Wane ne Zulkarnaini?

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Assalamu Alaikum malam. Wanene Zulkarnaini, shin Annabin Allah ne ko ko a’a?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Wa'alaikumus Salam Warahmatullahi Wabarkatuhu.

    Zulkarnaini ya kasance Sarki ne adali a bayan kasa, kuma Salihin bawan Allah ne Musulmi, Ya yi mulkin duk duniya kuma yakarade duniya gabas da yamma yana yaɗa Tauhid da Musulunci, yayi raga-raga da kafirci da zalunci a bayan kasa. Kuma sarki zulkarnaini yayi zamani ne tare da Annabi Ibrahim Alaihis Salam. A cikin zance mafi inganci.

    Malaman tarihi sun ruwaito ra’ayoyi mabambanta akan Zulkarnaini, An ce sarki ne na Daular farisa, an ce Annabi ne, wasu ma sun ce mala’ika ne shi zulkarnainin. An ce yayi rayuwa ne a kasar Himyar zamanin Annabi Musa ko Zamanin Annabi Ibrahim. Sannan an ce katangar da ya gina tana kasar Sin ne wasu suka ce tana cikin Taikun Atalantic wasu kuma sun ce ba’a san inda take ba. An samu saɓani mai yawa a cikin tarihin wannan bawan Allah.

    Allah Ta’ala ya ambaci Kissar zilkarnaini a al-Kur’ani Mai Girma cikin suratul Kahfi aya ta 83 zuwa 98

    وَيَسْأَلُونَكَ عَن ذِي الْقَرْنَيْنِ قُلْ سَأَتْلُو عَلَيْكُم مِّنْهُ ذِكْرًا ۝ إِنَّا مَكَّنَّا لَهُ فِي الْأَرْضِ وَآتَيْنَاهُ مِن كُلِّ شَيْءٍ سَبَبًا ۝ فَأَتْبَعَ سَبَبًا ۝ حَتَّىٰ إِذَا بَلَغَ مَغْرِبَ الشَّمْسِ وَجَدَهَا تَغْرُبُ فِي عَيْنٍ حَمِئَةٍ وَوَجَدَ عِندَهَا قَوْمًا قُلْنَا يَا ذَا الْقَرْنَيْنِ إِمَّا أَن تُعَذِّبَ وَإِمَّا أَن تَتَّخِذَ فِيهِمْ حُسْنًا ۝ قَالَ أَمَّا مَن ظَلَمَ فَسَوْفَ نُعَذِّبُهُ ثُمَّ يُرَدُّ إِلَىٰ رَبِّهِ فَيُعَذِّبُهُ عَذَابًا نُّكْرًا ۝ وَأَمَّا مَنْ آمَنَ وَعَمِلَ صَالِحًا فَلَهُ جَزَاءً الْحُسْنَىٰ وَسَنَقُولُ لَهُ مِنْ أَمْرِنَا يُسْرًا ۝ ثُمَّ أَتْبَعَ سَبَبًا ۝ حَتَّىٰ إِذَا بَلَغَ مَطْلِعَ الشَّمْسِ وَجَدَهَا تَطْلُعُ عَلَىٰ قَوْمٍ لَّمْ نَجْعَل لَّهُم مِّن دُونِهَا سِتْرًا ۝ كَذَٰلِكَ وَقَدْ أَحَطْنَا بِمَا لَدَيْهِ خُبْرًا ۝ ثُمَّ أَتْبَعَ سَبَبًا ۝ حَتَّىٰ إِذَا بَلَغَ بَيْنَ السَّدَّيْنِ وَجَدَ مِن دُونِهِمَا قَوْمًا لَّا يَكَادُونَ يَفْقَهُونَ قَوْلًا ۝ قَالُوا يَا ذَا الْقَرْنَيْنِ إِنَّ يَأْجُوجَ وَمَأْجُوجَ مُفْسِدُونَ فِي الْأَرْضِ فَهَلْ نَجْعَلُ لَكَ خَرْجًا عَلَىٰ أَن تَجْعَلَ بَيْنَنَا وَبَيْنَهُمْ سَدًّا ۝ قَالَ مَا مَكَّنِّي فِيهِ رَبِّي خَيْرٌ فَأَعِينُونِي بِقُوَّةٍ أَجْعَلْ بَيْنَكُمْ وَبَيْنَهُمْ رَدْمًا ۝ آتُونِي زُبَرَ الْحَدِيدِ حَتَّىٰ إِذَا سَاوَىٰ بَيْنَ الصَّدَفَيْنِ قَالَ انفُخُوا حَتَّىٰ إِذَا جَعَلَهُ نَارًا قَالَ آتُونِي أُفْرِغْ عَلَيْهِ قِطْرًا ۝ فَمَا اسْطَاعُوا أَن يَظْهَرُوهُ وَمَا اسْتَطَاعُوا لَهُ نَقْبًا ۝ قَالَ هَٰذَا رَحْمَةٌ مِّن رَّبِّي فَإِذَا جَاءَ وَعْدُ رَبِّي جَعَلَهُ دَكَّاءَ وَكَانَ وَعْدُ رَبِّي حَقًّا ۝

    Kuma suna tambayar ka daga zulƙarnaini, ka ce: ''Zan karanta muku ambato daga gare shi.'' ۝ Lalle ne Mũ, Mun bã shi mulki a cikin ƙasa kuma Muka bã shi daga kõwane abu, hanya (zuwa ga murãdinsa). ۝ Sai ya bi hanya. ۝ Har a lõkacin da ya isa ga mafãɗar rãnã, kuma ya sãme ta tanã ɓacwa a cikin wani ruwa mai baƙar lãkã, kuma ya sãmi waɗansu mutãne a wurinta. Muka ce: ''Yã Zulƙarnaini imma dai ka azabtar kuma imma ka riƙi kyautatãwa a cikinsu.'' ۝ Ya ce: ''Amma wanda ya yi zãlunci, to zã mu azabta shi, sa'an nan a mayar da shi zuwa ga Ubangijinsa, sai kuma Ya yi masa azãba, azãba abar ƙyãma.'' ۝ ''Kuma amma wanda ya yi ĩmãni kuma ya aikata aikin ƙwarai to, zã mu yi sakamako a gare shi (watau kyauta) mai kyau, kuma zã mu gaya masa sauƙi daga umurninmu.'' ۝ Sa'an nan kuma ya bi hanya. ۝ Har a lõkacin da ya isa ga mafitar rãnã, ya sãme ta tanã fita a kan waɗansu mutãne (waɗanda) ba Mu sanya musu wata kãriya ba daga barinta. ۝ Kamar wancan alhãli kuwa haƙĩƙa, Mun kwaye da jarrabãwa ga abin da ke gunsa. ۝ Sa'an nan kuma ya bi hanya. ۝ Har a lõkacin da ya isa a tsakãnin duwãtsu biyu, ya sãmi waɗansu mutãne daga gabãninsu. Ba su yi kusa su fahimci magana ba. ۝ Suka ce: ''Yã Zulƙarnaini! Lalle ne Yãjũja da Majũja mãsu ɓarna ne a cikin ƙasa. To, ko zã mu Sanya harãji sabõda kai, a kan ka sanya wani danni a tsakãninmu da tsakãninsu?'' ۝ Ya ce: ''Abin da Ubangijĩna Ya mallaka mini, a cikinsa yã fi zama alhri. Sai ku taimakeni da ƙarfi, in sanya babbar katanga a tsakãninku da tsakãninsu.'' ۝ ''Ku kãwo mini guntãyen baƙin ƙarfe''. (Suka kai masa) har a lõkacin da ya daidaita a tsakãnin duwãtsun biyu (ya sanya wutã a cikin ƙarfen) ya ce: ''Ku hũra (da zugãzugai).'' Har a lõkacin da ya mayar da shi wutã, ya ce: ''Ku kãwo mini gaci (narkakke) in zuba a kansa.'' ۝ Dõmin haka bã za su iya hawansa ba, kuma bã zã su iya hujwa gare shi ba. ۝ Ya ce: ''Wannan wata rahama ce daga Ubangijĩna. Sai idan wa'adin Ubangijĩna ya zo, ya mayar da shi niƙaƙƙe. Kuma wa'adin Ubangijĩna ya kasance tabbatacce.'' ۝ (suratul Kahfi aya ta 83 - 98).

    Allah ya yabe shi da adalci, da girman mulkin da yahade gabas da yamma. Kuma shi ne ya gina katangar da ta tsare Yajuju da Majuju daga ɓarna a cikin duniya.

    Kissar Zulkarnaini tana daga cikin tambayoyi Uku da Yahudawa suka sa Mushirikan Larabawa suyiwa Ammabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallam tambaya a kai. Lalle kissa ce da ke cike da labarai mabambanta. Kissar na cikin littafan Yahudu da Nasara. Saidai a matsayin mu na musulumai, za mu iya karanta duk labaran kuma mu saitasu da abinda al-Kur’ani ya kissanta mana.

    Lalle a kwai abin al’ajabi da lura da kuma darussa da dama da zamu fa’idantu da su a Najeriyar mu a yau, a cikin tarihin Zulkarnaini

    1. Mulki, mukami, shugabanci, daraja da ɗaukaka duk na Allah ne, kuma yana badawa ga wanda ya so, a lokacin da ya so kuma yadda ya so.

    2. Duk mai wata ɗaukaka na shugabanci, toh kada yayi girman kai, da nuna Izzah da isa, ko yayi tunanin yafi kowa.

    3. Aldalci shi ne ginshikin kasaitaccen mulki wanda duniya za tayi alfahari da shi ko bayan tafiyar mai mulkin.

    4. Mulki da shugabanci ana amfani da shi ne don inganta rayuwar al’umma ba don tara abin duniya ba.

    Allah shi ne mafi sani.

    Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.