TAMBAYA (112)❓
Assalamu alaikum Warahmatullah, malam fatan kana lafiya, don Allah malam a taimaka a amsa mini wannan tambayar, nine nayi mafarkin cewa gani ga Al'arshin Allah, kuma Al'arshin ma a cikin dakin mu na gansa, ina tayin kukan cewa gani ga Allah
AMSA❗
Waalaikumussalam, Warahmatullahi, Wabarakatuhu
✍️AMSA A TAQAICE
(Fassarar mafarkin ganin Al-Arshi na nufin alaqar bawa da
Ubangiji, bushara ne ga mai kyakkyawan hali sannan kuma gargadi ne ga mai sabon
Allah)
Bismillaahir Rahmaanir Raheem
Indai a yanda kayi bayanin nan haka mafarkin yake to mafarki
ne na bushara (alkahiri)
"Ganin Al-Arshin Allah a mafarki a yanda take {kamar
yanda Annabi Sallallahu alaihi wasallam} yayi bayaninta, hakan na nufin
albarka, bushara, da kuma daidaito akan imanin wanda yayi mafarkin"
Ibn Seerin (Littafin Kamus din Fassarar Mafarki)
Ibn Seerin (Rahimahullah) ya ci gaba da cewa: "Idan
mutum yayi mafarkin Al-Arshi amman ba yanda akai bayaninta ba to hakan na nufin
gafala da kuma yawan aikata bidi'a. Ganin Al-Arshi na nufin abinda yake mai
kyau ko kuma mummunar qaddarar da mutum zai riska. Ganin Al-Arshi na iya zama
samun babban matsayi ko kuma aiwatar da wani babban aiki, idan mutum ya
cancanci hakan, ko kuma fassarar na iya zama akan matar mutum, gidan sa, abin
hawarsa, nasara akan maqiyi, rubutun waqe, ko kuma wani aiki nagari da mutum
zai aiwatar a zahiri"
"Idan mutum yayi mafarkin ya ga Allah Azzawajallah akan
Al-ArshinSa hakan na nufin imani, yaqini, kula, da kuma aikata addini bisa
Sunnah. Idan kuma mutum yayi mafarkin shi ne akan Al-Arshin, Ubangiji kuma a
kasan Al-Arshin hakan na nufin, idan har mutum ya tsaya neman takara ko kuma
neman kujerar mulki to idan ya hau mulkin zai gallazawa malaman addinin
musulunci, zai yi girman kai, kuma zai yada fasadi a ban kasa"
"Idan kuma mutum bai cancanci mulki ba, to zai sabawa
iyayensa, zai yi rigima da malamansa, zai juyawa manyansa baya, kuma zai dinga
bada fatawa ba tare da cikakken ilimi ba, sannan zai musgunawa jama'a, idan
kuma alqali ne shi to bazai dinga adalci a cikin alqalancin sa ba"
SHARHI
Ka fi kowa sanin halin kanka da kanka. Fassarar wannan
mafarkin tana nuni ne akan indai har kai mutumin kirki ne mai biyayya ga
iyayensa, da malamansa biyayya irin ta shari'a to ka dage ka ci gaba da yi musu
biyayya indai ba a kan sabon Allah ba
Amman idan kasan halin ka ba shi da kyau, baka biyayya ga
iyaye da malamai sannan kuma baka da kyakkyawar mu'amala da al'umma to ya zama
dole ka gyara halin ka. Idan kai dan siyasa ne to dole kayi adalci ga wadanda
kake mulka. Ban san ka ba, haka kuma ban san komai akan halayenka ba to amman
irin wannan mafarkin yana tattare da saqo na musamman ne - ko dai na bushara
akan kyawawan halin ka ko kuma na gargadi akan munana
Sannan kuma a wata fassarar ta daban, da Ibn Seerin
(Rahimahullah) yayi dangane da mafarkin Hamalatul Arsh (Mala'ikun da suke dauke
da Al-Arshin Allah Azzawajallah) ya ce: "Ganin mala'ikun da suke dauke da
Al-Arshi na nufin; daukaka, jajircewa, iko, hadin kai, soyayya, yarjejeniya, da
kuma tarayya da mutanen kirki. Ganin Hamalatul Arsh a mafarki yana tabbatar da
imanin wanda yayi mafarkin, yardarsa da kuma kusancinsa da ma'abota
sarauta"
Don haka sai ka zauna ka nutsu ka duba alaqar ka da Allah,
ka dabbaqa Sunnah ka guji aikata Bidi'ah sannan ka godewa Allah silar mafarkin
nan da kayi sannan ka yawaita tsayuwar dare ko da raka'a 2 ne ka bi ta da wutri
kafin ka kwanta bacci
Amsawa
Usman Danliti Mato (Usmannoor_Assalafy)
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.