Citation: Dangulbi, A.R. & Hamidu, I. (2024). Tasirin Habaici a Waƙoƙin Sa’idu Faru Wajen Kare Martabar Sarki. Four Decades of Hausa Royal Songs: Proceedings from the International Conference on the Life and Songs of Makaɗa Sa'idu Faru, 3(3), 321-327. www.doi.org/10.36349/tjllc.2024.v03i03.044.
Tasirin Habaici a Waƙoƙin Sa’idu Faru Wajen Kare Martabar Sarki
Na
Aliyu Rabi’u Ɗangulbi
Sashen Harsuna Da Al’adujami’ar Tarayya Gusau.
Gsm No. 07032567689, 07088233390
Email: aliyurabiudangulbi@gmail.com
Da
Idris Hamidu
Adamawa State College of Education,
Hong
Gsm no. 080633440780
Email: idrishamidgagai@gmail.com
Tsakure
Masarautun
gargajiya gidaje ne masu daraja da ɗaukaka a idon
al’ummar Hausawa da suka kamata a girmama su a kowane ɓangare na rayuwa. Makaɗa Sa’idu Faru ya
taka rawa wajen ƙoƙarin kare martabar waɗannan gidajen
sarautu ta hanyar amfani da habaici a cikin waƙoƙinsa na sarauta.
Wannan muƙala mai suna ‘Tasirin habaici a cikin
waƙoƙin Sa’idu Faru wajen kare martabar sarki”za ta yi magana
ne a kan tasirin da habaici ya yi wajen kare martaba, da ɗaukaka darajar
masarautar gargajiya ta Sarkin yaƙin Banga Sale
Abubakar, a gundumar Ƙauran Namoda, a yankin
Arewa Maso-Yamma. Domin cimma manufar wannan muƙala, an yi amfani da hanyar samo kaset-kaset na waƙoƙin Sa’idu Faru da ya yi wa Sarkin Yaƙin Banga, a lokacin rayuwarsa. Habaici magana ce da mawaƙan Hausa suke furtawa zuwa ga sarakuna abokan hamayya ko
‘ya’yan sarakuna ko fadawa ko wasu makaɗan sarakuna da suke
adawa da sarkin da ake yi wa waƙa. Makaɗa Sa’idu Faru yana
daga cikin makaɗan fada da suka taka rawar gani wajen
kare martabar gidan sarautar gargajiya ta Banga ta hanyar amfani da habaici wajen
faɗakarwa da ilmantar da sarki game da irin shirin da ‘ya’yan
sarakuna da ‘yan adawa ko abokan hamayyarsa suke yi domin rushe martabar masarautarsa
ko kuma gidan sarautar. Makaɗa Sa’idu Faru ya yi amfani da wannan
hanya ta habaici domin ya kare martabar sarautar gargajiya daga mugun nufin ‘yan
adawa na ganin sun tarwatsa haɗin kai da sarki yake da shi tsakaninsa
da ‘yan sarautar Banga. Muƙalar ta gano cewa,
a cikin waƙoƙinsa da ya yi wa Sarkin Yaƙin Banga Sale Abubakar, Sa’idu Faru ya tabbatar da
martabar wannan masarauta a idon duniya ta hanyar jawo hankalin jama’a su
fahimci cewa ‘ya’yan sarakun da abokan hamayya ba waɗanda za a ba amana
ba ne. Koyaushe manufarsu su ƙulla wa sarki sharri
da fatar ya mutu su gaje shi, su yi sarautar Sarkin Yaƙin Banga. Muƙalar ta gano cewa
habaici dabara ce da makaɗa Sa’idu Faru ya yi amfani da ita wajen
jawo hankalin sarki da masu saurare su fahimci cewa, manufofin ‘ya’yan sarakuna
ko abokan hamayya ko fadawa ko sauran makaɗan fada zuwa ga
masarautar gargajiya, gyara kayanka ne, wanda Hausawa ke cewa ba ya zama sauke
mu raba.Sai dai wasu lokuta abubuwan da ‘yan adawa suke nunawa ga sarki ba wai
don ƙiyayya ba ce, a’a, domin su ƙara tunatar da shi ne wajen gyara tafiyarsa ta hanyar yi
wa talakawansa adalci ba tare da nuna banbanci ko son kai ba. Wannan dabara ta
amfani da habaici ta ƙara ɗaukaka daraja da
kwarjini da kare martabar Sarkin Yaƙin Banga a lokacin da yake mulki.
