TAMBAYA (113)❓
Assalamualaikum Dan Allah malam inada tambaya inaso insani
yanada kyau indinga Shan farjin matana
AMSA❗
Waalaikumussalam, Warahmatullahi, Wabarakatuhu, dan uwa
✍️AMSA A TAQAICE
(Malaman Mazhabobi guda 4 (Imam Malik, Imam Ahmad, Imam
Shafi'i da Imam Abu Hanifa) dukkansu sun tafi akan ya halatta to amman fa
abinda ake tsoron shine kada ka sha najasa wato maziyyi, wanda yana fita ne
silar karamar sha'awa ko kuma a halin takura)
Bismillaahir Rahmaanir Raheem
Shi ka ga maniyyi ba najasa bane amman maziyyi da wadiyyi
dukkansu najasa ne kamar yanda malamai sukai ijma'i akan hakan
Hujjar da malamai suka kafa akan tsotson farjin mace shine
fadin Allah (Subhanahu wata'ala): Matanku gonakin ku ne ku zo musu ta inda kuka
so, in banda inda aka haramta masa, kamar dubura da kuma lokacin da take jinin
haila
An tambayi Imam Abu Hanifa (Rahimahullah) shin mutum zai iya
taba al'aurar matarsa ko da mene ne (kamar amfani da harshe din) ko kuma matar
ta taba al'aurar mijinta ko da mene ne, saboda su motsa sha'awar juna, ko akwai
laifi yin hakan?
Sai ya ce: Babu laifi, saidai ina fatan ma hakan ya zama zai
kara musu lada ne
Haka kuma daga cikin manyan malaman mazhabar Malikiyya, Imam
Ibn al-Arabi al-Maliki (Rh), a cikin tafsirinsa (Ahkamul Qur'an) cikin Suratu
Nur,
(وَقُل
لِّلْمُؤْمِنَاتِ يَغْضُضْنَ مِنْ أَبْصَارِهِنَّ وَيَحْفَظْنَ فُرُوجَهُنَّ
النور
(31) An-Noor
"Kuma ka ce wa mũminai mãta su runtse daga gannansu,
kuma su tsare farjõjinsu..."
Da ya kawo misalan da suke a cikin wannan ayar sai ya kawo
batun cewar shin ya halatta mutum ya taba al'aurar matarsa ko kuma ita ta taba
ko da hannu ko harshe ko wani abu?
Sai ya kawo maganar Imam Malik Ibn Anas a cikin Almudawwana,
ya kawo maganar Ibnul Qasim da ya rawaito cewar, Imam Malik (Rh) yace babu
laifi yin hakan
Al-Imamu Asbag (cikin manya manyan daliban Imam Malik) yace,
ya halatta a gareshi yayi amfani da harshensa akan farjin matarsa ko kuma ita
tayi hakan gareshi
Aka sake tambayarsa, wasu sun ce makaruhi ne ba kyau, sai ya
ce: "Duk wanda yace ba kyau, yace ba kyau ne ta bangaren likitanci amman
indai ta fuskar ilimin addini ne to bakada dalilin da zai sa ka haramta. Don
haka babu laifi kuma ba makaruhi bane"
Kamar yanda na fada da farko ta fannin likitanci ya haramta
la'akari da shan maziyyi najasa ne ballantana kuma ya hadiye. Malamai suka ce
duk harshen da yake karatun Qur'ani bai kamata kuma ya dandana ballantana shan
najasa ba
Wallahu ta'ala a'alam
Amsawa: Shaikh Prof. Mansur Isah Yelwa
Rubutawa
Usman Danliti Mato (Usmannoor_Assalafy)
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.