Ticker

6/recent/ticker-posts

Haduwata Da Maciji!

Haɗuwata Da Maciji!

A jiya Alhamis, bayan na dawo daga Aliero kusan ƙarfe ɗaya na rana, na buɗe boot ɗin mashin in ɗauko wani abu, a rashin zato kawai sai na ga bindin maciji cikin mashin ya yi ƙasa ya shige cikin kwabar mashin, cikin kaɗuwa da mamaki na yi tsaye ina mamaki sororo, ta yaya aka yi haka wai namiji da suna Hajara, ban kammala mamaki ba har maciji ya ɓata ɓat a cikin lungu da saƙunan mashin, na samu sanda na yi ta takarar kwabobin mashin ko macijin zai fito in samu salama, kusan minti goma ina abu guda, har na ji an yi kiran sallar Azahar, na kira iyalina na ce ta tsaya da sanda ta yi dako ko macijin zai fito, zan je in yi alwala, bayan na kammala, na kama hanyar masallaci sai na haɗu da wani ɗan matashi maƙocina, na tambaya shi ko ya san yadda za a yi a fitar da maciji a cikin mashin? Sai ya ce maciji fa! Ƙwarai kuwa na tabbatar masa. Ya ce mu je in gani, ya zo ya kwance kwabobin mashin ya dudduba ko'ina babu shi babu alamu. Ya ce gaskiya bai ciki, wataƙila ya fito ban lura ba, na ce masa tabbas yana ciki! 

Ya matsa min a kan in buga mashin ɗina in tafi harkokin gabana, na ce ina! Ai tun da Allah ya tsare ni tun daga garin Aliero har zuwa Jega bai yi min komi ba, yanzu kam ba zan yi gangancin hawa ba, bayan na gan shi ra'ayul-aini. Ya ce to in ba shi makullin shi zai hau ya gani ko zai fito idan ya ji zafin mashin, na ce yanzu duk zafin da ya jiyo tun daga Aliero har Jega bai fito ba, wane zafi ne kuma zai fito da shi yanzu, amma tun da ka ce kana iya haɗe gatari to na sakar maka ɓota! Ya hau mashin ya tafi, ni kuma na kama hanyar masallaci ina ta salati, ina ta addu'ar Allah ya raba A'i da rogo ko dai ta faɗi ko ta ci riba, ko ta fitar da ƴan kuɗɗinta. Bayan na yi salla na yi azkar na kamo hanyar zuwa gida ina tafe ina addu'ar Allah ya raba ni da mugun ɗan ga. 

Na riga da na haƙiƙance cewa yau kam da ni da hawan wannan mashin sai na ga abin da ya ture naɗin buzu, bayan na dawo gida ina zaune ina addu'a irin ta Annabi Yunus wadda ya yi a lokacin da kifi ya haɗe shi, (لا لله ألا أنت سبحانك اني كنت من الظالمين) sai na ji ƙarar mashin a ƙofar garka, sai na yi zunbur na yo ƙofar gida, ina zuwa sai na ce mene ne labari? Shin ya fito? Sai ya ce ai ga shi sun gano shi, ashe a lokacin da ya shige cikin kwabar mashin, ya sulale ne har ya kai cikin kan mashin, suna banye/kwance kan mashin sai ga kahiri ciki, cikin zahin nama sai wani ya yi caraf da kan macijin ya riƙe. Sai na tuna da wani abokina mutumin Bunguɗu ta Zamfara, ya taɓa faɗamin dabarun kama maciji, amma sai na ga gangancin ya yi yawa, na ce ina, ba da ɗan Musa ba, wai gaɗa a maƙabarta! 

In gajarce maka labari haka suka yi dabara suka saka macijin cikin leda suka kawo min shi a raye.

Allahu Akbar, Alhamdu lillah, yau dai yau Allah wanda dama shi ke tsare ni tun ina cikin tsumman goyo, ya koma tsare ni daga sharrin halittar da nake matuƙar tsoro.

Shawarwari

1. Lallai mu riƙe azkar na safiya da yamma da zama da tashi da na bayan salla da na hawan abin hawa.

2. Lallai mu san inda za mu aje ababen hawa, musamman idan muka je wajen da za mu jima ba mu tashi ba.

3. Mu yi ƙoƙarin mayar da al'amari ga Allah a duk lokacin da muka shiga cikin wani tashin hankali.

4. Mu zama a faɗake a duk lokacin da za mu hau wani abin hawa. Sai na tuna da hadisin Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wasallama da ce a duk lokacin da mutum zai kwanta ya tabbatar da ya yi amfani da wani ƙyalle ya kakkaɓe wajen kwanciya, saboda bai san abin da ya maye masa ba, bayan ya tashi.

Abbas Musa Jega 
09111445H
17052024M.

Maciji

Post a Comment

0 Comments