TAMBAYA (104)❓
Aslm. Wllh wataqawatace sukayi aure da saurayinta ammah kafin auran sundanyi rashinji dan hartasami Ciki kafin aure. Kuma batafadawa iyayentaba tanada Ciki wata Daya akadauramata auren ahaka gashi har sunhaihu bayan wanna Dan da sukahaifa sunkara Yara Biyu
Shine take wasiwasi akan auran yanzu wai ya matsayin
auranta. Ahuta lafiya
AMSA❗
Lahaula wala quwwata illa billah
Laifin aikata zina yana daga cikin manyan alkaba'ira
(zunubbai) domin kuwa idan ka dauke laifin Shirka, Kisa, da cin Riba to sai
laifin Zina
Saboda girman laifin ne ma Allah (Subhanahu wata'ala) a
cikin Suratul Israa, yace kada mu kusanci zina;
( وَلَا
تَقْرَبُوا الزِّنَا ۖ إِنَّهُ كَانَ فَاحِشَةً وَسَاءَ سَبِيلًا
)
الإسراء
(32) Al-Israa
"Kuma kada ku kusanci zina. Lalle ne ita ta kasance
alfãsha ce kuma tã mũnãna ga zama hanya."
Ba ma aikata zinar ba, kusantar ta ma laifi ne babba
Sannan kuma Annabi (Sallallahu alaihi wasallam) ya ce:
"Da danyaku ya taba macen da ba muharramar sa ba, gara a saka kusa a kansa
a buga da guduma shine yafi masa sauqi"
(Sahihul Bukhari)
Haka kuma lokacin da Annabi (Sallallahu alaihi wasallam)
yayi mafarkin an nuna masa wasu mata da aka rataye mamansu da qugiya, an rura
wuta tana ci ta kasansu, kamar suna cikin gidan biredi ana gasasu, sunata
kwarmata ihu saboda azaba ya tambayi mala'iku mene ne laifin wadannan suka ce
masa wadannan mazinata ne
(Sahihul Bukhari)
Dangane da hukuncin auren su, ba wanda zai ce auren su bai
yi ba tunda kowanne aiki da niyya ake yin sa kuma Annabi (Sallallahu alaihi
wasallam) ya ce: "Innamal a'amalu binniyati" ma'ana: "Kowanne
aiki yana tare da niyya"
(Bukhari da Muslim, Musnad na Imam Ahmad, Abu Dawud)
Kafin suyi aure sunyi niyyar aikata zina kuma har ciki ya
shiga
Sannan kuma lokaci guda sai sukai niyyar aure shima wannan
niyyar daban take
Rashin sanar da iyayen nata cewar tana dauke da juna biyu
shine maslaha ga rayuwarta, rayuwar mijinta da iyayenta da kuma rayuwar shi
kansa abinda ke cikinnata
Domin kuwa Allah ya rufa musu asiri, sunyi laifi a boye, to
don me kuma zata yi kokarin fadawa iyayenta ga abinda sukai?
Allah Gafurur rahim ne, yana gafarta kowanne zunubi amman
banda shirka shima idan ka mutu kana yi ne. Idan Allah yaga dama yana yafe
kowanne zunubi ko kuma ya yiwa bawanSa azaba gwargwadon girman zunubinsa kamar
yanda ya fada a cikin Qur'ani:
( أَلَمْ
تَعْلَمْ أَنَّ اللَّهَ لَهُ مُلْكُ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ يُعَذِّبُ مَن يَشَاءُ
وَيَغْفِرُ لِمَن يَشَاءُ ۗ وَاللَّهُ عَلَىٰ كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ
)
المائدة
(40) Al-Maaida
Shin, ba ka sani ba cewa lalle ne, Allah Shi ne da mulkin
sammai da ƙasa,
Yanã azãbtar da wanda Yake so, kuma
Yanã yin gãfara ga wanda yake so, kuma
Allah a dukkan kõme,
Mai ĩkon yi ne?"
Don haka daga ita har mijin nata sai suyi ta tuba (Taubatun
Nasuha) akan zaluntar kansu da sukayi kamar yanda Allah ya ce:
( فَمَن
تَابَ مِن بَعْدِ ظُلْمِهِ وَأَصْلَحَ فَإِنَّ اللَّهَ يَتُوبُ عَلَيْهِ ۗ إِنَّ اللَّهَ
غَفُورٌ رَّحِيمٌ )
المائدة
(39) Al-Maaida
"To, wanda ya tuba a bãyan zãluncinsa, kuma ya gyãra
(halinsa), to, lalle ne Allah Yanã karɓar
tubarsa. Lalle Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai"
Don haka auren su yananan daram, kawai su rufawa kansu asiri
su ci gaba da raya sunnar Annabi (Sallallahu alaihi wasallam), ita kuma ta
dinga yi masa biyayya musamman ma idan ya neme ta domin kuwa duk sanda suka
raya sunnah to akwai lada mai yawa da Allah yake bayarwa ga mata da miji daga
lada 10 zuwa 100 har zuwa 700 wasu kuma ya ninninka musu ba iyaka kamar dai
yanda idan kuma mazina ci ya aikata zina zai samu zunubin wannan mummunan aikin
Kamar yanda Manzon ALLAH (ﷺ)
Ya ce: “Mala'ikan da yake hagu (wanda yake rubuta zunubi) Yana ɗaga alƙalaminsa
har tsawon awanni shida bayan musulmi yayi laifi yana jiran ko zai yi
da-na-sani ya roƙi gafarar ALLAH, idan ya tuba kafin haka sai Mala'ikan ya fasa
rubuta shi, idan bai tuba ba, bayan wannan lokaci sai ya rubuta masa zunubi ɗaya.”
[Saheehul Jamii: 2097]
Haka kuma Annabi (Sallallahu alaihi wasallam) ya ce:
"Kullu bani adam khadda'un, wa khairu khadda'un attawwabun" ma'ana:
"Dukkan bani adam masu laifi ne saidai wadanda suka fi alkhairi cikinsu
sune masu yawan tuba"
(Bukhari da Muslim)
Ya Allah ka tsaremu daga aikin da na sani ka yafe mana
zunubbanmu na zahiri da na badini sannan ka bamu iyali nagari
Wallahu ta'ala a'alam
Amsawa:
Usman Danliti Mato (Usmannoor_Assalafy)
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.