Halaccin Karanta Qur'ani Lokacin Jinin Al'ada

    TAMBAYA (115)

    Assalamu Alaikum mlm ya ayyuka yakokari da mutane Allah yataimakeku Ameen. Tambaya mlm nakasance inakaranta suratul Almulk duk dare idanzankwanta, to yanzu inacikin rashin tsarki shin yahalatta naduba qur anin gawayata nakaranta? Allah yakara basira mln🙏

    AMSA

    Waalaikumussalam, Warahmatullahi, Wabarakatuh

    ✍️AMSA A TAQAICE

    (A farko farkon Kitabul Haid dake cikin Sahihul Bukhari, sharhin Fathul Bari na Ibn Hajar al-Asqalani ya ce: "Tabi'ai suna aiken bayinsu mata wajen sahabban Annabi (Sallallahu alaihi wasallam) su amso musu Qur'ani alhalin matan suna jinin haila")

    Bismillaahir Rahmaanir Raheem

    Ya halatta macen da take haila ta taba Qur'ani

    Wadanda suke cewa bai halatta a taba Qur'ani ba saboda Allah Azzawajallah ya ce: "Laya massuhu illal mudahharuna" ma'ana: "Babu mai taba shi sai masu tsarki" anan ba Qur'ani ake magana ba, Lauhul Mahfuz ne, babu mai taba shi sai Mala'iku tsarkaka, amman da maganar mutane ake da sai yace "al muta dahharuna" wato mutane wadanda suke tsarkaka, sai yace "almudahharuna" wato mala'ikun can da suke gadin shi Allon Lauhul Mahfuz din. Don haka babu wata hujja ko dalilli da yake nuna baza'a dau Qur'ani a lokacin janaba ko haila ba, wasu malaman sukan ce saidai a dauki mai fassara ko a dauki juzu'i ko mai tafsiri ko a saka safar hannu duk wannan ra'ayoyin malamai ne

    A farko farkon Kitabul Haid dake cikin Sahihul Bukhari, sharhin Fathul Bari na Ibn Hajar al-Asqalani ya ce: "Tabi'ai suna aiken bayinsu mata wajen sahabban Annabi (Sallallahu alaihi wasallam) su amso musu Qur'ani alhalin matan suna jinin haila"

    Domin karin bayani sai a duba littafin Badrud dinil Aini a cikin nasa fassarar sharhin Sahihul Bukhari mai suna Umdatul Qari

    Haka kuma ya halatta macen da take jinin haila ta karanta Qur'ani

    Hadisin da aka rawaito cewar Annabi (Sallallahu alaihi wasallam) ya ce: "Bai halatta macen da take haila ta karanta Qurani ba"

    Wannan hadisi ne Da'ifi jiddan, munkar. Bai inganta ba

    Ki karanta littafin "al-Irwa al-Ghaleel" mujalladin farko wallafar Shaykh Muhammad Nasiriddin al-Albaany (Rahimahullah)

    Da littafin "Tamamul Minnah, da littafin "Nasbur Rayah fi Takhrij ahadith Hidaya" wallafar Alhafizuz Zaila'i (Rahimahullah)

    A taqaice dai ya halatta ki karanta Qur'ani a wannan yanayin na jinin haila

    Wallahu ta'ala a'alam

    Amsawa: Shaykh Auwal Albany (Rahimahullah)

    Rubutawa

    Usman Danliti Mato (Usmannoor_Assalafy)

    Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
    https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

     https://t.me/TambayaDaAnsa

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.