Fitilun Kalmomi: Habaici, Sarautun Gargajiya, Martabar Fada,
‘Ya’yan Sarki, da Abokan Hamayya.
1.1 Gabatarwa
Shugabanci irin na sarautar gargajiya salon jagoranci ne
da sarakuna da aka naɗa suke tafiyar da shi tare da haɗin kan waɗanda ake mulka. Wato, shugabanci ne na
al’umma da yake buƙatar a sami mutum jarumi, mai haƙuri da tausayi da riƙon amana da za su taimaka masa wajen tafiyar
da mulki cikin adalci ga talakawansa. Mawaƙan fada suna amfani da hikimominsu wajen zaƙulo kyawawan halaye da ɗabi’u na sarakunan da suke yi wa waƙa domin mutane su ƙara son su, su kuma girmama su. A cikin
wakoƙinsa na fada, Makaɗa Sa’idu Faru ya taka muhimmiyar rawa wajen wayar wa
jama’ kansu dangane da martaba da darajar da gidajen sarauta suke da su ga
al’umma. Ganin yadda wasu mutane da sauran al’ummar Hausawa, musamman ‘ya’yan
sarauta da fadawa da sauran ‘yan adawa suke bibiyar sarakunansu da gidajen
sarautu da mugun nufi, ya sa makaɗa Sa’idu Faru ya yi amfani da habaici
cikin waƙoƙinsa domin ya ƙasƙanta ‘yan adawa da ‘ya’yan sarakuna da fadawa
da sauran makiyan sarki a idon duniya, sannan ya kare martabar masarautun
gargajiya. Daga cikin saƙonnin da habaicin yake isarwa ga ‘yan adawa, akwai tozarta ko kushe wa ɗabi’unsu na rashin biyayya ga sarakuna da gidajen
sarautun gargajiya. Makaɗa Sa’idu Faru ya yi amfani da wannan
hanya ta habaici a cikin waƙar da ya yi wa sarkin yaƙin Banga domin ya kare martabarsa da
gidan sarautar Banga daga hassadar ‘yan adawa da abokan hamayya.
2.1 Habaici
Habaici wata magana ce da ake furtawa
zuwa ga wani mutum ko wasu mutane a matsayin hannunka- mai –sanda ko shaguɓe ko gugar-zana don wanda aka yi wa, ya ji kuma ya gyara
halayensa ba tare da an ambaci sunansa ba. Masana da manazarta sun yi bayanai
daban-daban dangane da ma’anar habaici. Bargery (1993) da Ɗangambo (1984) da Ɗangulbi (1996), sun ce, “habaici magana ce mai ɓoyayyar manufa”. Akan yi magana ce gajeruwa da
nufin isar da wani saƙo ko wani abu ga wanda aka yi maganar
dominsa. Wato akan yi habaici a cikin sigar karin magana don a gargaɗi wani mutum ko a yi masa hannunka- mai- sanda ko shaguɓe ga wani abu maras kyau da yake aikatawa domin ya ji, ya
daina.
Malumfashi da wasu, (2014:24) sun
bayyana cewa, habaici kan faru a lokacin da abu biyu ko fiye suka nuna ƙaunar su a kan abu ɗaya. Wato bisa ga al’ada irin ta ɗan adam, ba ya son ya haɗa, ko ya yi tarayya da wani a kan abu ɗaya da wani. Wannan ne ya sa Bahaushe yake amfani da
habaici don ya nuna rashin amincewarsa ga tarayya ga abin da yake so da wani mutum.
Umar (1987) ya ce “an fi samun habaici a tsakanin mata masu kishin juna, wato a
tsakanin mata masu kishi da juna aka fi samun habaici. Kamar yadda Koko (1989) ta
ce, habaici tsoro ne kuma yakan zo cikin sifar takala da kuma ramuwa a fakaice.
Koyaushe habaici yana tafiya tare da arashi da yake nuna shakku ko razana ta
mai magana zuwa ga wanda yake yi wa maganar a cikin sigar karin magana. Misali;
“wanda ya gani shika faɗi”.
Swift ed (2023) Encyclopaedia
Britannica,ya bayyana cewa habaici wata magana ce a fakaice ta shaguɓe da ake yi wa wani don a zolaye shi ko a yi masa hannunka-
mai sanda. Ya bayyana cewa waɗanda ake yi wa habaici su ne ‘yan adawa
ko abokan hamayyar siyasa ko sarautar gargajiya.
Ɗangulbi, (2013:95). Ya bayyana habaici
da cewa, wani kalami ne da ake furtawa a kaikaice a matsayin wanka-da jirwaye
ko gugar-zana domin a musguna wa wani mutum ko a faɗakar da shi a kan wani ko wasu miyagun halaye ko ayyukan
da yake aikatawa waɗanda suka saɓa wa buƙatar al’ummar Hausawa da yake zaune tare da su.
Ya ci gaba da cewa,ana amfani da karin magana a gina habaici domin a gargaɗi mutum ya gyara halayensa . Bugu da ƙari ana amfani da kalmomin lamirin suna
miƙau kamar ‘ka/kai, ke ku su da sauransu domin a
gina habaici. Har wa yau, ana amfani da lamirin suna sakayau da dangantau da
sauransu wajen furta kalaman habaici.
Habaici wani salo ne na jawo hankalin
mutane su fahimci saƙon da ake isarwa gare su cikin gaggawa
da mawaƙan Hausa suke amfani da shi cikin waƙoƙinsu na Hausa.
3.1 Matsayin Habaici a Waƙoƙin Sa’idu Faru
Mawaƙa suna amfani da habaici cikin waƙoƙinsu domin su isar da wani muhimmin saƙo ga jama’a. Haka kuma yakan zamo salon sarrafa
harshe da dabarar jawo hankalin masu saurare su fahimci saƙon da ake son isarwa zuwa gare su. Makaɗa Sa’idu Faru ya yi amfani da habaici wajen kushe waɗannan ‘yan adawa kamar haka:
3.1.1 Amfani da Habaici wajen Ƙasƙanta ‘Ya’yan Sarakuna
Makaɗa Sa’idu Faru makaɗi ne mai hazaƙa da hikima wajen sarrafa harshensa
domin ya isar da saƙo ga masu sauraron waƙarsa cikin hanzari.Mawaƙin ya yi amfani da habaici a cikin waƙoƙinsa domin ya kushe ‘ya’yan sarakuna dangane da rashin
biyayya da kuma ƙoƙarin ganin cewa sun bi duk wata hanyar da za su ga ƙarshen mulkin sarkin da yake a kan
karagar mulki. Wannan ɗabi’a tasu ita ce take jawo hankalin Makaɗa Sa’idu Faru ya jefe su da habaici domin ya naƙasa su a idon duniya ko ga masu sauraron
waƙoƙinsa. Misali, a cikin waƙarsa wadda ya yi wa Sarkin Yaƙin Banga Sale, Sa’idu yana cewa:
Jan zakara ya yi ƙiƙiriƙi ya tare garkar gidan Ubanai,
Ya bar kwaɗɗo yana cikin rame ya laƙƙwace tsara,
Kai ni bana sai na yi lalaben kwaɗɗo na kai gaban wuta.
(Sa’idu Faru:Wakar sarkin yaƙin Banga, Sale Abubakar).
Makaɗa Sa’idu Faru ya yi wannan habaici ne zuwa ga wani ɗan sarki da suka yi takarar neman sarautar Banga da sarki
Sale, amma bai samu nasara ba. Ganin haka, sai ya koma fadama yana noman rani.
Wato, yana tu’ammali da ruwa wajen bai wa dashen kayan marmari ruwa. , wato ya
koma sana’ar noman kayan lambu har sanyi ya kama shi,wanda yin haka ga al’adar
sarauta ƙasƙanci ne ga ‘ya’yan sarauta. Hausawa suna girmama
sana’o’insu da suka gada tun daga iyaye da kakanni,saboda haka kowane gida suna
alfahari da sana’arsu, kamar yadda gidan sarauta suke alfahari da sarautarsu. A
al’adance idan aka sami wani mutum ya bar sana’ar gidansu ya koma wata wadda ba
su gada ba, to sai a kalle shi da idon ƙasƙasnci domin ya wulaƙanta sana’ar da ya gada ya koma wata ta dabam.
Saboda haka, duk ɗan sarki da ya bar gadon gidansu na
sarauta, ya kama sana’ar da ba ta gidansu ba, to ya lalace; ya ɗauki abin da zai jawo wa gidansu zubewar mutunci a idon
duniya. Makaɗa Sa’idu faru ya dubi wannana ɗan sarkin Banga da aka kayar wajen neman sarauta ya yi
masa habaici dangane da sana’ar noman ranin da ya jefa kansa, sai ya yi masa
habaici domin ya jawo hankalinsa ya bar sana’ar da ba a san gidan sarauta da
ita ba. Ya dawo cikin hayyacinsa ya rumgumi ƙaddarar shan kaye da ya yi a hannun Sarkin
Yaƙin Banga Sale Abubakar. Sai ya jefe shi
da habaici, yana cewa, jan zakara ya yi ƙiƙiriƙi ya tare garkar gidan ubanai, ya bar
kwaɗɗo yana cikin rame, ya laƙƙwace tsara, Kai ni bana sai na yi
lalaben kwaɗɗo na kai gaban wuta.
Wannan wata dabara ce ta kare martaba
da mutuncin Sarkin Yaƙin Banga a idon masu sauraro da ‘ya’yan
sarautar Banga da sauran ‘yan adawarsa. Mawaƙin ya yi amfani da habaici don ya naƙasa wannan ɗan sarki domin ya kare martabar sarkinsa.
Sa’idu Faru ya yi amfani da salon jinsintarwa,
inda ya siffanta sarki da Zakara, wato ya dabbantar da shi kamar yadda ya
dabbantar da ɗan sarki da kwaɗo. Wato dukkansu ya dabbantar da su ta fuskar siffanta kamannunsu
da ya yi da dabbobi. Ya sifanta sarkin da ‘jan zakara’ domin ya nuna matsayinsa
na fifiko ga kwaɗo, wanda ya kamanta sarki da sadaukantaka
da kwarjini bisa ga ɗan sarkin da ya sha kaye wajen neman sarautar
sarkin yaƙin Banga. Ya nuna wa jama’a da masu saurare
cewa, tun da sarkin yaƙi ya haye kujerar mulki da ya gada daga
mahaifinsa, to duk wani ɗan sarauta da yake jayayya, ya koma
gefe domin jan zakara ya yi ƙiƙiri ya tare garkar gidan ubansa. Makaɗin ya kamanta ɗan sarkin da kwaɗɗo domin ya naƙasa shi a idon masu saurare. Duk da kasancewar darajar
kwaɗo ba ta kai ta jan zakara ba a halitta,
amma Sa’idu Faru ya yi wannan haɗi ne domin ya nuna kasawar wannan ɗan sarki ga zama sarkin yaƙin Banga. Makaɗa Sa’idu Faru ya kammale habaicinsa da cewa, sai ya yi
lalaben kwaɗo ya kai gaban wuta, wato duk inda kwaɗo yake a cikin ruwa, babu shakka sanyi zai ishe shi wanda
zai hana shi ya yi walwala, sai idan an fito da shi an kara shi ga wuta sannan
ya ji zafi ya warware. Saboda haka ɗan sarkin nan da ya ɓoye cikin fadama yana noman lambu, sai ya tono shi ya danƙa shi ga sarki domin ya ladabtar da shi.
3.1.2 Amfani da Habaici wajen Ƙasƙanta Abokan Hamayya (Sarakuna)
Wasu Sarakuna suna nuna adawarsu ga
sarki saboda wani kwarjini da ɗaukaka da suke zaton ya fi su.A
sanadiyar haka sai su yi ƙoƙarin jawo hankalin mawaƙansa su koma gare su domin su yi masu
kiɗa, su bar sarkin da suke yi wa waƙa saboda su ma su samu ɗaukaka. Wannan dalili ne ya sa Sa’idu Faru ya jefi wani
sarki da habaici domin ya kare matsayin Sarkin Yaƙin Banga da ma shi kansa. Ga abin da
yake cewa kamar haka:
Sa’idu: Amman ɗaki ko yana ruwa,
Mu’azu don ya ɗara wuri,
Amshi: Ko da sarkin yaƙi na yi man rowa
Ka bar biyar wani.
Amsh: Ko da sarkin yaƙi na yi man rowa
Ka bar biyar wani.
Sa’idu: kowacce za shi ba ka bi shi ka
bi shi
Amshi: kamar bita zai yi ma,
Al’amarin duniyag ga sai Allah
ɗan Tumba Rungumi.
Sa’idu/Amshi: Duka al’amarin duniyag ga
sai Allah
ɗan Tumba Rungumi.
Sa’idu Faru: Gogarman Namoda bai magana
Wani ya walwalar.
Maimaici
(Sa’idu Faru: Waƙar sarkin yaƙin Banga)
A al’adar ƙasar Hausa, kowane sarki yana da makaɗinsa na musamman wanda ba ya yi wa kowa kiɗa sai shi. Kowane sarki shi ke ɗauke da nauyin makaɗinsa, da cinsa da shansa da suturarsa
da ta iyalansa; duk wannan sarki shi yake dauke da nauyinsu. Saboda haka, ba
wani makaɗi da zai yi wa wani sarki waƙa komi soyayyar da ke tsakaninsu, sai
ya sami izini daga sarkinsa sannan ya yi wa wani sarki waƙa. Makaɗa Sa’idu Faru yana ɗaya daga cikin makaɗan da suke da uwayen gida, bayan da ya gama zagaye-zagayen
yi wa sarakuna waƙa, ƙarshe ya kama Muhammadu Macciɗo a matsayin uban gidansa.Don haka komi kuɗinka ba zai bar ubangidansa ba, ya yi wa wani sarki waƙa, sai da izinin uban gidan nasa. A
dalilin haka ne ya sa, ya yi wa wani sarki habaici wanda ya neme shi da ya rera
masa waƙa a lokacin yana ƙarƙashin sarkin yaƙin Banga, amma ya ƙi, domin ya nuna cewa ko da Sarkin Yaƙin Banga yana yi masa rowa, ba zai guje
shi ba. Guje wa ubangida ga makaɗi kasawa ce da butulci. Saboda haka shi
Sa’idu Faru ba makwaɗaici ba ne, wanda zai yi wa wani waƙa don neman abinci ko abin duniya. Mawaƙin ya ci gaba da koɗa sarkinsa yana cewa:
Faru: Ga sarkin kiyawa ga galadima
Ga kwasau da Amadu
Amshi: Na Garba giyen Garba ɗan Hassan
Mai fada ka diba agogo nan
Faru/Amshi: Sakkwato ƙarfe bakwai cikin shawa
Ɗan Sambo ya iso.
Faru/Amshi: Sakkwato ƙarfe bakwai uban tafiya
ɗan Sambo ya iso.
Faru: Ga sarkin Kano gami da sarkin
Ikko
Sun kammale ɗiya,
Amshi: Ga sarkin Zariya da sarkin Borno
Sun kammale ɗiya,
Ga sarkin Funtuwa da sarkin Bauchi
Sun kammale ɗiya
Faru/Amshi: Ga sarkin Bunguɗu da sarkin Gobir
Sun kammale ɗiya
Ga kuma sarkin ƙayar Maradun
Mai kudu ɗan Shehu ya iso
Amshi: Ga sarkin Yauri da sarkin Gwandu
Sun kammale ɗiya
Ga sarkin Yamma gami da Arɗon shuni
Banaga ya iso
Duk duka an taru ba a yin magana
Sai Sale ya iso
Sarki ya lura ba ka yin magana
Duk sai da gaskiya.
(Sa’du Faru: Waƙar Sarkin Yaƙin Banga).
A taƙaice Sa’idu Faru yana nuna martabar Sarkin Yaƙin Banga, wadda ya ce duk sarakunan ƙasar Hausa sarkin yaƙin Banga shi ne a gabansu. Haka kuma
har sarkin Musulmi Abubakar na uku ya yarda da sarkin yaƙin Banga ya faɗi ba ya ƙarya. Wannan matsayi na daraja da makaɗin ya bai wa Sarkin Yaƙin Banga wata ƙarin daraja ce ta gidan sarautar Banga.
3.1.3 Amfani da Habaici wajen Ƙasƙanta Fadawa
Kowace masarauta tana gudana ne tare da
taimakawar fadawa. Fadawa su ne maƙarraban da suke zama a fadar sarki
domin su taimaka masa ga tafiyar da wasu al’amuran mulki, musamman ta fuskar
karɓar gaisuwa da karɓar baƙi da kuma taya sarki hira a lokacin
zaman fadanci. Haka kuma fadawa sukan kawo wa sarki rahoton abubuwan da suke
faruwa a masarautarsa da wasu wurare a wajen masarauta. Mafi yawan makaɗan fada sukan dubi yadda yanayin zaman fada yake gudana a
kowace masarauta, sai su yi ƙoƙarin faɗakar da sarki irin mutanen da yake
zaune tare da su, wato fadawa. Makaɗa Sa’idu Faru yana amfani da irin
wannan yanayi ya gano masoya sarki da kuma maƙiyansa a cikin fadawa. Akwai fadawa da suke
nuna soyayyarsu ga sarki ta hanyar faɗa masa gaskiyar abubuwan da suke faruwa
a masarautarsa domin ya ɗauki matakin gyara idan ba na alheri ba
ne. Haka kuma akwai fadawan da suke zaune da sarki, amma suna munafuntarsa ta hanyar
yi masa ha’inci suna ɓoye masa abubuwan da suke faruwa a
masarautarsa, domin kada ya samu nasara a mulkinsa. Suna ƙoƙari ta fuskar faɗa masa labaran ƙarya dangane da halin da talakawansa da
al’ummarsa suke ciki. Wannan yanayi ne da yake taimaka wa sarki ya ƙara fahimtar halaye da ɗabi’un fadawansa dangane da salon mulkinsa. A cikin
wannan hali ne makaɗa Sa’idu Faru yake amfani da habaici
cikin waƙoƙinsa domin ya kambama mai sarauta ta hanyar faɗakar da shi abubuwan da suke gudana a cikin fadarsa don
ya gane masoyansa da kuma munafukai a cikin fadawa. Sa’idu Faru yana cewa:-
Faru:Sale da sauna da mai nagarta ka riƙa na Bubakar,
Faru/Amshi: Wandara Allah ya taimake ka
riƙon kowa da gaskiya.
(Sa’idu Faru: Waƙar sarkin yaƙin Banga).
Wannan ɗan waƙa yana nuni ne ga mutanen da sarki yake
mulki domin a tsari irin na sarauta, wajibi ne sarki ya tafi da kowa a cikin
mulkinsa ba tare da nuna son rai ba. Duk da kasancewar fadawa mutane ne da suke
kewaye da sarki, sukan zama madubi ga sarki ko fitilar da zai haska ya gano
wata illa ko nasara dangane da yadda yake gudanar da mulki. Akan samu wasu
fadawa su riƙa munafuntar sarki, ta hanyar ɓoye masa gaskiyar abubuwan da suke faruwa a masarautarsa.
Sa’idu Faru bai bar irin waɗannan fadawa ba, domin yakan nuna wa
sarki hotonsu a fakaice ta hanyar yi masu habaici don ya faɗakar da sarki illar zama da su a fadarsa. Kamar yadda ɗan waƙa na sama ke nunawa, dole ne sarki ya
tafi tare da irin waɗannan mutane saboda kowanensu yana da
rawar da yake takawa a fuskar cigaban masarauta. Wato bayyana wa sarki irin waɗannan fadawa kan taimaka ma masarautun gargajiya wajen ɗaukar matakan gyara tafiyar da salon mulkinsu. Habaici yakan
taimaka wajen kare martaba da ɗaukaka darajar masarautun gargajiya a ƙasar Hausa, musamman idan aka yi
la’akari da inda Sa’idu ya ci gaba da cewa:
Faru: Ko jiya na iske gam –da- yaƙi da Tuji
Sun iske jinjimi
To! sun ko murɗe gardama’
Sun iske su bubuƙuwa ruwa
Amshi: Da nan ni kau ina gaton gaɓa
Sai niƙ ƙwala gaisuwa
Su kau sun dwaƙile ni dut
Ni kau niƙ ƙara gaisuwa
Dan nan kulmen da ac cikin gurbi
ya amsa gaisuwa.
Dan nan sai Jinjimi da yad darzaza
Yas suntule su dut
Shi kau Tuji da ad da girman baki
Yak kwashe Jinjimi
Dan nan Bubuƙuwa da tar rura tag gangame su dut.
