Ticker

6/recent/ticker-posts

Dajjal Ne Zai Fara Bayyana Ko Kuma Yajuj Da Ma'ajuj?

TAMBAYA (120)

Allah yasaka da alkairi pls tanbayata shine dajjal da yajuju da majuju wanne ne zaifara bayyana sannan suratul al khaf tana kare mutun daga fitinar dajjal

AMSA

Amin ya rabbal alamin

✍️AMSA A TAQAICE

(Dajjal ne zai fara bayyana. Ya'ajuj da Ma'ajuj daga baya zasu zo domin neman mafita daga wadannan fitin-tinu sai ki yawaita karanta: "Allahumma inni a'uzubika min azabil qabr, wamin azabi jahannam, wamin fitnatil mahya wal mamati, wamin fitnati sharril masihid dajjal" bayan kin gama Tahiyya kafin kiyi Sallama)

Bismillaahir Rahmaanir Raheem

Ingantaccen hadisi ya tabbata cewar Annabi (Sallallahu alaihi wasallam) ya ce: Annabi Isah (AS) zai sauko daga sama ta 2, hannayensa dafe da fuka-fukan mala'iku, zai sauka a saman (minaret) hasumiyar masallachin Ummayad (Masjid Umayyad) dake Damascus, birnin kasar Syria

Lokacin ana gab da sallar Asubah, kowa yana ta tunanin fitinar da Dajjal yazo da ita, a lokacin Imam Mahdi (Muhammad Bin Abdullahi) ya bayyana, musulmai suna ganin Annabi Isah (AS) zasu gane shi, zasu ce ya ja su sallah, sai ya koma wajen mamu yace ga shugabanku nan (ya nuna Imam Mahdi) yace shi zai ja mu sallah

Ana fitowa za'a doshi kasar Palestine, lokacin Dajjal yana qoqarin shiga Masjid al-Aqsa don ya kwace masallachin (wanda Aljanu ne suka ginashi tun a zamanin Annabi Sulaiman AS), nan take sai ya ga Annabi Isah (AS), ya fita a guje saboda daman yasan shine kadai zai zama sanadin ajalinsa, yana gudu yana zagwanyewa kamar gishiri a ruwa, sai Annabi Isah dan Maryam (AS) yasa takobi ya kashe shi a daidai wata kofa da ake kira da Baab Lud dake Palestine (inada video din wajen yanzu haka, kwanakin baya na taba dora shi a status)

Bayan an kashe Dajjal ana tunanin komai ya lafa, sai kuma Yajuj da Ma'ajuj su bayyana, suna da matuqar yawa kamar yanda Allah Azzawajallah ya fada a Qurani mai girma

(حَتَّىٰ إِذَا فُتِحَتْ يَأْجُوجُ وَمَأْجُوجُ وَهُم مِّن كُلِّ حَدَبٍ يَنسِلُونَ)

الأنبياء (96) Al-Anbiyaa

"Har sa'ad da aka bũde Yãjũju da Mãjũju alhãli kuwa sunã gaggãwa daga kõwane tudun ƙasa"

Wasu malaman tarihin sun ce katangar Ya'juj wa Ma'ajuj itace: "The Great Wall of China" wato babbar katangar China, wasu kuma sun ce a'a, Katangar dake tsakiyar Asia ce, dake maqotaka da garin Bukhara da Tirmidh, sunan wajen Darband, wasu kuma suka ce: a Russia katangar take anan Daghistan kuma ana kiranta da Darband da kuma Bab al-Abwab (Kofar kofofi). Masana ilimin tarihi irinsu: Yaqut al-Hamawi a littafinsa Mu'jam al-Buldan, Idrisi (wanda ya fitar da map din duniya) a littafinsa Geographiyah, al-Bustani a littaginsa Da'irah al-Ma'arif duk sun tafi akan cewar katangar Ya'juj wa Ma'juj itace Bab al-Abwab

Saidai a shekarar 2008 ne Geoarcheologists (masana ilimin tarihin kasa) suka gano ainihin katangar Ya'juj da Ma'ajuj a wani waje da yake yammacin Darband Pass dake maqotaka da yankin kasar Turkey da Iran zuwa Arewacin Georgia gabashin dutsen Kazbek (tsayin 1,800 meters kusan kafa 5,900), sunan wajen "The Valley of Daryal (Dariel)" wato kwarin Daryal, yana tsakanin Qafqaz da Taflas, wannan shine ra'ayi manyan malamai irinsu Wahb, Abu Hayyan, Ibn Khardad, Allamah Anwar Shah, da kuma Azad, a wajen da akwai wasu manyan duwatsu guda biyu wanda binciken ya tabbatar da anan katangar take, wajen da Zulkarnaini ya je ya tarar da wasu mutanen gari da basa jin yarensa

