TAMBAYA (130)❓
Assalamu Alaikum warahamatullahiwabarakatuhu. Malam inaso
abani shawara. Dan Allah
Malam dan inada wata matsalane wajan wata biyu koda yaushe banida tunani da ya wuce sai na mutuwa kome nake koda second daya tunanin nan baya fita daga raina
Shine nace abani shawara 😭😭 bana sakewa
kwata kwata bana walwala
✍️AMSA A TAQAICE
Waalaikumussalam, Warahmatullahi, Wabarakatuh
(An karbo daga Abu Hurairah (Radiyallahu anhu) yace: Annabi
(Sallallahu alaihi wasallam) yace: "Ku dinga yawan tuna mai tarwatsa farin
ciki" ma'ana: mutuwa #Sunan Ibn Majah: 4258, An-Nasaa'i 1824, At-Tirmidhi
2307)
Bismillaahir Rahmaanir Raheem
Alhamdulillah
To da farko dai yar uwa, ina tayaki murna domin kuwa kina da
Imani
A wannan zamanin da yawancin mutane basa son a dinga zancen
mutuwa - mai Imani ne kadai yake iya tuna mutuwa a kowanne hali yake wanda kuma
indai har ka tuno da mutuwa to zaka tuna makomar kalar aikin da kake a lahira,
Aljannah ko Wuta
Allah (Subhanahu wata'ala) yace
( كُلُّ
نَفْسٍ ذَائِقَةُ الْمَوْتِ ۗ وَإِنَّمَا تُوَفَّوْنَ أُجُورَكُمْ يَوْمَ الْقِيَامَةِ
ۖ فَمَن زُحْزِحَ عَنِ النَّارِ وَأُدْخِلَ الْجَنَّةَ فَقَدْ فَازَ ۗ وَمَا الْحَيَاةُ
الدُّنْيَا إِلَّا مَتَاعُ الْغُرُورِ )
آل عمران
(185) Aal-Imran
Kõwane rai mai ɗanɗanar mutuwa ne. Kuma ana
cika muku ijãrõrinku kawai ne a Rãnar qiyãma. To, wanda aka nĩsantar daga barin
wuta, kuma aka shigar da shi Aljanna, to, lalle ne yã tsĩra. Kuma rãyuwar
dũniya ba ta zama ba fãce jin dãɗin
rũɗi.
Da kuma ayar
( كُلُّ
نَفْسٍ ذَائِقَةُ الْمَوْتِ ۗ وَنَبْلُوكُم بِالشَّرِّ وَالْخَيْرِ فِتْنَةً ۖ وَإِلَيْنَا
تُرْجَعُونَ )
الأنبياء
(35) Al-Anbiyaa
Kõwane rai mai ɗanɗanar mutuwa ne. Kuma Munã
jarraba ku da sharri da alhẽri dõmin fitina. Kuma zuwa gare Mu ake mayar da ku.
Da kuma
( كُلُّ
نَفْسٍ ذَائِقَةُ الْمَوْتِ ۖ ثُمَّ إِلَيْنَا تُرْجَعُونَ
)
العنكبوت
(57) Al-Ankaboot
Kõwane rai mai ɗanɗanar mutuwa ne, sa'an nan
zuwa gare Mu ake mayar da ku.
Ba laifi bane musulmi ya dinga tuna mutuwa dalili kuwa shine
shahararren hadisin da aka karbo daga
Abu Hurairah (Radiyallahu anhu) yace: Annabi (Sallallahu alaihi wasallam) yace
"Ku dinga yawan tunawa da mai tarwatsa farin ciki"
(ma'ana mutuwa)
Sunan Ibn Majah 4258, An-Nasaa'i 1824, At-Tirmidhi 2307
Kawai ki kwantar da hankalinki ki ci gaba da bautar Allah
har mutuwa ta riske ki kamar yanda Allah (Subhanahu wata'ala) ya fadawa
ManzonSa
( وَاعْبُدْ
رَبَّكَ حَتَّىٰ يَأْتِيَكَ الْيَقِينُ )
الحجر
(99) Al-Hijr
Kuma ka bauta wa Ubangijinka, har mutuwa ta zo maka.
Indai har tunanin mutuwa zai hanaki sakewa da walwala to bai
kamata ki sakata ki wala a lokacin da kike bacci ba domin kuwa bacci kanin
mutuwa ne saboda duk lokacin da mutum ya kwanta bacci to ransa baya jikinsa
kamar yanda Allah (Subhanahu wata'ala) ya fada
( اللَّهُ
يَتَوَفَّى الْأَنفُسَ حِينَ مَوْتِهَا وَالَّتِي لَمْ تَمُتْ فِي مَنَامِهَا ۖ فَيُمْسِكُ
الَّتِي قَضَىٰ عَلَيْهَا الْمَوْتَ وَيُرْسِلُ الْأُخْرَىٰ إِلَىٰ أَجَلٍ مُّسَمًّى
ۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَآيَاتٍ لِّقَوْمٍ يَتَفَكَّرُونَ )
الزمر
(42) Az-Zumar
Allah ne ke karɓar
rãyuka a lõkacin mutuwarsu, da waɗannan
da ba su mutu ba, a cikin barcinsu. Sa'an nan Ya riƙe wanda Ya hukunta mutuwa
a kansa kuma Ya saki gudar, har zuwa ga ajali ambatacce. Lalle a cikin wancan,
haƙĩƙa, akwai ãyõyi ga mutãne
waɗanda ke yin tunãni.
To idan da ace mutane suna tuna mutuwa akai - akai kamar
yanda kike tunawa haka ai da an dan samu raguwar wasu abubuwan. Duba ki ga
yanda azzaluman shugabannin kasarmu suke sace kudaden talakawa, ko gajiya basa
yi yanzu da ace suna yawan tunanin mutuwa kina ganin zasu ci gaba da satar da
suke ? Tunanin mutuwa yayin aikata zunubi yana saka mutum gaba daya ya haqura
da aikata wannan laifin domin duk sanda ka tuna mutuwa to zaka tuna haduwarka
da Allah. Kuma mutuwar nan dai wajibi ce tun da ga Annabi (Sallallahu alaihi
wasallam) wanda Allah Azzawajallah yafi so fiye da kowa a cikin halittunsa
amman Allah yace masa zaka mutu
( إِنَّكَ
مَيِّتٌ وَإِنَّهُم مَّيِّتُونَ )
الزمر
(30) Az-Zumar
Lalle kai mai mutuwa ne, kuma su mã lalle mãsu mutuwa ne.
Ki koyi iya sarrafa tunanin mutuwar ta hanyar daina tada
hankalinki, ki daina gudun mutuwar, kawai kedai ki shirya zuwanta a kowanne
lokaci. Allah (Subhanahu wata'ala) yace
( قُلْ
إِنَّ الْمَوْتَ الَّذِي تَفِرُّونَ مِنْهُ فَإِنَّهُ مُلَاقِيكُمْ ۖ ثُمَّ تُرَدُّونَ
إِلَىٰ عَالِمِ الْغَيْبِ وَالشَّهَادَةِ فَيُنَبِّئُكُم بِمَا كُنتُمْ تَعْمَلُونَ
)
الجمعة
(8) Al-Jumu'a
Ka ce "Lalle mutuwar nan da kuke gudũ daga gareta, to,
lalle ita mai haɗuwa
da ku ce sa'an nan kuma anã mayar da kũ zuwa ga masanin fake da bayyane, dõmin
Ya bãku lãbãri game da abin da kuka kasance kunã aikatãwa."
Ki tuno da dalilin da yasa fa aka halicci ita kanta mutuwar
da rayuwa shine don ayi mana jarabawa
( الَّذِي
خَلَقَ الْمَوْتَ وَالْحَيَاةَ لِيَبْلُوَكُمْ أَيُّكُمْ أَحْسَنُ عَمَلًا ۚ وَهُوَ
الْعَزِيزُ الْغَفُورُ )
الملك
(2) Al-Mulk
Shi ne Wanda Ya halitta mutuwa da rãyuwa domin Ya jarraba
ku, Ya nũna wãye daga cikinku ya fi kyãwon aiki, Shi ne Mabuwãyi, Mai gafara.
Duk sanda kika tuna mutuwa to ki tuno da cewar a Aljannah fa
ba'a mutuwa. Jin dadin wannan dawwamar ta Aljannah kadai ya isa ya tafiyar da
wancan qunci da baqin cikin da kike na tunanin mutuwa. Allah (Subhanahu
wata'ala) yace
( وَالَّذِينَ
آمَنُوا وَعَمِلُوا الصَّالِحَاتِ أُولَٰئِكَ أَصْحَابُ الْجَنَّةِ ۖ هُمْ فِيهَا خَالِدُونَ
)
البقرة
(82) Al-Baqara
Kuma waɗanda
suka yi ĩmãni kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, waɗannan,
'yan Aljanna ne, sũ a cikinta madawwama ne.
Ki tuna firar dan Aljannah da dan Wuta, lokacin da dan
Aljannah zai ce saura kadan ka halakani (batar dani) a duniya
( فَاطَّلَعَ
فَرَآهُ فِي سَوَاءِ الْجَحِيمِ )
الصافات
(55) As-Saaffat
Sai ya tsinkãya, sai ya gan shi a cikin tsakar Jahim.
( قَالَ
تَاللَّهِ إِن كِدتَّ لَتُرْدِينِ )
الصافات
(56)
Ya ce (masa), "Wallahi, lalle, kã yi kusa, haƙĩƙã, ka halakãni."
( وَلَوْلَا
نِعْمَةُ رَبِّي لَكُنتُ مِنَ الْمُحْضَرِينَ )
الصافات
(57)
"Kuma bã dõmin ni'imar Ubangijĩna ba, lalle, dã na
kasance daga waɗanda
ake halartarwa (tãre da kai a cikin wutã)."
( أَفَمَا
نَحْنُ بِمَيِّتِينَ )
الصافات
(58)
"Shin fa, ba mu zama mãsu mutuwa ba."
( إِلَّا
مَوْتَتَنَا الْأُولَىٰ وَمَا نَحْنُ بِمُعَذَّبِينَ )
الصافات
(59)
"Sai mutuwarmu ta farko, kuma ba mu zama waɗanda ake azabtarwa
ba?"
( إِنَّ
هَٰذَا لَهُوَ الْفَوْزُ الْعَظِيمُ )
الصافات
(60)
Lalle, wannan shĩ ne babban rabo mai girma.
( لِمِثْلِ
هَٰذَا فَلْيَعْمَلِ الْعَامِلُونَ )
الصافات
(61) As-Saaffat
Sabõda irin wannan, sai mãsu aiki su yi ta aikatãwa.
A karshe ina jan hankalinmu daga ni harke da mu gaggauta
neman gafarar Allah don rabauta da Aljannah wadda fadinta yakai sammai 7 da
kassai 7 kamar yanda Allah (Subhanahu wata'ala) ya fada
( وَسَارِعُوا
إِلَىٰ مَغْفِرَةٍ مِّن رَّبِّكُمْ وَجَنَّةٍ عَرْضُهَا السَّمَاوَاتُ وَالْأَرْضُ
أُعِدَّتْ لِلْمُتَّقِينَ )
آل عمران
(133) Aal-Imran
Kuma ku yi gaugawa zuwa ga nẽman gãfara daga Ubangijinku da wata
Aljanna wadda fãɗinta
(dai dai da) sammai da ƙasa ne, an yi tattalinta dõmin mãsu
taƙawa.
Ya Allah ka sa muyi kyakkyawan karshe.
Wallahu ta'ala a'alam
Subhanakallahumma
wabi hamdika ash-hadu anla'ilaha illa anta astaghfiruka wa'atubi ilayk
Amsawa
Usman Danliti Mato (Usmannoor_Assalafy)
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.