Faru/Amshi: Ran nan nis san duniyag ga
komi na ne,
Wani mayen wani.
(Sa’idu Faru: Waƙar Sarkin Yaƙin Banga).
3.1.4 Amfani da Habaici wajen Ƙasƙanta Wasu Makaɗan Fada:
Sa’idu Faru ya yi amfani da basirar da Allah
(S.W.A) ya yi masa ta hanyar jawo hankalin makaɗan fada ‘yan’uwansa da su riƙa sa haƙuri ga duk wani mawuyacin halin da suka
samu kansu na talauci. Kamar yadda aka sani, sarakuna su suke ɗauke da nauyin makaɗansu gaba ɗaya, dangane da abin da ya shafi cinsu da suturarsu da ma
aurar da ‘ya’yan makaɗansu. Saboda haka ne, su makaɗan suke mayar da hankalinsu kacokam ga uwayen gidansu, su
ƙi yi wa kowane sarki waƙa sai nasu. Makaɗa Sa’idu Faru, ya yi wa wasu makaɗan fada habaici dangane da rashin haƙurinsu na barin uwayen gidansu su je su
yi wa wasu sarakuna da suka ba su kuɗi waƙa. Yin haka rashin haƙuri da dangana ne ga makaɗi. . Shi dai Sa’idu Faru yana ganin haka ya saɓa wa al’adar makaɗan Fada. Saboda haka sai yake yi wa
mawaƙan habaici da su tsaya ga sarakunansu
domin su kare martabarsu da mutuncinsu a idon duniya. Sa’idu yana cewa:
Faru: Kwasau taron da mun ka tai Sakkwato
Mun ɗaɗɗaki ƙawa
Amshi: Yau ba mu da haushin kiɗa da kowa yau
Ko Isa ko Gumi
Faru/Amshi: Ko da Gurso da shi da Jankiɗi yau
Sun gaida Rungumi
Faru/Amshi: Maimai
Faru: Domin in na ɗiye Ma’azu ka gyara, ɗan Tumba Rungumi,
Amshi: Kai ko ɗandada zan ki sa launi kai ar riƙa ƙasa.
Duka al’amarin duniyag ga sai Allah ɗan Tumba Rungumi.
(Sa’idu Faru: Waƙar Sarkin Yaƙin Banga).
Babu shakka waɗannan ɗiyan waƙa suna kushe makaɗan fada da ba su da azancin sarrafa harshen Hausa saboda
rashin ilimi ko gogewa a fagen waƙa.Sannan yana ƙara jaddada matsayinsa na shahararren
mawaƙin fada da sarakuna ke alfahari da shi
a ɓangaren waƙoƙin fada.Haka kuma Makaɗa Faru ya kushe mawaƙan fada da ba su da fasahar sarrafa harshe, ya ƙalubalance su da su maimaita salon
magana da yake faɗa. Ya yi masu habaici dangane da ƙwarewarsa game da harshen Hausa. Yana cewa:
Faru: Yaro in taƙamar salon magana kaka yi,
Ce tsari tsare tsara,
Amshi: Tahi tsantsame tsattsara,
Ka tsantsame tsari tsab ga tsamiya.
Faru: Tunkuɗa Tunku cikin Tukar Rukubu
Tukuɗin Tumba yai Tuɓus
Amshi: Tumba taho da ke da Tabo da Taɓo
Da Taɓus da ‘yat Tuɓus.
(Faru: Waƙar Sarkin Yaƙin Banga).
4.1 Kammalawa
Dukkan bayanan da suka gabata a cikin
wannan sun tabbatar da cewa habaici da Makaɗa Sa’idu Faru ya yi amfani da shi cikin waƙar da ya yi wa Sarkin Yaƙin Banga ya yi tasiri wajen kare
martabar masarautun gargajiya, musamman a yankin da mawaƙin yake zaune. Wato habaici babban al’amari
ne da mawaƙan baka suke amfani da shi wajen ƙara ɗaukaka daraja da kare martabar masarautun gargajiya da
raya al’adun masarautu a ƙasar Hausa. Ta fuskar ‘ya’yan sarauta
da abokan hamayya da su kansu makaɗan fada da sauran makaɗan Hausa, habaici yana taka muhimmiyar rawa wajen faɗakar da su mahimmancin dogara ga Allah wajen neman
sarauta. Haka kuma habaici yana koyar da masu neman sarauta ido rufe cewa Allah
ke bayar da mulki ga wanda ya so.
5.1 Sakamakon Bincike
Muƙalar ta gano cewa habaici dabara ce da makaɗa Sa’idu Faru yake amfani da ita wajen jawo hankalin
sarakuna su fahimci kushewar da ‘ya’yan sarakuna ko abokan hamayya ko fadawa suke
yi zuwa gare su, ba wai don ƙiyayya ba ce, a’a domin su ƙara jajircewa ne wajen gyara tafiyar da
mulkinsu ba tare da fargaba ba. Wannan dabara ta amfani da habaici tana ƙara ɗaukaka daraja da kwarjini da kare martabar masarautun
gargajiya a idon jama’a da kuma duniya baki ɗaya.
Wannan muƙala ta gano cewa, amfani da habaici a
cikin waƙar sarkin yaƙin Banga ya ilmantar da mutane da
sauran masu ruwa da tsaki a kan masarautun gargajiya muhimmancin riƙe amana da girmama gado. Yin haka ya
taimaka wajen kare martabar al’adun da sana’o’in
gargajiya da ma gidajen sarautu a ƙasar Hausa. Har wa yau, muƙalar ta gano cewa, habaici hanya ce da
mawaƙa suke bi wajen jawo hankalin ‘ya’yan
sarauta da sarakuna da fadawa su gyara ɗabi’u da halayensu domin su sami karɓuwa ga al’ummarsu har a aminta da su shugabancial’umma. Masarautun
gargajiya gidaje ne na tarbiya da ake sa ran duk wanda ya sami kansa a waɗannan gidaje ya zama kamili mai biyayya ga gidansu da
shugabanninsa domin wata rana yana iya gadon gidansu. Saboda haka, Sa’idu Faru
ya yi ƙoƙari wajen jawo hankalin ‘ya’yan sarauta da fadawa da sauransu su san cewa kyawawan ɗabi’u su ne tushen samun sarki na gari mai kwarjini da
adalci ga talakawansa. Habaici gyara kayanka ne, wanda ya fi sauke mu raba.
Manazarta
Bagari, D. (1986).
Bayanin Hausa: Jagora Ga Mai Koyon Ilimin
Bayanin Harshe. Rabat-Morocco: Imprimerie El-Maarif Al-Jadida.
Bashir A. (2012) The Morphosyntax of Diminutive in Hausa. Kundin Digiri Na Farko. Sashen Nazarin Harsun Nijeriya. Kano: Jami’ar Bayero.
Bergery, G. P. (1993).
Hausa-Enlish and English-Hausa Vocabulary. London: Oxford University Press.
Birniwa,
H.A.(1987). Conservatism and Dissent A Comparative Study of NPC/NPN and
NEPU/PRP Hausa Political Verse From Circa 1946-1983, (Unpublished) Ph.D thesis,
Department of Ni gerian Languages. Sokoto: Usmanu Ɗanfodiyo.
Ɗangambo, A. (1984). Rabe-raben Adabin Hausa da Muhimmancinsa Ga Rayuwar Hausawa. Kano: Triumph Publishing Company.
Ɗangulbi, A. R. (1996). Habaici da Zambo a Cikin Waƙoƙin Baka Na Hausa. Takardar
da aka gabatar a taron ƙara wa juna sani a Kwalejin Ilimi ta Shehu Shagari. Sakkwato
Ɗangulbi, (2013). Tasirin Habaici a Cikin Waƙoƙin Siyasa: Nazarin Waƙar Sarkin Yamman Sakkwato Alhaji Aliyu
Magatakarda Wamakko ta Alhaji Ibrahim Aminu Ɗandago. A cikin Journal of Languages and Linguistic Inquiry. Katsina: Federal
College of Education.
Encyclopedia
Britannica Updated Feb. 11,2023. An article History.
Koko, H. S. (1989).
Jagoran Nazarin Tatsuniyoyi. Sakkwato: College of Education.
Faru, S.(1950). Waƙar Sarkin Yaƙin Banga Sale Aubakar Banga. Fadar
sarki.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.