TAMBAYA (128)❓
Assalamu Allaikum. Barka da safiya mllm, ya aiki. Mllm
tambaya gareni Dan Allah
Mllm macece ta haihu har tayi kwana 40 jini Bai dauke mata ba ,zatayi wanka ne taci gaba da sallah ko zata jirane har ya dauke ? Nagode mllm
AMSA❗
Waalaikumussalam, Warahmatullahi, Wabarakatuh
Alhamdulillah
Idan har jinin ya ci gaba da zuba sannan kuma ya hade mata
da jinin al'ada to zata dauke shi a matsayin jinin haila saboda abune mai
yiwuwa jinin al'ada ya biyo bayan jinin haihuwa (an-nifas)
Idan kuma jinin haihuwar ya ci gaba da zuba ne har bayan
kwanaki 40 din sannan kuma bai hade da jinin al'ada ba to ba jinin haihuwa bane
(an-nifas) kuma ba jinin al'ada bane (haidah), wannan shi ake kira da jinin
al-Istihaadah (cuta) sai ta tuntubi likita
Wallahu ta'ala a'alam
Subhanakallahumma wabi hamdika ash-hadu anla'ilaha illa anta
astaghfiruka wa'atubi ilayk
Amsawa
Usman Danliti Mato (Usmannoor_Assalafy)
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.