Notcoin Da TapSwap: Tarihi, Mining, Fashewarsu da Matsayin su a Mahangar Shari’ah

    Haƙƙin Mallaka:
    Prof. Ahmad Murtala

    Bismillahir Rahmanir Rahim

    Allah ya yi Salati da Salami ga Annabinmu Muhammad da Alayensa da Sahabbansa baki ɗaya.

    Bayan haka. A yau Juma’a 23 ga Zulka’ah 1445H. daidai da 31 ga May 2024 zan amsa tambayoyin da mutane suke yin waya, suna kuma turowa ta ko’ina a kan hukuncin yin mining da cryptocurrency baki ɗaya. Daga ciki, wasu sun turo da cewa, “Don Allah Malam kada a gaji damu. Menene hukuncin Cryptocurrency da kuma mining, don Allah?”.

    A kan wannan tambayar aka rubuta wannan amsar. Duk da cewa za a fadada wasu bayanan don a sami damar fahimtar abinda ake magana a kansa. Wanda yake son ya fahimce ni da kyau sai ya karance rubutun duka. A kokarin fito da mas’alar fili, zan yi amfani da kalmomin da nake sa ran kowa zai fahimta. Ga bayanin yadda yake. Allah ya bamu sa’a da dacewa.

    1-Hadahadar Cryptocurrency na daga cikin sababbin mas’aloli da suka zo a wannan zamanin, irin wadanda malamai suke kira da - النوازل-. Irin wadannan mas’aloli, idan ana son fitar da hukuncin su, ana yin bincike ne mai zurfi sosai. Ba wai kawai a ji daga bakin masu yi su kadai ba. Tare da yin hakan yana da kyau, amma ana da bukatar kuma a zurfafa bincike a bangaren ta inda suka taso don a fahimci dabi’arsu, a gane mashiga da mafitar su, a duba manufofin su na kusa, da na tsakiya, da na nesa. Domin al’umar Musulmi suna tunkarar duniyar murdiya da dakusarwa. Duniyar da take son ta tursasawa Musulmi su karbi tsare-tsaren da zasu kautar da su daga bin tsarin Shari’ar Allah, ballantana su barsu su yi kokarin dawo da ainihin Shari’ar Allah a bayan ƙasa.

    Ta nan ne za a gane cewa masu yin nazari a kan irin wadannan sababbin mas’alolin suna da bukatar su yi a sannu, ba wai da gaggawa, a na rawar jiki a yi saurin fitar da hukunci na halattawa ko na haramtawa, sakamakon duba abu daya ko biyu ko hira da mutum daya ko biyu ba! Yin hakan zai haifar da kwaba a fitar da hukunce-hukuncen matsaloli.

    2-Idan muka kalli tsarin cryptocurrency baki ɗaya zamu iya kasa shi gida uku kamar haka:

    i- Cryptocurrency wanda ya halatta, wato wanda bai ci karo da ka’idojin Musulunci ba, ya yi daidai da tanaje-tanajensa. Misalin irin wadannan shi ne wanda gwamnatoci kamar na Bahamas, China, UK, Brazil, Jamaica, da India, har da nan gida Nigeria suka yarda da shi har suka kafa na ƙasar su. Misalin sa kamar E-Naira. Haka nan wanda kwandalarsa ta crypto tana daidai da kwandalar waje kamar USDS, idan ya zamo ba shi da wasu matsalolin a makale tare da shi. Irin wadannan sun halatta.

    ii- Cryptocurrency wadanda ya haramta kai tsaye. Wadannan sun shafi irin cryptocurrency din da kamfanonin caca da casino da sauransu suke fitowa da su ɓaro-ɓaro don a yi caca da su. Wadannan sun hada da irinsu Casinocoin, funtoken, da sauransu. Wasu kuma an yi su da zubin “game” wanda yake koyawa mutane rigima da ƙeta da mugunta da faɗa da tayar da fitina. Duka irin waɗannan haram ne a shige su. Sai dai akwai mutane da yawa cikin manyan kasa da ‘yan boko da suka fi ganewa irin wannan hadahadar. Suna yin abin su ba wanda ya sani, sai Allah wanda shi ne ya haramta hulɗa da cacar! (Baƙara:219).

    iii- Cryptocurrency wanda yake halaccin sa ko haramcin sa bai bayyana ba ɓaro-ɓaro. Wannan ya haɗa da Bitcoin, Etherium, da sauransu. Haka nan, a wannan ɓangaren za a iya sa mining da mutane suke yi wa kamfanonin Avacoin, da Notcoin da TapSwap da sauransu.

    A kan irin wannan nau’in na ƙarshe, malamai suke ta saɓani. Wasu su halatta kai tsaye. Saboda a zahiri su ba su ga abinda zai haramta ba. A wurinsu duk matsalolin da ake tuhumar irinsu Bitcoin da su, akwai waɗannan matsalolin ko fiye da su a kuɗaɗen da suke hannun mutane. Don haka ba haramci ga cryptocurrencies a wurin wadannan malamai. Wasu malaman kuma sun ga ma’anonin da zasu sa a haramta wannan mu’amalla, don haka suka bayyana daidai wuraren haramcin. Ma’ana da za a kauce musu, a rungume tsarin Musulunci a hulɗar, da ta halatta!

    3-A cikin rubutu da na yi mai taken “BITCOIN: Tarihinsa, Amfaninsa da Matsalolinsa da Matsayinsa a Musulunci“ wanda aka rubuta a January 29, 2021 (Ga link din da za a sameshi; https://www.facebook.com/share/p/TJoqgDWKWRPiwhJ4/?mibextid=oFDknk) an yi bayanin yadda tarihin cryptocurrency ya taso har ya burinƙasa cewa an yi nufin zare hannuwan gwamnatoci a kan kudade, ya zamo ƙato da ƙato (Peer-to-Peer) ne kurum suke hulɗa. Sannan an fadi matakan da ake bi daki-daki har a kai ga yadda ake samun ƙwandalar crypto. An dauki misali da Bitcoin, saboda shahararsa wurin mutane. An kawo ƙasashen Musulmi waɗanda suka dogara bisa fatawoyin malamansu suka haramta wannan mu’amullar ta cryptocurrency kamar su Misra, Saudiya, Palestine, Libya, Turkey, Morocco, da sauransu har da wasu ƙasashen na turawa. (https://www.techopedia.com/cryptocurrency-bans-explained-which-countries-have-restricted-crypto). Sannan an kawo bayanan wasu manyan Majalisai (Councils) na malaman duniya da suka haramta hadadahadar cryptocurrency. A kan wannan, hukunci wannan mu’amalla a wurina shi ne “Haram Li Gairihi” ce. Wato saboda dinbin matsalolin da suke baibaiye da cryptocurrency ta ko’ina, ba zai yiwu a halatta ba.

    An kawo wannan ne don tunatarwa. Ga wanda yake so sai ya koma ya karanta.

    4- Zuwa watan March 2024 akwai nau’uka na ƙwandalar crypto dubu goma sha uku da ɗari biyu da sha bakwai (13,217) a duniya. Wannan ya haɗa har da wadanda suka mutu, aka daina amfani da su. Idan aka kwashe wadanda ba sa motsi, za a sami ragowar sun kai dubu takwas da ɗari tara da tamanin da biyar (8,985). Suna yawo a tsakanin mutane miliyan ɗari hudu da ashirin (420 million). (https://explodingtopics.com/blog/number-of-cryptocurrencies).

    Idan aka kalli ayyukan da ake yi daga farko har a mallaki ƙwandalar crypto, za a ga abubuwa ne da yawa, amma “mining” ginshiki ne babba, wanda yake tsakiya, ba za a yi ba sai da shi. Dole sai an bi takansa sannan za a cimma kaiwa ga sauran abubuwan. Duk wanda ya fara mining, to ko yana sane ko baya sane, a hankali zasu ja shi ya karasa, ya yi sauran abubuwan da ake yi na a hadahadar cryptocurrency. Don idan ta fashe, zai so ya ɗebe kudinsa. To a nan za a ce sai ya bude “wallet” a kan wata manhajar. Bayan nan sai a ce sai ya yi hulda da kamfanin da zai sayi ƙwandalolin. Sai ya yi kaza, si ya yi kaza. A karshe sai ya ji shi a ciki zundum! Wannan wata manufa ce babba, wadda ta hanyarta ake son a jefa duniya baki ɗaya cikin harkar crypto!

     A bayanan da aka yi a wancan rubutu na “Bitcoin”, ba a faɗaɗa wannan bangaren sosai ba. Saboda a can ana son a bada bayani ne na jimlar ayyukan da ake yi baki ɗaya. Amma a halin yanzu, ɓangare mining ya fito fili sosai ta yadda bayanan da za a yi a nan zasu fi ƙarfi a kansa, musamman dangane da sabuwar manhajar NOTCOIN da TapSwap da makamantansu da suka yawaita a yanzu. Amma akwai wasu ƙarin daruruwan manhajojin mining da masu yin harkar suke bibiyarsu.

    5- “The Open Network” wanda aka fi sani a takaice da sunan (TON), wani gagarumin aiki ne (project) wanda masu shi suka nufi haɗa hancin daukacin “blockchain” da suke kan internet. An yi wannan yunkuri ne tun 2017. Daga baya sai mamallakin kamfanin Telegram mai suna Pavel Durov, ya canza masa suna ya koma “Telegram Open Network”. Sannan aka bude shi a 2021. Daga nan abin ya soma. Amma abubuwan da suka faru daga baya sun kunshi bayanan da zasu zo:

    i-Akwai manhajojin yin wasan “game” da yawa yanzu a kan Telegram, da X (Twitter a baya) da sauransu. Ana zuba tsarin game din a kan kwaikwayar rayuwar yau-da-gobe (Simulation Games). Wannan ya haɗa da irin su NOTCOIN da Tapswap, da sauransu. Akwai kuma wani gungun na “games” waɗanda ake yinsu don izgilanci da ba’a da zambo da ban dariya (Meme Games). Akwai irin wadannan manhajojin masu dimbin yawa a kan Internet, kusan sun ninninka manhajoji na gaskiya da na Simulation din ma yawa. Irinsu sun haɗa da Dogecoin, Shiba Inu, Turbo, Mog Coin, Bonk, Hamster Kombat, da sauransu da yawa. –(https://coinranking.com/coins/meme).

    Abin la’akari shi ne da yawa daga mutanen Arewacin Nigeria suna kama wani “meme game” su yi ta yi da zaton zata fashe, bayan izgilanci ne suke ta dannawa, aikin rashin sani da abin yi! Matsalar ɗaukacin masu mining ita ce, ba su san ainihin su waye mutanen da suka bude kamfanoni da sunan “mining” ba, ba bu wata “whitepaper” da kamfanin ya saki game da project din nasa, amma sai mutane su danna kai suna bata lokaci, wai suna mining!

    ii-A lokacin da aka bude NOTCOIN an fara shi ne a matsayin wasan “ Simulation Game” a kan Telegram don ya koyawa mai wasa yadda ake yin mining da sauran matakan da ake bi. Sai dai ba wata takamaimai manufa da masu shi suka bayyana cewa sun tsara ne don su cimma mata. Kawai dai “game” ne ga shi nan, kowa zai iya shiga ta “Messenger” a shiga “Telegram Community”, sai ya jona, kowa yana kallonsa a Community din ya fara, ya yi ta yi, in ya gaji ya bari. Amma sun yi amfani da Telegram ne saboda jama’ar da suke kansa da masu amfani da shi a duniya sama da mutum miliyan tamanin (80) a lokacin. Sannan mai mallakar Telegram din, Pavel Durov, ya yi amfani da wannan dama ya shelanta a kan Telegram din cewa Notcoin zai iya fashewa don haka mutane su bi shi!

    iii- Duba ga cewa wannan “game” din zai fi samun karɓuwa da wuri, sai a Watan November, 2023, “Open Builder Team” suka yi amfani da manhajar, amma da sunan za a rika yin “mining” da ita. A satin da aka fara an sami mutane sama da milayna biyar sun fara amfani da shi. Wannan abu ya bawa NOTCOIN damar ya zamo wanda ya fi samun karɓuwa a kan manhajar (Web3). An dora shi shi a kan (Web3) domin samun sauƙin sarrafa shi, wanda yake sabon tsari ne da ke amfani da Cloud wajen sauƙaƙe wasa da game da sauran manhajoji irinsa.

    Yanzu haka TapSwap shi ne na biyu da mutane sama da miliyan ashirin ko wani abu kamar haka.

     iv-An sami mutane sama da milayan talatin da biyar sun jona kansu da “game” din NOTCOIN. A duk rana kuma na samun mutane kusan miliyan shida da suke bude NOTCOIN a kan Telegram. Akwai kamar miliyan biyu da suke bude shi a kan X.

    Ta hanyar tura bayani a kan X, masu kamfanin NOTCOIN sun sanar da cewa za su dakatar da “mining phase” na “game” da ake yi, a ranar ɗaya ga wata April, 2024. Suka kara da cewa, za a sami sakamako wato “airdrop” ta hanyar “The Open Network” (TON) nan gaba.

    v-A ranar 30 ga watan March 2024, masu NOTCOIN suka sanar da cewa manhajarsu ta tanadi Ladan Gabe guda 102,719,221,714. Sannan suka bayyana cewa suna son su rabar da wannan adadi ɗari bisa ɗari ga mutane masu hulɗa da su. Sannan Binance suka ce za su Notcoin akan jadawalin su tun ranar 16 ga wata May 2024.

    6- Ma’anar “mining” da Hausa shi ne haƙa da zabari da tattonawa ko za a dace a sami wani gwal ko azurfa ko wani dutse mai alfarma a cikin ƙasa. A zamanin yanzu sai a ka dauki ma’anar ta koma kan zabarin da ake yi kan wasu manyan manhajoji da ke kan internet, wadanda sai an warware wasu kulli na lambobi sannan za a sami damar samun kwandalayen crypto a matsayin ladan wahalar aiki wanda ake kira “Reward” ko “Token” ko a dogon turanci a ce “Crypto Token Reward”.

     Akwai jimlar abubuwan da ake la’akari da su a karkashin wannan. Su ne kamar haka:

    i-Mining kala biyu zuwa uku ne a yanzu. Ga bayanansu:

     Na daya shi ne wanda mutum daya zai girka kwamfiyutoci don ya yi ta zabarin shi kaɗai. Shi ake kira da (Solo Mining). Yana da wahalhalunsa da irin amfani da masu yi suke samu.

    Na biyu shi ne wanda ake kira da (Group ko Pool Mining). Shi ne wanda mutane da yawa suke shiga aikin haƙowar da zabari ta hanyar amfani da kwamfiyutocin su. Abinda suka samu sai su raba bisa yarjejeniyar da suka yi. A wasu lokutan ana ƙirƙirar masu harkar mining suna tattaruwa su yi “Mining Pool” don su samu damar warware wasu ƙulle-ƙullen da ke kan “blockchain” da suka gagara har sai an yi musu taron dangi. Wannan yana daga cikin tsarin bawa kowa dama ya shiga a dama da shi (Decentrization) da aka shigar harkar mining. Masu wannan aikin ana kiransu da “Farmers”. Suna haɗa ƙarfin kwanfiyutocinsu ne don su yi aikin tare (Farm of computers).

    Na uku shi ne wanda a yanzu yake tashe yanzu, wato (Cloud Mining). Wannan nau’i ne na “Pool Mining”, amma ana bi ta kan wasu manyan manhajoji da ake amfani da su a kan waya ko kwamfiyuta, sai a dora shi a kansu, ta yadda mutune zasu yi mining din ba tare da sun yi amfani da kwamfiyutocin su ko wayoyinsu kai tsaye ba. Domin yana kan hadarin yanar-gizo. Kamar dai yadda Avacoin, NOTCOIN, TapSwap suke makale da Telegram. Za a ga ba application ne mutum yake downloading dinsa ba, “Link” ne mutum yake bi sai ya hau da shi kan hadarin Telegram. Daga nan sai ya fara dannawa. Kasancewar a kan Cloud “Hadari” abin yake, shi ya sa za a ga wayoyi ba sa saurin daukar zafi sai sun dade sosai. Sannan kuma ana ta yi ba wata damuwa ko nauyi da cunkoso a kan wayar da zai sa ta ƙi sauri da yawa!.

    ii- Abinda ya kamata a sani shi ne, ga masu amfani da kwamfiyuta, yin mining yana buƙatar kwamfiyutoci na musamman, ba irin waɗannan gama-gari da muke amfani da su ba, da lokaci mai yawa. Duka wannan sai an sami wutar lantarki mai matukar ƙarfi da kwamfiyutocin za su dade suna aiki ba tsayawa kafin a kai ga samun ƙwandalar crypto guda ɗaya ko wani bangare nata. Da yawa daga kamfanonin da suke yin mining na “Solo” da “Group” suna satar wutar lantarki kasashensu don yin zabarin ƙwandalar crypto. Shi ya sa wasu ƙasashen suka dauki matakai masu tsauri a kan kamfanonin mining. Cikinsu akwai: Abu Dabi, da Labanon, da Iran, da Kasashen Latin Amurka kamar Venezuela, da Prague, da Argentina, da Brazil, da sauransu. (https://ar.beincrypto.com/63247/).

    Ta wani bangaren kuma, wannan yana daga cikin jimlar dalilan da suka sa wasu ƙasashe da yawa suka haramta yin cryptocurrency, har suke zabarin wasu masu kamfanonin crypto don su kamasu, a dalilin cin amanar ƙasa.

    iii- A lokacin da wani ya tara tokens da yawa, sai ya sami wuri na musammam da tsarin ya tanada ya adanasu da nufin sai sun kara ƙima sosai zai fito da su-kamar dai yadda ake boye kayan masarufi kenan-, suna kiran wannan da “Stacking” wato “Adani”! Da yake lamarin nasu na ‘yan jari hujja ne a duk lokacin da mutum ya fi yin stacking y fi ƙima da samun cigaba s tsarin. Ana zabo waɗanda suka fi boye Tokens a ba su matsayin “Validators”. Ana ganin tunda su suka san ƙimar abin, sai a ka basu kulawa da tsaro da tabbatar da cewa abubuwan suka tafiya yadda ya kamata a kan wannan blockchain ɗin nasu. Ba aikin banza zasu rika yi ba, za a rika ba su wani kare kamar Riba “Interest” bisa boyewar da suka yi! Da yawa manyan ‘yan mining suna yiwa ƙanann wayo, su saye nasu don su yi stacking!

    iv-Bayan dora Notcoin a ka jadawalin saye-da-sayarwa na “Binance”, Kamfanin NOTCOIN ya fitar da tsarin da yake ganin ta haka za a rika raba ladan gaben NOTCOIN tsakanin masu ruwa-da-tsaki da sauran Ya-ayyuhannasu! Wato 78% za a warewa masu mining (miners) a duk inda suke. Sai mutanen da aka samu tun asali suna harka a kan Jadawalin Binance, su ma suna da alfarma ta 3% don a riƙa damawa da su (Binance louchpool). Sai kuma 9% zasu tafi a (ecosystem fund) kudaden gudanar da shi kansa Binance din. Kaso 5% kuma na tallafi ne ga jama’ar su na kan Telegram (Community Incentive). Na karshe kuma 5% za a rika habaka harkar da shi (Development). (http://amp.coincodex.com/article/42684/binance-launchpool-notcoin-not/).

    v- Tun daga rahotannin yawaitar talauci da rashin aikin yi gami da kwaɗayi mai yawa da rashin sanin ƙimar lokaci da yawan son banza da suke cikin zukatan samari a kasashen Afrika da sauran kasashe masu tasowa, daga nan ne manyan masu kamfanonin mining na duniya suka sake dabara. Dabararsu kuma ita ce su buɗa mining, su daɗa yin (decentralizing) na mining sosai ga duniya don a sami hannaye marasa aikin yi su taya su yin group mining don abin ya faɗaɗa sosai. Zamu iya cewa an fara gwada yiwuwar yin mining a kan waya da project din manhajar Pi Network, wanda daliban digiri na uku a Standford University suka kirkiro shi, aka fara shi a 14 March 2019. Har yanzu kuma yana nan a matsayin gwaji (testing stage). Daman tun asali ba a yi Pi don ya fashe a sami ladan gabe ba.

    An yi shi ne don a gwada a ga irin karɓuwa da mutane zasu yiwa mining don su rika yinsa a wayoyinsu. (https://stanforddaily.com/2019/09/16/stanford-grads-develop-cryptocurrency-for-smartphone-users-to-increase-its-accessibility/) Wannan ya bude idanuwan manyan kamfanonin mining da masu sa hannun-jari a crypto. Don haka suka samar da irin wadannan manhajoji da yawa, sannan suka auno aikin nasu ya taho kasashen da ake cewa da su Kasashe masu martaba ta biyu da ta uku “Second and Third World Countries”. Wannan ya haɗa da su India, Brazil, Nigeria, Ghana, da sauransu. Don su sami masu yi musu dimbin mining, amma ba ko anini ko kuma idan aka ɗan watsa musu ‘yar tsaba, ta ishesu!

    7-Sai mu zo ga bayanin ta ya ya aka yi NOTCOIN ta fashe har mutane suka sami wasu ‘yan kuɗade, wasu kadan wasu da yawa.

    i-A harkar cryptocurrency akwai abinda ake kira da “Token Distribution”, wanda zamu iya fassara shi a Hausa da “ Rabon Ladan Gabe”. Ma’anar sa ita ce wata kyauta ce wadda ake samu sakamakon yin mining kai tsaye ko don saka hannun-jari ko don amfani da manhajarsu ko don taimakawa kamfanonin mining din ta wasu fuskoki da suka nemi a taimaka musu.

    ii- Sannan akwai manufofi daban-daban da suka sa ake yin Rabon Ladan Gabe a tsarin crypto. Fitattu a cikin su akwai shigo da mutane cikin “project” ɗin, ba wai ya takaita ga wasu ‘yan tsiraru ba. Sannan ana karfafa gwiwar wadanda suke cikin tsarin. Daga cikin manufofin akwai nuna ƙarfi da matsayin da “project” din zai samu in aka buɗe shi “Launching” a kasuwa. Da sauransu.

    Kafin Lauching, masu kamfanin suna samo adadi kaɗan na coin din sannan su nemi mutane don a saye shi. Manyan investors su fara saya da sauki, ya fara yawo a hannunsu. Wannan shi ake kira da Pre-ICO (Initial Coin Offering), ko Token Pre-Sale. Manufar ita ce, a fara tattara wasu makudan kudade da za a gudanar tare da kulawa da kariya ga Coin din. Bayansa ne kuma da wani lokaci sai a yi Launching dinsa. Sannan a dora shi a kan Jadawalin saye-da-sayarwa.

    iii-Haka nan akwai hanyoyi da yawa da masu “project” daban-daban a cikin harkar crypto suke bi su yi rabon ladan gabe (Tokens). Daga cikinsu akwai: “Public Sales Model”, da “Venture Capital Model”, da “Lockdrop Model”, da “Airdrop Model” da “Rewards Model”. Ba bayanansu zamu tsaya yi dalla-dalla ba. Amma abinda ake son a nuna a nan shi ne, a zahiri masu project din NOTCOIN suna yin amfani da hanyoyi guda biyun ƙarshe wajen raba ladan gaben su ga mutane.

    vi-“Airdrop” wanda za a iya fassara shi da samun “Bulus”. Wato kyauta ce da masu project suke bayar da ita ga mutanensu ba tare da wani aikin a-zo-a-gani ba. Saboda haka mutun ya sameshi ne a bulus! Shi kuwa “Reward”, ana bayar da shi ne sakamakon aiki da masu project din suka tabbatar mutum ya yi musu don habaka project din da ciyar da shi gaba.

    v-Ana bada ladan gabe a lokuta daban-daban, musamman a project. Ba wai dole sai kudaden da ake rabawa mutane sun zamo daga ainihin kudin “Coin” din da aka samu ba. Su kansu masu sa hannun-jari a project din zasu iya fitar da makudan kudade su raba ladan gabe ga mutanen da suke tare da su akan manhajar. Saboda hasashen cewa yin hakan zai taimakawa project ɗin ta hanyoyi da yawa.

    vi-A baya kadan an yi bayanin cewa Kamfanin hadahadar kwandalayen Crypto, wanda aka fi sani da “Binance” ya ɗauki gabarar tallata NOTCOIN a kan jadawalin sa. Shi dai wannan kamfani shi ne ya dauki nauyin raba ladan gabe ga masu yin mining a kan wayoyi. An sanya 13 zuwa 15 ga May 2024, a matsayin kwanakin da zai yi rabon kaso uku bisa ɗari na ladan gaben NOTCOIN ga masu hulɗa da su. (http://amp.coincodex.com/article/42684/binance-launchpool-notcoin-not/). Shi ne wanda a ka ga mutane suna ta shewa cewa Notcoin ta fashe!

    A sama an fada cewa Notcoin ya tanadi ladan gabe har sama da biliyan ɗari da biyu da ɗigo bakwai (102.7 billion tokens).

    A cikin wannan ne aka ɗauki biliyan uku (3,081,576,651) don rabawa ga masu danne-dannen NOTCOIN! Masu account da Binance ko wadanda aka budewa account dinsu a wannan kwanaki, sannan suka bi sauran tsare-tsare da tanaje-tanajen har a karshe suka sami wadannan kudade a aljihunansu. A takaice wannan shi ne ma’anar ta fashe!

    8- Yanzu bari mu zo ga muhimman matsaloli ta fuskar Shari’ar Musulunci wadanda suke tattare da yin mining na NOTCOIN da TapSwap, da makamantansu

     na kamfanonin Cryptocurrency. Ga fitattu daga ciki:

    i-Akwai Kasada da Garari mai karfi a cikin yin mining. Domin ya yi kama da abinda ake cewa da shi ‘Cinikin kifi a ruwa’, ko abinda Hausawa suke kira da ‘Cinikin biri a sama’. Saboda mutum zai yi ta daddannawa, yana salwantar da lokacinsa da karfinsa tun safe har yamma na watanni, amma bai san lokacin da zata fashe ba. Da yawa masu danne-dannen ba su san ma abinda suke bata lokaci a kansa ba. Shi dai kurum ya samo babbar waya, an buɗe masa, sannan a ce da shi ita danna nan, in ta fashe zaka samu kudi! Shikenan. Ga shi ana gani mutane sun dauki lokaci suna danna TapSwap da cikakken buri da tsammani, amma sai a wayi gari sun kori mutum, sun ma rufe masa damarsa da cewa (Your bot blocked). Yana ganin miliyoyin da ya tara, amma duk sun zama shirme. Wannan shi ne ainihin “garar”, irin wanda Abu Huraira (R.A.) ya ruwaito cewa Annabi (S.A.W) ya hana da cewa, “Manzon Allah (S.A.W) ya hana cinikin garari”-(Muslim, L:1513)

    عن أبي هريرة- رضي الله عنه- قال نهى رسول الله-صلى الله عليه وسلم- عن بيع الغرور".

    Akwai nau’ukan kasada da garari guda takwas kuma dukansu kusan suna cikin mu’amallar mining da crypto baki ɗaya. Ga bayanin yadda suke a takaice:

    a-Ya zamo abin da ake mu’amalla da shi yana nan lafiya garau - - السلامة A sha’anin mining, mutum ba shi da tabbacin abinda yake wahalar tarawa ko za a karba ko za a ce da matsala a kansa.

    b-Lokaci -الاجل - Lallai akwai bukatar a san gwargwadon lokacin da za a yi mining din, ba wai a yi ta yi sai kamfanonin sun bushi iska can daga baya sun sa lokaci kaza da zata fashe ba.

    c-Jinsi - - الجنسAkwai bukatar a san jinsin abinda za a bawa mutum ta bangaren kyautar. Amma mining ba a san nawa za a ba shi ba. Yana na dai yana ta fama! Wañnan shi ne ma’anar rashin sanin jinsin a nan.

    d-Nau’i النوع-- Tantance nau’in abinda mutum zai samu yana da muhimmanci. Bayyana nau’i yana nuna yadda Shari’a ta kula da fitowa da mutane hakkinsu cikakke. A tsarin mining mutum yana cikin kila-wa-kala domin wani karamin dalili zai iya sawa a hana mutu kwandala daga abin da ya yi watanni yana tarawa.

    e-Gwargwado - المقدار- Za a iya cewa an san gwargwadon abinda mutum zai yi na danne-danne, kada ya zamo kasa da kaza misali. Ta bangaren su kenan, amma ta bangaren mai dannawar bai san gwargwadon kuɗin ladan gaben (Tokens) da zasu ba shi ba An daure mutum ne da igiyar zato da jiran tsammani.

    f-Samuwar abinda ake yin aikin dan shi - الوجود- Idan ya zamo abin da za a yi aikin baya nan kuma ba bu takamaimai lokacin da za a sameshi, wañnan ma garari ne. Ma’ana mutum bai sani ba ko mining din da yake yi ya sami karɓuwa a wurinsu ko bai samu ba, shi dai bai sani ba. Sai bayan watanni bayan ta fashe zai sani. Shi ya sa tsarin crypto yake cike da haɗari a Musulunce.

    g-Tantance abin da aka karba da wanda za a biya , -التعيين -shi ma wajibi ne. In ba haka ba, za a iya fadawa cikin garari. Matum ba ya sanin gwargwadon abin da masu kamfanonin mining za su karba, su ba shi ladan gabe. Sai sun gama lamuransu sannan za su yanke nawa mutum zai samu.

    i-Samuwar abin da aka yi aikin a kansa - الحصول- Duk abin da yake ba bu tabbas ko samunsa yake da wahalar kamar cinikin kifi a ruwa ko tsuntsu a sama, wañnan nau’in garari ne. Ba a yarda a kulla mu’amalla ta irin wannan hanyar ba. Misali a irin mining da mutane suke yi, mutumin da ya dauki watanni yana faman danne-danne, ba shi da tabbacin mai zai samu. Wani zai iya samun da yawa.

     

    Wani ma takai ga cewa ba za su ba shi komai ba.-(Al-Kawa’id na Imamu Al-Makri, sh/402, L:8303; Bidayatul Mujtahid na Ibnu Rushd: 2/111; Al-Muntaka na Baki: 5/41-42; Azzakhirah na Karafi: 4/355 da 5/260, Kawa’idul Ahkam na Izzuddini Ibnu Abdissalam: 2/116-117, Sharh Al-Lu’lu al-Masun karkashin ka’ida , L:353 kaso na farko da L: 37 da 52 kaso na biyu.)

    Ƙwaƙƙwaran misali na kasada da gararin da ya faru a kwanan nan shi ne fitaccen mawaki dan Nijeriya mai suna Davido, ya yi amfani da roman baka da ake ta yi game da manhajar “Solana”. Sannan ya rudi mutane da cewa a kan Telegram dinsa yana da masu binsa mutune kusan dubu talatin. Don haka nan take a ranar Laraba 28 May 2024 ya tallata wata karamar manhaja ta mining mai suna “$DAVIDO crypto token”. A awowin farko an sami riba mai dinbin yawa. Amma cikin awa goma sha daya sai ya kwashe kudinsa, abinda ya jawo manhajar ta rikito da kaso 90% cikin ɗari. Duk wadanda suka shiga sun yi asara. Wannan ba shi ne lokaci na farko da Divido ya fara yaudarar mabiyansa a kan su fada cikin wata hadahadar kwandalar crypto ba. Domin a 2021 ya jagoranci buɗe wata manhajar, mai suna $echoke. Ita ma ba dadewa aka rufe ta. Sannan ya daɗa shigewa gaba wajen tallata “Racksterli, Ponzi scheme”, mutane suka shiga da yawa. Amma a karshe sai da aka yiwa mutanen almundahanar Dollar billiyon daya. Sannan kuma a yanzu ga shi ya dada dawowa a wannan ‘yan kwanakin, ya kuma sa an tafka asara!- (https://techcabal.com/2024/05/30/davido-solana-coin/ da kuma : https://techpoint.africa/2024/05/30/is-davido-a-scam/)

    Muhimmin darasi a nan dai shi ne harkar crypto harka ce mai hadari. Sau tari kamfanonin Cryptocurrency suna amfani da fitattun mutane, Balarabe ko Bature, ɗan Rasha ko ɗan Pakistan,da sauransu, su yi ta tallan wata manhaja ta cryptocurrency har mutane su yaudaru su shiga, sai kuma yadda hali ya yi. A wasu lokutan ma kamfanonin na su ne ko kuma sunada hannun-jari mai ƙarfi a ciki. Amma sai a yi amfani da rashin wayon mutanemu a yi ta danna kansu a rami! A sani Ka’idar Musulunci ta kiyaye daraja da mutuncin dukiya, ba zata taba daidaituwa da wannnan tsarin da ake tafiya akansa na crypto ba!

    ii-Tsarin wannan mining da ake yi, yana tattare da danne hakkin masu barje guminsu a wurin yin mining. Domin bai dace a ce mutum zai bata lokaci da ‘data’ da kuzarin jikinsa kuma ya tara gwargwadon abinda aka ce ya tara, wani ma har ya tafi zubi biliyoyin units, amma zai tashi a tutar babu, idan an zo rabon ladan gabe ba! Haka ta faru da yawa. A cikin mutanen kasashen duniya da suka zunduma a mining din NOTCOIN, da Tapswap, fiye da kaso saba’in da biyar basu sami komai ba. Bayan kuma suna yin mining din, iya bakin kokarin su. Idan da akwai adalci a tsarin, ya kamata fiye da wannan adadin ta fashe da su. Idan da kuwa za a kalli abin ta tsarin Musulunci, to da kowa cikin wadanda suka yi, zai samu ladan gaben ko ya ya kankantar abinda ya yi mining yake kuwa!

    Masu ganin yin mining kamar wata hidima da aiki ake yiwa masu kamfanin NOTCOIN da Tapswap a misali, ya kamata su auna tuninsu da wannan zaluncin da kamfanonin da suke sa mutane su yi mining suke yi. Da yawa daga manyan masu yin mining da ma wadanda suka sami wani abu a waccan fashewar da ta yi, ba zasu kula da wannan zaluncin ba, saboda ba su ya shafa ba. Amma mu a Musulunce abin kulawa ne. Duk da tsarin ne azzalumi tsari tun asali, a haka yake, amma dole a fadakar da mutane.

    iii-Ta wata fuskar kuma, su kansu talakawa da aka ƙwadaitawa yin kuɗi a dare ɗaya, suna barnatar da lokacin su da kudaden sayan “cooling fan” da “data” dinsu, ko ya ya kankancin ta yake kuwa, a kan abinda basu da tabbaccin fashewarsa sai dai sa rai, da kwadayi. Idan ma ya fashe, mutum bai san mai zasu jefe shi da shi ba! Wannan shi ma almubazzaranci ne da dukiya da lokaci. Allah Madaukakin Sarki yana cewa, “Kada ka yi almubazzaranci. Hakika masu yin almubazzaranci sun kasance ‘yan uwan Shaidanu. Shi kuwa Shaidan ya kasance mai kafircewa ne ga Ubangijinka”.-(Al-Isra’: 26-26)

    قال الله تعالى: "ولا تبذر تبذيرا. إن المبذرين كانوا إخوان الشياطين وكان الشيطان لربه كفورا".

    Har ila yau Annabi (S.A.W) ya hana tozarta duniya kamar yadda Mughirah bn Shu’uba ya ruwaito.-(Bukhari, L:1477; Muslim)

    iv-‘Yan kudaden da aka raba a cikin watan May 2024 ga wasu mutane masu danna NOTCOIN, ya sa an dauki project din a matsayi babba. Don haka mutane da yawa suka bazama, suka shiga sahun masu danna TapSwap don su zama suna tare da shi saboda jiran tsammanin samun garabasa daga wurin masu project din nan gaba. Irin wannan wasa da hankalin shi ne za a yi ta yi da samari da ‘yan mata a hana su mayar da hankali kan neman ilimi da yin sauran sana’o’in da zasu amfana da su!

    iv-Kudaden da aka bawa wasu ba su ne ainihin abinda mutum ya rika tarawa sakamakon danna NOTCOIN ba. Abinda aka bayar a matsayin “Airdrop” ko “Reward”, manufarsu da shi ita ce a ja hankalin mutane sosai zuwa ga harka da cryptocurrency. Dalilin fadar haka shi ne, a lokacin da ta fashe, mutane suka sami kudaden, ba ma a fara dora Notcoin din a kan jadawalin saye-da-sayarwa ba. Don haka masu kamfanin ne ko masu sa hannun-jari su ne suka debi kudadensu suka bayar. Sun yi haka ne don su cimma abubuwa guda biyu:

    a- Kullum masu jiran tsammanin nan suna ta yin mining wanda zai taimaka wajen motsa blockchain na wannan kamfani, kada ya yi sanyi.

    b-Za su riƙe dimbin mutanen da suke bin Community na wannna “game” ɗin NOTCOIN da igiyar zaton za a dada sako wasu kudaden na bulus nan gaba. Shi ne za a ga mutane suna ta binsu irin bin da suke kira da bita-zaizai ! Wanda yake son ya gane cewa kudaden da NOTCOIN’ suka saki, wato fashewar da ta yi (Airdrop), wata sabuwar yaudara ce don jan hankali ya duba wannan rubutun: (https://www.linkedin.com/pulse/impact-notcoins-airdrop-crypto-adoption-accessibility-heng-ching-tek-btacc).

    Ƙa’idar masu crypto ita ce “ka zamo kana da kulawar mutane, to wannan ma jari ne”. Shi ne suke fada da turanci cewa, “In the crypto industry, attention is money”.-( https://www.legit.ng/people/1594938-tapswap-cryptocurrency-expert-lists-interesting-people-dont-coin-mining-games/)

    v-Harkar cryptocurrency harka ce da take a duƙunƙune, musamman daga can sama. Abubuwa suna kasancewa, wadanda suke sawa mai basira, wanda idonsa bai rufe da so da tunanin samun kudin bulus ba, yana rika duba irin wadannan abubuwan. Tun daga tarihin Bitcoin, an fada cewa ba a san wanda ya kirkiri ma hajar ba, amma dai ana ta bin abin a haka. Sai kuma ga shi, kamfanin NOTCOIN sun saki “Whitepaper” dinsu a wani yanayi mai sarƙaƙiya! Ita “Whitepaper” ana yinta ne ga duk sabon “project”, a cikin kalmomi warawara don a fayyace wa mutane manufofin wannan “project” din, da sharaɗansa, da dokokinsa, da yadda ake so a tafiyar da shi, da abinda ake so har da wanda a ba so, za a iya nunasu a cikin takardar. Domin wanda zai shiga, ya shiga da masaniya. Wannan duka sabanin “Whitepaper” ta NOTCOIN. Takardar tana da shafi tara, amma a shafin Farko ne kawai aka rubuta cewa, “NOTCOIN Whitepaper November, 2024”. Daga wannan ba ƙari. Ragowar shafukan haka suke farare tas ba komai a cikinsu. Wannan kuwa ba haka ya kamata abin ya kasance ba. Domin an bar mutane cikin rudami da rashin sanin alkibilar NOTCOIN din. Wannan yana daga cikin abubuwan da suka sa ake tabbatar da akwai lauje cikin naɗi !

    Shi kansa Tapswap da mutane suka koma kansa, suna fatan fashewarsa karshen May, masu kamfanin suka ce sun fasa yi a lokacin. Yanzu sun mayar da shi cikin June, don suna so su dora shi a kan jadawalin saya-da-sayarwa a farkon July, shi kansa ba shi da wata Whitepaper. An sake shi ne kawo a kan Telegram. Sai aka faɗawa mutane cewa zai fashe ne a kan Solana. Daga baya kuma aka sami bayani daga kamfanin Solana cewa ba su da alaƙa da Tapswap. Amma abin mamaki har yanzu mutane suna makale da su suna jiran tsammani! Su kuma suna kara daure mutane da igiyar zato. Domin sun sa a kan X cewa, akwai babban rabo yana tafi.

     

    (The biggest reward ever: 3 million Shares and the possibility to get a $600 Binance voucher!”- (https://www.legit.ng/people/1595238-tapswap-announces-special-mission-offers-biggest-reward-nigerians-mining/). Sun mayar da lokacin ƙaddamar da TapSwap daga 30 ga May zuwa 1 ga July. Kafin haka zasu yi aiki don su tantance masu mining na gaskiya. Sun ce, “we've uncovered many bots. That earned an unrealistic amount of Shares. To maintain justice in token distribution. We're taking measures to stop and ban these bots”. "Our top priority is ensuring fair allocation of TAPS and rewarding those who've earned them honestly."

    Ko ma dai ya abin yake, Musulunci ba ya halatta a shiga cikin mu’amalolin da suke da ƙunbiya-ƙunbiya!

    vi-Idan aka matsa duba a kan yadda NOTCOIN da Tapswap da sauransu da suke gudana za a ga cewa a cikin wannan “game” din da ake yi akwai burbushin caca. Amma ga bayanin yadda aka haihu a ragaya:

    a-Tare da cewa ba a kan manhaja guda mutane suke ta faman yin mining ba, amma a cikin masu yi babu wanda yake da tabbas cewa zata fashe ya samu, kowa zato yake yi da jiran tsammani ( game by chance) ko za a dace ta fashe! Irin wannan yanayin kuwa shi ma dan uwan caca ne. Tun a 2018, Travis Sztainert, masani ne a kan hadahadar kudade da crypto, yake cewa, “Matsalar cryptocurrency ita ce har mutanen da ba sa yin caca kai tsaye, na iya yin cacar ba kai tsaye ba ta hanyar rashin samun tabbas a hawa da saukar sauyin kuɗi (speculation). Gaskiya akwai kasuwar musayar kuɗi mara tabbas, inda masu sauyi ke siye da sayarwa, da riƙe kwandalolin cryptocurrencies don samun riba daga ƙazamin sauyin kuɗin da ya yi musu daɗi a rai."- (Sztainert (2018) Blockchain, cryptocurrency, and gambling; https://eu.docworkspace.com/d/sIEXd66LVAdbU5rIG)

    Stainert said, “An additional issue with cryptocurrency is that even people who don’t directly gamble may be indirectly gambling through currency speculation. Indeed, there is a large exchange market in which speculators buy, sell and hold cryptocurrencies in order to profit from favorable fluctuations in exchange rates”.

    b-Akwai tsare-tsare da suke dauke da caca a cikinsu. Amma bari mu yi misali da guda ɗaya wato wanda ake kira da “Squad”. NOTCOIN yana bawa mutane da yawa damar su hadu su yi mining ta yadda zasu zarce wasu abokan karawarsu. A nan ma ana samun rashin tabbas na sakamakon abinda mutum zai samu bayan dinbin wahala. Sannan ana samun mai ƙarfi yana danne mara ƙarfi a wajen rabon ladan gabe!

    9-Mining a NOTCOIN ko TapSwap ko Avacoin ko wata a manhajar kwandalar crypto din daban, da daukacin tsarin cryptocurrency, akwai abubuwan da suka baibaye shi, kuma za a iya la’akari da su a matsayin ‘haram’ a ciki ta fuskaokin da yawa. Ga wasu muhimmai daga cikinsu:

    i- Hauhawar farashin ƙwandalayen crypto da rikitowarsa a cikin ƙanƙanin lokaci ya wuce yadda ɗabi'ar hadahadar dukiya ta haƙiƙa take. Sannan, hatta ƙimar wasu coins ɗin, musamman Bitcoin a Dalar Amurka abin dubawa ne saboda farashin ya wuce yadda ɗabi'ar kasuwanci ko canjin kuɗi na ƙasashe take. Wannan ya sa, akwai "volatility" mai yawan gaske a cikin harkar crypto. Wannan ma kansa wani nau'i ne na garari.

    ii- An yi bayanin Stacking a sama cewa adana Tokens ne a matsayin boye kaya. Idan aka duba da kyau za a ga, a gaskiya, ya fi karfin haka. Domin yana daidai da ajiye kudi a savings account bayan wani lokaci a fito da shi. Sun yi bayanin cewa za a iya ajiye wa kullum ko duk sati ko sati biyu ko wata ko wata uku ko hudu, da sauransu. Sannan mutum yana samun sakamako bisa tsahon ajiyar da ya yi. Abin ya danganta kuma da manhajar da yake bi. A cikin takardar wani masanin harkar yana cewa, “In return for staking their crypto, users earn more cryptocurrency. Staking is similar to depositing cash in a high-yield savings account, where banks lend out your deposits and you earn interest on your account balance”.

    iii- An yi bayanin cewa sai an bi ta kan kamfanonin canji irinsu Binance sannan za a tallata shi. Waɗannan kamfanoni kala biyu ne. Akwai wadanda za a mika musu ƙwandalolin, su za su shirya yadda za a saya ko a sayar da su. Ana kiransu da “Centralized Exchange” (CEX). Su ne kamar Binance, Kraken, Coinbase, da Gemini, eToro, Huobi, OKEx, Bitfinex, da sauran su. Za a iya canja kudi na hakika a karbi na ƙwandalolin crypto ko a sayar da ƙwandalolin da kudi na haki. Shi suke kira da (On-ramps da off-ramps).

    Sai kuma ɗaya kalar wanda ake bawa mai ƙwandalolin dama ya sayar yadda ransa ya yi masa daɗi, kuma kai tsaye zuwa ga wanda yake son saya. Ana kiransu da “Decentralized Exchanges” (DEX). Su ne kamar Uniswap, Pancakeswap, Curve, Uniswap, Sushi swap, Open Ocean, IDEX, GMC, dYdX da sauransu.

    An kawo wannan ne don a fito da wani gagarumin sabawa dokokin Allah da ake yi a cikin hulɗa da wadannan kala biyu na kamfanonin saye-da-sayarwa. Ga sunan fitattun hanyoyin cinikayyar: Spot Trading, Margin Trading, Futures Trading, P2P Trading, Options trading, Day trading, Swing trading. A gaskiya banda Spot Trading da kuma P2P Trading, duka ragowar riba na shigar su. Kuma su aka fi yi sosai, musamman a kan tsarin CEX, irin wanda Notcoin ta shiga. Shi ne kuma tsarin da Tapswap suka fada cewa nasu ma zai fito a kansa.

    A “Spot Trading” ana yin canji ne nan take ba tare da wani jinkiri ba. An fi yinsa tare da DEX. Shi kuma P2P wanda yake nufi ln (Peer-to-Peer) shi ne canjin da yake gudana tsakanin mutum da mutum ba wani a tsakaninsu. Kasancewar ba shi da tsarabe-tsarabe shi ya sa dan kubuta daga riba.

    Ana yin Future Trading ne ta yadda wanda ba shi da kaya kamar kamfanin Binance, zai saya ko ya sayarwa da wani kayansa, a kan farashi na musamman, da sanya ranar karbar kayan, batare da izinin mai kayan na asali ba. Wannan cinikayyar ita kusan duk kamfanonin CEX suke yi. A bayyane yake kuma wannan haram ne a Musulunci.

    Shi kuma “Margin Trading”, mutum zai ranci kuɗi daga kamfanin Binance misali don a kara a kan nasa da zai yi saye-da-sayarwa da su. Wannan shi ake kira da "Leverage". Wannan bashin da ruwa zasu bawa mutum. Idan an juya an sami riba,sai su ɗebe nasu mai yawan. Idan kuma ba a sami amfani ba, sai su ja hankalin mutun ya karo kudade. Idan asarar ta yi yawa, sai su rike kudaden mutun, shi kuma su koreshi daga tsarin. Shi ma tarin Leverage haramun ne a Musulunci.

    Haka shi ma “Swing Trading”, ana rantar kuɗi ta hanyar Leverage, sannan boye kayan zuwa wasu kwanaki, ana ta duba hawa da sauka na kasuwa. Da zarar an ga farashin da ake son kayan su kai, sai a fito da su a sayar. Idan kuma an boye kayan ne tun safe, ana neman babban farashi, har zuwa kafin a rufe kasuwar ranar, shi ake kira da Day Trading. Duka tafiyarsu ɗaya ce, biye kaya ne a lokacin buƙata. Sannan kuma ga ribar da take ciki na Leverage. An san masu leverage kuma, a tsarinsu su ba sa faduwa, kulkum riba suke ci!

    Shi kuwa “Option Trading” caca ce baro-baro. Domin cinikayya ce za a dora ta a kan ga kudi tun yanzu an sayi abu kaza, wanda nan gaba farashinsa zai kama daga kaza zuwa kaza. In ya zo daidai kaza kurum an saya. (https://bircheshealth.com/resources/options-trading-gambling)

    Abinda ya aka kawo wannan dalla-dalla don ‘yan crypto su san hadarin da suke ciki. Wanda duk yake yin harkar crypto tun daga mining har kololuwa da ya tabbatar yana taimakawa riba, da garari, da caca, da sayar da abinda mutum bai mallaka ba, da sauran nau’ikan cinikayyar da ba su halatta ba. Mutum ba shi da sauran uzuri. Idan da bai sani ba, yanzu ga shi an fito masa komai fili.

    iii-Tsarin Crypto yana son kafa wani tsari na hadahadar kudaden da basu da lasisi daga gwamnati. Malaman Musulunci sun tabbatar da cewa duk kudin da gwamnati bata tabbatar ba (Legal Tender), ba kudi ba ne a musulunci. Ba laifi a dada kawo bayanan manyan malaman Musulunci a nan:

    a- Imamu Malik yana cewa, “Da a ce mutane zasu yarda da fatun dabbobi a tsakaninsu a bugasu a matsayin kudade, da ba zan so a sami jinkiri ba idan sun yi canja fata da dinare da azurfa".-(Al-Mudawwanah: 3/5. A dada duba ra’ayin Hanafiyya a Littafin Tanbihur Rukud Ala Ahkamiln Nukud na Ibnu Ibidn: sh/25)

     قال الإمام مالك-رحمه الله-:"ولو أن الناس أجازوا بينهم الجلود حتى تكون لها سكة وعين، لكرهتها أن تباع بالذهب والورق نظرة".

    Ma’anar maganarsa ita ce duk abin da gwamnati da mutane suka hadu a kan cewa shi ne kudi, kuma suka gina rayuwarsu a kansa, ya zama kudi. Kalmar سكة ita ta nuna cewa kudade ne da gwamnati ta yarda da su, ta kuma buga su, ko ta yi musu sitamfi na yarda. Duk hukunce-hukuncen Shari’a na kudi zasu tabbata a kan wannan kuɗin. Kudi suna da sifar zamowa tsanin da kowa-da-kowa zai yi amfani da shi wajen saye-da –sayarwa. Ba a la’akari da kudaden da suka zamo masu gudanawa tsakanin wasu tsurarun mutane.-(Al-Warkun Nakadi na Sheikh Abdullah bn Mani’i sh/17).

    Kwandalolin crypto ba kuɗade ba ne da kowa-da-kowa da yake da ikon amfani da su cikin sauki. Kudade ne-in har an yarda ma cewa kudin ne-da suke yawo a kan internet kurum a matsayin kudin gaibu. Wadanda suke huldar su, su kadai suka san da su, kunzumin mutane ba su da alaka da wadannan kudaden na boye!

    b- Imamu Ahmad bn Hanbal yana cewa, “Ba wanda zai buga kudi sai gidan buga kudi (na gwamnati) da izinin shugaban. Saboda mutane in an yi musu rangwame a kansa, sai su wuce gona da iri”. Sai Imamu Abu Ya’ala ya ce, “Imamu Ahmad ya hana a buga kudi ba tare da izinin shugaban ba. Saboda yin hakan wani ta’addanci ne gareshi”.—(Ahkamus Suldaniyyah na Abu Ya’ala: shi/181; Mukaddimatu Ibnu Khaldun: sh/226; Annukud Wal-Bunuk Fin Nizamil Islami na Dr. Auf Muammad Al-Kafrawi:sh/20-56)

     قال الإمام أحمد-رحمه الله-:"لا يصلح ضرب الدراهم إلا في دار الضرب بإذن السلطان، لأن الناس إن رخص لهم ركبوا العظائم". فعلق الإمام أبو يعلى الحنبلي قائلا:"منع من الضرب بغير إذن سلطان لما فيه من الافتيات عليه".

    c-Imamu Nawawi shi ma ya yi bayanin cewa duk malaman Mazahabin Shafi’iyya ba su yarda da wani ko wasu gungun mutane su ware su buga kudi ko su kirkiro wasu kudade daban, wanda gwamnati ba ta yarda da shi ba. Ya ce, “Ana kin wanda ba shugaban ba ya buga kudi (kamar dinare da azurfa) ko da kuwa masu kyau ne sosai. Saboda buga kudade aikin shugaba ne. Sannan kuma ba za a sami aminci ba, don za a iya samun algus da barna a ciki”. (Al-Majmu’u na Nawawi:6/11; Raudatud Dalibina na Nawawi:2/258)

    قال الإمام النوي-رحمه الله-:"يكره لغير الإمام ضرب الدراهم والدنانير، وإن كانت خالصة. لأنه من شأن الإمام. ولأنه لا يؤمن فيه الغش والفساد".

    Cryptocurrencies ba su da wata ƙima a Nigeria. Domin Gwamnati bata ɗaukesu a bakin komai ba, ba Legal Tender ba ne. A kan haka ne ma Central Bank ya fitar da sanarwa tun January 12, 2017 a kan an yi watsi da tsarin ƙwandalayen crypto. Bankin ya dada maimaitawa a 2018. A 5 ga February 2021 kuma ya Dada jan kunnen bankuna cewa kada su yarda a hada kai da su wajen huldar cryptocurrency. A December 22, 2023 an sami canje-canje wajen yadda Bankin yake kallon cryptocurrency, amma dai sun bayyana baro baro cewa kada bankuna su shiga hulɗa da masu shi. Ga abinda aka bada Circular ta ƙarshe take cewa “banks and other financial institutions are still prohibited from holding, trading and/or transacting in virtual currencies on their own account”.- (GUIDELINES ON OPERATIONS OF BANK ACCOUNTS FOR VIRTUAL ASSETS SERVICE PROVIDERS (VASPs) @ www.cbn.gov.ng). A kan wannan an ta yin rubuce-rubuce. -(https://www.linkedin.com/pulse/legality-cryptocurrency-ban-central-bank-nigeria-leke)

    Ma’anar wannan, ko da an sake masa kallo a matsayin “Assets”, an dai hana bankuna su buɗe kansu account a na crypto. Saboda har yanzu ƙwandalolin crypto ba Legal Tender ba ne a Nigeria.

    iv-Mutanen da suke yin mining a kan wayarsu ko a kan kwanfiyutocinsu suna taimakawa wajen tabbatar da matsaloli da jimlar mu’amalolin da Shari’a bata yarda da su ba.

    Saboda duk abinda aka tara na lambobin da suke fitowa a lokacin daddanna wayar, su ne kamfanin NOTCOIN da Tapswap da sauransu za su tattara na mutane musamman wadanda suke yi miliyoyi sai su dora su a kan na su babban injin don su sami karfin da zai bude musu zuwa ga blockchain, wanda shi ne ake samo ƙwandalar Notcoin da sauransu daga wurinsa. Sannan a zo a bi duk hanyoyin da ake bi na tallata ƙwandalar da sayar da ita. Ita kanta tallatawar (trading) tana cike da nata matsalolin da sauran abubuwan da an yi bayaninsu a rubutu a kan Bitcoin!

    Wannan taimakekeniyar ita ma matsala ce mai zaman kanta. Al-Kur’ani ya hana Musulmi su rika yin haka. Don ya ce, “Ku yi taimakekeniyar a kan biyayya ga Allah da taƙawa. Kada ku yi taimakekeniya a ka sabo da wuce gona-da-iri”-(Al-Ma’ida:2)

    قال الله تعالى: "وَتَعَاوَنُوا عَلَى الْبِرِّ وَالتَّقْوَى وَلا تَعَاوَنُوا عَلَى الإثْمِ وَالْعُدْوَانِ".

    Masu yin mining a Notcoin da Tapswap da irinsu daidai suke da wanda zai noma alkama, sai dillalin kamfani giya ya zo, sai su sayar masa suna sane da cewa shi wakilin gidan giya ne! Idan sun ce a da ba su sani ba, to yanzu an fada musu. Sai mutum ya bi imaninsa da Shari’ar Allah!

    v-Idan muka koma kan Shubuhohi (kame-kamen dalilai) da ake ta fada cewa aiki masu mining suke yiwa kamfanonin NOTCOIN da TapSwap da sauransu, to tambayar a wane babi za a sa mining? Muna da babin Ijara- الإجارة- wanda za a dauki mutum aiki kaza a biya shi albashi kaza, ko kuma babin Ji’alah - الجعالة-wanda mutum zai sanya kudi kaza ga duk wanda ya yi masa aiki kaza ko ya gano masa motarsa-misali da ta bata. Wadannan babuna su ne suka fi kama da inda za a sanya mining da ake yi. Amma idan aka bi yadda tsarin mining din yake za a ga ba su yi daidai da kowane ɗaya daga cikin wadannan babuna ba. Bari mu duba yadda suke:

    a-Sun bambanta da Ji’alah ta fuskar cewa mining bai cika wasu sharadai a ƙalla guda biyu ba. Na farko kamfanin NOTCOIN da TapSwap ba su sanya takamaimai zunzurutun kudaden da kowa zai samu idan ya kammala musu aiki ba. Ba wai su ce zasu ba shi Token misali 30 ba, domin shi kansa token din nasu tun farko ba a san ƙimarsa a kasuwa ba. Mutum yana yi ne dai da tunanin da hasashe-hasashen ko ƙimar zata yi Dala ɗaya ko santi tamanin ko kaza da kaza zata zamo ko kuma kaza ko kaza idan ta fashe, amma ba bu tabbas. Su can ba su fada ba. To, a Musulunci ba a zunduma yin aikin Ji’alah ba tare da an san nawa mai aikin ya sanya zai biya ba.

    Na biyu aikin da kamfanonin manhajar suke yi a ƙarshen sa bai halataccen aiki ba ne a tsarin Musulunci. Don yana kunshe da kasada da garari da sabawa tsarin kudade na gwamnatoci da sauransu.

    b-Ta bangaren Ijarah kuma, aikin mining bai hau kan wasu sharaɗan Ijarah ba. Mining ya saɓa mata saboda dalilai huɗu. Biyu da aka faɗa a sama a ƙarƙashin Ji’alah da kuma karin wasu biyun. Su ne:

    Na uku dole a san wanda za a yi hulɗa da shi, ta yadda za a sa sharadai da dokoki dalla-dalla. A nan rashin cikakkiyar “Whitepaper” da zata yi bayanin tsarin aikin shi ma zai shigo. Ɗan bayanin da suke gutsurawa a manhajar X ba zai wadatar ba. Don ana bukatar a san wannan tun farko.

    Na huɗu a tsarin Ijarah ko ya ya mutum ya yi aiki sai an kimanta iya wannan gwargwado abinda ya yi a biya shi. Su kuwa kamfanonin Cryptocurrencies ba haka suke ba. Mutum zai iya ɗebe watanni, dare da rana yana daddannawa, amma a karshe su share shi!

    10 - A ƙarshe, ina jan hankalin ‘yan uwa Musulmi ta ɓangarori daban-daban kamar haka:

    I - Kada mu sake mu ruɗu da kwandalayen da ake samu a hadahadar crypto, musamman za a ji wasu suna cewa su aiki suke yiwa manyan kamfanonin mining. Daga nan ba ruwansu da abinda kamfanonin zasu yi da abinda suka tara musu. Su dai sun biya su, shikenan. Wani ma ya ce ku rabu da malaman nan da suke hanaku shiga harkar crypto! Wadannan duka suna amfani da jahilcinsu su kansu da jahilcin mutum suna zuga gwaiwa ta hau ƙaya, har mutum ya je ya fada cikin wadanda Annabi (S.A.W) ya bada labari a karshen zamani.

    Abu Huraira (R.A.) ya ruwaito daga Annabi (S.A.W) yana cewa, “Lallai wani zamani zai zo wa mutane, mutum bai damu da ta inda ya samu kudi ba; ta hanyar halal ne ko ta hanyar haram ne?!”-(Bukhari, L:2083)

    عن أبي هريرة -رضي الله عنه- أن رسول الله -صلى الله عليه وسلم- قال: "ليأتين على الناس زمان، لا يبالي المرء بما أخذ المال، أمن حلال أم من حرام".

    ii-Akwai bukatar gwamnatoci daga Federal da States har Local Governments da su dage wajen samar da ayyukan yi ga samari. Kada a barsu ana ta yaudararsu da igiyar tsammani cewa 2030 Najeriya ce mafi yawan arzikin crypto. Manufar wannan rahoton yaudara ce da karya. Dabara ce kurum ta kamfanonin yin mining don samarinmu su dukufa a kan yi musu bauta. Sai su daina yin tunanin sana’o’i da noma da kasuwanci da sauransu. Zaluncin wasu shuwagabannin da rashin tafiyar abubuwa yadda ya kamata a Ƙasa ba hujja ce da zata sa a shiga yin shirman da yake cikin irin wannan mining din da mule gani yanzu ba!

    iii-Ya wajaba iyaye su kula da ‘ya’yansu, musamman samari da ‘yan matan cikinsu. Idan aka ayi sake wannan musu bata lokacin a kan mining zasu zo su mamaye su, su kuma hana su karatu da neman ilimi. A lokacin da su can ‘ya’yan turawan suna ta karatu don su kara zurfi a iliman rayuwa, musamman na crypto din, don su ci gaba da bautar da ‘ya’yanmu da jikokinmu kamar yadda iyayensu suke yi a yanzu!

    A dunkule, mining da mutane suka dukufa a kansa yanzu hanya ta tallafawa tsarin samar da cryptocurrency. Shi kuma irin waɗannan cryptocurrencies da ake kokarin a ƙaƙabawa duniya, musamman ƙasasjen Afrika da na Musulmi, an gina su ne tun asali ba a kan tsarin Musulunci ba. Sannan cike suke da hanyoyin -a fili da boye- kasada da riba da caca da bujirewar tsarin kuɗaɗen gwamnati da sauransu. Kuma ana suna nema musu wurin zama na dindin a tsakanin al’ummar Musulmi. Bugu da kari, mining yana taimakawa wajen tozarta lokaci da almubazzaranci da dukiya da sanya fargaba da tsabagen kwaɗayi da jiran tsammani mara dalili, a cikin zukatan samari.

    Don haka, mining da ɗaukacin tsarin samar da cryptocurrency sun haramta ne, ba wai a karan kansu ba, sai dai saboda dimbin matsalolin da suke baibaye da su (wato Haram Li Gairihi). A wurina haramcin su irin haramcin taba-cigari. Ta haramta ne saboda dimbin matsalolin da take haifar wa mai sha, amma ba ita karan kanta ba. Tsarin cryptocurrency zai halatta ne idan aka zare matsalolin da suka ci na karo da Musulunci ko aka musuluntar da shi. A wannan lokacin sai mu ce halal ne, kuma marhaban !

    Sai a yi hattara. Wallahu A’lam.

    Allah ya ba mu sa’a da dacewa a duniya da Lahira

    Daga taskar:
    Prof. Ahmad Murtala

    Notcoin Da TapSwap: Tarihi, Mining, Fashewarsu da Matsayin su a Mahangar Shari’ah

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.