Ticker

6/recent/ticker-posts

Shin Dole Sai Liman Ya Saka Hula Idan Zai Ja Sallah

TAMBAYA (114)

Aslkm. Allah ya gafata Malam! Akwai wani masallaci a unguwar mu limamin yana korar mutane idan suka shigo sahun gaba sbd Basu da HULA akan su. Dan Allah inaso a gayamin inda akace idan mutum bashi da hula akan sa bazai shiga sahun gaba ba ko Kuma bazai Yi limanci. Da wace hujja ya dogara. Nagode. Dan Allah taimaka a amsa min

AMSA

Waalaikumussalam, Warahmatullahi, Wabarakatuh

Alhamdulillah

Kamata yayi ku da kanku ku je ku same shi, ku tambayeshi cikin siyasa da girmamawa, Baba a ina ka samo dalili akan dole sai da hula a kai sannan mutum zai shiga sahun gaba? Farillah ne ko Sunnah ce, ko kuma Mustahabbi ne?

Alal haqiqa, babu wani nassi da ya tabbata cewar dole sai da hula sannan sallah zata amsu

Ya manta da hadisin da Annabi (Sallallahu alaihi wasallam) ya ce: "Allah ba ya duba izuwa ga surorinku da dukiyoyinku saidai yana duba ne izuwa ga ayyukanku da zuciyoyinku"

(Sahih Muslim)

Saidai, yana da kyau mutum ya yi shigar kamala idan zai gana da Ubangijinsa ta hanyar saka sutura mai kyau saboda hadisin: "Innallaha jamilun, yuhibbul jamal" ma'ana "Allah kyakkyawane kuma yana son abu mai kyau"

(Sahihul Bukhari)

A iya dan karamin ilimi na bansan cewar yana daga cikin karbuwar sallah ace dole sai mutum ya saka tagiya (hula) ba

Wallahu ta'ala a'alam

Amsawa

Usman Danliti Mato (Usmannoor_Assalafy)

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments