Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Take Wando

TAMBAYA (129)

ance matan da basa rufe jikinsu ko kamshi aljanna bazasuji ba sukuma maxan da basa dage Wanda mai hukuncin su

AMSA

Alhamdulillah

A cikin Mi'ati Hadith (Hadisai sahihai guda 100) da malaman hadisai suka tattara

Abu Hurairah (Radiyallahu anhu) ya rawaito hadisi sahihi cewar Annabi (Sallallahu alaihi) yace: "Ma'asfalu Minal Ka'abaini, Minal Izari Fin Naari"

(Bukhari da Muslim)

Fassara

Duk wanda yabar tufarsa qasa da idon sahu, ragowar za a saka a cikin wuta

(Muttafaqun alaihi)

Kinga kenan duk namijin da ya take wandonsa da gadara, don ya nuna shi mai wadata ne to daga kan idon sahu zuwa inda ya take a wuta za'a babbake wannan wajen

Shi yasa zaki ga malaman Ahlus Sunnah suna taka tsantsan basa bari wandonsu ya wuce idon sahu, a maimakon yan bidi'a da suke dinka wando suna taka shi da duga-duginsu

Allah ya sa mu dace

Wallahu ta'ala a'alam

 Subhanakallahumma wabi hamdika ash-hadu anla'ilaha illa anta astaghfiruka wa'atubi ilayk

Amsawa

Usman Danliti Mato (Usmannoor_Assalafy)

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments