TAMBAYA (103)❓
Dan Allah malam wai idan yaro yayi azumi bashi ake bawa ladan ba. yaro karami wanda baifi shekara taraba goma haka. Wasune suke musu wai bashi ake bawa ladan ba
AMSA❗
Alhamdulillah
An tambayi Shaikh Saleh al-Munajjid dangane da hukuncin
ayyukan yaron da bai kai matsayin balaga ba. Ya ce:
Na'am, yara za'a basu lada idan sukai aikin alkhairi, saboda
hadisin da Imam Muslim ya rawaito a cikin Sahih dinsa (1335) daga Ibn Abbaas
(Radiyallahu anhum), ya ce: "Wata mata ta daga yaronta tace: "Ya
Rasulullah, shin Allah zai karbi hajjin yaron nan?" Sai Annabi (Sallallahu
alaihi wasallam) ya ce: "Na'am, kuma zaki samu ladan hakan"
Mawallafin littafin Mawaahib al-Jaleel fi Sharh Mukhtasar
Shaykh al-Khalrrl yace akan umarnin da aka bawa yara suyi addu'a idan sun
balaga: "Al-Qaraafi yace, a cikin al-Yawaaqeet fi'l-Mawaaqeet: "Yara
zasu samu lada idan suka aikata aiki nagari saboda wancan hadisin na macen
Khath'ami {da ta daga yaron ta ta tambayi Annabi (Sallallahu alaihi wasallam)
yayin aikin Hajji}
Ibn Rushd ya ce: "Munanan ayyukan yara ba'a rubuta su
amman kyawawan ayyuka ana rubuta wadannan, a bayani mafi inganci"
Ibn Abd al-Baar yace, a cikin littafin al-Tamheed, inda yayi
sharhin hadisin macen Khath'ami: "...Abu'l-'Aaliyah al-Riyaahi ya ce:
"Umar ibn al-Khattab ya ce: "ana rubuta kyakkyawan aikin yaron da bai
balaga ba amman ba'a rubuta mummunan aikinsa"
Mawallafin Mawaahin al-Jaleel yace, dangane da shiga Ihraam
na yara a Umrah da Hajji:
"Malamai basu samu sabani ba dangane da hukuncin yara
za'a basu ladan aiki kyakkyawa (wanda suka yiwa Allah), sannan kuma ana lissafa
ayyukansu marasa kyau a matsayin kuskure"
Haka kuma a cikin Mukhtasar al-Waadihah: "Hajj ba
wajibi bane akan yaro ba, har sai ya balaga, yarinya kuma har sai ta fara
al'ada amman ba matsala bane idan an tafi dasu aikin Hajji. Sannan kuma
mustahabbi ne kuma Annabi (Sallallahu alaihi wasallam) yayi hakan"
Sannan kuma ya rawaito cewar Talhah ibn Musarrif ya ce:
"Yana daya daga cikin al'adun musulmi su tafi aikin Hajji tare da yayansu
don neman rahamar Allah"
Ibn Abd al-Barr, a cikin al-Tamheed, ya ce: "Anso aje
aikin Hajji tare da yara kuma ijma'in malamai sun fadi hakan". Haka kuma ya
ce: "Ba abin mamaki bane, a ranar lahira, a ga yaro ya samu ladan sallah,
zakkah, Hajji da sauran kyawawan ayyuka idan har yayisu kamar yanda shari'ah ta
koyar saboda hakan (samun ladan) rahamar Allah ce kamar yanda Allah (Subhanahu
wata'ala) yake bada lada ga mamaci idan anyi sadaka a madadinsu. Ba ku ganin
cewar, malamai sun yarda akan a umarci yaro yayi sallah idan yakai shekarun
wayo, kamar yanda Annabi (Sallallahu alaihi wasallam) ya yi sallah tare da Anas
(Radiyallahu anhu) da maraya?
Yawancin Salaf (magabatan farko) sunce a biya Zakkar marayu,
sannan kuma bazai yiwu ace baza'a ladan wannan Zakkah ba. Manyan su, da kuma
wadanda suka bayar da Zakkar a madadinsu su ma zasu samu lada silar hakan,
kamar yanda wanda ya kaisu aikin Hajji zai samu lada, saboda girman rahamar
Ubangiji (Subhanahu wata'ala). An karbo daga Umar (Radiyallahu anhu) ya ce:
"Za'a bawa yara ladan kyakkyawan aiki, amman banda mummuna". Banga
wani wanda aka fifita ra'ayinsa sabanin wannan ba
al-Ikmaal ya ce: "Malamai dayawa sunce, yara zasu samu
lada idan suki bi umarnin Allah Azzawajallah, zasu samun ladan kyawawan
ayyukansu amman banda zunubbansu"
An rawaito a cikin Awaa'il al-Muqaddimaat, cewar:
"Abinda ya inganta a fahimta ta shine: an karfafe su (yaron da wakilinsa)
su aiwatar da hakan saboda dukkansu zasu samu lada. Annabi (Sallallahu alaihi
wasallam) yacewa wannan macen (da tayi tambaya akan Hajjin dan ta):
"...kuma zaki samu ladan hakan". Wallahu ta'ala a'alam
Ibn Jamaa'ah ya ce: "Malaman mazhabobi hudu sunce, yara
zasu samu ladan aiki nagari, ko sun balaga ko basu balaga ba. An karbo hakan
daga Umar (Radiyallahu anhu). Wasu malaman sunce akwai ijmaa'in malamai akan
wannan hukuncin. Idan muka tattara wadannan hujjoji waje guda zamu ga cewar
fadaa'il (falala) ne hakan kamar yanda Annabi (Sallallahu alaihi wasallam) ya
ce: "Jihadin tsoho da jihadin yaro shine Hajji da Umrah da kuma hujjar da
take a cikin wancan hadisi na matar da ta daga dan ta
Wallahu ta'ala a'alam
Amsawa:
Usman Danliti Mato (Usmannoor_Assalafy)
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayaDaAnsa
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.