Ticker

6/recent/ticker-posts

Addu'ar Shiga Kasuwa

TAMBAYA (121)

Assalamu Alaikum. Mlm mai hukuncin Wanda ya nema maganin kasuwa

AMSA

Waalaikumussalam, Warahmatullahi, Wabarakatuh

✍️AMSA A TAQAICE:

(Duk wanda ya zo shiga kasuwa sai yace: "Laa ilaaha ill-allaahu wadahu laa shareeka lah, lah-ul-mulku wa lahul-amdu, yuyee wa yumeetu wa huwa ayyun laa yamootu, bi yadi-hil-khayru, wa huwa ‛alaa kulli shay’in qadeer". Allah (Subhanahu wata'ala) zai rubuta masa lada miliyan daya (1,000,000), zai kankarewa mutum zunubbai miliyan daya (1,000,000) sannan a daga darajar sa sau miliyan daya (1,000,000). Idan kuma a gida kike business din sai ki dinga karanta: "Allahumma Arzuqni, warfa'ani, wahdini, wajburni" bayan kin dago daga Sujuda ta farko kafin ta biyu)

Bismillaahir Rahmaanir Raheem

Maganin kasuwa ko kuma neman albarkar kasuwanci, yin hakan ba haramun bane ba matuqar an yi koyi da yanda Annabi (Sallallahu alaihi wasallam) ya koyar

Annabi (Sallallahu alaihi wasallam) yace: Duk wanda zai shiga kasuwa sai yace: "Laa ilaaha ill-allaahu wadahu laa shareeka lah, lah-ul-mulku wa lahul-amdu, yuyee wa yumeetu wa huwa ayyun laa yamootu, bi yadi-hil-khayru, wa huwa ‛alaa kulli shay’in qadeer"

Ma'ana:

"Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, shi daya tilo, ba tare da abokin tarayya ba, Mulki gareShi yake, godiya ta tabbata gareShi. Shi Ne mai rayawa, mai kashewa, rayayyeNe kuma baya mutuwa. A hannunSa dukkan alkhairai suke kuma Shi ga dukkan komai mai Iko Ne"

Duk wanda ya fadi haka, Allah (Subhanahu wata'ala) zai rubuta masa lada miliyan daya (1,000,000), zai kankarewa mutum zunubbai miliyan daya (1,000,000) sannan a daga darajar sa sau miliyan daya (1,000,000)

A wata riwayar kuma za'a ginawa mutum danqareren katafaren gidan bene a Aljannah

(At-Tirmidhi ne ya rawaito a hadisi mai lambata ta # 3428 da kuma 3429; Ibn Majah # 2235 da sauran su. Haka ma a cikin Sahih Al-Kalim Al-Tayeb lamba ta # 230)

Don Allah mene ne yafi wannan? Shi yasa wasu magabata a cikin tabi'ai musamman fa suke daukar kafa su tafi kasuwa alhalin ba siyayya zasuyi ba, suna zuwa ne don kwadayin samun wadannan tarin ladaddaki masu yawa

Don haka sai ki yi kokari ki haddace wannan addu'a domin dacewa da samun ladan. Amman dangane da abin da wasu suke aikatawa na shirka, kamar irinsu rataya qaho ko laya a saman shagon kasuwa don neman ribar kasuwanci wannan duk shirka ne, sai a guji aikata hakan

Ina yan kasuwa masu neman lada? Ka samu shugabannin kasuwa ka ce musu su samo allon qarfe su rubuta wannan addu'ar a jiki ta yanda duk wanda yazo shiga kasuwa zai dinga karantawa domin kuwa wasu sun iya addu'ar amman shaidan yana mantar dasu idan sun zo shiga kasuwa domin kuwa kamar yanda masallachi shine dakin Allah anan duniyar to haka kuma kasuwa itace inda shaidan yafi so shiyasa waje mafi sharri a wajen Allah anan duniyar shine kasuwa. Wallahi duk wanda yazo shiga kasuwa indai ya karanta ta to kaima zaka samu ladan can da za'a bashi. Kaga kenan ko ba ka yi cinikin kaya a wannan ranar sosai ba to zaka samu gidan bene for free a Aljannah

Wannan itace shawarar da na bawa wani Attajiri dake Kasuwar Dawanau ta jihar Kano. Allah kadai yasan adadin miliyoyin ladan da kaima zaka samu idan har ka zama silar saka wannan addu'ar a kofar shiga kasuwarku

Idan kuma kasuwancin naki a gida kike yi to sai ki nesanta da siyan kayan haram, ki katange kanki daga cin riba (kudin ruwa) sannan ki yawaita karanta addu'ar da Annabi (Sallallahu alaihi wasallam) ya koyar bayan kin dago daga Sujjadar farko kafin ki koma Sujjada ta biyu. Zaki ce:

"Allahumma Arzuqni, warfa'ani, wahdini, wajburni"

(Duba littafin Sifatu Salatin Naby na Shaikh Muhammad Nasiriddin Al-Albaany, Rahimahullah)

Wallahu ta'ala a'alam

Amsawa:

Usman Danliti Mato (Usmannoor_Assalafy)

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments