Haƙƙin Mallaka: BBC Hausa
Hikayata Ta 2024: Ƙa'idojin Shiga Gasar Hikayata ta 2024 Ta BBC Hausa
Hikayata gasa ce ta ƙagaggun gajerun labarai wadda ke samar da
dama ga mata marubuta, waɗanda
ba su ƙware
ba da kuma ƙwararru.
Hakan kuwa zai ba damar nuna fasaharsu da kuma ba da damar
karanta labaran nasu a harshen Hausa.
To sai dai dole ne labaran da za a shiga su kasance ƙagaggun labarai kan wani jigo.
Ga ƙa'idojin Shiga Gasar:
Dole ne duk wani labari da za a turo da nufin shiga gasar
Hikyata ya cika waɗannan
sharuɗɗan:
1.Wajibi labarin ya kasance mace ce ko mata ne suka rubuta
shi. Lallai ne labarin ya kasance cikin ingantacciyar Hausa, da bin duka ƙa'idojin
rubutu. Wajibi ne mai turo da labarin ta kasance ta kai shekara 18 da haihuwa
sannan ba ta wuce 35 ba. Ga masu turo da labarin haɗin guiwa, wajibi ne ko waccensu ta kasance
shekararta 18 sannan ka da ta wuce 35. Ba a yarda ma'aikatan BBC ko 'yan uwansu
su shiga gasar ba.
2. Dole ne labarin ya kasance kagagge kuma gajere da bai
gaza kalma 1,000 sannan bai haura kalma 1,500. Za kuma a aiko da shi ta hanyar
kwafo labarin a zuba shi akwatin da aka tanada da ke cikin fom din nan (Yadda
za a shiga gasar) ko kuma ta tsarin manhajar uploader da ke shafinmu na
bbchausa.com.
2. Dole ne labarin ya kasance kagagge kuma gajere da bai
gaza kalma 1,000 sannan bai haura kalma 1,500. Za kuma a aiko da shi ta hanyar
kwafo labarin a zuba shi akwatin da aka tanada da ke cikin fom din nan (Yadda
za a shiga gasar) ko kuma ta tsarin manhajar uploader da ke shafinmu na
bbchausa.com.
3. Dole ne masu son shiga gasar su cike fom din nan (Yadda
za a shiga gasar) sannan a aike da labarin ta zuba shi ko kuma makala shi a
manhajar uplodaer da ke nan (Yadda za a shiga gasar). Ba a yarda mace ɗaya ta aiko da labari fiye
da ɗaya ba. Mata biyu
za su iya shigar da labari ɗaya
a gasar, amma kada su wuce haka. Dole ne wadda za ta turo da labarin ta zama
ita ce ainihin wadda ta rubuta shi; ba a yarda wata ta aiko da labarin da wata
ko wani suka rubuta ba. Sannan wajibi ne a nemi amincewar abokiyar hadaka.
4. Za a rufe wannan gasa da karfe 23:59 agogon GMT na ranar
31 watan Agustan 2024. Ba za a yi maraba da duk wani labarin da aka aiko bayan
nan ba. Ba za a dawo muku da labarin da kuka aiko mana ba saboda haka ku ajiye
kwafin labarin naku kafin ku aika. Za kuma mu tuntubi wadanda aka zabi
labaransu ne kawai.
5. Matakin Farko - Tantancewa: A cikin ma'aunin da za a yi
amfani da shi don tantance labaran da aka turo akwai:
Dole ne ya kasance mace ce ta rubuta labarin
Labari ya kasance ƙirƙirar shi aka yi, ma'ana ba kwafo shi aka
yi ba.
Amfani da ƙwarewa, ma'ana labari ya zama mai jan
hankali da taurarin da suka dace;
Bin ƙa'idojin nahawu da na rubutun Hausa
Ka da labari ya ci zarafi ko mutumcin wani
6. Tawagar BBC za ta zabi labarai guda 20 da suka yi fice
bisa doron ka'aidojin da aka wassafa a sama. Ta hanyar aiki tare da alkalai
bisa jagorancin ma'aikacin BBC, za a zabi guda uku da suka ciri tuta sannan za
a sake zabar guda 12 da suka yi rawar gani. BBC ka iya gayyatar waɗanda suka yi nasara da wasu
waɗanda labaransu suka
cancanci yabo, domin halartar taron bayar da kyaututtuka a Abuja wanda za a yi
a watan Nuwamban 2024. Za a sanar da lokacin bikin karramawar a shafinmu na
bbchausa.com.
7. Wadda ta zo na ɗaya,
da ta biyu, da ta uku ne kawai za su samu kyauta: Za a bayar da N1,000,000
(naira miliyan daya) da lambar yabo ga labarin da ya zo na ɗaya; N750,000 (naira dubu
dari bakwai da hamsin) da lambar yabo ga labarin da ya zo na biyu; da kuma
N500,000 (naira dubu dari biyar) da lambar yabo ga labarin da ya yi na uku. BBC
za ta wallafa sannan za ta watsa labaran wadanda suka yi nasarar a shafinta na
intanet da kuma rediyo. BBC za ta ɗauki
nauyin kuɗin mota da
masauki wanda bai wuce ƙima ba. Waɗanda
aka gayyata su ne ke da alhakin nema wa kansu izinin shiga Najeriya idan su ba
'yan kasar ba ne.
8. Dole ne labaran da za ku aiko su dace da tsarin aikin BBC
da ke kunshe a nan a wannan shafin na kasa:
https://www.bbc.com/editorialguidelines/
Abubuwan kuwa sun haɗa
da
Ka da su nuna banbanci ga wata ƙabila ko jama'a;
Ka da labari ya tallata rikici ko kuma ta'addanci ko tallata
'yan siyasa da ma yin barazana ga tsaron kasa;
Ka da labari ya tallata wata haja indai ba BBC Hausa ba, ko
kuma
Haddasa ƙiyayya bisa doron addini ko ƙabila ko jinsi ko kuma nuna ƙyama
ga masu nakasa.
9. Wajibi ne labarin da za a aiko ya kasance aikin wadda ta
turo da shi, kuma ya dace da ƙa'idojin da aka shimfiɗa. Kada labarin ya shiga haƙƙin
wani (wanda ya haɗa da
bayanan sirri), kuma kada a ɓata
wa wani suna ko a aikata abin da ya saɓa
wa doka.
10. Waɗanda
suka yi na ɗaya da na
biyu da na uku da kuma waɗanda
suka cancanci yabo dole ne su san cewa babu wani abu da zai hana BBC watsa ko
wallafa labaran nansu kamar yadda aka fada.
11. Mutum uku da suka zamo zakara na nufin sun bai wa BBC
damar amfani da labaran nasu har abada kuma ta kowace irin kafa. Wannan ya
kunshi bai wa wasu damar yin amfani da labarin. Sannan sun bai wa BBC 'yancin
gyara ko fassara labaran nasu domin dacewa da yadda ake son yin amfani da shi.
Wannan dama ta shafi hadaka da mata biyu suka hadu suka rubuta labari.
12. BBC ba za ta ɗauki
alhakin komai ba idan masu shiga wannan gasa suka yi biris da waɗannan ƙa'idoji,
sannan kuma masu shiga gasar sun amince su bai wa BBC cikakkiyar kariya daga
duk wani iƙirari
da wani zai yi sakamakon yin karan-tsaye ga waɗannan
ka'idoji. BBC na da ikon soke ko cire dukkan labarin da ya saɓa wa ko wanne daga cikin waɗannan ƙa'idojin.
13. Idan ba a iya tuntubar wata daga cikin wadanda suka zamo
zakara ba bayan duk wani kokarin yin hakan ya ci tura, to BBC na da damar bai
wa wadda take biye da ita damar.
14. Wadanda suka zamo na daya ko biyu ko uku da kuma 12 da
aka alkalai suka ce sun cancanci yabo (ko da kuwa hadaka ce) za a bukaci su
shiga karin yarjejeniya da BBC kafin ci-gaba. Kin yin hakan ka iya sanya BBC
dakatar da labarinki, inda za ta koma ga labaran wasu daban.
15. Shiga gasar na nufin amincewa da dukkannin dokokin da
BBC ta gindaya da suka hada da na soke duk labarin da ta ga dama a kowane
lokaci idan har ta gamsu da cewa an yi dokokin nata karan tsaye ko kuma an
aikata wani abu da yake kaskantar da ita.
16. BBC na da ikon sauya waɗannan
ƙa'idojin
a kowanne lokaci, ciki har da sauya hanyoyin zaɓen
ko kuma alƙalan.
Idan hakan ta kasance, to za a sanar a wannan shafin na intanet: bbchausa.com.
17. BBC da dukkan abokan huldarta ba za su dauki alhakin
rashin amincewa da duk labarin da aka samu matsalar aikowa da shi sakamokon
matsalar na'ura.
18. BBC ba za ta dauki alhakin duk wata asarar kudi ko kuma
zubewar kima ba.
19. Ka'idojin da BBC ta shimfida sun shafi wannan gasar ne
kawai:
https://www.bbc.co.uk/terms
20. Wadanda suka shiga gasar suna da hakkin malllakar
labaran nasu. Kuma sun bai wa BBC 'yancin yin amfani da labaran nasu kamar
yadda yake a ka'idodjin nan.
21. An tsara waɗannan
Ƙa'idojin
ne bisa tanade-tanaden dokokin Ingila da Wales..
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.