan damina ya zo, a sami amfanin gona mai albarka. Sana’ar ta haɗa da shuke-shuken kayan marmari da na sarrafa abinci a lambu da ma kiwon dabbobi da tsuntsaye da ƙwari don amfanin Ɗan’adam.

Noma fitacciyar sana’a ce da talakawa suke riƙo da ita don samun arziki na dogaro da kai. Talaka na tinkaho da noma a matsayin abin da zai iya duƙawa ya yi da zufar jikinsa, ya kuma sami arziki. Bala Ganɗo na cikin mutane da suke duƙawa su yi noma da kansu a lokuta da dama. Shi kuma takin zamani yana agaza wa yabanya da take cikin gona maras takin gargajiya. Haka kuma takin yana taimakon ƙaramar yabanya wajen saurin girma, musamman wadda ruwan sama ya yi wa yawa, sanyi ya rinjaye ta. Ire-iren waɗannan dalilai suka sanya talaka yake bukatar takin zamani don ya sa a gonarsa.

A ɓangare ɗaya, talaka na sane da ko da taki ko babu, samun amfanin gona abu ne daga Allah. Ikon Allah yake sanya iri da ake shukawa cikin ƙasa ya tsiro, ya girma har ya ba da abin da ake bukata. Muhimmin abu dai ga talaka, Allah ya ba da ruwan sama domin samun ruwan shi ne sila na ingancin damina, a sami abinci. Wannan tauhidi ne Bala ya tabbatar a waɗannan ɗiyan waƙa na sama.

Kowa Ya Tsaya Matsayinsa

A tsarin zamantakewar rayuwar al’umma, mutane sun bambanta dangane da daraja ko matsayi da kowa yake da shi. Wasu shugabanni ne, wasu attajirai, wasu malamai, wasu kuma sauran jama’a waɗanda su ne talakawa. A irin wannan yanayi, an so kowa ya tsaya matsayinsa, ya ba da gudummuwa gwargwadon matsayinsa domin ci gaban al’umma. Idan wani ya tsallake iyakarsa, ya shiga farfajiyar wani, yakan haddasa ganin laifi, wani lokaci har a sami gardama ko mugun zama.

A dukkanin rukunonin jama’a, talaka ya fi kusanci da jin sanyin malami. Shi malami uba ne, kuma jagora ga talaka, musamman ga al’amurran da suka shafi koyo da koyarwa na addini. Wannan ya sa ƙimar malami ga idon talakawa babba ce. Darajar malami ga talakawa ya sa suka fi ganin laifin malami da zarar ya tsallake matsayinsa na malanta, ya shiga wani na daban. Talakawa na kiran malamin da ya shiga wata sabga da sunaye kamar malamin fada ko malamin siyasa ko jam’iyya da sauransu. Sunayen na biyowa ne gwargwadon inda aka ga malami ya karkata. Bala Ganɗo ya kawo irin wannan suka da talakawa ke yi ga malamin da ya shiga fagen da bai dace ga malamai ba. Ga abin da yake cewa:

Jagora: Mallamin ga mai ce muna an kashe yin roƙo,

Can nig ga nai gidan Alhaji Sani shina roƙo.

Jagora: Ga shi yay karatu da yawa ya watce mai,

Don na ga nai wurin hwati saboda kwaɗan sure.

Jagora: In wanga yab biya wai a kawo na malammai,

Da wanga ya wuce kai ku kawo na malammai,

A bincika ga Ƙur’ani wag ga na malammai.

Jagora: Ai mallamin ƙwarai ba salare yaka dako ba,

Shi mallamin ƙwarai na can zaune da littahwai,

Ai na ga nai da bulala tare da ‘yan yara,

Duw wanda bai karatu dole a ɗwaɗwa mai.

A ɗan waƙa na farko da aka kawo an ga yadda mawaƙin ya jingina wa wani malami yin roƙo. Shi roƙo sana’a ce da aka fi kallon aikata ta daga wurin mawaƙa da maroƙan baka. Ɗangambo (1984: 36) ya kawo ma’anar roƙon baka da cewa; ‘Yabo ne da maroƙin da ake kira ɗan ma’abba ke yi. Akan yi shi lokacin bukukuwan suna da aure ko kuma dai duk lokacin da maroƙin ya ga damar zuwa ya yi roƙo. Roƙo dai na nufin neman kyauta daga wani (Sa’id, 2006: 374). Shi kuma Yahya da wasu (2016: 401) sun kawo ma’anar roƙo, inda suka ce, “Roƙo al’ada ce da aka san mawaƙa da yin sa a inda suke sakaɗa wani kalami a cikin waƙa wanda zai bayyana bukatarsu ta neman a yi musu wani abu. A taƙaice dai, Roƙo wata hanyar samun abinci ce ga wasu talakawa. Ana yin roƙo ne tsakanin mutane ko asirce ko a bayyane. Ta kowace hanya al’ummar Hausawa dai suna ƙyamar roƙo, suna ganin abu ne na zubar da girma sai idan akwai larura. A asirce, ana yin roƙo ta yadda wani zai keɓance da wani mutum ya nemi wani abu daga gare shi. A bayyane, ana yin roƙo ne galibi a wuraren hidimar taron jama’a na aure ko suna ko naɗin sarauta da sauransu. A waɗannan wurare ake jin ɗan ma’abba ko mawaƙi yana yi wa wani kirari da zuga yana roƙonsa.

Malami a matsayinsa na mutum mai daraja cikin jama’a ba a so a gan shi yana irin wannan roƙo na bainar jama’a. A asirce ma, ba a son a ji malami yana roƙo sai idan akwai lalura, kuma ya zama keɓance ga wasu mutane ƙalilan cikin mabiyansa. A waɗannan ɗiyan waƙa, Bala Ganɗo ya soki wani malami da ya bar matsayinsa, ya shiga roƙo a bainar jama’a. A nan Bala ya bayyana abin da wasu malamai suke yi na buɗa bakinsu suna cewa, a ba da na malamai ai roƙo ne a cikin wata siga. Ya ƙarfafa zancensa da nuna babu inda aka ce a roƙi rabon malamai cikin Alƙur’ani mai girma. A ɗan waƙa na ƙarshe da aka kawo, Bala ya fito ne da siffar malamin ƙwarai ga Hausawa. Shi malamin ƙwarai ana samunsa ne a wurin karatunsa tare da ‘yan makaranta da kayan karatu. Hausawa na girmama ire-iren waɗannan malamai da suke kame kansu, su tsaya matsayinsu na malamai. Ba su cika shiga hidimar duniyar mutane ba sai don an gayyace su ko kuma ta zama dole a kansu. A cikin jama’a, malaman sukan kame kansu, ba su roƙo, ba su bayyana kwaɗayinsu ko bukatarsu ga abin wani. Waɗannan su ne Bala Ganɗo yake nufi da malaman ƙwarai.

Gargaɗi

Gargaɗi na nufin jan kunne ko yin kashedi ko horo (Sa’id, 2006: 159).  A zamantakewar jama’a, gargaɗi na taimakawa wajen kyautata lamurran mutane. Ta hanyar gargaɗi ake nusar da wani mutum ya daina aikata wani aiki saboda illarsa ga rayuwarsa ko ta jama’a. Yawancin lokuta ana samun gargaɗi ne daga na sama zuwa ga na ƙasa. Wannan ya ƙunshi gabaci na ilimi ko shekaru ko shugabanci da sauransu. Mai yin gargaɗi yana yi ne saboda abin da yake da shi na sani game da illar wani aiki da ya ga wani ya jefa hannunsa a ciki. Ana gargaɗi ne domin mutane su nisanci wani abu da yake da illa ga rayuwa ko addini ko muhalli domin a gudu tare, a tsira tare.

Makaɗa da mawaƙa na cikin rukunin talakawa da ke gargaɗin jama’a kan wani abu da suka san illarsa ga zamantakewar al’umma. Bala ya yi irin wannan gargaɗi a cikin wannan waƙa inda yake cewa:

Jagora: Duk inda za a sheri shi ɗai aka jayowa,

Wallahi na hwaɗa mai bari bai yi dubara ba,

Saboda ƙulla sheri ai ba shi da umhwani,

Duw wanda yah hwake sheri sai ya hwaɗa shi.

Sharri da ƙulla shi yana cikin abubuwa masu muni da Hausawa suke ƙyama. Sharri na nufin ƙaga wa mutum laifin da bai ji ba bai gani ba (Sa’id, 2006: 409).  Sharri na nufin ƙulla wa wani mugun abu ba tare da haƙƙinsa ba kawai domin ƙiyayya ko domin cim ma wata muguwar manufa.[5]. A zamantakewar jama’a ana so koyaushe mutum ya zama sanadi na alheri, ba sanadi na sharri ba. Bahaushe ba ya son mai ƙulla masa sharri. Idan mutum ya zama ɗan sharri ko mai ƙullin sharri, mutane kan yi kaffa-kaffa da shi. Mutane kan janye jikinsu daga wanda yake mai ƙullin sharri. Rashin amfanin sharri ya sa mutane ba su da aminci da mai ƙulla shi.

 Wani muhimmin abu shi ne Hausawa sun yi amanna da sharri kare ne mai shi yake bi. Yau da gobe, mai ƙullin sharri ko aikata sharri, wata rana sai sharri ya koma kansa. Wata rana sai ya shirya sharri sai ya faɗa ciki domin ramin mugunta ne. Ana kuma iya wayar gari kowa ya gane shi, abin da duk ya shirya a warware, ba tare da ya yi nasara ba. A irin wannan yanayi sai ya rasa`abokin mu’amala domin babu mai yarda da shi. Wannan shi ne Bala Ganɗo ya gargaɗi mutane su bar ƙulla sharri domin su tsira ga aibin da ke tattare da shi.

Kammalawa

Waƙa ta kasance tsararriyar maganar hikima da ake isar da saƙonni a cikinta. Mawaƙi kan iya shirya waƙarsa kan wani batu, sai kuma a can ciki ya baje kolin wasu batutuwa da suke taimakawa ga rayuwar mutane. Bala Ganɗo Ambursa ya bi sahun mawaƙa ya shirya wannan waƙa Ba A Gane Manya Sai Ci Ya Samu wadda a cikinta ya bayyana wasu muhimman abubuwa masu ci wa talaka tuwo a ƙwarya. An yi sharhin waɗannan abubuwa cikin wannan maƙala. Maƙalar ta gano cewa, shirya waƙa yana tusgowa ne saboda gittawar wani lamari ga mawaƙi. Ba kasafai mawaƙi ke ƙirƙira waƙa babu wani sanadi ba. A cikin wannan takarda an ji cewa, Bala Ganɗo ya assasa wannan waƙa ce saboda ɓacin rai da ya samu wajen rabon takin zamani.

Wani abu kuma shi ne idan aka lura da ɗiyan wannan waƙa, sai a fahimci akwai jan hankalin magabata don su fahimci, talakawa ba ido rufe suke ba. Suna gani, kuma suna fahimtar zalunci da shugabanni ke yi musu. Suna shiru ne domin ba su da ƙarfin fito-na-fito. Da zarar suka sami dama sai sun bayyana ɓacin ransu kowa ya ji. Irin haka ne Bala Ganɗo ya yi, an zalunce su, an hana shi taki, shi kuma ya yi amfani da waƙa ya sauke haushin da aka tara masa.

An lura akwai bukatar faɗaɗa nazari cikin wannan waƙa da sauran waƙoƙin Bala Ganɗo. Akwai batutuwan tarihi da bayanin siffofin wasu halittu da dangantakarsu da mutane da sauransu. A wannan takarda an taƙaita ne kan batu guda ɗaya shi ya sa ba a shiga cikin bayanin wasu batutuwan da aka gani cikin waƙar ba.

Manazarta

Abba, M. da Zulyadaini, B. (2000). Nazari Kan Waƙar Baka Ta Hausa. Zaria: Gaskiya Corporation.

Abubakar, R. (2023). Hira da Shi a Gidansa da Ke Unguwar Kamitawa Katsina. Ranar Alhamis 24 ga Agusta da Misalin Ƙarfe 11: 30 na Safe

Abdulƙadir, D. (1975). The Role of an Oral Singar in Hausa/Fulani Society: A Case Study of Mamman Shata. Kundin Digiri na Uku. Indiana: Indiana University.

Ado, A. da Ibrahim, S. (2021). Gudummuwar Gobirawa Wajen Bunƙasa Gundumar Malumfashi. A cikin Maishanu, I. da Usman, I. da Gobir, Y. A. (2021), Transformation in Gobir Kingdom Past And Present. Kaduna: Amal Printing Press.

Alhassan, H. da Isah, Y. da Daura, B. (1988). Zaman Hausawa. Ibadan: Evans Publishers

Amin, M. L. (2011). Gudummuwar Dr. Mamman Shata Katsina Wajen Bunƙasa Falsafar Bahaushe. A cikin Funtua, A. I da Gusau, S. M (2011), Waƙoƙin Baka Na Hausa Kano: Century Research and Publishing Ltd.

Ɗangambo, A. (1984). Rabe-Raben Adabin Hausa da Muhimmancinsa ga Rayuwar Hausawa. Kano: Maɗaba’ar kamfanin Triumph

Ɗangambo, A. (2007). Ɗaurayar Gadon Feɗe Waƙa (Sabon Tsari). Kano: Amana Publishers Ltd.

Ewa-Udu, M. (2008). Social Studies for Senior Secondary School Students. Ibadan: Evans Publishers

Garba, A. (1991). Nazarin Wasu Waƙoƙoin noma A Garin Kiyawa. Kundin Digiri na Farko. Katsina: UMYUK

Gumel, I. (1992). Waƙoƙin Noma a Ƙaramar Humar Gumel. Kundin Dirigi na Farko. Katsina: Jami’a UMYUK.

Gusau, S. M. (1983). Makaɗa da Mawaƙan Hausa. Century Research and Publishing Limited Nigeria

Gusau, S. M. (1993). Jagoran Nazarin Waƙar Baka. Kano: Benchmark Publishers Limited.

Gusau, S. M. (1996). Makaɗa da Mawaƙan Hausa. Kaduna: Fisbas Media Services.

Gusau, S. M. (2003). Jagoran Nazarin Waƙar Baka. Kano: Benchmark Publishers Limited

Gusau, S. M. (2008). Waƙoƙin Baka A Ƙasar Hausa. Yanaye-Yanayensu da Sigoginsu Kano: Benchmark Publishers Limited.

Gusau, S.M. (2009). Diwanin Waƙoƙin Baka. Zaɓaɓɓun Matanoni na Waƙoƙin Baka na Hausa. Kano: Century Research and Publishing Limited Nigeria.

Gusau, S. M. (2015). Mazhabobin Ra’i da Tarke a Adabi da Al’adu na Hausawa. Kano: Century Research and Publishing Limited Nigeria.

Hamza, M. A. (2023) Hira da shi a Makarantarsa da ke Yammawa Katsina. Ranar Alhamis 24 ga Agusta. Da Misali Ƙarfe 4:00 na Yamma

Idris, Y. (2009). Fura Farin Ciniki: Nazarin Sana’ar Fura a Garin Katsina. Kundin Dirigi na Farko. Kano: Jami’ar Bayero

Iliyasu, K. (2020). Hira da shi a Matsayinsa na Sarkin Noman Dabaibayawa Katsina a Gidansa da ke Unguwar Madawaki, Katsina misalin ƙarfe 4:30 na yamma.

Muhammad, Y. M. (2005). Adabin Hausa. Zaria: ABU Press.

Rima, J. Da Gaidam, Y. M. Da Joseph, O. (2009). Agriculture in African History. Lagos: Promise Press.

Safana, A. (2007). Sana’ar Noma da Yadda Take Bunƙasa Tattalin Arzikin Hausawa. Kundin Digiri na Farko. Katsina: Jami’ar UMYUK

Sa’id, B. (2006). Ƙamusun Hausa Na Jami’ar Bayero. Zariya: ABU Press.

Sheme, I. Da wasu (2006). Shata Ikon Allah. Kaduna: Informat Publishers

Yahya, A. B. (1984). Matsayin Waƙoƙin Baka Cikin Adabin Hausa. Maƙalar da aka gabatar a makarantar Larabci ta horon malamai mata ta Gusau ranar Laraba, 18 ga watan Yuli, 1984.

Yahya, A.B. (1997). Jigon Nazarin Waƙa. Kaduna: Fisbas Media Serɓice.

Yahya, A. B. (2016). Salo Asirin Waƙa Sabon Bugu. Sokoto: Guaranty Printers.

Yahya, A. B. da Ainu, H. Da Idris, Y. (2016). Alun Nan Dai: Sharhi Kan Waƙoƙin Da Aka Yi Wa Dr. Aliyu Magatakarda Wamakko (Sarkin Yamman Sakkwato). Zaria: Ahmadu Bello University Press.



[1] Hira da Alhaji Abdullahi Fati Ambursa. Alhaji Abdu Fati Ambursa aboki ne ga Bala Ganxo Ambursa. Shi Abdu Fati mawaqi ne, hasali ma tare suke a can wurin rabon takin, kuma tare da shi aka fara gina xiyan arashin da Bala Ganxo ya faxaxa, ya gina wannan waqa. Abdu Fati har zuwa yau yana nan raye cikin garin Ambursa. Ya yi waqoqi masu dama ga mutane da sauran abubuwa. Daga cikin waqoqinsa akwai wadda ya yi wa Mai Shari’a, Alhaji Muhammad Sulaiman Ambursa da wadda ya yi wa Kwamishina, Marigayi Alhaji Muhammad Audi Ambursa da sauransu.  Akwai waqar da ya yi sanadiyyar ambaliyar ruwa na shekara. Ga  gindin waqar kamar haka:

Ruwa ya ci gwani bale wanda ab bami garai,

Ruwa ya halakar da manyan manoman zamani.

 

Allah mai ci da xa, mai nufinshi da arziki,

Jalla ba ni abin da zan ci da yarana da shi.

 

[2] . A dubi xure na farko.

[3] . A dubi ta xure na farko.

[4]. Hira da Malam Abubakar, 2023

[5] . Hira da Alaramma Hamza Yammawa Katsina, 2023

Post a Comment

0 Comments