𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Shin wasu alamomi ne ke nuna cewa mamaci ya cika da imani kuma shin akwai waɗanda za su shiga aljanna Ranar alqiyama ba tare da an yi musu hisabi ba?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Daga cikin alamomin akwai:
1. CIKAWA DA KALMAR SHAHADA: saboda faɗin Annabi Sallallahu alaihi
Wasallam "Duk Wanda maganarsa ta karshe ta zama La'ilaha illallahu zai
Shiga aljanna".
2. MUTUM YA MUTU YANA AIKIN ALHERI: kamar sallah ko Hajji,
saboda faɗin Annabi
Sallallahu alaihi Wasallam "Ana tashin bawa akan abin da ya mutu yana
yi".
3. IDAN MUTUM YA RASU DAREN JUMA'A KO YININTA: saboda faɗin Annabi Sallallahu alaihi
Wasallam "Duk Wanda ya rasu Daren juma'a ko yininta Allah zai kare shi
daga azabar Kabari"
4. IDAN MUTUM YA RASU DA GUMI A GOSHISA: kamar yadda ya
tabbata a hadisin Tirmizi.
5. Idan mutum ya yi shahada kamar mace ta mutu wajan haihuwa
ko ciwon ciki ko nutsewa a ruwa ko ya mutu a ciwon Kwalara ko kare kansa ko
dukiyarsa da sauransu.
Idan aka koma can cikin littafin Ahkamul Jana'iz Sheikh
Albani yakawo alamomin a farko farkon littafin. Amma wannan ana kyautatawa
mutum zatone ba'a yanke hukunci kai tsaye ace mutum ɗan aljanna ne ko ace kai tsaye ya cika da
imani.
Manzon ALLAH (Sallallahu alaihi Wasallam) Ya ce: "Lalle
za a samu masu shiga Aljanna a cikin al'umma ta mutum dubu Saba'in, babu Hisabi
ko Azaba agare su, tare da kowani dubu ɗaya
akwai mutum dubu saba'in da zasu shiga Aljanna.” [Saheeh Al-jami: 5366]
Abin da hadisin yake nufi: mutum Biliyan Huɗu da miliyan ɗari Tara (4.9B ko
4,900,000,000) Za su Shiga Aljanna Babu Komai Salin Alin.
Waɗanda
suke shiga aljanna babu hisabi sune waɗanda
Annabi Sallallahu alaihi Wasallam ya faɗesu
acikin hadisi Ukasha binu Mihsan wato waɗanda
suke basa camfi basa neman magani da sauransu.
ALLAH Yasa mu dace, Yasa muna daga cikin Al'ummar Annabi
(Sallallahu alaihi Wasallam) waɗanda
zasu shiga Aljanna ba tare da Hisabi ba (Aameen)
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.