(حَتَّىٰ إِذَا بَلَغَ بَيْنَ السَّدَّيْنِ وَجَدَ مِن دُونِهِمَا قَوْمًا لَّا يَكَادُونَ يَفْقَهُونَ قَوْلًا)

الكهف (93) Al-Kahf

"Har a lõkacin da ya isa a tsakãnin duwãtsu biyu, ya sãmi waɗansu mutãne daga gabãninsu. Ba su yi kusa su fahimci magana ba"

(قَالُوا يَا ذَا الْقَرْنَيْنِ إِنَّ يَأْجُوجَ وَمَأْجُوجَ مُفْسِدُونَ فِي الْأَرْضِ فَهَلْ نَجْعَلُ لَكَ خَرْجًا عَلَىٰ أَن تَجْعَلَ بَيْنَنَا وَبَيْنَهُمْ سَدًّا)

الكهف (94) Al-Kahf

Suka ce: "Yã Zulƙarnaini! Lalle ne Yãjũja da Majũja mãsu ɓarna ne a cikin ƙasa. To, ko zã mu Sanya harãji sabõda kai, a kan ka sanya wani danni a tsakãninmu da tsakãninsu?"

(قَالَ مَا مَكَّنِّي فِيهِ رَبِّي خَيْرٌ فَأَعِينُونِي بِقُوَّةٍ أَجْعَلْ بَيْنَكُمْ وَبَيْنَهُمْ رَدْمًا)

الكهف (95) Al-Kahf

Ya ce: "Abin da Ubangijĩna Ya mallaka mini, a cikinsa yã fi zama alhri. Sai ku taimakeni da ƙarfi, in sanya babbar katanga a tsakãninku da tsakãninsu."

(آتُونِي زُبَرَ الْحَدِيدِ ۖ حَتَّىٰ إِذَا سَاوَىٰ بَيْنَ الصَّدَفَيْنِ قَالَ انفُخُوا ۖ حَتَّىٰ إِذَا جَعَلَهُ نَارًا قَالَ آتُونِي أُفْرِغْ عَلَيْهِ قِطْرًا)

الكهف (96) Al-Kahf

"Ku kãwo mini guntãyen baƙin ƙarfe". (Suka kai masa) har a lõkacin da ya daidaita a tsakãnin duwãtsun biyu (ya sanya wutã a cikin ƙarfen) ya ce: "Ku hũra (da zugãzugai)." Har a lõkacin da ya mayar da shi wutã, ya ce: "Ku kãwo mini gaci (narkakke) in zuba a kansa"

(فَمَا اسْطَاعُوا أَن يَظْهَرُوهُ وَمَا اسْتَطَاعُوا لَهُ نَقْبًا)

الكهف (97) Al-Kahf

"Dõmin haka bã za su iya hawansa ba, kuma bã zã su iya hujwa gare shi ba"

(قَالَ هَٰذَا رَحْمَةٌ مِّن رَّبِّي ۖ فَإِذَا جَاءَ وَعْدُ رَبِّي جَعَلَهُ دَكَّاءَ ۖ وَكَانَ وَعْدُ رَبِّي حَقًّا)

الكهف (98) Al-Kahf

Ya ce: "Wannan wata rahama ce daga Ubangijĩna. Sai idan wa'adin Ubangijĩna ya zo, ya mayar da shi niƙaƙƙe. Kuma wa'adin Ubangijĩna ya kasance tabbatacce."

Dangane da batun da mutane suke akan cewar Ya'juj wa Ma'juj halittu ne masu fala falan kunnuwa, su kwanta da guda daya su rufa da guda daya, duk wannan zancen mutane ne. Zancen gaskiya shine: su Ya'juj wa Ma'juj mutane ne daga cikin bani Adam, kuma kakanninsu sune Tatars kuma suna daga cikin qabilar Mongols. Sun kasance tsatson Yafith dan Annabi Nuhu (Alaihis Salam) kamar yanda Ibn Khathir (Rahimahullah) yayi bayani a cikin shahararren littafinsa: Albidaya wan Nihaya

ʿAllāmah ibn Kathīr, ʿAllāmah Abū al-Layth as-Samarqandī, ʿAllāmah Abū al-asan al-Māwardī, da malamai da yawa duk sunyi bayani a cikin Tafsir dinsu cewar Ya’jūj da

Ma’jūj sun fito ne daga Yāfith ibn Nū

Idan suka bayyana, za su dinga kashe mutane, ba wanda zai iya kashe ko da daya daga cikinsu, ko Annabi Isah (AS) ma guduwa zai yi tare da sauran musulmai zuwa kan wani tsauni

A lokacin ne Allah Azzawajallah zai saka wasu qananan halittu kamar tsutsotsi su fito a jikinsu su kashe kowannensu, daganan sai a turo wasu halittu masu dogayen wuya su dauke gawarwakinsu daga kan doron kasa (suna da matuqar yawa ne)

Bayan komai ya lafa, Annabi Isah (AS) zai koma ga Allah bayan ya yi aure sannan za'a binne kabarinsa a kusa da na Annabi (Sallallahu alaihi wasallam) da Abubakar (RA) da Umar (RA), daganan kuma sai addini ya fara samun tasgaro a fara fasadi a bayyane, lokaci zai zo har a manta da Sallah da Azumi. Saboda wadatar kudi babu wanda zai karbi Zakkah

A lokacin kuwa tuni an dade da rushe Kaabah, sunan wanda zai rushe ta "Dhu As-siwaqatayn al-afhaj" ya kwashe zinaren da aka binne a karkashinta, ya kasance dan kasar Yemen ne (kasar su daya da Sarki Abrahata wanda yazo da manyan giwaye, yaso ya rushe Ka'abah duba cikin Suratu Fil), Dhu As-Siwaiqatayn al-afhaj gajere ne, wada, kafarsa ta baude ma'ana gwame ne, kuma kansa cibir cibir ne kamar yanda Annabi (Sallallahu alaihi wasallam) ya fada a cikin hadisi ingantacce

Za'a maida masallachin Annabi (Sallallahu alaihi wasallam) wajen zubar da shara, za a mai da shi kamar gidan zoo, wani wajen ana kiwo, lokacin Makka da Madina ta koma karkashin mulkin yahudawa (wanda a binciken da nake yanzu, ya tabbata cewar manufarsu shine su kafa World Totalitarian Government da sukewa laqabi da The Greater Israel wato babbar Israela)

Shi yasa yanzu suke ta kokarin korar Palestinians daga Gaza, Rafah, Khan Yunus da sauransu don su mamaye ba iya Palestine ba har maqotansu wato Misra (Egypt), Syria, Jordan da Jaziratil Arab gaba daya wanda kuma Saudi Arabia tana ciki

Za'a tashi alqiyama ne ranar Juma'a akan fasiqan kafirai wadanda basu taba tunanin duniya zata zo karshe ba, kamar daukewar ruwan sama haka zasu ji, sai kuma karar busa kaho daga Mala'ika Israfil (AS), za'a fara guje guje, yayin busa ta biyu kuma kowa zai mutu, a busa ta uku ne kowa zai tashi daga kabarinsa. Allah zai zo (Zuwan da ya dace daShi) tare da mala'iku, sahu sahu, za'a kawo Jahannama, a shimfida siradi akan Wutar tun daga filin lahira har zuwa kofar shiga Aljannah. Kowa zai bi takai (Da ni: Usmannoor da kai/ke mai karatu), gwargwadon ayyukanmu gwargwadon saurin wucewarmu. Sai mu tsaya mu gyara halayenmu, muyiwa kanmu hisabi kafin ayi mana

Allah yasa mudace yasa muyi kyakkyawan karshe, mu mutu muna musulmai kan tafarkin Salaf (Magabatan farko)

Sahihin hadisi ya tabbata daga Manzon tsira (Sallallahu alaihi wasallam)

Yace karanta ayoyi 10 na farkon suratul kahfi suna maganin fitinar Dajjal ne ba Yajuj wa Majuj ba

(Sahihul Bukhari)

Amman dangane da addu'ar neman tsari daga Ya'juj wa Ma'juj, abinda yafi sauqi shine karanta "Allahumma inni a'uzubika min azabil qabr, wamin azabu jahannam, wamin fitnatil mahya wal mamati, wamin fitnati sharril masihid dajjal"

Ki dinga karantawa bayan kin kammala tahiyya kafin kiyi sallama

Duba cikin littafin

(Hisnul Muslim)

Wallahu ta'ala a'alam

Amsawa

Usman Danliti Mato (Usmannoor_Assalafy)

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments