Ticker

6/recent/ticker-posts

Mafarkin Siradi Da Taurari Da Sabon Wata Da Girgije

TAMBAYA (105)

Assalamu alaikum waraha matullah Malam barka da war haka

Malam wata baiwar Allah ce take wayansu kalan mafarkai daban daban kamar haka

1) tajera kwana uku tana mafarkin taurari marasa adadi masu haske asararin sama

2) shikuma wannan so daya tayi girgirje tagani suna saukowa gabanta sannan sukoma sama

3) shima wannan sodaya tayi Annunamata wani guri amafarkin akace mata siradine siriri kamar silinn gashie gefensa hagu da dama ramine mara karshe Allah ya bata iko tawuce bayan ta haure gurin shine taganta awani lambu me matukar kyau acinsa akwai Yara Yan kananu suna rike da kwarya a hanna yensu kowa wanne akwai rijiya agabansa Yana bata ruwan me matukar dadi sosai tana sha awannan halin ta farka

4) tayi mafarki wata sabon kamawa asama

mafarkin na 1 2 4 tayisune dab da watan Ramadan na 3 shikuma tayishi lokaci meyawa daya wuce

AMSA

Alhamdulillah

Kusan dukkansu guda 4 din suna cikin mafarkin "ar-Ru'ya" wato mafarkan bushara daga Allah Azzawajallah

Malami kuma Tabi'i masanin ilimin fassarar mafarki, Imam Muhammad Ibn Seerin (Rahimahullah), dalibin Imam Malik (Rahimahullah) ya ce:

"Siradi wata gada ce wadda kowanne mutum zai bi ta kai don domin haduwa da Ubangijin sa a ranar alqiyama. Saukin tsallake wannan gadar yana da alaqa da nauyin ayyukan mutum. Wasu zasu tsallake gadar tamkar walqiya yayin da wasu kuma zasu yi dakon ayyukansu su dinga tafiya gwargwadon ayyukan nasu"

"Tafiya akan siradi na nufin wata doguwar tafiya da mutum zai yi. Idan gadar ta tsage ta kasan kafar mutum to hakan na nufin asara da kuma mutuwa. Ganin Siradi na nufin ilimi, gaskiya, yarda da dayantakar Allah da kuma bin koyarwa da sunnar Annabi Muhammad (Sallallahu alaihi wasallam)"

"Idan kayi mafarkin kafar ka ta zame a siradi hakan na nufin zaka karkata hanyar bidi'a. Idan ka ga kana tafiya a daidai kuma hakan na nufin kana kan sunnar Ma'aiki, kana bin abinda aka umarce ka kana nesantar abinda aka haramta. Haka kuma mafarkin Siradi na nufin mutum zai ga canji a rayuwarsa, hidindimu da dawainiya zata hau kansa duk da cewar zai yi nasarar sauke nauyin da za'a rataya masa. Idan kafar mutum ta zame hakan na iya zama silar aikata zunubbai da kaucewa tafarki madaidaici"

(Ibn Seerin: fassarar mafarkin Siradi)

Na 2)

"Kallon taurari a mafarki na nufin mutum zai mulki al'umma"

(Ibn Seerin (Rh) a cikin littafinsa mai suna Kamus din fassarar mafarki)

"Idan mutum yayi mafarkin taurari masu matuqar haske hakan na nufin zai samu alkhairi a tafiyar kwadagonsa ko kuma yana nufin zai dawo gida lafiya daga wannan tafiya"

"A cikin mafarki, tauraro na nufin mutumin kirki. Ganin taurari suna haskakawa kuma sun tattaru waje guda a gidan mutum na nufin mutanen kirki, ko kuma shugabannin wannan kasar zasu hadu a wannan gidan"

"A takaice, mafarkin taurari na nufin shugabannin siyasa, manyan malamai, mutum nagari a cikin al'umma da kuma shahararren attijiri. Ganin taurari dayawa a gidan mutum na nufin zai samu iyali da yawa. Ganin taurari "yan bakwai" (ana kiransu da Plaedias) na nufin kasuwanci, ciniki, ilimi da kuma shugabanci a kasa"

"Idan kayi mafarki kana cin tauraro kamar abinci, hakan na nufin damfarar kudin mutane. Hadiye tauraro a mafarki na nufin haduwa da mutane nagari da kuma sanar dasu sirrinka ko kuma hakan na nufin zagin sahabban Annabi (Sallallahu alaihi wasallam), Allah ya kara yarda a garesu. Tsotsar tauraro na nufin karatu a hannun babban malamin addini ko kuma wani mai hikima"

"Ganin taurari sun fado daga sama yana nufin zaka zamo mara gashi ko kuma zaka iya rasa gashin ka gaba daya saboda anan taurarin suna nufin gashi sama kuma tana nufin kan mutum"

(Ibn Seerin: fassarar mafarkin tauraro)

Na 3)

"Ganin sabon wata a mafarki, kuma a daren da ake neman watan, na nufin: matar mutum zata haifa masa namiji ko mace. Mafarkin jinjirin wata na nufin: gaskiyar alqawarin mutum, ko kuma karbar kudi, la'akari da yawanci ana biyan bashin gidan haya ne a farkon kowanne wata. Bayyanar jinjirin wata a yankin kudu ko arewa a maimakon gabas ko yamma, na nufin: aikata ko kuma ganin mummunan aikin da zai zama silar ajalin gaggawa gwargwadon dadewar da wannan watan zaiyi a inda aka gan shi"

"Mafarkin ganin wata na nufin: shugaba, malami, kyakkyawan yaro, azzalumi, ko kuma maqaryaci. Ganin wata ya zauna akan cinyar mutum, a mafarki na nufin mutum zai yi aure"

"Idan mace mai dauke da juna biyu ta ga tana kokarin taba wata da hannunta kuma ta kasa tabawa, hakan na nufin: tana son samun da namiji. Idan kayi mafarkin kana sujjada ga wata ko rana na nufin: zaka aikata mummunan aikin zunubi. Idan kuma ka ga rana da wata suna maka sujjada a mafarki, hakan na nufin: mahaifiyarka da mahaifinka suna alfahari dakai. Idan wata ya tsage gida biyu a mafarki, na nufin: iftila'i zai fadawa wani babban mutum, ko kuma za'a ga wata babbar ayar Allah da zata bayyana a wannan yankin. Idan kayi mafarkin rashin lafiyar wata (luna eclipse) ko ya rasa haske, ko kuma watan ya zama ja jawur, hakan na nufin: babban canji zai faru ga rayuwarka. Ganin watanni dayawa a mafarki na nufin: zaka je aikin hajji. Ganin jan wata na nufin mace zatayi barin cikinta. Idan kuma wata ya fado duniya a mafarki hakan na nufin: haihuwar jariri"

(Ibn Seerin fassarar mafarkin wata)

Na 4)

"Mafarkin girgije na nufin: mu'ujiza, alfarma, hali mai kyau, ruwa, qauna, albarka saboda suna bayyana ne a lokacin da wani Annabi ko bawan Allah ya roqi ruwa ko kuma kange mutumin da yake jin zafin rana. Mafarkin girgije na nufin: tafiya a teku (jirgin ruwa) ko kuma iska (jirgin sama)"

"Mafarkin kana hada giragizai waje guda kuma baka dauki komai daga ciki ba na nufin: zaka hadu da malaman addini amman ba zaka amfana da iliminsu ba. Mafarkin kana tafiya akan girgije na nufin: zaka shahara ka samu daukaka silar ilimi da hikima. Mafarkin jin sautin wani mutum yana kiranka ta cikin girgije na nufin: zaka je aikin hajji. Idan kayi mafarkin girgije na maka maraba, yana tarbarka hakan na nufin: albishir"

(Ibn Seerin fassarar mafarkin Girgije)

SHARHI:

A yanda na fahimta, wannan baiwar Allah mutuniyar kirki ce. Mafarkin da tayi na taurari marasa adadi yanada alaqa da kirki da halayenta nagari kamar yanda Ibn Seerin yayi bayani. Shi kuma jinjirin wata da ta gani yanada alaqa da dayan biyu: idan matar aure ce mai juna biyu to zata haihu lafiya (in sha Allah) idan kuma budurwa ce to tanada riqe alqawari kuma tanada hali nagari

Mafarkin girgijen da tayi yana saukowa kusa da ita sannan ya koma hakan yana nufin ana mata albishir da tsallake siradi lafiya (matuqar ta dawwama akan kyawawan halayenta da aka san ta dasu)

Sannnan dangane da mafarkin da tayi na tsallake siradi wannan yana da alaqa da halayenta. Kamar yanda ta fada tabbas siradi ya kasance sirantarsa tafi ta gashi kaifinsa yafi na takobi kamar yanda Annabi (Sallallahu alaihi wasallam) ya fada

(Sahihul Bukhari)

Kamar yanda ta gani, hagu da damsa rami ne mai tsananin zurfin da idan aka gangara dutse sai yayi shekaru 500 kafin ya fada kasan Jahannama. Kamar yanda Annabi (Sallallahu alaihi wasallam) ya fada a hadisi sannan kuma su kansu sahabbai da kunnensu sun taba jin karar da ta tsorata su, sai Annabi (Sallallahu alaihi wasallam) yace wani dutse ne aka wulla shi wuta bai kai kasan ta ba sai yanzu dinnan, alhalin shekaru 500 da jefashi

(Akwai hadisin a cikin "Albidaya wan Nihaya na Ibn Khathir (Rh)

Wannan lambun da ta gani, Aljannah ce, madaukakiya (Ya Allah ka sakamu cikin Alfirdous), wadannan yaran kuma sune wadanda...Subhanallah...sune wadannan da Allah Azzawajallah ya ambata da suna "Wildanun Mukalladun" a cikin Suratul Waqi'ah ayata 17-18;

( يَطُوفُ عَلَيْهِمْ وِلْدَانٌ مُّخَلَّدُونَ )

الواقعة (17) Al-Waaqia

"Wasu yara samãri na dindindin gwaya a kansu."

Sannan kuma kamar yanda tace yaran suna dauke da qwarya a hannuwansu kowanne akwai rijiya a gabansa yana shayar da ita ruwa mai matuqar dadi, wannan abin shan ai shine wanda Allah (Subhanahu wata'ala) ya ambata a aya ta gaba:

( بِأَكْوَابٍ وَأَبَارِيقَ وَكَأْسٍ مِّن مَّعِينٍ )

الواقعة (18) Al-Waaqia

"Da wasu kõfuna da shantula da hinjãlai daga (giya) mai ɓuɓɓuga"

Da kuma cikin Suratu al-Insaan ayata 15 har zuwa ta 18:

( وَيُطَافُ عَلَيْهِم بِآنِيَةٍ مِّن فِضَّةٍ وَأَكْوَابٍ كَانَتْ قَوَارِيرَا )

الإنسان (15) Al-Insaan

"Kuma ana kwayãwa a kansu da finjãlai na azurfa da kofuna waɗanda suka kasance na ƙarau"

( قَوَارِيرَ مِن فِضَّةٍ قَدَّرُوهَا تَقْدِيرًا )

الإنسان (16) Al-Insaan

"karau na azurfa, sun ƙaddara su ƙaddarawa, daidai bukãta."

( وَيُسْقَوْنَ فِيهَا كَأْسًا كَانَ مِزَاجُهَا زَنجَبِيلًا )

الإنسان (17) Al-Insaan

"Ana shayarwa da su, a cikinta, finjalan giya, wadda abin gaurayarta ya kasance zanjabil ne."

Wannan rijiyar kuma itace marmaron da Allah (Subhanahu wata'ala) ya ambata da suna "Salsabil" inda ya ce:

( عَيْنًا فِيهَا تُسَمَّىٰ سَلْسَبِيلًا )

الإنسان (18) Al-Insaan

"Wani marmaro ne, a cikinta, ana kiran sa salsabil"

Sannan kuma idan ta mutu ba ta sha giyar duniya ba to zata sha ta cikin Aljannah kamar yanda Allah Azzawajallah ya fada a cikin wannan surar dai aya ta 5 zuwa ta 6;

( إِنَّ الْأَبْرَارَ يَشْرَبُونَ مِن كَأْسٍ كَانَ مِزَاجُهَا كَافُورًا )

الإنسان (5) Al-Insaan

"Lalle ne, mutãnen kirki zã su sha daga finjãlin giya abin gaurayarta yã kãsance kãfur ne"

( عَيْنًا يَشْرَبُ بِهَا عِبَادُ اللَّهِ يُفَجِّرُونَهَا تَفْجِيرًا )

الإنسان (6) Al-Insaan

"Wani marmaro ne, daga gare shi bayin Allah suke sha, suna ɓuɓɓugar da shi ɓuɓɓugarwa"

Bayan Allah Azzawajallah ya bawa AnnabinSa wannan labari na gaibu dangane da tanadin da yayi masa a Aljannah sai kuma ya lallashe shi, ya ce:

( فَاصْبِرْ لِحُكْمِ رَبِّكَ وَلَا تُطِعْ مِنْهُمْ آثِمًا أَوْ كَفُورًا )

الإنسان (24) Al-Insaan

"Sabõda haka ka yi haƙuri ga hukuncin Ubangijinka, kuma kada ka bi, daga cikinsu, mai zunubi ko mai kãfirci"

( وَاذْكُرِ اسْمَ رَبِّكَ بُكْرَةً وَأَصِيلًا )

الإنسان (25) Al-Insaan

"Kuma ka ambaci sũnan Ubangijinka, sãfe da maraice"

( وَمِنَ اللَّيْلِ فَاسْجُدْ لَهُ وَسَبِّحْهُ لَيْلًا طَوِيلًا )

الإنسان (26) Al-Insaan

"Daga dare, sai ka yi sujũda gare Shi, kuma ka tsarkake Shi dar mai tsawo"

"Don haka kema anan sai ki yi haquri da duk wani qalubale da zai sameki a rayuwa, kuma ki nesanta daga aikata zunubbai, kuma ki yawaita tuba saboda Allah yana son masu yawan tuba. Sannan ki yawaita ambaton Allah safiya da maraice, ki riqe azkar. Ki dinga tsayuwar dare domin kuwa tsayuwar dare suffa ce ta mutanen kirki

Wannan shine fassarar mafarkin ta

Wallahu ta'ala a'alam

Amsawa:

Usman Danliti Mato (Usmannoor_Assalafy)

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments