Ticker

6/recent/ticker-posts

Su Waye Ashabul Kahfi?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Shin su waye ashabul Kahfi, sannan a wani zamani akayi su?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Alkur’ani Mai Girma ya labarto mana tarihin magabata irin su ashabul Kahfi ba don mutanen ba ne, saidai don mu fa’idantu da halin da suka shiga sannan kuma suka tsare imaninsu.

Wannan Qissa ta Ashabul Kahfi Kur’ani ya hakaito ta ne a lokacin da Mushirikan Quraishawa su ke son Jaraba Annabi Sallallahu alaihi Wasallam, sai suka tambayi Yahudawa cewa wacce irin jarabawa za su yima Annabi Sallallahu alaihi Wasallam. Akan hakane Yahudawa suka fadamu cewa su tambaye shi akan wasu mutane da suka shiga cikin kogo, da wani mutumin da ya zagaye duniya, da Ruhi (RAI).

Suratul Kahfi tana ɗauke da bayanin Ashabul Kahfi, wato wasu matasa su bakwai (7) tare da karensu, da suka rayu a zamanin mulkin wani azzalumin sarki Daqayanusa bayan Annabi Isa (AS) ko kafin zuwansa da sheraka 250. A zamanin ana bautan gumakane karkashin wannan sarki, a garin Amman da ke kasar Jordan a yau.

Sai matasan su 7 suka kyamaci bautan wannin Allah, kuma suka yi imani da Allah sannan suka yi hijira don tsoron tsananin azabar da sarkin zai yi musu idan yakamasu.

Matasan sun gudune don su tsira da Imaninsu, kuma suka shiga wani kogon dutse. Bayan shigarsu sai Allah yasa musu barci tsawon shekaru 300 ko 309 a kirgar watan sama. Sannan Allah ya tashe su daga barcin cikin hikimar sa.

Alkur’ani mai Girma ya ambata wannan kissa kuma a da sauran littafan kiristanci da na tarihi. Amma akwai saɓani da yawa a cikin tarihin waɗannan bayin Allah, Kamar haka

1. Adadin su.

2. Kasar da kogon da suka ɓoye.

3. Shin kafin zuwan Annabi Isa ne ko bayan zuwan sa ne.

4. Sunayen su, da sauran wasu bayanai da yawa.

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments