Citation: Bugaje, H.M. (2024). Nazarin Kwalliya a Waƙar Sa’idu Faru ta Sarkin Yaƙin Banga, Alhaji Sale Abubakar Ƙauran Namoda. Four Decades of Hausa Royal Songs: Proceedings from the International Conference on the Life and Songs of Makaɗa Sa'idu Faru, 3(3), 328-331. www.doi.org/10.36349/tjllc.2024.v03i03.045.
Nazarin Kwalliya a Waƙar Sa’idu Faru ta Sarkin Yaƙin Banga, Alhaji Sale Abubakar Ƙauran Namoda
Daga
Dr. Hauwa Muhammad
Bugaje
hhmbugaje@gmail.com
Sashen Harsuna da Al’adun Afrika
Jami’ar Ahmadu Bello, Zaria
Tsakure
Nazarin salo fanni
ne da masana da manazarta suka daɗe suna bincike a kansa. Haka abin yake
idan aka yi maganar nazarin salo a waƙoƙin Hausa. An sami masana irin su Yahya (2001) da Gusau (2003) da suka yi rawar gani wajen nazarin sa.
Kodayake masu iya magana kan ce “ilimi kogi ne...” wannan ya sa aka zaɓi nazarin wani
muhimmin fanni na salo a wannan maƙala, wato nazarin
kwalliya a waƙoƙin Sa’idu Faru, sai dai muƙalar za ta taƙaita ne ga waƙa ɗaya tilo wadda sha-kudun ce idan dai a
batun salo ne a waƙa. Manufar nazarin
kuwa ba ta rasa nasaba da ƙara fito da baiwar
da Allah ya yi wa wannan mawaƙi ta naƙaltar harshen Hausa da iya sarrafa shi a waƙa har a ce da wannan waƙa tubarkalla. An saurari wannan waƙa, tare da tarken salon kwalliya da ya fito a cikinta. An
fahimci cewa Sa’idu Faru gwani na
gwanaye ne wajen amfani da jinsi daban-daban na tsuntsaye da sauran halittu
wajen sakaya ma’ana da adonta waƙa.
1.1
Gabatarwa
Nazarin waƙa musamman a Hausa, fanni ne da yake
bayar da dama a fahimci tagomashin harshe da baiwar da Allah ya yi wa masu
shirya waƙa wajen iya sarrafa kalmomi. Haka kuma,
fannin yana bayar da dama a gane hikima da fasahar mawaƙa wajen adana tarihi da fayyace tunanin
al’ummar da suke
wakilta. Har ila yau, fannin nazarin waƙa yana bayar da dama a fahimci saƙonnin da mawaƙan suke ƙoƙarin isarwa ga jama’a, wato jigogin waƙoƙinsu. Saboda haka, masana suka raba
fannin nazarin zuwa muhimman sassa uku, wato nazarin jigo da tsari da salo. A ƙarƙashin salo ne aka fi baje kolin fasahar harshe,
kasancewar salo shi ne dokin jigo, kuma shi ne sinadarin da ke ƙara wa waƙa armashi. Yahya (2001) ya yi wa salo
laƙabi da asirin waƙa.
A wannan muƙala mai suna “Nazarin kwalliya a Waƙar Sa’idu Faru ta Sarkin Yaƙin Banga Sale, an yi tsokaci ne a
fannin salon da wannan mawaƙi ya yi amfani da shi a matsayin
dabarar isar da saƙon wannan waƙa. Duk wanda ya saurari wannan waƙa, zai fahimci cewa mawaƙin gwani ne na gwanaye wajen iya
sarrafa harshensa, har adon da ya yi a waƙar wani lokaci yakan rinjayi saƙon waƙar. Domin haka, a iya cewa in dai a
nazarin waƙoƙin malamin waƙa Sa’idu Faru ne, salo
shi ne ja-gaba.
Makaɗa Sa’idu Faru yana ɗaya daga cikin sahun gaba na manyan
mawaƙan baka na Hausa da ake tinƙaho da su musamman a fagen waƙoƙin iko. Haka kuma, mawaƙi ne da ya yi tashe ya shahara a faɗin ƙasar Hausa a zamaninsa, kuma har zuwa
wannan lokaci waƙoƙinsa na nan a cikin zukatan al’umma tamkar yau ya yi su. Har ila yau,
waƙoƙin Makaɗa Sa’idu Faru sun taskace muhimman
fannoni na rayuwar Hausawa, kama daga tarihi da al’ada har ma da falsafar
Bahaushe, kasancewar shi mutum ne da Allah ya yi wa baiwa da hikima wajen iya
shirya waƙa. (Gusau, 2005)
1.2 Taƙaitaccen Tarihin Makaɗa Sa’idu Faru
An haifi
Sa’idu a wuraren 1932, a garin Faru da ke cikin Maradun, Ƙaramar Hukumar Talatar Mafara. Sunan
mahaifinsa Abubakar ɗan Abdu ɗan Alu Maikurya. Ta fuskar mahaifiyarsa kuwa ita ‘yar
asalin garin Banga ce. Sa’idu ya yi ƙuruciyarsa a garin Banga, wato garin da aka haifi
mahaifiyarsa, amma daga baya ya koma wurin mahaifinsa a garin Faru. Sa’idu ya
samu damar samun ilimin addinin Musulunci, amma bai sami damar yin karatun
zamani ba, wato karatun boko.
Alaƙar Sa’idu da waƙa kuwa daɗaɗɗiya ce, domin ya gaji kiɗa da waƙa tun daga kakansa na biyu, wato Alu
Maikurya, wanda tsohon makaɗin yaƙi ne. Shi ma kakansa Makaɗa abdu da kuma mahaifinsa Makaɗa Abubakar dukkaninsu ‘yan gado ne ba haye suka yi ba.
Amma Sa’idu ya fara shiga cikin harkokin shirya waƙa tun yana kimanin ɗan shekara goma da haihuwa. Ya fara ne da bin mahaifinsa
da kuma koyon dabarunsa na waƙa, wanda su ne ya ɗabbaƙa a galibin waƙoƙinsa. (Gusau, 2005).
Makaɗa Sa’idu Faru ya zauna ƙarƙashin mahaifinsa yana masa karɓin waƙa, har zuwa lokacin da ya fara cin
gashin kansa, inda ya nuna fasaharsa da ƙwarewarsa. Ya yi wa sarakuna da ‘ya’yan sarakuna da dama waƙa, amma fitattun iyayen gidansa su ne
sarkin yaƙin Banga Sale da kuma Sarkin Kudu Muhammadu
Macciɗo. Makaɗa Sa’idu Faru ya yi waƙoƙi da dama waɗanda galibinsu na fada ne.
2.1 Ma’anar Kwalliya
Kwalliya tana ɗaya daga cikin nau’o’in adon harshe wadda ta kasance
ginshiƙi a salon sarrafa harshe. Kamar yadda
sunanta ya nuna, da ita ake ƙawata waƙa ta hanyar siffanta ko kwatanta wanda
ake wa waƙa da abu kai tsaye. Wannan kwatancin
kan sa abin da ake wa waƙar ya ɗauki siffa ko kama da abin da aka kwatanta shi da shi.
Masana irin su Yahya (2001) da Baldic (2004) da sauransu, sun yi tsokaci a kan
matsayin kwalliya a fannin nazarin salo. Yahya ( 2001) ya bayyana kwalliya da
cewa nau’i ce ta salo da ake amfani da ita wajen kawo hoton abu yadda mawaƙi yake buƙatar mai sauraro ko mai karatu ya kalle
shi da idon zuciyarsa ko da tunaninsa. A ra’ayin Baldic (2004), cewa ya yi ita
kwalliya ko siffantawa ginshiƙi ce a fagen nazarin adon harshe, wato
tana da matuƙar muhimmanci kuma idan an kwatanta ta
da sauran dabarun adon harshe, za a ga cewa ta fi su shahara a cikin ayyukan
adabi.
3.1 Waƙar Sarkin Yaƙin Banga, Sale “Gwabron Giwa Uban Galadima, Ɗan Sambo Ginshimi.”
Wannan waƙa tana ɗaya daga cikin fitattun waƙoƙin Makaɗa Sa’idu Faru wadda ya yi wa sarkin yaƙin Banga, Alhaji Sale Abubakar Ƙauran Namoda kuma dagacin garin Banga.
Shi da kansa Sa’idu Faru ya tabbatar da cewa, wannan waƙa tana ɗaya daga cikin waƙoƙinsa da suka girku dangane da tsarinsu,
kuma jama’a na sha’awarta matuƙa.
Turken wannan waƙa ya nuna cewa waƙar yabo ce da nuna biyayya irin ta mawaƙi da uban gidansa. Haka kuma, wannan
turke wato “Gwabron Giwa Uban Galadima, Ɗan Sambo Ginshimi.” Ya fito da sigar turken waƙoƙin iko musamman in aka yi la’akari da zaɓin kalmomin da suka kafa turken, kalmomi ne da suke nuna
alaƙar saraki da ƙasaita. Misali, kalmar Gwabron Giwa
wadda take nufin namijin giwa mai ƙarfi da kuma kalmar ginshimi.
4.1Kwalliya a Waƙar “Gwabron Giwa Uban Galadima, Ɗan Sambo Ginshimi.”
Makaɗa Sa’idu Faru ya fara amfani da kwalliya a wannan waƙa tun daga turken waƙar wato:
Gindin Waƙa: Gwabron Giwa Uban Galadima, ɗan Sambo Ginshimi,
: Gamsheƙan Amadu na mai Gandi kai ah uban zagi.
A nan mawaƙin ya yi amfani da kalmar Gwabron Giwa
wajen siffanta ƙarfi da kwarjinin ubangidansa wato
sarkin yaƙin Banga Sale. Haka kuma, a dai wannan ɗiyan kuma turken waƙar ya yi amfani da kalmar ‘Ginshimi’ kai tsaye ga ubangidan nasa
wadda take nufin ƙaton abu, ko wani abu mai girma.
Dukkanin waɗannan kalmomi ne da suke siffanta girma
da ƙarfi da kwarjinin sarkin yaƙi. Haka kuma, a layi na biyu na ɗiyan waƙa na farko, ya kira sarkin yaƙi kai tsaye da gamsheƙa, an sani cewa, gamsheƙa mafaɗaciyar macijiya ce da take taso wa mutum da zarar ya tunkare
ta. Domin haka, ya yi amfani da hoton gamsheƙa wurin surantawa yadda sarkin yaƙi kan zabura da zarar an taɓo Ahmadu.
Mawaƙin ya yi amfani da wannan salo tun a farkon
waƙar, kasancewar wanda ake yi wa waƙar mayaƙi ne, dole a yi amfani da wasu siffofi
da za a kawo wa mai sauraro hoton ƙarfinsa da kwarjininsa.
Haka kuma, Sa’idu Faru ya yi amfani da
kalmomi irin su Gogarma wadda Bargery, (1934:396) ya bayyana ta da cewa kalma
ce da ake amfani da ita ga mutum ƙaƙƙarfa domin nuna ƙarfinsa. Mawaƙin ya kawo wannan ne a ɗiyan waƙa kamar haka:
Jagora: Gogarman,
‘Y/Amshi: Namoda bai magana wani ya walwalat.
Har ila yau, Sa’idu Faru ya yi amfani
da salon kwalliya inda ya yi amfani da kalmar dangalin gabas kai tsaye ga
ubangidan nasa sarkin yaƙi. Ita ma wannan kalma ta dangali,
Bargey (1934: 387) ya bayyana ta da cewa wata irin doguwar katanga ce da ake
yin ta domin samar da kariya ga gari, ko kuma a ce wata doguwar kofa ce da take
bayar da tsaro ga gari. Ke nan amfani da wannan kalmar na siffanta sarkin yaƙi a matsayin garkuwa ga al’ummarsa. Ga ɗiyan waƙar kamar haka:
Jagora:
Ni dai fatad da nay yi ma,
: Kwasau na Alu dangalin gabas,
‘Y/Amshi : Don na ka gama lafiya,
Jagora
: Don na ka gama lafiya,
‘Y/Amshi : Na Sarkin Gobir na Sambo
ginshimi.
Haka kuma, a ƙoƙarin wannan mawaƙi na nuna fasaha da naƙaltar harshe da kuma iya siffanta mai ƙarfi da mulki har jama’a su fahimci ƙarfin mulkinsa, Sa’idu ya siffanta sarkin yaƙi Alhaji Sale Abubakar da buda. Shi
buda wata irin iskar hunturu ce da take rufe gari har sararin samaniya wanda
yake zuwa da hunturu, wato tsananin sanyi (Bargey, 1934: 121). Hikimar mawaƙin na siffanta sarkin yaƙi da buda saboda karfin iskar da yadda
take takura jama’a, haka sarkin yaƙi yake ƙage abokan gaba da saka fargaba a gare
su. Mawaƙin ya kawo wannan ne a ɗiyan waƙar da yake cewa:
Jagora: Kai ah buda mai jice ƙasa,
‘Y/Amshi: Baban goga Sale ɗan Alu,
: Na Garba sai ka wuce maza ka faɗin,
: Sun tasari ƙwarai.
A wani ɗiyan waƙa kuma, Sa’idu Faru ya siffanta dagacin Banga da
ginshiƙi. Bargery (1934:387) ya bayyana ginshiƙi da cewa wani gini ne da yake tare
rufin ɗaki ya hana shi faɗuwa. Wannan salo na kwalliya ya nuna cewa sarkin yaƙi ginshiƙi ne ga talakawansa, wato mai jiɓintar al’amuransu ne ya hana su kokawa. Sa’idu ya kawo
wannan ɗiyan waƙa kamar haka:
Jagora: Zama kai a ginshiƙi,
‘Y/Amshi
: Kana tsaye, bango ba ya razana,
: Ko da an shekare ruwa.
Hikimar da take cikin salon kwalliya
irin ta Sa’idu Faru hikima ce da take ƙara fito da yalwa da martabar da Allah ya yi wa harshen
Hausa na tulin kalmomi da suka dace da kwatance wanda kan sa a dunƙule magana cikin kalma ɗaya.
5.1 Kammalawa
Wannan maƙala ta yi tsokaci a kan ɗaya daga cikin salailan da Makaɗa Sa’idu Faru yake sarrafawa a cikin waƙoƙinsa wato salon kwalliya. An zaɓi waƙa guda kuma sha kudun a ɓangaren salo wajen fito da misalai na salon kwalliya a
ciki. Haka kuma, an fahimci cewa mafi yawa daga kalmomin da Sa’idu Faru ya yi
amfani da su a waƙar, ya zamo waɗanda za su dace da kwarzanta sarkin yaƙi ne da ɗaga martabarsa, har a yi tunanin a filin daga yake.
Manazarta
Bargery, G. P (1934), A Hausa- English Dictionary and English-Hausa
Vocabulargy. Zaria: ABU Press.
Baldick, C. (2004) Concise
Dictionary of Literary Terms. London: Oxford University Press.
Gusau, M.S (2003). Jagorar Nazarin Waƙa Baka. Kano: Benchmark Limited
Gusau, S. M. (1996). Dabarar Alkunya A Waƙoƙin
Makaɗan Baka. A Cikin The West African Journal of Language, Literature and Criticism Vol. 1 No. 1 K. Zafar
(ed). Kano: Jami’ar Bayero.
Gusau, S. M. (2002) Saƙo a Waƙoƙin Baka: Tsokaci Kan Turke da Rabe-Rabensa. A Cikin Studies in
Hausa Language, Literature and Culture. Kano: Jami’ar Bayero.
Gusau, S. M. (2009), Diwanin Waƙoƙin
Baka, Zaɓaɓɓun Matanonin Waƙoƙin Baka na Hausa. Kano: Century Research and Publishing Limited.
Rabi, M. (2014) Salo a Waƙar Baka ta Hausa: Misali Daga Waƙoƙin Makaɗan Jama’a Waɗanda Suka Yi Wa Mata. Kaduna: Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya Da Ilmin
Harsuna, Jami’ar Jihar Kaduna.
Rabiu, B. (2020), Salon Sarrafa Harshe a Wasu Waƙoƙin
Alh. (Dr.) Mamman Shata. Department of Nigerian Languages and
Linguistics. Kaduna: Kaduna State University.
Tsoho, M.Y. (2001) Tubalan Gina Waƙoƙin Yabo: Tsokaci Kan Yabau a Waƙoƙin Iko. Department of Nigeria and African Languages. Zaria: Ahmadu Bello University.
Tsoho, M. Y. (2002) Eulogues the Building Blocks of Hausa
Praise Song: A Thematic and Structural Examination. Department
Nigerian and African Languages. Zaria: Ahmadu Bello University.
Tsoho, M.Y. (2002) Eulogues, the
Building Blocks of Hausa Praise Song. Ph.D Dissertation. Department of Nigeria and African Languages. Zaria: Ahmadu Bello University.
Tsoho, M.Y. (2013) Bayanin Yabau
Matakin Waƙar Ummaru Ɗanɗanduna
Na Gwandu Ta Alhaji (Dr) Mamman Shata Katsina: Ɗunɗaye Journal Of Hausa Studies, Vol, No 5, Department Of Nigerian Languages.
Sokoto: Usman Ɗanfodio University.
Umar, M. B. (1984) Symbolism in Oral Poetry: A Study of
Symbolical Indices of Social Status in Hausa Court Song. Department of
Nigeria and African Languages. Zaria: Ahmadu Bello University.
Yahaya, A.B (2001), Salo Asirin Waƙa. Kaduna: Fisbas Media Services.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.