Daga Sani Shehu Lere, Kaduna
Ina fara wa da addu'ar shiga Kushewa " Assalamu alaikum Darul Kaumul Mu'amin, Wa'inna In sha Allahu La-ragibun" bayan haka.
Ya aka ji da
jimirin rayuwa 'Barzhakiyya"? Bisa Lissafawa, yau a kidayar
"Girigori" 6 ga watan 6, kana da shekaru goma cif-cif da fakuwarka
daga wannan duniya tamu mai cike da zub da jini zuwa rayuwar Barzakhu, Allah
Yasa ana da isasshen guzuri na wannan doguwar tafiya, Mu ma Allah Ya bamu
guzurin tassheku amin.
Allah ya
haskaka Kabarinka, nasan wasikata bata zame maka sabon abu ba, domin kuwa ba
ita ce ta farko ba, kuma ba lallai ta zama ta karshe ba, matukar muna da
ragowar numfashi, kuma matukar ana samun "Muhdasatul Umuri" musamman
a Masarautarka.
Idan Allah
Yasa na baya basu bace Maka ba, wannan ita ce kwafi ta uku cikin wasikuna gare
ka, inda nakan tsegunta maka halin da ka bar Masarautarka da kuma in da ta
koma.
A wasikar
farko, na fada maka yadda ta kaya bayan rasuwarka, Inda aka hana Danka da
Jama'ar Kano ke kauna wato Sunusi Ado ya gaji kujerarka, Inda aka musanya shi
da jikan Sarkin Kano Muhammadu Sunusi (Danka na zumunta kuma Surukinka) saboda
kawai siyasa.
Bayan cikar
wa'adin masu gidansa kuma, shi kuma ya kasa yi wa bakinsa linzami, ita ma
sabuwar gwamnati ta tsige shi tare da yiwa Masarautar kishiyoyi har guda hudu,
aka mate gurbin Sunusi da Danka Alh. Aminu Ado, tare da tasa keyar tsohon Sarki
zuwa wani Kauye da ke yankin Jahar Nasarawa, ko da yake daga bisani yayi amfani
da alfarmar da yake da ita ya dawo Jihar Legos.
Faruwar haka
ke da wuya, Gidan Tijjaniya da ke Kasar Morocco tayi masa tukuici babba bisa
tausaya wa ba bisa cancanta ba, da mukamin Khalifar Tijjaniyya na Afurka, wai
don dai ya sami natsuwa, domin kasan mutumin da ya sa wa ransa zama Shugaba to
baya samun natsuwa Sai da Shugabanci.
To an dauka
shikenan wannan matsala tazo karshe... Zan ci gaba
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.